Skip to content
Part 73 of 73 in the Series So Da Buri by Bulama

Sai da aka yi sati d’aya tukunna Aslam ya bar Huda ta je wajen Mama da kyar, dan sai da ta dinga yi masa kuka wiwi tukunna amma ya ce,

“Daga ranar sai wata wata zata dinga zuwa”.

Tana ta fushi haka suka nufi gidan da yamma bayan ce mishi ta yi wuni takeso ta yi.

Tana zuwa aka yi sa’a su Ummu suma sun zo ita da Sumayya da Khadija
dan haka farin cikin ya had’e mata biyu.

Gaisawa kawai Aslam ya yi da su da kyar daga haka ya juya ya fita da sauri.

Dariya su Ummu suka yi suna mamakin irin tashi kalar kunyar.

Cikin tsananin farin ciki suka zauna anata hira har su Shuraim waenda Mama ta damu Abba har sai da ya kwaso mata su yau da safe tukunna hankalinta ya kwanta.

Tun suna nuk’u nuk’u har suka ware aka shiga tab’a hirar da su abun gwanin ban sha’awa.

Hudan ce ta ce “bara ta kira Sakina itama ayi da ita”.

Dan haka ta kirata video call, Mura take yi sosai dan hatta muryarta ma ta d’an disashe sannan sai goge hanci take yi ya yi jaaa sosai har ma da fuskar tata gaba d’aya.

A haka sukai mata sannu sukai mata sallama a cewar su “ta je ta huta”. Ba dan taso ba ta ce “tou” ta yi musu sallamar itama ta kashe.

BAYAN SATI BIYU

Duk yadda Aslam ya so ya hana ta fita haka yanaji yana gani yau ma ya barta ta fita gidansu Mama bayan doguwar magiyar da su Sudais suka yi ta jera masa.

Kasancewar yau birthday d’in Mama yasa suke son had’a mata surprise birthday kafin ta dawo.

Tun Safe Abba ya d’auketa suka fita daga gidan, ya kaita spa suka je shopping daga nan suka biya park!

Sai da Sudais ya tura mishi ‘we are done’ Tukunna ya ce mata “ta taso su koma gida”.

Ba wani hayaniya ballons d’inma ba wasu masu yawa ba ne sai k’atoton cake d’inta mai hotanta a jiki
da drinks kala kala.

Haka suka shirya surprise d’in.

Tana shiga ta gansu har Mommy da Aaima duk sun zo suma.

Ta yi tsananin farin ciki kuwa harda y’ar kwallar ta ba abunda yafi mata dad’i irin yadda Shuraim da Sudais suka maida ta uwa suke ji da ita kamar yadda itama take ji da su.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, Mama bata bawa Sudais da Shuraim single reason d’in su yi kukan rashin uwa ba!

Daman tun ranar farko a bikin su Huda da ta gansu Yaran suka shiga ranta matuk’a.

Yadda take yi musu ko Ummin iyakar abunda zata yi musu ne.

Tarbiyya kam da gaske take basu ita, idan lokacin raha yazo ayi in sun yi kuskure kuma ta nuna musu kuskurensu ta yi musu gyara…..

Suma su Shuraim d’in tun basu sake da ita ba har suka sake, ko shawara suke nema wajenta
komai wajenta dan tabbas yadda take jinsu a cikin ranta haka nan suma suke jinta
suke kuma tsananin girmamata.

Tsakaninta ita da Abba kam tabbas Mama zata iya cewa tana cikin mata first class a sa’ar miji a duniya, ko kuma ma ta ce ita kam ta fi kowa sa’ar Miji a duniya.

Tsantsar zallar k’auna da kulawa had’e da tattali yake bata baya duba shekarunsu sam dan shi
idan ya tashi gwada mata soyayya kamar wasu teenagers haka yake ganinsu shi da ita.

A b’angaren Mommy itama bata bawa Aaima reason d’in da zatayi missing Mammy ba, kulawa da shak’uwa ce a tsakaninsu ta musamman dan ita Mommy ce mata ta yi ta d’auketa a matsayin best friend d’inta.

Kamar kullum yadda suka saba yau ma Sakina ta kirata suka shiga hirarsu gwanin ban sha’awa duk da kuwa Sakinar ba wani dad’i take ji ba saboda murar da take ta faman mata on and off!

Ta rasa sukuni gaba d’aya sanyin garin ya isheta.

Jin yanayinta da muryarta da kuma rashin lafiyar da take ta yi kwana biyu ya sanya Hudan ta ce
“Maman baby je ki kwanta ki huta Allah ya sauwake.”

Ta k’arashe maganar da d’an dariya k’asa k’asa sannan tana addu’ar Allah yasa harsashenta akan Sakinar ya zamo gaskiya ne.

“Ok na gode sai da safe” Sakinan ta ce..Ba ta kashe wayar ba ta d’an yi shiruu kamar mai tunani sai kuma ta kwashe da dariya kafin ta ce, “Ai ni sai yanzu ma na fahimceki!

Tab! Inaaa ba wannan tukunna wallahi iyaka mura ce kawai take damu na.”

Cikin rashin fahimta Huda ta ce “Ba kince an sallameku ba?”

Dariya Sakina ta yi ta ce “to kuma daga an sallamemu sai me?”


Bata jira amsar ta ba tana dariya ta ce

“Eh, an sallamemu dan jikin nashi ya yi kyau amman muna lek’awa, kullum,
check up”.

Shiruuu, Huda ta yi kafin ta ce “Anya kuwa Sakina?”

Sai da Sakina ta yi dariya sosai tukunna ta ce mata “Allah da gaske, babu komai ma fa tsakaninmu har yanzu sai dai hira kawai da tsantsar kulawa da soyayyyar da yake gwada min.

Da sauri Hudan ta ce, “Kai!”

Cikin murmushi Sakina ta ce,

“Kin san Allah nima kaina ina mamakin shi, ba daban ina fahimtar yanayin sa ba.

Tou da sai in iya cewa ma bashi da lafiya…Ban san dalilinsa ba kinga ni kuwa ai bazan ce gani ba!
Besides ni nama fi son haka.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin ta ce,

“Kuma bai chanja miki ba? As in ba ya wani fushi da ke”

“Ko d’aya, wallahi, kulawar ma da yake bani ni kaina banyi tunanin ta ba, kawai dai maybe shi tsarinshine haka ko kuma dai wani abun besides ai bamu fa wani dad’e ba so it’s not an issue.”

“Shikenan tou, ki gaidashi”.

Shine abunda Huda ta ce. Daga nan suka yi sallama suka kashe wayar.

Murmushi kawai ta yi tana duba wayar, a hankali ta sauk’e ajiyar zuciya ta shiga tunani.

Kullum tare suke kwana, a jikinsa take yin bacci, tana jin yanayin bugun zuciyarshi da yadda yanayinsa yake alamun lafiyarsa k’alau kuma a k’age yake amman in banda hug ba abunda ya tab’a shiga tsakaninsu.

Sam bata san ya shigo d’akin ba dan yaje siyo musu milkshake a chan k’asan hotel d’in da akeyi wani mai dad’i!

Sai da ta ji ya kwanta a bayanta tukunna ta yunk’ura da sauri tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa, “Sakina I love you fisabilillah.

Ba wai wani abu daban ba! Shiyasa kika ga ban yi yunk’urin komai ba saboda.

Ina so ne har sai kin fahimci hakan, kin yarda dani, kin saki jiki dani tukunna.

Na san zan takura amman yadda nake jin ki a raina tsaf zan iya rayuwa dake a haka muddin baki gama fahimtar kalar k’aunar da nake yi miki ba.”

A hankali ta juyo sosai tana kallonshi suka yi facing juna a kwancen!

Kasa cewa komai ta yi kawai sai ta sunkuyar da kanta k’asa kafin chaan! Ta ce

“Ya Auwal na yarda da kai na yarda da chanjin da na gani a tattare da kai.

Tunda har kaga na aureka tou yarda da k’auna ce ta kawo hakan. Sannan zan rayu da kai a ko wanne hali.”

Yadda ta ga yana kallonta ne ya sanya ta yi saurin b’oye fuskarta a k’irjin shi dan tashi d’aya sai ta ji duk kunya ta lullub’eta.

Murmushi ya yi yad’an shafa kanta, a hankali ya yi kissing kan nata yana mai shak’ar k’amshin da yake fitarwa kafin ya shiga binta da wani mayen kallo k’irjinsa yana bugawa da masifar gudu.

