Skip to content
Part 60 of 73 in the Series So Da Buri by Bulama

Tana sauk’a k’asan ta ga shiru ba kowa. Da alama ma har masu aikin sun tafi side d’insu dan har an rufe main door sannan an kashe globes.
Hasken fitilun barander waje da suka ratso ta windunan parlourn ne suka taimaka mata ta k’arasa bakin k’ofar d’akin nasu.

A hankali ta d’anyi knocking, ita bama ta yi tunanin za aji ba amma sai taji yace “Come in”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e sannan ta sa kai ta shiga.

A zaune kan sofa ta sameshi, da alamun wanka yayi dan ya chanja kaya zuwa wata jallabiya ruwan zuma mai dogon hannu da hula, bai
sanya hular ba ya barta ta fad’a baya ba k’aramin kyau yayi ba.

Yana a zaune yana latsa computer ga tea a gefe kan d’an stoll d’in da ya d’aura computer. Gaba daya hankalinsa yana kan aikin da yake yi
shiyasa ta yi mamakin ta yadda ya ji d’an mitsitsin knocking d’in da tayi, kuma kamar ma ba shi ya amsa ta ba dan tunda ta shigo be ko kalli inda take ba! Haushi abun ya bata yadda ko d’agowa bai yi ya kalleta ba kamar ba d’an Adam ne ya shigo d’akin ba
dan haka itama ta d’auke kai bayan ta d’an hararesa ta shige tayi wucewarta.
Inda ta ajjiye akwatinta ta nufa cikin closet, ga mamakinta sai taga wani akwatin wanda ta tabbatar nasa ne!
B’ata rai tayi kawai ta hau zabgawa akwatin harara wanda ita kanta bata san dalili ba. Sai da tayi me isarta tukunna ta d’auki inner wears, toothbrush, tooth paste, hijab da sleeping dress ta shiga toilet d’in. Wanka tayi ta d’auro alwallah, a nan cikin toilet d’in ta chanja kayanta..sai kuma ta fara tunanin a ina zata shanya bra da pant d’inta (waenda ta wanke yanzun) inda ba zai gani ba.

Babu inda bata duba ba amman ta rasa mab’oya, k’arshe dai shanyawa kawai tayi a wajen shanya sannan ta d’aura hijabinta akan rigar barcin jikinta ta fito.

Still yana zaune a yadda yake har yanzun. Tsayawa tayi dan so take ya tashi ta kwanta! Tafi minti biyar a tsayechaan! Ta tsinkayo muryarsa
“Kina buk’atar wani abun ne?” Yayi mata tambayar ba tare da ya kalleta ba…

‘Itafa gaskiya ya fara k’ular da ita! Ta tsani ayi mata magana ba tare da an kalleta ba, wato ba ma ta kai ya kalletan ba kenan ko me?’ Huda ta aiyyana hakan a ranta. Gani tayi kawai ya d’ago kyawawan idanuwansa ya zuba mata su! Da sauri ta sunkuyar da kanta a ranta tace “Ko dai a fili na yi maganar??”

Shi kuma Aslam shirun da tayi ne yasa ya d’ago ya kalleta, ganin ta sunkuyar da kanta ne still bata ce komai ba ya sanya shi kiran sunanta, a hankali taji yace “Huda”

Da mugun k’arfi k’irjinta ya buga! Saboda yanayin da ya kira sunan nata da muryarsa mai mugun dad’in sauraro sannan very calm kamar baya son maganar ta fito. ‘Ita kam, tunda take anya akwai wanda ya tab’a kiran sunanta da dad’i kamar haka kuwa?’
Ta aiyyana hakan a ranta.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e
kafin ya rufe computer ya mik’e
ya nufi inda take tsaye.

