Skip to content
Part 53 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar, tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina. Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba.”

“To” Kawai Sakina tace, tana mai sake goge fuskarta sannan ta koma gefe ta fara warware laffayar jikinta da d’aurin d’ankwalin dake kanta.
Sai da ya rage daga ita sai long camisole d’inta wadda ta saka a ciki mai dogon hannu yayinda dogon gashinta ya kwanta a gadon bayanta sannan ta fara k’ok’arin kiran Arshaad.

Tayi mishi misscalls sun fi ashirin amman shiru. Dan haka nan da nan hankalinta ya sake tashi. Tun jiya take danne zuciyarta take k’ok’arin kawar da maganar da Aaima ta gaya mata a cikin kwakwalwarta amman kuma attitude d’in Arshaad da k’in zuwan shi a yanzu ya yi matuk’ar bata tsoro.
Ba wadda take jin fargabar taji wannan batu irin Hudan shiyasa jiya ta kwana Sallah akan Allah yasa maganar Aaima ta zama k’arya
idan kuma gaskiyace Allah yasa su Abba su gyara lamarin cikin sauk’i.
Gabad’aya hankalinta a tashe yake dauriya ce kawai take yi, tana kuma k’ok’arin taga ba wanda ta bari ya ma ji zancen har a samu a gyara lamarin in sha Allah. Ganin Arshaad d’in bashi da niyyar amsa ta ne yasa kawai ta kira Auwal dan taji me ke faruwa
a ina aka tsaya.

Shi sai a bakinta ma yake jin wai ‘Arshaad d’in bai je ba’. Saboda shi suna asibiti.

Ganin kamar bai san me yake faruwa ba ya sanya taja bakinta tayi shiru
saboda ance yawan yayata magana kan iya tabbatar da gasgatuwar ta. Dan haka kawai sai tace mishi
“ya duba musu Arshaad din pls”
Daga haka suka yi sallama.

Daman shima yana da shirinshi zai je wajen. So yanzu zai duba Arshaad d’in sai su wuce tare kawai dan haka ya cewa Dad “Bara yaje gida, Sakina ta kira shi wai har yanzu Arshaad bai k’arasa ba.” “to” kawai Dad d’in yace masa. Yana fita shima Dad din ya d’au waya ya kira Gwaggo Asabe yace
“Dan Allah tazo ta ji da Ummi.
Zai yiwa drivern da zai kawota kwatancen asibitin da suke.”

Drivern da ya kawota (Gwaggwo Asabe) shi ya maidashi mansion d’in.
Yana zuwa ya tarar da Daddy ya shirya chap yana jiranshi da akwatuna dozen biyu sun sha decoration sai kuma basket na gift guda biyar, da akwatunan uwa uba gwaggwo da kawu. Duk sun had’a. Tun sassafe Mommy ta aiko da kayan shi kuma ya duba ya tabbatar komai dai dai.

Sai da aka gama loda kayayyakin a motoci wajen goma tukunna Abba ya fito da shirin shi shima da alama raka su zai yi!

Dad, yana shirin shiga mota har driver ya bud’e mishi k’ofar motar ya hango tahowar Abba! Wani takaici ne ya d’ebesa, bai san lokacin da ya daka masa tsawa ba! Ya ce “Idan ka k’araso nan wallahi sai mun kwashi y’an kallo ni da kai! Ka ji dai na rantse wallahi!!”
Ya k’arashe maganar yana mishi nuni da yatsar shi manuniya yana nuna sama.

Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kafin yace “Dad nima fa rakaku zan y…”

Cikin fushi Dad d’in ya ce “Kaga mota nan, zo ka shiga! Amman direct
Asibitin da aka kwantar da Ummi zaka je Idan kuma ba haka ba to ka koma ka zauna a ciki. Zab’i d’aya!”

idanuwa direbobin da masu aikin suka tsura musu. Ganin da Abba yayi har sun fara kwasar y’an kallon kamar yadda Dad d’in ya ambata ne yasa kawai ya juya ya koma ciki ranshi a mugun b’ace!.

Tsaki Dad yayi ya shige motar
yana mai cewa “ba za ku haukata ni ba, wallahi!”.