Sannu a hankali yanayinsa yana k’arasa sauyawa ya sa hannu ya janyota ya saka ta a jikinsa sosai!.

Sai da numfashinta ya kusan d’aukewa sakamokon wasu sak’onnin da ya shiga aika mata waenda suka girmi hankali da wayonta.

Da sauri cike da tsoro da fargaba muryarta na rawa ta ce “Dan Allah!!! Ni fa da nace haka bawai ina nufin yanzu ba.”

Ko sauraronta Auwal bashi da niyyar yi, dan tun kafin a je ko’ina notikan kansa suka kwance hankali ya fara barin gangar jikinsa.

Tabbas ya yarda kuma ya sake tabbatarwa ‘kamilalliyar mace daban ta ke! Sannan matar sunna sinadarinta na musamman ne’ Gashi kuma abun sai ya taru ya had’e masa da giyar zazzafan feelings da soyayyar da yake yi mata, shi yasa ya manta kowa ya manta komai hatta shi da karankansa ya manta kansa.

A ranar Huda ta sha Allah ya isa dan ita ce ta kirata a waya har ta janyo mata wannan jalalar.

Sam ba ta tab’a tunnanin zatayi rai ba dan Mr Auwal sai da ya yi mata dalla dalla.

Tun daga ranar kuwa ta rasa nutsuwa da sukuni. Daga nan ma Las Vegas suka wuce Honeey moon.

Auwal shi kad’ai yake k’ibarsa yana enjoyment d’inshi.

Ita kam in banda rama ba abunda take yi dan kwata kwata ba enjoying garin take yi ba
dan ita gani take ma kamar su suke tunzurashi yin wasu abubuwan.

Da kyar Aaiima ta iya samun Abba ta yi masa maganar Junaidu dan zuwa wannan lokacin kam soyayya mai k’arfin gaske ta k’ullu a tsakaninsu.

Abba ne ya samu su Dad ya yi musu bayani su kuma suka ce a tambayi su Mama indai har ba shi da wani mugun hali sai a shirya komai dan kasancewarsa d’a ga Usman hakan ba shi zai sanya su shiga tsakanin Aaima da farin cikin ta ba dan k’iri k’iri ta nuna shi take matuk’ar so!.

Sannan su a ganinsu yanzu Aaiman abar tausayi ce duk da kuwa sun san idan suka ce rashin Mammy yana a cikin matsallolin Aaima ba su yiwa Mommy adalci ba duba da yadda take iyakar k’arshen k’ok’arinta wajen ganin Aaiman bata rasa komaiba.

Amman kuma uwa dole daban take. Dan haka za su yi k’ok’ari wajen ganin sun taimaka farin ciki ya wanzu a rayuwarta na dindindin.

Tabbas Mama ta ji dad’in wannan had’in dan haka tashi d’aya ta faiyyacewa Abba halayen Junaidu wanda tun tasowarta dashi bata tab’a ganin shi da wani mummunan hali ba sai dai mai kyau sannan yanada zuciyar nema da amana ga sanin ya kamata.

Abba ma ya ji dad’in jin haka dan haka ya ce “bara ya je kawai ya samu su Dad ayi komai a gama. Kafin Aaiima ta tafi rubuta finals d’inta a saka rana, tana dawowa a d’aura aure in shaa Allah.”

A hankali Mama ta ce, “Amman fa Abba akwai wani abu guda d’aya!

Kasan case d’in Junaidu na zaman jail wanda tunda ya je ya dawo ya kud’ance! Kud’i na ban mamaki.

Last week ma sai da aka sake gano Gidaje da kadarorinsa dan shi b’oyewa yake yi..a iyaka Kano fa.

Gidajensa masu matuk’ar kyau da tsada sun fi ashirin ga kadarori ga filaye wanda bamu san source of income d’inshi ba!

Inda hali gaskiya a d’an yi mishi tambayoyi akan wannan lamari a bincika.

Naji dai kwanaki su Abba Madu sun ce sun yi mishi tambaya amman banji sun ce ga amsar da ya bayar ba.”

Jinjina kai Abba ya yi daga nan ya ce ‘zai nemi zama da Junaidun ko zuwa gobene in shaa Allah, su tattauna.”

Har gida kuwa Junaidun ya zo ya sameshi bayan ya ce masa ‘ya zo yana son ganinsa’.

Shi da Daddy ya tarar dan haka ya gaidasu cikin girmamawa suka amsa masa da kulawa.

Ba tare da b’oye b’oye ba Abba ya ce “sun san bashi da wani mummunan hali amman kuma suna buk’atar sanin kwakkwaran source of income d’inshi”.

A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara basu labari.

“A lokacin da aka sallame ni daga prision. Mun fito mun kama hanya, bamu kai ga zuwa inda za mu je ba cikina ya b’aci! Dan haka na nemi alfarmar su tsaya in d’an yi uzuri. Suna tsayawa na fita. Ina kutsa kai cikin d’ajin kamar an ce in juyo nan na ga wasu maza da mask su uku sun nufi motar. Duk sai da suka fito da y’an motar suka dubasu amman sam babu abunda suke nema wanda sai daga baya na gane waenda Arshaad ya tura ne kuma ni suke nema.

Kamar na sani a lokacin sai na b’oye kaina. Bayan na b’oye kaina su kuma suka gama dube duben su suka tafi.

Su kuma Abokanan tafiyar tawa inaga tsorata suka yi dan ina shirin fitowa naga duk sun shige motar suna shirin tafiya.

Da sauri na yunk’ura zan tafi na ji an rik’e min k’afa! Sai da gabana ya fad’i da na juya dan ni sam ban lura akwai tsoho ma a wajen ba a durkushe sai da ya rik’o nin.

Cikin kuka tsohon ya ce “bawan Allah ko baiwar Allah dan Allah taimakon musulunci zan mutu yunwa nake ji.”

Da sauri na ce “Baba dan Allah Abokanan tafiya ta za su tafi ka cikani In wuce.”

Cikin kuka tsohon ya ce “yunwa nake ji ka taimakeni dan Allah”.

Haka nan inaji ina na gani na kama hannunshi ya mik’e su kuma Abokanayen tafiyar tawa suka wuce dan maybe sunga na dad’e su kuwa a tsorace suke.

Na ji takaici sosai amman yadda tsohon nan yake karkawa da kuka yasa kawai na yanke shawarar In taimakeshi.

Sai da muka fara tafiya na fahimci ashe makaho ne!

Haka muka yi ta kutsawa dan hanyar ba jama’a sosai har muka iske wata mai k’osai da kunu na siya da d’an kud’in da aka bani in yi na mota na bashi ya ci ya sha.

A hankali muna zaune a wajen ya ce “in bashi labarina”. Haka kurum ban sanshi ba amman na tsinci kaina da fad’a mishi komai na rayuwata har kawo yanzu.

A hankali ya ce “kuma kana ganin ba kai ake nema ba kuwa!?

Ka zo mu je Gidana ka d’an b’uya kafin kwana biyu sai ka wuce gudun kar ka je suna nan har yanzu ka fita a kama ka.”

Tsoro ya sanya ni na amincewa wannan tsohon, dan a yadda naga mutanen nan babu kalar imani a tattare da su.

Gidan nasa y’ar bukka ce sai band’aki wanda aka yishi da langa langa a gefe, sai wani murhu da rijiya. Sam babu wani katanga ko wani abun da yake nuni da wajen keb’antacce ne.

Y’ar bukkartashi muka shiga muka zauna anan yake ce mini “Matarsa ta rasu watan da ya mutu,
Allah bai bashi d’a ba!

Danginsa kuma duk sun guje shi saboda basa son d’awainiya.”

A take na ji tausayin bawan Allahn nan ya rufe ni, kuma a take muka saba shak’uwa ta shiga tsakaninmu.

Kwana na biyu a wajensa, na siya mishi abinci da d’an abun da ba a rasa ba duk a cikin kud’in da aka bani
a lissafina idan na tashi ni sai in d’auki drop har gidan Abokina ya biya.

Ban b’oyewa tsohon nan ba na ce masa “mu ma ba wasu masu arzik’i bane ba, ba daban haka ba da na tafi da shi” dan na lura yana cikin kad’aici da buk’atar taimako “kuma akwai abubuwa da dama a kaina amman dai bara mugani in shaa Allah idan na koma gida na yi settling zan dawo in duba shi.