Tunda ya mik’e ta d’ago ta fara kallonsa, ganin ya nufota gadan gadan yasa ta rikice tashi d’aya, da sauri tace
“sofa, sofa! Sofar nake buk’ata zan yi bacci”. Kafin ta rufe bakinta ma already ya riga ya k’araso inda take!
Da kyar ya iya danne dariyarsa, yana kallonta yana mamakin yadda duk ta duburce kamar ba ita ta gama zuba masa harara yanzun nan ba. Hannunsa yasa ya kamo nata!
Da sauri ta d’ago ta na kallonsa, shima itan yake kallo ido cikin ido!

K’asa tayi da kanta tana jin yadda zuciyarta take bugawa! Haka kurum taji hawaye sun tarun mata a ido. Tunda take da Ya Arshaad ko da wasa bai tab’a kama mata hannu ba 4 years! Amman shi wannan she just knew him amma bashi da aikin da ya wuce ya shafa mata kumatu ko kuma ya kama mata hannu. Tabbas! Ta san akwai difference tunda shi wannan Mijinta ne amman kuma duba da yanda basu wani saba ba sannan kuma basa k’aunar juna ai bai kamata ace yana saurin tab’ata haka ba! Ko da yake ai ance daman a uk ya girma…ta tabbata inda Ya Arshaad ne aka yi musu irin wannan auren had’in da shi da ba zai tab’a yunk’urin rik’e mata hannu ba har sai ya bari sun d’an saba tukunna.
A take case d’in Jalila ya fad’o kanta, ta tuna yadda ta d’aura masa laifin da ba nasa ba bawan Allah har da AlQurani ya zo zai rantse mata gaskiya Ya Arshaad yana sonta ba kadan ba! Tana cikin wannan tunanin bata yi auni ba kawai taji kuka ya kufce mata!.

Ajiyar zuciya taji Aslam yana ta faman sauk’ewa akai akai kamar shine yake kukan! Be hanata yin kukan ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru.

K’afafuwanta har sun fara zafi saboda tsayuwa. Har tayi shiru bata ji ya daina sauk’e ajiyar zuciyar ba, chaan, taji yace “Ki tabbatar duk lokacin da tunanin Arshaad yazo miki, kika yi, kin yi istighfari!” Yana gama fad’in haka ya ja hannunta ya kaita har kan gadon sannan ya ajjiye ta yace “sleep”
daga nan ya juya.

Huda gabad’aya tsoron sa ne ya rufeta!
A ranta tace “Anya wannan ba aljani bane ba kuwa?”

Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo, ganinta yayi still a zaune bata da niyyar kwanciyar. Yunk’urowa yayi zai yi mata magana kawai yaga da mugun sauri ta juya ta d’aura k’afafuwanta akan gadon ta kwanta ta lumshe ido. Tabbas ya san me ta tuna
dan haka kawai ya girgiza kai ya juya ya koma yaci gaba da aikin shi. Itama Hudan a tunaninta kwantar da ita zai yi k’arfi da yaji kamar yadda ya durk’usa zai kinkimeta ranar a asibiti
shiyasa ta shafawa kanta ruwa ta kwanta tun kafin ya sake matsowa kusa da ita zuciyarta ta tarwatse! Dan har yanzu bata bar uban bugun da takeyi ba.

Bata san lokacin da yayi bacci ba dan ita kam tana kwanciya bacci ya kwasheta.

Ta riga sa tashi dan tun kafin assalatu ta farka ita. D’akin da duhu ba kamar yadda tayi bacci ta bari da haske ba. Jinta ta yi a lullub’e cikin lallausan bargon da ta gani a gefe kan gadon.
A hankali ta karanto addua kafin ta mik’e ta zauna sakamokon kiran sallar farko data fara ji, dan ita da a tunaninta ma farkawar tsakar dare ta yi. Sai da baccin yad’an ragu a idonta sannan ta yaye bargon ta mik’e bayan ta d’auki wayarta.