Shi dai Daddy shiga yayi ya zauna a kusa da shi, yana son tambayar shi
wata zuciyar kuma sai ta bashi shawarar ya bari ya Dad d’in ya d’an sauk’o tukunna sai suyi magana.
A haka drivern ya ja su suka nufi Gandun Albasa. Daddy yana mamakin meye haka yake damun Dad? Dan tabbas ya san akwai abunda aka yi mishi.

GANDUN ALBASA.

Baaba Talatu tana fita harabar gidan ta tarar gurin har ya fara kachamewa!
Dan bayan Sakina ta bar wajen Umma da Anty Zainab kan Ummu suka dawo
wai “ai ita ce bata yi mata tarbiyya mai kyau ba shiyasa ta raina manya har haka…” Ga kuma wannan tsohuwa ita ma ta kafa ta tsare ta ce “Sai Ango ya fito tukunna za a fara gabatar da komai!” Yayin da Ummu da wasu cousins d’inta suke ta k’ok’arin ganin sun yayyafa wa lamarin ruwa amman abun ya faskara!.

Baaba Talatu ce ta k’arasa ta ja wannan tsohuwar gefe suka had’u ita da Shuwa suna mata magana k’asa k’asa. Ganin kamar ana shirin fara traditional event d’in cikin kwanciyar hankali ne yasanya Umma ta sake cewa “Nima fa kamar uwa nake a wajen Hudan! Dan haka ba zan bari kowa ya tab’a ta ba har sai Angon nata ya k’araso, idan kuma fasawa yayi ne to kawai a fito a fad’a wa mutane sai a fasa sakata a lallen, dan ba girman mu bane mu tsaya muna yiwa mutane wasa da hankali! Ko ya kuka gani?”
Ta k’arashe maganar tana kallon cousins d’in Ummu waenda suke gefen ta! Ba su kad’ai ba kusan kaff wajen babu wanda bai ji abinda tace ba hatta su Shuwa.

“Ga Angon nan”. Muryar Mommy wadda suka fito su uku yanzu ta daki dodon kunnuwansu! Da sauri Mama da Aslam suka kalleta! Ba tare da ta kalle su ba ta kama hannun Aslam ta fara janshi Mama na binsu a baya kamar rak’umi da akala shi kuma yana binta!. Bata cikashi ba sai da ta kaishi gefen Hudan sannan ta zaunar da shi.

Da sauri Ummu ta matso k’asa k’asa ta ce “Mommy a Al’ada fa dole sai Angon zai. Cikin katseta Mommy tace “A addini fa?” Bata jira Ummu ta bata amsa ba ta sake ce mata “Kalla nan kinga” Tayi maganar tana nuna mata Huda wadda sai a lokacin Ummu ta lura da yanda mayafinta ya jik’e sharkaf! Wanda kana gani ka san ruwan hawaye ne, Mommy bata jira jin me zata ce ba ta ci gaba da yi mata magana k’asa k’asa irin na masu hankali, ta ce, “Saboda ita kawai ki bari ayi a gama! Na tabbatar ba wai rashin zuwan Arshaad kad’ai bane ya saka ta kuka ba! Har da maganganun matar nan! Tun muna parlourn bayan kun nan muke juyo komai. Dan Allah kar kice a’a! Kalla kiga mutane kowa ya zuba ido an fara k’ananun maganganu, na tabbatar in dai ba Angon suka gani ba to haka za a tashi ana gulmace gulmace shima kuma sai idan an samu waenchan matan sun bari anyi d’in kenan. Na tabbatar mutane k’alilan ne kuma na jikinku sosai suka san ba Arshaad bane wannan, ba kowa ne zai gane ba
so dan Allah ki kwantar da hankalinki ayi abun nan a gama without any more dramas. Saka lalle ai ba d’aurin aure bane ba, ba komai kawai bidi’a ce so mu bisu kawai ayi a gama.” Tana gama fad’an haka ta juya ga jamaar wajen tace “Kuyi hak’uri mun yi latti wani d’an uzuri ne ya tsaida mu!
Sunana Hajiya Aisha Maman Ango, mun gode kwarai da zuwanku dan taya mu farin ciki.” Daga nan ta juya ta cewa Ummu, “Ni zan fara ko ke?”
Da murmushi kwance akan fuskarta.

Kallonta kawai suke yi daga Ummu har Mama.