Dan nima a yanzu ina matuk’ar buk’atar kud’i.”

Daga nan na nemo wata mata a gefe na rok’eta akan “dan Allah ta d’an dinga lek’ashi”.

Ita kam Matar mamakima ta dinga yi dan a cewarta “duk zaman ta a k’auyen ita bata san da shi ba”.

Bayan Matar wuce ne muka yi sallama muna ji kamar kar mu rabu.

A bakin bukkar tashi ina fitowa na ci karo da wani mutum cikin suite! Da akwati a hannunshi.

Kamar yana cikin sauri, ya nuna min hotonshi da wannan tsohon kamar lokacin tun suna samari ya ce min “an ce yana nan! Da kyar da wuya ya samu location d’insa, dan Allah na san shi?”.

Ba tare da b’ata lokaci ba na ce masa “eh”. Dan haka mutumin ya ce mini “sun tab’a yin businesses da tsohon ne, tsohon ya aminta da shi amman shi sai ya gudar masa da kud’insa so tun daga lokacin abubuwa basu yi mishi kyau ba!

Shiyasa ya yanke shawarar dawo mishi da dukiyarsa.” Ya d’aura da cewa. “Dan Allah in bashi in ce masa
ya ce sunanshi Kabir, Alhaji Kabir. Ya taimaka ya yafe masa.”

Yana min maganar ne shi duk a tunaninsa ma ni d’an tsohon ne.

Jin muryar tsohon ya fito yasa ya yi sauri ya yi min sallama a cewarsa ‘ba zai iya facing d’insa ba dan
kunyarshi yake ji.’

Duk da nace ya d’an tsaya ko ruwa ne ya sha saboda naga inba magana ya yi ba tsohon ba zai gane shi ba dan ba gani yake yi ba, amma sam yak’i yarda, ya damk’a min akwatin yana d’an waiwayowa yana kallon tsohon har ya shige motarshi driver ya ja suka tafi.

Akwatin na ja na kai d’aki na fito na kama hannun tsohon muka shiga ciki na zauna.

Na zuge akwatin ba tare da na ce komai ba.

Sai da gabana ya yanke ya fad’i dan gabaki d’aya akwatin cike yake da mak’udan kud’ad’e dollars!

A hankali na ji tsohon ya ce “Kai da waye d’azu a waje?”

Cikin In inaa na ce “wani mutum ne ya zo neman ka! Ya ce kun tab’a yin buisiness kai da shi ya gudar maka da kud’i.”

Shirruuu tsohon nan ya yi kafin chaan! Ya yi murmushi ya ce, “na kasa tunawa”.

Kafin ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya ce. “Akwai abunda ban gaya maka ba.


Inada sabara a kwakwalwata shiyasa ma kaga wasu lokutan Ina zama ina yin kuka ni kad’ai.

Wani makwafcina anan ya d’auke ni satin baya ya kaini asibiti aka tabbatar da cewa ‘ba zan k’ara sati uku a duniya ba!’.”

A take wani tsananin tausayinshi ya lullub’e ni! Ga dai kud’ad’e nan ya samu bayan ya sha wahalar rayuwa amman a lokacin da kud’ad’en suka riskeshi sai ya zamana ba za su yi mishi amfanin komai ba.

Ban san lokacin da kuka ya kufce mini ba!.

Jin ina kuka yasa tshon ya hau tambayata “menene? Mai ya faru?

Me ye a cikin jakar? Ko wani abun tsoron na gani?”

Shiru na d’anyi kafin ince mishi. “Kud’i ne a ciki, Dollars.”

Shiruuu na ji ya yi. Ya jima tukunna ya ce, “Ka taimakeni ko masallatai ne in gina dan Allah.

Saboda kaga ni ba ido da lafiya gare ni ba.

Ba na bukatar ka gina min gida ko wani abu daga kud’in tunda kaga ba lallae inga k’arshen aikin bama
kawai dai ka rik’e Allah ka tayani gyara lahirata ta hanyar gina masallatai da islamiyoyi a k’auyukan nan.”

A lokacin tabbas ina son komawa gida amman kuma wannan tsohon yana buk’atar taimakona a yanzu
sannan inaso a ida auren Huda da Arshaad kafin In koma dan tabbas na kasa cire ta a cikin zuciyata
kuma na riga na d’auki alk’awarin ba zan aureta ba!

Tunda na lura sam bana cikin zuciyarta tun ranar da ta ce min Arshaad zata aura
k’ok’ari kawai nake yi inga na fitar da ita a raina.

Saboda no matter how much I love her ba zan tab’a iya zama da ita idan bata ra’ayi na ba!

Amman kuma bana buk’atar a aurar da ita a gaban Idona, sannan still ina jin fargabar fitowata
duba da sharrin da aka yi min da kuma waenda nake tunanin ni suke nema..A ganina gara In d’an fahimci abubuwa daga b’oye kafin a kaini lahira tun da ban san waye yake farautata ba! Sannan aikin da zan yiwa wannan tsoho tabbas lada zan samu. Shiyasa a take na yanke shawarar jifan tsuntsu biyu da dutse daya.

Haka nan na tsaya tsayin daka wajen taimaka masa kamar yadda ya buk’ata aka shiga gina masallatai a duk k’auyukan da makarantun islamiyya, gini mai kyau da had’uwa, na ban mamaki.

Tabbas Ina da buk’atar kud’i, amman ban tab’a yunk’urin d’aukar ko naira biyar ba!

Apart from kud’in motar da yace In dinga d’auka a ciki dana abinci da shelter.

Akwai kud’i sannan na samu maaikata masu yawa sosai dan ko wanne k’auye masu ginin daban suke
shiyasa kafin wata uku aka fara shirin kammalawa.

Ba abunda yafi sakani farin ciki irin yadda Allah ya arawa wannan tsohon tsawon rai har na tsawon lokacin da aka zo kammalawa duk da dai jikin nashi sai a hankali.

Ranar da na kammala aikin da washegari ya tashi da tsananin ciwo wanda kana gani ka san sai a hankali kawai. A wannan bukkar tashi muke har kawo wannan lokacin amman fa muna cin mai kyau mu sha mai kyau.

Ina ganin yana yin jikin nashi na ce “bara inje In nemo mai abun hawa a kaishi asibiti cikin gaggawa”
Amman sai ya rik’eni ya rok’eni akan in tsaya akwai maganar da yake so ya yi da ni.

Abu na farko da ya fara tambayata shine sunana! Duk tsawon lokutan nan Yaro yake kirana da shi ni kuma in kirashi da Baba.

Sai da mutanen last k’auyen da aka yiwa masallaci suka tambayeni ‘suna son
rubuta sunanshi’. Tukunna da kyar ya ce min sunanshi ‘Alhaji Kabir mai fetur’

A hankali na ce mishi “sunanan ‘Junaidu’.”

Da kyar cikin tsananin ciwon da yake ciki ya iya ce min “in d’auko masa wata y’ar jaka”.

Ya yi maganar yana mai yi min nuni da wajen da jakar take! Tabbas na shiga rud’ani, saboda yadda ya juya ya nuna min jakar yasa na fahimci yana gani.

Ina d’aukowa ya ce “In bud’e”. Ko da na bud’e d’in wasu takardu ne a ciki da waya
had’ad’d’iya mai kyau da tsada.

Wayar ya umarceni da in d’auko, in yi dialing number dana ga an yi saving da ‘barrister’.
Haka akayi, tana shiga bugu d’aya ana biyu aka d’aga!

Cikin girmamawa na ji ance “sir”. Da mamaki na kalli tsohon wanda shi kuma yake mik’a min hannu alamun in bashi wayar.

Kaina bai gama d’aurewa ba sai da na ji kalar turancin da tsohon yake yi inda cikin harshen turanci na ji yana cewa wannan wanda suke waya “Suna kusa ko? To su yi sauri suzo yanzu.”

Tsoro da firgici suka sanya na mik’e da sauri na fara ja da baya.

A hankali tsohon nan ya ce, “Dan Allah kada ka ji tsoron komai. Matso kusa in baka wani d’an tak’aitaccen labari.”

Da farko k’in yarda na yi in matsa d’in dan ni a tunanina ko d’an shan jini ne ko kuma d’an 419 bare ma da na tuno da mak’udan kud’ad’en da aka kawo mishi gaba d’aya sai na sake duburbucewa.

Da kyar da sid’in goshi ya lallab’ani na matsa kusa da shi.