Flash ta kunna sannna ta nufi hanyar bathroom, idanuwanta ne suka sauk’a kan Aslam wanda yake kwance akan sofa! Dogo ne shi d’in sosai shiyasa sofar tayi masa kad’an, saboda kujerar ba wata mai girma bace ba dan da kyar In tafi 3 seater. Ya tankwashe k’afafuwansa akan sofar duk dan ta ishesa amman duk da haka a takure yake da alama kuma sanyi yake ji, gashi taga kamar blanket d’aya ne a d’akin kuma ya rufa mata Pillow kawai ya d’auka ya kwanta a kai
ya turo k’ananan throw pillows d’in sofar k’asa.

Hasken fitilar ta ne ya farkar da shi, ya farka amman bai bud’e ido ba.

Tsintar kanta tayi da komawa gadon, a nan ta ajjiye wayarta still bata kashe flash d’inba (dan ta ga haske) ta d’auko blanket d’in ta dawo wajen da yake kwance. A hankali gudun kar ya farka
ta d’an sunkuyo ta lullub’a masa blanket d’in tun daga k’afafuwansa har zuwa wajen wuyansa. Ajiyar zuciya taji ya sauk’e dan haka ta yi saurin kallon fuskarsa a tunaninta ko ya farka ne amma sai taga baccinsa yake yi peacefully. Gabad’aya sai taji tausayinshi ya rufe ta…ta tabbata d’umin ne ya sanya shi jin dad’i har cikin baccinsa yana sauk’e ajiyar zuciya…ya san yana jin sanyi amman ya hak’ura ya lullub’a mata shi ya kwanta a haka. A hankali take nazarin tana kallon kyakkyawar fuskarsa.
Durk’usawa tayi sosai a gabansa kamar mai zaman tahiyya. A hankali ta shiga kallon fuskar tasa tun daga kan sumar kanshi zuwa straight girarsa, duk da idanunsa a rufe suke amman hakan bai hana ta ganin kyawun da idanun suka k’arawa fuskar tasa ba, ga wasu kyawawan zara zaran lashes, dogon hancinsa ta kalla tana mamaki da girmama kyawun halittar Ubangiji. Ta dad’e tana kwad’ayin son ta yiwa fuskarshi nutsatstsan kallo saboda ita har ga Allah tunda take a rayuwarta bata
tab’a ganin kyakkyawan Namiji kamar Ya Aslam ba! Komai nasa mai kyau ne, ga muryarshi idan yana magana kamar kar ya daina. Kallonsa kawai take yi sosai tana nazarin, dan har
d’an matsawa ta yi kusa da shi sosai ba tare da ita kanta ta sani ba! So take ta gane me yafi kyau a fuskarsa! Hancinsa ne ko kuma idon ko cikakkaiyar straight brows d’insa, amma ta kasa, taso ace idanunsa
biyu ta samu ta yiwa idanuwan nutsatstsen kallo kamar haka.

So take ta d’auke kai ammman kwata kwata ta kasa. A hankali take bin skin d’insa da kallo, fuskarsa tass babu alamar k’urji ko zanzana ko wani tabo! K’ayataccen sajensa ne kawai ya bambanta fuskartasa da ta babies.

A hankali idanuwanta suka kai kan d’an mitsitsin pink lips d’insa wanda yake a zagaye da lallausan siririn saje!
Ta jima tana kallo chan ya ji tace “Astaghfirullah!!” kafin tayi saurin runtse idanunta sai kuma ta mik’e da sauri ta juya ta fad’a toilet ko wayar tata bata d’auka ba! Tana shiga ta banko k’ofar!.

Sai a lokacin Aslam ya bud’e idanunsa, yana wani sassanyan murmushi mai had’e da dariya.

Ta jima a toilet d’in kafin ta fito.
A zaune ta same shi this time around da waya a hannunsa, a ranta tace “sai kaje garin daddanna na’ura ka lalata idon”. Wucewa tayi ta d’au hijabinta ta zura ta fara k’ok’arin gabatar da nafila shi kuma ya mik’e ya nufi band’akin
da gudu ta k’arasa ta shige toilet d’in kafin shi ya shiga ta rufo k’ofar! Chaan, ta bud’e ta fito ta wuce ba tare da ta kallesa ba. Bayanta ya bi da kallo kafin ya girgiza kai kawai yana murmushi ya shige toilet d’in,
kamar ance ya d’aga kai, yana
kallon wajen dariya ta kufce masa, abunda bata sani ba shine jiya already ya rigada ya gani dan kafin ya kwanta sai da ya shigo yayi alwala. Yana dariya yana murmushi shi kad’ai haka yayi wanka cikin farin ciki da annashuwa dan shi kam Hudan already made his day yau before it even begins.

Da towel ya fito d’aure a k’ugunsa lokacin ita kuma juya baya tana sallah.
Cikin nutsuwa ya hau shiryawa, tana cikin sallar hancinta ya fara jiyo mata wannan azababben k’amshin turaren nasa yana k’aruwa akan wanda already ya riga kama d’akin. Tana idarwa tayi addua ta shafa, ta gyara zamanta a nan gaban gadon kan kafet ta na jira a kira sallah. Takun sa ta ji a hankali yana k’arasowa inda take..
Lumshe idanuwanta kawai tayi tana shak’ar k’amshinsa tana kuma sauraron yadda bugun zuciyarta yake k’aruwa dede da takun nasa. A hankali taji yace “Gyara in yi nafila”. D’agowa tayi suka had’a ido. Sanye yake cikin jallabiya bak’a mai shek’i amman
ta k’asan jallabiyar tana iya hango dogon wando bak’i kamar na suite saboda jallabiyar bata ida rufe duk k’aurinsa ba.

Da sauri ta mayar da kanta k’asa ta mik’e ta koma kan gado.

Yana idar da nafila ana tadaa iqama a masallaci dan haka ya mik’e ya nufi k’ofa. Har ya kama handle zai murd’a
sai kuma ya juyo ya kalleta, yace “Zan fita yau da wuri. Ina da bak’i tun jiya cikin dare suka zo kuma yau da safe suke son komawa. Get me something simple to eat, please. Kafin in dawo a masallaci.” Bai jira jin me zata ce ba ya murza handle d’in ya fice.

Shiruu, tayi na y’an mintuna
chan kuma ta mik’e ta tada sallah.

A nutse ta gabatar da sallarta.
Sai da ta idar ta yi azkar tukunna ta mik’e ta d’au wayarta ta fita a d’akin.

Tana shiga kitchen d’in ta nemi globe ta kunna, ta fara k’arewa kitchen d’in kallo dan ita bama ta san ta ina za ta fara ba. Ganin babu lokaci yasa kawai
ta soya omelet ta had’a salad ta d’auko bread da kifin gwangwani ta had’a masa sandwich da tea.

Tray ta d’auko ta jera akai ta d’aura cup da tea flask d’in da su madara da sugar da teaspoon ta ajjiye dik a kai sannan ta d’au tray d’in ta fita.

Tana fita ta gansu akan dining shi da Abba duk sun shirya, da wasu takardu suna dubawa.

A hankali ta k’araso ta ajjiye tray d’in sannan ta d’an rissina tukun tace
“Abba Ina kwana”. Tunda ta fito Abban yake kallonta yana murmushi, ba k’aramin dad’i yaji ba “Lafiya Alhamdulillah”. Yace da ita yana murmushi yana kallonta.

A hankali ta d’an kalli Aslam tace
“Ina kwana”. Sai da ya d’ago ya d’an kalleta tukunna yace “Lafiya”. Sai kuma ya mayar da kanshi kan tray d’in yace, “Thank you”. Daga nan ya maida kallonshi ga takardun….

Abba ne yace “Princess yau abun son kai ne? Ina nawa cup d’in? Da alama ma breakfast d’in baku yi da ni ba”

Gaba d’aya kunya sai ta rufeta cikin shagwab’e fuska tace “Abba ai ban san kaima zaka fita da wuri ba” Tana gama fad’in haka ta koma kitchen ta d’auko cup ta kawo da tea spoon. Har zata sake komawa sai yayi sauri yace
“No wannan zai ishemu, wasa nake miki”

Murmushi tayi daga nan ta juya ta wuce d’akin nasu.