Ina zama ya ce min, “Kar ka ji tsorona d’ana,.

Ni ba macuci bane ba” Bai bani damar yin magana ba ya cigaba da cewa, “Kamar yadda na fad’a maka da farko Allah bai bani haihu wa ba.

Na kasance attajiri na gaske dan a k’asar nan idan akwai waenda suka fini kud’i tou bana jin
za su fi mutum biyu! Arzik’i na ya samo asali ne daga sana’ar man fetur, da na samu Ubangiji ya sanya mini albarka harkar tawa ta bud’e sai na fad’a sana’a.

Business ko wanne iri ne zan yishi kuma da ikon Allah Ina farawa sai ya habb’aka ya yi albarka ta ban mamaki.

Ni asalina maraya ne, tun Ina gidan marayu muke soyayya da matata da na ce maka ta rasu watan baya.

Ina matuk’ar k’aunarta, sai dai kuma kishiyoyinta suka zamo silar da ya sanya bata ji dad’i a rayuwarta ba!
Ta rayu cikin tsananin k’unci da azabar rayuwa.

Ni mutum ne wanda yake son mutane masu amana, bayan son da nake yi wa uwar gidanaa
tsoron Allah da amanarta ne suka k’ara min tsananin k’aunarta.

Apart from her bana jin akwai wanda ya tab’a rik’e mun amana yayi mun abu tsakaninshi da Allah
sai kai Junaidu.

Na sha adopting Yara in rik’esu tsakani da Allah amman kowa idan ya lek’a ya hango tarin dukiyata sai ya nemi cutar da ni!

Rabinsu ma buri suke kawai suga sun halaka ni.

Da taimakon Allah da taimakon uwar gidana nake tsere wasu tarkunan wanda fahimtar da aka yi tana taimaka min ne yasa aka shiga tsakaninmu na juya mata baya.” Cikin kuka ya ce, “Ban tashi gane gaskiya ba
sai a ranar da zata bar duniya tukunna aka samu asirce asircen suka bar jikina na ganta a matsayin masoyiyata instead of da da nake ganinta as my enemy.

Na yi kuka ma yi takaici! Saboda ita take d’awainiya da ni idan ciwona ya motsa Ina kyararta Ina komai
ashe itama bata da lafiya.

Duk da na saki ragowar mata na biyun da na fahimci laifin su ne sannan na bata hak’uri ta ce ta yafe min amman na kasa yafewa kaina! A ranar da zata bar duniya maimakon ni in lallasheta.

A dead bed d’inta sai ya samana ita take lallashina.

Na yi rashi tabbas sannan na san na rasa mutum d’aya tak da ya tab’a rik’e mun amana.

Ita ce ta ce min ‘In kwantar da hankalina zan samu wanda zai rik’en amana kamar ita
I should mark her words.’

Bayan ta rasu da kwana biyu.. daman tun kafin a shiga tsakanin mu na yanke shawarar ‘zan damk’awa mutum mai amana guda d’aya rabin dukiya ta idan na samu kenan, rabi kuma in rarraba a gidan marayu, ba wai kuma masu kula da gidan marayun zan bawa in ce su raba musu ba, A’a Yaran gidan marayun zan bud’ewa account each, In saka musu kud’insu a ciki, saboda yadda duniya ta lalace, tsaf mutane za su iya danne kud’in dan na ga yadda mutum yake komawa akan dukiya. Saboda haka na fara
searching. A yadda na je maka a haka nake zuwama mutane amman har da waenda suka mareni!

Mutum d’aya na samu kafin kai ya taimaka min kamar yanda ka yi sai dai shi ana kawo kud’i kamar yanda aka kawo aka baka ya gudu! Ko lek’e na bai sake yi ba.”

Muna cikin wannan zancen, Mutannen da ya kira suka k’araso. Manyan lauyoyine, da kuma wani babba a efcc.

Da mamaki nake kallonsu. Ban san sanda hawaye suka zubo mini ba! Jin yana musu bayani
akan yadda ya yi alk’awarin bawa mai kyakkaywar zuciya dukiyarsa. Hope takardun sun zama ready? Saboda gani nan” Ya yi maganar yana nuna ni ya ce. “Nine successor d’insa”

A take suka ce “eh, komai is ready”. Sannan suka mik’o min takardu suka ce “in yi signing.”

Da farko kasawa na yi saboda yadda mamaki aljabi da tsoron Allah ya lullubeni, sai da tsohon ya rik’e mun hannu tukunna na dawo dede na shiga signing takardun da kwakwalwa ta ta kasa d’aukar d’umbin kud’ad’en da idanuwa na suke gane min!.

Ina gama cike wadannan tsohon ya ce “yaso ya rabawa marayun kud’ad’en da kanshi
amman kuma bashi da isheshen lokaci, so zai d’aura wannan nauyin a kaina”.

Nan ma wasu takardun na cike na kud’i shima dede adadin wanda aka gama mallakamin
wanda zan rabawa marayun nan.

Jakar da d’azu ya ce ‘In d’auko in bashi waya a ciki’. Ita kuma filayene da gidaje da gidajen man fetur d’insa, ya ce min “I should consider it shikuma as thankyou from him, dan bai san ta Ina zai fara yi min godiya ba! Na tabbatar da maganar matarshi sannan na bashi hope na cika mishi burinshi.”

Daga nan duk ya saka na yi signing, Ina kuka yana kuka.

Sannan ya bada will d’in nine d’ansa sannan ya rok’eni, ‘ko bayan ranshi in dinga yi mishi addua dan Allah.’

Ganin numfashinshi yana d’aukewa yasa na kinkimeshi muka kai shi motar da mutanen nan suka zo a ciki.

Amman Ina kwantar da shi a seat d’in baya na ji yayi kalmar shahada a hankali
sannan jikinshi ya sake.

Na yi kuka matuk’a.

Ban yi k’asa a guiwa ba, tundaga Adamawa har Abuja sai da na je da kaina na fara rarrabawa marayun nan rabin kud’ad’en shi da na yi alk’awari wanda har yau ina kan aikin.”

A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce. “Wannan shine sanadin arzik’i na.

Babu k’arya k’ari ko ragi a cikin labarina.”

A hankali su Abba suka sauk’e ajiyar zuciya bayan sun gama saurarenshi, kafin Abba ya ce
“Tabbas Junaidu samun irinka a zamanin yanzu sai an tona.

Allah ya yi maka albarka. Ka cigaba da rik’e amana da alk’awari.

Allah yasa ka gama da duniya lafiya.

Idan mun gaMa magana za ka ji sak’on mu daga wajen Aaima in sha Allah.”

Cikin girmamawa ya yi musu godiya, daga nan suka yi sallama ya wuce.

Bayan sati d’aya Aaima ta ce masa “su Daddy sun ce yana iya turowa anytime idan sun shirya”.

Tsakanin Aaima da Junaidu ba zaka iya tantance wanda yafi wani farin ciki ba.

Su Kaka da Ya Jamilu ne suka zo suka nemawa Junaidu auren Aaima.

A parlourn Daddy aka tarbesu, tarba ta mutunci!

Cikin mutunta juna suka yad’a manufarsu suka nema aka basu.

Wata biyar ciff! Aka saka ranar auren daga nan suka bayar da goronsu da alawa da kud’i nera miliyan d’aya!

Aka watse cikin farin ciki barkwanci mutunta juna da nishad’i.

*****
Sai da Sakina ta fara kukan gida tukunna Auwal ya yarda suka dawo a lokacin watansu biyar a k’asashen waje.

Ya so ta tsaya su biya Paris dan nan ne kad’ai basu je ba a cikin k’asashen da ake yawan zuwa a d’an shak’ata. (Har Hajji da Umaara sun yi)

Amman ganin yadda ta d’aga hankalinta sannan ga yanayin condition d’inta yasa kawai ya hak’ura suka dawo.

Direct gidansu, Daddy ya ce su wuce dan ta samu ta d’an huta.

Tabbas Daddy ya san in ba da kyar ba to kuwa za a yi irinta Granpa da Aslam. A shi da d’an cikin jikin Sakina saboda yadda yake jin son jika ko jikar tashi tun kafin su zo duniya a ransa Allah kad’ai ya sani.

Ita Sakina har mamaki da kunya ma take yi, haka nan fa takanas! Zai kirata ya yi ta jero mata adduo i ita da babyn.