Tana cikin karatu taji fitarsu, sai da ta ida tukunna ta tashi dukda cewar d’akin bai yi wani datti ba amman sai da ta goge ta share ta wanke toilet, ita kad’ai tana ta mitar Aslam bashi da kunya wai k’ato da shi amman ya wani shanye mata boxes tazo ta gani ma shi bai damu ba kenan!

Sai wajen 9:00am sannan ta fito, lokacin gidan ba kowa daga ita sai Ummi.

A cikin parlourn ta hango ta
amman da alama ma bata san ta fito ba! Ta rafka tagumi tana kallon gefen tv d’in da take ta faman aiki ita kad’ai. Sai da Hudan ta zo inda take ta ce “Ummi ina kwana”. Tukunna tayi firgigit ta juyo, suna had’a ido ta fara murmushi, kafin tace “Lafiya, Alhamdulillah daughter. Ya kika kwana?”

“Alhamdulillah” itama Hudan tace tana me zama a kujerar gefenta 1 seater. “Ki yi breakfast mana”
Cewar Ummi.

“Ok” kawai Huda tace

sannan ta mik’e taje tayi, har ta gama ta dawo ta zauna. Ummin tana wajen bata ko chanja yana yin zama ba.

A hankali ta zauna kafin tace “Ummi tunanin me kike yi?”

Kallonta Ummin tayi kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tace
“Huda, gaba d’aya har yanzu na kasa yafe wa kaina. Sannan guilt yak’i barina In samu peace of mind!
Ki taimaka ki yafe min sannan
inaso ki rakani wajen Mamanki In nemi yafiyar ta na san na zalunceku”

Da sauri Huda tace “Ummi dan Allah ki daina. Ni kam wallahi na yafe miki duniya da lahira. Mama itama na san ta yafe miki. Ki kwantar da hankalinki
ki daina yawan tunani, please.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Huda dukda cewa na san kina da kyakkyawar zuciya ba lalle ki aikata irin abunda na aikata ba, amman still ina me baki shawarar ki rok’i Ubangiji ya tsareki daga aikata aikin dana sani’
Guilt d’in bashi da dad’i kwata kwata na rasa sukuni, nan san tayaya zan yafewa kaina ba.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace “Ummi, ki saka a ranki da ni da Mama mun yafe miki har abada!
Sannan bamu rik’e ki a zuciyoyinmu ba ko kad’an! Mun yafe miki har gaban abada kuma ganin ki ne kamar
komai bai tab’a faruwa ba! Ta hakan ne zaki iya yafewa kanki.

Wallahi Ummi kinji dai na rantse miki
har k’asan zuciyata na yafe miki kuma ban rik’e ki a zuciyata ba kwata kwata”.

D’an guntun murmushi Ummi tayi tana jin k’aunar Hudan na sake shigarta, a hankali tace “Na gode Huda but some facts will never change, Ina jin kunyar Abba sosai Ina jin kunyar sa…”

Hudan ta bud’e baki zata yi magana kenan! Suka fara jiyo kuka a waje.
Da sauri suka kalli juna sai kuma suka mik’e suka yi wajen.

Kaya suka gani a zuzzube gefe guda kuma ga Jalila tana ta kurma kuka tana tattare kayan nata. Tana ganin Hudan tayi saurin k’arasawa inda take ta rik’e mata hannu tana cewa “Huda dan Allah ku taya ni bata hak’uri, ni gani nake ma kamar ba ita ba ce ba ko
kuma aljanuntane suka tashi! Lokaci d’aya kawai tace wai In fitar mata a gida! Dan Allah Huda kar ku bari ta kore ni.”

Daidai nan Mom ta fito ba tare da ta kalle su ba ta k’arasa ta finciko hannun Jalila ta wulla ta gefe sannan tace “oya! Tattare ki fice kafin In kwace kud’in motar da na baki”

Da sauri ta mik’e tsaye ta share hawayenta ta k’araso inda Mom d’in take tsaye tace “Mom dan Allah kiyi hak’uri, wallahi ko wanke wanke da shara kika ce zan yi please Mom, dan Allah ki ara min kwana 7. Na yi miki alk’awarin nan da sati d’aya zan tafi wallahi.”

Cikin b’acin rai Mom tace “Nan da kwana bakwai na san me zaki yi???
Na san kalar asirin da zaki k’ulla? Na san makircin da zaki shirya? Eh Jalila?” Ta yi mata tambayar tana kallonta. Bata jira jin amsarta ba taci gaba “Kinga, wallahi tallahi tun muna sheda juna ni da ke! Ki fice mini a gida” Da sauri Jalila ta rik’o hannunta tace “Momina dan Allah dan annabi…”
Tass!! Mom ta d’auke ta da wani gigitaccen mari, cikin fushi tace “idan kika sake ce min Momin ki sai na datse miki harshe billahillazi. Ki kwashe tsummokaranki ki kama gabanki tun kafin raina ya ida b’aci!” Mom d’in ta k’arashe maganr cikin fushi da tsawa.

Tun da ta kifa mata mari ta dafe wajen tana kallon k’asa, bata motsa ba! Sai da
ta bari ta kai aya tukunna ta d’ago manyan idanuwanta da suka yi jaaa tana kallon ta! Cikin dakiya ta b’acin rai tace “Babu inda zan fita inje Adama.” Dariya Mom ta kwashe ta ita
kafin tace “Perfect!” tana me gwadawa da hannunta sannan ta ci gaba
“Wannan Jalilar dama nake so ta fito ba wachchar ba!. Yanzu zaki ga yadda ake hauka da rashin mutunci a cikin gidan nan!” Tana gama fad’in haka ta nufi gate. Wani christian mai gyaran fulawa ta nemo da wani soja ta had’o su su biyu ta dawo.

Tana zuwa ta kalli Jalila tace “Jalila ba da ni za kiyi wanann rashin kunyar taki ba da waennan za kiyi” Tayi mata nuni da k’artin bayanta, sannan cikin bada order ta juya ta kallesu tace
“Mai aikinta ce tayi mata sata, so ta sallameta ta koreta amman tak’i tafiya dan haka su fitar mata da ita idan
tayi turjiya su yi mata dukan mutuwa!”

Jalila ba wani turancin kirki ta iya ba amma ta fahimci me Mom d’in tace.
Ganin sojan ya tunkarota ba alamun annuri a fuskarsa yasa ta durk’usa da sauri ta fashe da kuka, tace “Wallahi tallahi kika saka aka fitar dani sai naje na tona muku asiri ke da d’anki a wajen Granpa.”

Dakatar da sojan Mom tayi kafin a hankali ta k’arasa inda take durk’ushe. Durk’usawa itama tayi sannan ta saka yatsa ta d’ago fuskar Jalilan. B’ata rai tayi ta yamushe fuska kalar tausayi kamar wadda zata fashe da kuka kafin a hankali yadda ta tabbatar babu mai ji tace “Ayyah Jalila! Wajen Granpa zaki je? Bismillah to ki je. Amman inaso ki san ko da ace kin je wajensa baki da wata shedar da zaki iya nunawa against ni ko Auwal! Mai yasa kike tunanin na barki kwana uku?”
Bata jira jin me Jalilan zata ce ta bata amsar tambayar da tayi mata da kanta tace “To get rid of all the evidence!
Sannan ta ci gaba da cewa “Sannan tun farkon zuwanki ranar cewa nayi
Inna tayi min message tace min wata zata zo ta tayani y’an aikace aikace saboda an saka ranarta so tana buk’atar kud’in kayan d’aki, kinga yanzu In aka kira Inna tunda ba ita ta turo ki ba zata ce bata sanki ba ba kuma ta san da zancen ba! Nima kuma daman kinga Innar nace ta had’ani da ke… Questions d’in da zasu fad’owa y’an estate d’innan a karon farko shine
“Wacece ke? Mai yasa kikayi outsmarting d’inmu? Taya ya kika iya hacking wayar Innaa? Sannan me kike so me ya kawoki? Waye kuma ya turoki gidan nan? Jalila bincike In yayi bincike believe you me har sharrin y’ar boko haram sai na d’aura miki wallahi!