Sannan ya yi ta turo mata important things akan condition d’inta, abunda ya kamata ta ci da wanda bai kamata ta ci ba saboda lafiyarta da babyn…

Wasu lokutan ita kam har kukan farin ciki take yi dan gata da soyayyar da Auwal
yake nuna mata bata jin she could ever ask for more.

Tunda ta lura yana d’an wasa da sallah ta kafa ta tsare sannan ta nuna mishi b’acin ranta!

Yanzu sam Auwal ya manta rabon da ya bari lokacin sallah ya wuce shi.

Zaman lafiya da k’aunar juna shine definition d’in rayuwar su ga families d’inshi suma hatta Granpa da Mom kiranta suke yi su ji ya lafiyarta da babyn dan Auwal a ranar da ya sani washegari ya kasa rufewa
farin ciki yasa sai da ya fad’awa su Mom da Gramma har su Abba tukunna hankalin shi ya kwanta,
sai da ya gama sanarwa kuma sai ya d’anji kunya.

Idan ka gansu tsaf da su sun yi k’iba sun yi fresh in banda glowing ba abunda suke yi!
Gashi sun yi mugun dacewa da juna, kamar ka sace su ka gudu.

Gidan da Arshaad ya siya zasu zauna da Huda nan ya mallakawa Auwal, hatta
lefe da kayan d’akin suma su Daddy duk suka bashi.

Sakina taso biyawa ta ga Huda amman jin yadda Daddy ya damu akan ta huta wai ‘ta hawo jirgi ta yi jigila jigila’ yasa kawai ta hak’ura suka wuce gidan ba dan ranta yaso ba.

A hakan ma kuma Daddyn ya ce “zuwa gobe su je asibiti a tabbatar da komai dai lafiya”

A chan suka tarar da Gwaggo Asabe tana gyaggyara musu gidan ita da wata mai aiki har girki sai da tayi
musu.

Suna gama oyoyo d’insu ta sulale ta fice ko sallama bata yi musu ba dan karma su rik’eta
saboda ita tun kwanakin baya da Mommy ta tilastamata zama a wajen su Hudan ko kwana d’aya bata iya yi ba, ta gudu ta koma gidan Mommy a ranta kuwa ta raya ‘ta gama zama gidan sabbin Amaren nan gaskiya’.

Aslam, yana tuk’i yana d’an satar kallonta.

Ganin tak’i ta yi shiru yasa ya sauk’e ajiyar zuciya ya yi parking a d’an gefen titi kad’an ya kashe motar ya juyo ya kamo hannunta.

Kamar za a fashe da kuka ya ce. “Hudatie, kukan nan ya isa haka dan Allah.

Saboda ke fa na je wai dan ki d’an samu ki shiga mutane amman ni kam na jima ma rabona da shi.

Da ace na san kuka za ki d’ebo Allah da ba za mu je ba gaskiya.

Ki share hawayenki.

Come here.” Ya fad’a hakan yana mai janyota izuwa jikinshi.

Da kyar ya samu ta d’an yi shiru kafin ya ce, “Ya Aslam matar nan ta bani tausayi..wallahi ba ita ta d’auka ba!

Sannan Yaron ina ganin lokacin da Maman shi ta bawa wannnan maid d’in shi a wani lungu wajen ba kowa time d’in ni kuma na fita yin waya da Sakina ne.”

Da sauri Aslam ya ce “are you sure?”

Cikin tabbatarwa ta d’aga mishi kai alamun ‘eh’.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce, “Tun farko daman maganar sark’ar nan na fahimci makircin mata ne.

Wannan maganar Babyn kuma da kika fad’a min yanzu ya sake tabbatar min.

Zan je in samu Yash d’in in fad’a masa sannan In tsaya har sai naga an fitar da ita tun kafin a shiga kotu ma.


Amman wacce iriyar dak’ik’iyar uwa ce zata yiwa d’an da ta haifa a cikinta haka?”

Cikin share hawayenta ta koma gefe ta zauna ta ce “Nima dai abunda na ce kenan, amman wallah yadda naga ta bawa wannan maid d’in Yaron Allah yasa In ga Annabi.

Sannan jakar MANNUBIYAn a hannuna take!

Ta bani bayan ta d’auki abu a ciki ta ce ‘in rik’e mata bara ta je ta yi chanjin ta dawo’.

A gabana ta bud’e ta d’auka abun da zata d’auka, ba komai a cikin jakar sai y’ar k’aramar fasashshiyar wayarta da abunda ta d’auka sai d’ari biyu wallahi.

Tana dawowa ko tab’a jakar bata yi ba na ajjiye mata akan cinyarta. Kuma ko da ta dawo d’in babu komai a hannunta haka nan ta nemi waje ta zauna da jakar a gefenta.

Tana zama wayarta ta d’au ringin ta bud’e ta d’auka.

Tana gama wayar muka ci gaba da hira take ce min ‘Babanta ne Za’a yi sadakar arbain d’in Mahaifiyarta jibi.’

Daman tun zama na na fahimci tana cikin damuwa, tun farko ita kad’ai a gefe na hango
shiyasanya ma na je na zauna kusa da ita. Ashe dalilin kenan.”

Cikin jinjina kai Aslam ya ce “shikenan, zan je In samu Yash d’in.

I wonder why ya yi believing da sauri haka har ta kai shi ga yi mata wannan wulak’ancin!

Yanada zurfin tunani ban san me ya shiga kanshi ba. Anyways zan je in sameshi.

Yanzu ki daina kuka share hawayenki kin ji honey…”

Cikin share hawaye Hudan ta ce “Ta bani tausayi ne sosai wallah, har da kukanta dama tana bani labarin Mahaifiyarta, sai kuma kawai muka ji sanarwa. Ni a ganina lokacin da wajen ya hargitsene aka saka mata sark’ar a cikin jaka saboda tabbas a k’asa muka hango jakar a jefe tana d’auka kuma aka k’araso kanta.”

“Hmmm, makircin mata ne kawai.”

Cewar Aslam yana mai kunna motar.

A hankali Hudan ta ce, “D’an Indiya ne? Friend d’in naka, na ji sunansa ‘Yash’.”

Murmushi Aslam ya yi kafin ya ce “sunanshi Yashjub, Itama MANNUBIYAn baki ji Manu ake ce mata ba.”

Cikin son faranta mata rai da kawar da zancen ya ce “Good news, sannan surprise.

Bara dai mu je In munje za ki gani.”

Tunda suka shiga gidan suka zauna Aslam ya yi waya ya ce “suna parlour” ta kasa nutsuwa, in banda gyara zama da kalle kalle ba abunda take yi.

Ta so ta gane wasu items a cikin gidan kamar waenda suka zab’a ne ita da Sakina
lokacin bikinta da Arshaad.

Da sauri ta kalli Aslam ta ce “Laaa Ya Aslam Sakina ce ta dawo ko?”

Dai dai nan suka k’arasa sauk’owa ita da Auwal.

Jikinta ne kawai ya bata tana bayanta, ga kuma Aslam yana kallon wajen yana murmushi.

Da sauri ta juya sai kuma ta mik’e da gudu ta zagaye kujerar ta tafi zata fad’a jikin Sakinar.

Da sauri Auwal ya shiga gaban Sakina tsakaninsu ya tsaya ya ce “a,a,a,a careful!!”

Yana d’an zaro ido da d’aga gira da d’an murmushi akan fuskarshi.

Da sauri Huda ta ce, “Au sorry na manta, Daddy ya Auwal” tana d’an dariya.

Dariyar shima ya yi yad’an matsa ai kuwa da sauri Sakina ta rungumeta ta na share hawayen murnar ganin y’ar uwartata.

Cikin farin ciki da k’aunar juna suka hau gaggaisawa da tambayar bayan rabuwa.

Sun jima suna hira kafin Sakina ta ja Huda suka yi sama.

Auwal kuma ya kira Arshaad suka hau video call su uku! Ba k’aramin dad’i suka ji ba
da ganin yadda Arshaad d’in ya sake sakewa ya ware sosai kamar komai bai tab’a faruwa ba.

Suna hawa saman Huda ta fara tab’a cikin Sakina tana murna har da kwallarta…

Nan suka zauna Huda ta fara zab’an sunayen da zxata sakawa Babyn In sakina ta haihu.

Ganin da tayi kamar Sakinar is moody ne yasa ta shiga tambayarta da damuwa akan fuskarta.

A hankali Sakina ta ce, “Ni inata mita mu ba a cikin estate za mu zauna kusa da ku ba, ashe ba ma a garin zamu zauna ba gaba d’aya.”

Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin ta ce “Ai kin san Ya Auwal shi ke da MT d’in Abuja, dole kinga a chan za ki zauna kusa da shi mana Sakina.

Za mu dinga zuwa ai ku ma kuma na san za ki dinga zuwa sannan na san maybe ma ya dawo dashi Kano gaba d’aya ko?”

A hankali Sakina ta ce “Ai cewa yayi wai a chan Cairo zan yi karatu kuma de!

Ni duk kaina a d’aure yake ban ma san wajen zama d’aya tak’ameme ba, ya ce min dai wai zan ji dad’in karatun sosai.”

Dariya Huda ta yi kafin ta ce “ashe ya yarda kenan.

Ya Aslam ne ya sama mana karatun mu biyu ni da ke, da yayi mishi maganar da farko sai kamar bai yarda ba ya ce‘shi yana Abuja family suna Kano ke d’in idan kika yi masa nesa aganinshi abun zai d’anyi wuya’
Shiyasa Ya Aslam ma ya ce min kar In gaya miki yet ki d’aga mishi hankali tunda bai riga ya amince ba.
Kinga yanzu kuma ashe ya amince…”

Da sauri Sakina ta rungume Huda ta ce “Na ji dad’i da za mu yi karatu tare”.

Sai da dare ya yi sosai tukunna su Huda suka kama hanyar estate.

Aslam sarai ya lura da Huda, yadda duk jikinta ya yi sanyi kuma tabbas ya san damuwarta.

A hankali ya ce “Hudatie kowa fa da lokacinshi, sannan ai lokacima bai wani ja ba, Manu fa matar Yash Indai zan iya tuna lokacin da ya turo min iv d’in bikinsa tou ina jin yanzu shekararta uku da aure!

Amman har yanzu bata haihu ba kuma kinga kishiyarta ita har ta haihu. Ita kuma tace me?


Ga Mommy itama sai da ta yi shekara kusan…”

Kukan da ta fashe masa da shi ne ya sanya shi sauk’e ajiyar zuciya yad’an kamo hannunta ya ce,

“Gaskiya Hudatie zan fara miki bulala! Gaba d’aya kin zama shagwab’abb’iya, abu kad’an kuka?”

Cikin kukan ta ce “tou Ya Aslam bakaga ita Manu d’in an yi mata kishiya ba?”

“Da sauri Aslam ya ce “Woow!!

Good idea Huda, kai! Amma Allah ya yi miki albarka, kin kawo shawara kinga nima sai in k’ara auren kenan!

Bara muga daman ina son k’asar Egypt dan haka y’ar egypt zan fara aurowa, sai in auri y’ar indiya.

Sai in je garin Taraba In auro saboda Mommy, sai kuma In tafi Chad in auro, saboda inyiwa Dad shima kara.”

Cikin k’ara sautin kuka Huda ta ce “Ya Aslam ka fa lissafa hud’u kenan, ni kuma a ina za ka saka ni?”

Tana tambayar tana sake fashewa da kuka.

Cikin dariya k’asa k’asa ya ce, “Au haba??

Ok tou bara in cire y’ar indiya tunda kema ai kinada gashi sosai Irin nasu”

This time around duka ta fara kai masa.

Cikin tsananin dariya da nishad’in da yake ciki ya ce, “Haba mana, Hudatie Ubangijine fa ya ce
mu yi biyu uku har hud’u indai za mu yi adalci.”

Ya fad’i haka yana Parker motar a harabar gidansu dan har sun iso.

A hankali ya kamo. Hannunta cikin kulawa ya ce “Kinga ni kuwa ba zan iya yin adalci,
tsakaninki da ko wacce mace ba shiyasa na zab’i in zauna da guda d’aya!

Dan nasan muddin na k’ara aure to zan kasance cikin mazan da suke tashi da shanyeyyen b’arin jiki ranar gobe k’iyama.”

Kamar wata wawuya sai kuma ta fara murmushi kad’an kad’an tana kuka.

A hankali ta kwanta a jikinshi yasa hannu ya yi hugging d’inta.

Dariya ya yi kafin ya ce, “Irin wannan zafin kishi haka?

How much do you love me??”

Ya yi mata tambayar yana murza tafin hannunta.

A hankali ya ji ta ce “Stars da ruwa kansu inda ace za a iya kirga su tou baza su kai adadin yadda nake k’aunarka ba Ya Aslam.. I love you so much!!! Till eternity, I’ll always love you.”

BAYAN SHEKARU GOMA!
Abubuwa da dama sun faru. An samu cigaba k’ari d’aukaka da farin ciki, sannan an samu rashi
na rasuwar Gramma Kaka da K’asimu.

Shekara biyu Mom ta yi a wajen Innaa, da kyar da fad’a da lallashi da shawarwari aka samu Daddy ya amince ta komo amman fa ya k’ara aure!

Dan tana tafiya ko shekara ba a yi ba ya auri wata k’anwar Abokinsa y’ar gayuu Budurwa amman zata kai 35 years. Ana kiranta da ‘Kaulat’.

Tabbas sai da Mom ta yi da gaske tukunna ta yi kokawa da zuciyarta dan, Kaulat ta fita ta ko wacce hanya Kyau! Ilimi! Aji! Kud’i! Gata!!

Sannan sai take gani kamar ma Daddyn ya fi son Kaulat d’in a kanta.

Amman kuma da ta yi hak’uri bata yi komai ba sai abun ya zo mata da sauk’i dan Kaulat sam babu ruwan ta a waye take sosai kowa nata ne shiyasa ana aurota ma ta siye zuciyar kowa a cikin estate d’in.

Mammy kuwa hukuncin life inprisonment aka yanke mata na kisan Ummi, dan k’iri k’iri Mommy ta kafa ta tsare tak’i yarda a yi shari’ar case d’inta da Mammy.

Mammy ta yi nadama da gaske a prison. Sukan je su ganta dan ba a chanjawa tuwo suna she’s still part of the family.

Banda sauk’a da haddar Alqurani, nafila da neman yafiyar Ubangiji ba abunda ta saka a gaba…..

Yanayin karatun su Huda wanda Aslam ya tsara akan za su yi a Cairo hakan bai faru ba.
Saboda Mama da Daddy cewa suka yi ‘Huda ta yi BUK tunda a kano Aslam yake
Sakina kuma ta yi gwagwalada.’

Mazajen nasu sam! Basu so hakan ba amman ba yadda suka iya haka nan suka amince domin sun san duk abunda babba ya hango Yaro ba zai iya hangowa ba.

Cikin sa a suka fara karatun nasu. Allah ya taimake su ba a samu strike da delay ba ko sau d’aya har suka kammala karatunsu da first class ba tare da sun samu delay ko tangarda ba.

Hudan ta zab’i fannin Paediatric Sakina kuma Gynecologists.

Suna kammala karatunsu suka tafi course na k’aro Ilimin sani a fannukansu na shekara bibbuyu a UK.

A lokacin both Aslam da Auwal kowa ya bud’e sabbin company d’insa a chan uk d’in dan haka kusan tare
suka tafi da mazajensu da ‘ya’yan su har suka kammala!

Sai a wannan lokacin ne kuma Arshaad ya yanke shawarar dawowa gida tare da Amaryarsa mai suna ‘Jahad’ y’ar k’asar Saudi Arabiya wadda ya aura last year!

Kaff familyn MT babu wanda bai je bikin Arshaad ba har su Ummu, tun a lokacin suka so ya koma gida yak’i, yanzu kuma shi da kanshi ya yanke shawarar komawa gida dan he’s pretty sure baya yiwa Huda zazzafar soyayyar da yake yi mata a baya.

A ranar da suka dawo Huda da Sakina suka tarar da babbar kyauta daga Granpa wanda ya bud’e musu tangamemen asibiti mai hawa wajen biyar! Ya basu ya ce “su zab’i suna su saka”.

Da farko sunan Madu suka so su saka amman sai Mama da Ummu suka basu shawarar su saka
‘Mai Turare’.

A ranar Granpa ya had’a walimar welcoming Arshaad da Amaryarsa. Bud’ewar Asibitin su Huda
da kuma saka ranar Sumayya da Shuraim, wadda Sumayya ta amince da auren da kyar!

Bawai don bata son Shuraim ba sai dan ita a ganinta bai kamata ta auri age mate d’in ta ba.