Family d’innan is a well known family so dole muna da mahassada da masu son cutar da mu so kinga kema a wannan sahun za a jefaki ta yiu ke kika zo da kan ki ko kuma wanine ya saka ki kizo gidan nan kiyi aiki ko bincike ko wani abun wanda Allah kad’ai ya san na menene!

Granpa kuwa kinga dole ya tashi tsaye yayi bincike in ta kama a hukuntaki hukunci mai mugun tsanani Idan anyi miki mai sauk’i shine a kaiki cell ayi ta laftarki ace sai kin fad’i waye ya turoki… Shawara ta gareki shine. Ki guji mutumin da kika ga Auwal yana mugun jin tsoronsa! Ki duba kiga fa
surukan gidan nan ne mu amman da muka yi laifi ya aka yi da mu?.

Sanann maganar ciki Already tun a ranar na biyasu y’an asibitin sun goge history d’inki! So kinga ko kince aje chan kina da evidence to nan d’in ma sai dai ki sake k’ulle kanki infact duk inda kikaje ma Jalila kud’i kawai zan bayar amaida lefin kanki. Sannan hatta chat da number Auwal duk na goge wani evidence a wayarki d’azu d’azun nan da nace miki ki ara min wayarki already kuma na san pin d’inki ba tare da kin farga ba shiyasa komai ya zo mini da sauk’i…baki da wayo Jalila sannan baki iya takun ki ba dan haka baki ta evidence ko wani abu da zaki nuna against me… So be a good girl! Ki kwashe tsummokaranki
ki yi gaba tun kafin waennan k’artin su miki illar da na san ko kud’in magani ma ba lalle ki samu ba!” Tana gama fad’in haka ta cika mata hab’arta ta mik’e ta bar gurin tana karkad’e hannunta.

Still sojan ne ya sake nufarta yace “Stand up and leave!”

Banza tayi da shi tana wani kalar kuka mai cin rai.

K’afarsa ya d’aga yayi wani mahaukacin ball da ita wanda sai da ta hantsila sau biyu!

Da gudu Ummi da Huda suka k’arasa wurin suka dakatar da shi dan har ya sake nufar ta.

Ummi tana duba ta taga gefen kanta ya fashe saboda yadda ta kifa a kan interlock d’in. Cikin tsananin b’acin rai ta d’ago ta cewa Mom “Haba Adama!
Meye haka? Kin san fa ba ita kad’ai bace ba. Yanzu na tabbatar ko mik’ewa ma bazata iya yi ba balle ta fitar miki a gidan da kike ta faman ik’irari!”

Tab’e baki Mom tayi sannan ta kalleshi cikin harshen turanci tace
“Jata ka fitar idan ba zata iya tashi ba.”

Ummi tana rik’e da hannunta amman mutumin nan bai damu ba haka ya kamo d’ayan hannunta ya fara janta kamar ba mutumba….
Sai da suka yi kusan rabin gidan tukunna Ummi ta hak’ura ta daina binsu rik’e da hannun Jalilan tana masa magana dan har ta fara haki.

Haka nan ya jaata ya fitar da ita kamar kayan wanki ya jefar a bakin gate!

Mai gyaran flowers kuma ya watso mata kayanta waje suka ja k’aramar k’ofar gate d’in suka rufe gidan……

BULAMA ✍️

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 59So Da Buri 61 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×