Yau da kanta take so ta je ta d’auko Yaran saboda tana son zuwa wajen Jalila da su, duk da cikin wajen wata bakwai d’in dake a jikinta hakan bai hanata driving da kanta ba.

Tunda wuri dama ta kira driver ta ce masa ‘kar ya je, da kanta zata je ta kwaso su’.

Tana zuwa tun a bakin gate mai gadin da ya bud’e mata ya ce “ta je da wurwuri office d’in principal yana ta fad’a!

Tun d’azu ake kiran layin office d’insu ita da Maman Arshaad amma duk su biyun basa d’auka.”

Da sauri ta k’arasa office d’in, tana shiga ta sauk’e ajiyar zuciya ta girgiza kanta, a ranta ta ce
“Dama na sani”

Tana k’arasawa ta kamo kunnen Arshaad ta jaaa da k’arfi ta d’aga shi ya mik’e, cikin fushi ta ce
“yau ma ko? Wai mai yasa baka jin magana ne?”

Da sauri principal d’in ya ce, “Mrs Aslam. This boy must leave this school gaskiya!
We can’t tolerate him anymore!!

Wallahi saboda share d’in Dad d’insa a makarantar nan ne yasa muka barshi, amman yanzu kam mun gama yanke shawarar sallamarshi.

Zamu fitar wa da Dad d’in nasa share d’insa idan yak’i amincewa.”

Hudan na shirin fara lallab’asa principal d’in ya katseta ta hanyar cewa
“Mun rigafa mun gama magana!

Saboda Allah ko malamai bama bari su daki Yaro saboda iyaye basa so amman bamu huta da case ba kullum duk akan Arshaad.

Fad’a da zuciyar shi yayi yawa gaskiya.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e sannan ta cikawa Arshaad wanda yake ta faman kumbure kumbure kunne
ta mik’awa, Anum key d’in motar ta ce, “Na san ya girmeku, amman kun fishi hankali!

Gashi ke da A’ish. Ku ja Yaran ku je ku jirani a mota gani nan zuwa.”

Har suka fice yana nan a tsaye bai motsa ba dan haka ta daka mishi tsawa ta ce. “Bisu kaima ka je ka jirani!

Saura kuma idan na fito in ji sabon labari”.

Yana fita ta nemi guri ta zauna. Da kyar da sid’in goshi ta lallab’a principal d’in, dan zuciyarshi ta zo wuya game da lamarin Muhammad Arshaad….

Wani abun mamakin tana fita ta tarar da wani sabon damben!

Ko ba a fad’a mata ba ta san waye. Tun kafin ta k’arasa ta hangoshi akan ruwan cikin wani almajiri yanata kimarshi, d’ayan almajirin kuma yana kanshi yana dukan shi amman ko a jikin sa.

Da kyar da taimakon wasu samari aka janyeshi daga kan almajirin da ya danne dan shi d’ayan almajirin yana hangota ya matsa gefe.

Sosai kuwa ya yiwa almajirin jina jina dan dama a fusace ya ke su kuma suka tab’osa.

Sai da ta d’an duddubashi ta ga ba wata matsala tukunna ta basu kud’i ta had’asu da samarin da suka raba damben ta ce ‘su taimaka su kaisu chemist tana da Yara k’ananu a mota’ daga nan ta basu hak’uri ta ce “su bisu su tafi chemist aje ayi masa dressing.” Daga nan Arshaad ya shiga motar, ta ja suka wuce, daman su Anum ana fara fad’an suka tura su Abbakar suka hana su fita suka rufe motar ba wanda ya fito a cikin su balle a had’a da shi.

Gidan Jalilan da bata je ba kenan, haka ta kama hanyar estate da su tana mamakin Arshaad, chan wani murmushi ya sub’uce mata, a hankali ta girgiza kanta, a ranta ta ce. “Sai dai ba d’an Sakina da Auwal ba”.

K’ala! Ba ta ce mishi ba. Driving d’inta kawai take yi dan a mugun takure
take jinta.

Tun da Yaron ya ga an zo gidansu ta lura da yadda yad’an tsorata, aikuwa tana gama parking a compound jikinshi ya fara karkarwa ya ce, “Ummi dan Allah kar ki gayawa Ammi komai.”

Ko kallonshi Huda bata yi ba ta ce “Ai naga ni ka rainani!

Jiyan nan ka gama yi min alk’awari amman fad’a har biyu yau kad’ai?

Haba Arshaad!”

Shiruu ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta ce “Ka san wani abu?” Bata jira ya Bata amsa ba ta ce “Na ma daina kiran ka da ‘Arshaad’ daga yau dan baka yi halin mai sunan ka ba wallahi, dan haka chanja
maka suna zan yi. In maidaka mai sunan me gadi! za ka sha mamaki.”

Takaici da zafin zuciya dan har yanzu fushi yake da waenda sukai fad’a yau bai gama hucewa ba
yasa ya fashe da kuka.

Daidai nan, Auwal Aslam da Arshaad suka shigo compound d’in, suna hira suna raha da dariya.
Arshaad, yad’an yi k’iba kad’an. Auwal kuma ya tara k’asumba da gemu kamu d’aya.

Aslam kam ba abunda ya k’ara ba abunda ya rage.

Tun kafin su k’araso Yaron ya tafi wajen Arshaad da gudu ya fad’a jikinshi ya ce
“Uncle kaga wai Ummi za ta maidani mai sunan me gadi!”

Sai da sukayi dariya k’asa k’asa tukunna Arshaad d’in ya d’an b’ata rai ya d’auke shi ya ce “Eh to.
Ni na bata shawara saboda naga ka cika fad’a sosai.”

Ai kuwa nan ya rikice da kuka.

Dariya kawai Aslam da Auwal suka yi sukai gaba suka barsu.

Sai da Aslam ya k’arasa wajen Huda ya d’an shafa fuskarta da tirtsetsen cikin ta tukun ya ce “Baki je wajen Jalilan ba kenan”

Sai da tad’an kalli Arshaad da takwaranshi tukunna ta ce, Abhu,.

Gaskiya ya kamata yau a saka Yaron nan a gaba a yi mishi fad’a sosai wallahi, saboda shi na dawo, dambe har da almajirai a waje sabida Allah.”

A hankali Auwal wanda ya d’auka mai sunan Dad ya ce, “Mu je ciki yau inga har duka sai ya sha”
Ya fad’i hakan yana mai wucewa ciki.

Dariya Aslam ya yi ya ce
“Kiga yadda yake wani had’e rai kamar ba a wajen shi ya gado ba”

“Um um fa! Yarintar shi kad’ai ka gani, baka san na mamansa ba”
Hudan ta bashi amsa.

Murmushi duk suka yi Huda ta wuce shi kuma ya juya wajen su A’ish waenda suka gama kwasar lunch box da jakankunan su.

Murmushi ya yi ya d’aga A’ish sama ya ce, “Mamana ya school ke ba kya fad’a ai ko?”
Sai kuma da sauri ya sauk’eta ya d’auki Anum yana cewa “sorry kakata
yi hak’uri na manta na yi alk’awarin yau ke zan fara kulawa.”

Da d’an k’arfi Huda ta ce, Kar ki yarda ya yi miki dad’in baki”. Tana mai wucewa
bayan ta kamo hannun Abbakar k’anin su Arshaad wanda yake a kindergarten suka shige ciki…

Sakina taso ta yi mishi shegen duka bayan ta gama jin bayanin abunda ya yi yau
dan ta zo wuya da halinshi amman sai Aslam ya jata gefe ya yi mata Nasiha..

Nutsatsen fad’a sosai suka taru suka yi mishi dan har Jihad Arshaad ya kira ta zo itama saboda Yaron yad’an shak’u da ita itama dan tun yana zuwa hutu wajen Arshaad a Uk suke video call da ita, lokacin da su Sakina suka tafi course d’insu kuma a gidansa ma ya zauna gaba d’aya ko da yayi aurenma tare suke har lokacin da suka dawo Nigeria tukun ya gudu gidan su Huda. Dan sam baya san zama waje d’aya da Ammi
saboda ya san zai yi laifi itakuma zata dake shi ta yi fushi da shi,duk da yanayin rigimarshi amman yana tsananin k’aunar iyayenshi shiyasa baya son yaga tana fushi da shi. Sannan baya son fad’a da duka.

Haka nan suka had’u su shidda! Da turanci da Hausa da larabci duk aka yi mishi fad’an.
Kuma da alamu fad’an ya shige shi sosai. Tun daga ranar an d’an samu ya nutsu amman ba a yi cikakken wata d’aya ba ya koma ruwa dan haka kawai suka bishi da addua.

Sai da bikin su Shuraim da Sumayya ya rage saura sati tukunna Aaima suka zo
dan a Abuja itama take tun aurenta. Ya’yanta uku biyu maza Farouk da Bashir sai auta Aisha.

Tun aurensu har kawo yanzu cikin kwanciyar hankali suke sai dai y’ar rigimar Mata da Miji wanda wannan normal ne a ko wanne aure.

Sai da Ya Ja’afar ya yi shekara biyar tukunna aka samu ya dawo daidai, idan ka ganshi yanzu ya nutsu sosai kamar ba shi ba.

Yana fitowa Junaidu ya bashi jari aka nema mishi mata ya yi aure shima y’ar bazawarar da Baba ya aura y’ar garin Katsina dutsanma bafulatana.

Umma har yau tana nan jiya i yau! A nan gidan Baba da Junaidu ya rushe ya sayi filin bayansu ya had’e ya yi musu ginin zamani take itama, amman b’angarenta daban, ita da masu aikin da Junaidu ya d’auko suke kula da ita.

Wani lokacin Huda idan ta je dubata har kuka take yi saboda Umma ta zama abun tausayi. Duk k’asar da take ji da kwararrun likitoci Junaidu sai da ya kaita…an yi maganin Hausa da turanci amman har yau babu ci gaba sai ma abun da ya k’aru dan wasu lokutan har duka take yi.

Anty Zainab itama bata koma gidan Mijinta ba! Ganin tana zaune haka ba wanda ya fito mata yasa itama Junaidun ya bata nata jarin suke zaune ita da Baaba Talatu a gidan Kaka wanda nan ma ya gyara musu sosai.

Idan ka ga Jalila ba zaka ce ta tab’a yin rashin ji ba!

Ta nutsu sosai. Bayan aurenta sai da ta yi sauk’a yanzu haka a islamiyyar da Mijinta ya bud’e take koyarwa.

Ta rungumi Mama a matsayin Uwa. Sakina da Huda da Sumayya kuma a matsayin y’an uwa
sannan ta rik’e Mijinta wanda ta fahimci shine gatanta kuma shine masoyinta na gaskiya.

Tabbas Jalila tana cikin matan da za ace sun yi sa’ar samun Miji mai tsananin k’auna da tausayinsu tsakani da Allah.

Wani lokacin har ce mishi take yi ‘ya k’ara aure’ saboda duba da a yanda ya sameta ita!
Amman duk sanda ta yi mishi wannan zancen sai taga fushinshi a cewarshi ‘shi ita yake so ba wani abun ba kuma ya tabbatar ba zai tab’a iya had’ata da wata y’a mace a zuciyarshi ba.’

Ibraheem irin mazan nan ne masu zuciya. Mahaifiyarsa ta rasu itama two years back k’anwarsa ma ta dad’e da yin aure.

Dukda Ubangiji ya rubuta mishi rayuwar middle class zai yi, hakan bai hanashi siya mata y’ar k’aramar mota ta mata ba!

Sannan ya tashi daga gidan Junaidu ya yi gidansa.

Ita ma kuma tana business d’in kaya daga India Dubai wanda Junaidu ne yake kawomata duk zuwanshi, itanma kuma ta tab’a zuwa sau d’aya da kanta ta je ta sari kayan ta dawo bayan Hajji da Umara da Junaidun ya biya musu suka je ita da Mijinta tun farko farkon aurensu.

Ya’yan ta biyu mace da Namiji, ta farkon sunanta Maryam mai sunan Huda tana ce mata didi
na biyun kuma mai sunan Kaka, Bashir.

Sai kuma tsohon cikin jikinta maybe su haihu tare da Huda ko kuma Huda ta rigata.
Tsakaninta da Aaima akwai zaman lafiya da friendship da mutantanta juna ga zumunci.

Tunda aka fara bikin su Sumayya Hudan take nak’uda sama sama.

Sanin da ta yi lokacin haihuwar ta bai yi ba yasa kawai ta yi shiru a tunaninta juyi ne!

Sai dai ranar da za a kawo Amarya jikinta ya motsa sosai!

Dama Sakina ta fahimceta tun jiya dan haka ta yi rushing nata zuwa asibiti ba tare da ta gayawa Aslam ba dan ya ce ‘ba a nan yake so ta haihu ba, tunnda haihuwa ta uku tana zuwa da complications gara ya fita da ita waje’. Kuma ta san in dai ya ji Huda tana nak’uda ne amman ta yi shiru to zai ji haushi sosai.

Tun kafin su k’arasa asibitin faya ta fashe, ko minti talatin baayi da shigar da itaba ta haifo y’ay’anta biyu kyawawa maza masu kama da Aslam sak.

Sai after one week tukunna Granpa ya had’a walima iya family kawai na welcoming Sumayya da twins waenda suka ci sunan Arshaad da Auwal (Abhi da dada).

Takanas Granpa ya aikawa su Shuwa nasu invitation d’in.

A compound d’in tsakar gidanshi aka yi decoration manya manyan dining table masu seat 20 guda biyu aka k’awata. D’aya na manya d’ayan kuma na Yara jikokin gidan.

Wajen 5:00pm kowa ya hallara, tun rasuwar Kaka Granpa ya zama shine Abokin Madu,
shiri suke yi sosai. Allah ya arawa Granpa tsahon rai tubarkallah, sai dai fa ya tsufa sosai dan baya ma iya takawa a kan wheelchair yake.

Haka aka fara gabatar da walimar bayan Madu ya bud’e taro da addua.

In ka gansu kowa cikin farin ciki da walwala da annashuwa
Mama na zaune kusa da Abba, Mom da Anty Kaulat sun saka Daddy a tsakiya
Mommy a kusa da Dad, Hudan kusa da Aslam sun d’au twins d’insu a hannu
Arshaad da Jihad Sakina da Auwal Aaima da Junaidu, sai Jalila da Mijinta.

D’ayan dinning d’in kuma Yaran ne tun daga kan Arshaad har kan Abbakar Saddik.

Ana gama cin abincin Granpa ya yi gyaran murya ya ce “Hudan Maryam Aisha inaso in sake baku hak’uri” Da sauri Madu ya ce “Dan Allah ka yi shiru. Yanzu haka kana ganin akwai grudges?
Komai ya wuce, mu yafi juna. Allah ya yafe maana.”

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana kallonsu Mama one by one. Cikin had’in baki Mama da Mommy suka ce “Granpa iyaye basa laifi a wajen y’ay’ansu, komai ya wuce.”

A hankali Huda itama ta ce, “Mune za mu nemi yafiya da albarkar ka. Komai ya wuce
ka manta komai kamar bai faru ba! Ka sanya mana albarka dan mu samu haske a rayuwarmu.”

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e sannan ya russunar da kanshi k’arasa
yana jin yadda hawaye suka fara taruwa a tsofaffin idanuwanshi da suka ga jiya suka ga yau.

Cikin zolaya Madu ya ce, “Stop being emotional mana old man!”

Da sauri Granpa ya d’ago ya ce “Ai ka fini tsufa!”

Dariya aka saka saboda ansan dama sun saba, duk cikin su, biyun ba wanda yake so d’an uwanshi ya ce mishi tsoho!

Watarana ma Granpa cewa yake yi Madu ya girmeshi kuma ya tubure! Dole a hak’ura a tafi akan an yarda Madun ya girmeshi.

A hankali Huda da Mama suke kallon family d’in nasu. Tun daga kan tebur d’in su har na su Arshaad
kowa kawai dariya da farin ciki yake yi.

A tare Mama da Huda suka share kwallar farin cikin da ta zubo musu ba tare da kowa ya gani ba
sannan a tare a hankali suka ce “ALHAMDULILLAH!”.

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

Na godewa Allah da ya bani ikon kammala littafina mai suna ‘So da Buri’.

Kuskuren da na yi a ciki Allah Ubangiji ka yafemin, darussan da suke a ciki kuma Ubangiji kasa mu amfana.

Godiya ta musamman tare da fatan alkhairi ga Anty Aisha Gadanya, Ina godiya kwarai Anty, alkhairin Allah ya Isar miki a duk inda kike.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 73

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×