Mama da Ummu sun so hana mai video coverage da pics d’auka amman ganin yanda hankalin kowa yake a kansu da kuma Mommy wadda ta ce ‘su bari kawai tunda ga wasu ma a gefe suna ta d’auka da waya’ ne ya sanya kawai suka hak’ura.
K’awayen su Huda kuwa abun ba k’aramin d’aure musu kai yayi ba dan tabbas sun san wannan ba da shi aka yi cocktail jiya ba, kuma ba shine a pre wedding ba! A haka dai suka bar maganar akan in an tashi za suni komai a bakin Sakina.

Aslam kuwa so yake ya mik’e amman sam ya kasa! Ya rasa dalilitun da yake bai tab’a jin fargaba irin wadda yake ciki a halin yanzu ba! Ana cewa k’afafuwa da gangar jikin mutun suna sagewa ya koma kamar gunki bai tab’a yarda da hakan ba sai yau da ya faru a kansa dan hatta kwayar idanunsa ya kasa juyawa, so yake ya runtse idanuwanshi ya samu ya dedeta zuciyar shi amman sam ya kasa!
Yana nan a haka yaji Ummu na rufa mishi wata jibgegiyar alkyabba akan jamfar jikinshi Akan hular kanshi
Ummu ta d’aura mishi wani jan kyalle mai tambarin moon a gaba golden colour (Allah yaso suna da extra).
Daga nan ta mik’a mishi wata sanda wadda ta ci ado! Tace masa “ungo, rik’e” Mommy ce ta kama hannunshi ta sanya mishi sandar sannan ta had’a da nata hannun ta maste! Sai a lokacin ya samu nasarar lumshe idanuwanshi
sannan ya d’an bud’e su kad’an yana kallon k’asa.

Ba tare da b’ata lokaci ba aka fara gudanar da alada. Bayan uwar Amarya da uwar Ango sun yi, ragowar jama a suma suka zo suka sanya musu suka basu gift daga nan aka fara serving abinci.

Sai a lokacin Anty Zainab da Umma suka samu suka iya zama. Umma so take yi ta sake mik’ewa tsaye ta ce
“To Ina y’an unwan Ango!?” ta sake creating scene amman sam ta kasa dan in banda dishi dishi babu abunda take gani! A ranta ta shiga aiyyana. Tabbas sai taci uwar malam ado! Wallahi sai ta saka an yi mishi yasin mai walk’iya!
Ba Malami ba ko uban waye shi. Kuma sai ya bata kud’inta. Jiya jiyan nan fa ta sake komawa wajenshi dan ta sake nanata mishi, shi kuma ya tabbatar mata da “babu aure tsakanin Hudan da Arshaad ya riga ya gama aiki
kuma ya buga k’asa ya tabbatar ba Mijin ta bane ba sannan ya ingiza zuciyar iyayen shi (Arshaad) ya rura wutar k’iyayyar Hudan a cikinta
ta yadda ba zasu tab’a bari ayi auren ba musamman ma Mahaifiyarshi (Arshaad).” Amman kalli yadda Maman nasa take ta jan Hudan a jiki,
anyi musu hoto yafi kala nawa tare sai faman fara’a take yi tana washe baki kana ganinta ka san tana cikin tsantsar farin ciki! Inaaaaa!!!!! Taya ma zata tsaya ta yarda Hudan ta auri wannan
No1 kyakkyawan da ita tunda take a rayuwarta ko a telebijin bata tab’a ganin mai kyawunsa ba! Ga uban kud’i ga kyau kamar aljani Allah sarki Jalilan ta dole ta mutu akan soyayyar Arshaad, ai kuwa idan zata yi yawo tsirara wallahi sai ta raba auren Huda da Arshaad ko sama da k’asa zasu had’e Wallahi sai dai in rabo ya kasheta akan dai ta zauna ta nad’i wannan abun takaicin da ta san k’arshe in dai bata d’auki mataki ba to shine ajalinta! Kuma ko yana so ko baya so sai ya auri Jalila! Wannan alkawari ne ta d’aukarwa Jalila da ita kanta! D’an halal ka fasa.

Anty Zainab ce ta tab’o ta
wanda hakan ne ya katse mata tunani.
Da kyar ta iya motsa wuyanta dan ji take kamar ba jini da rai a dukkannin ilahirin jikinta. Suna had’a ido taga itama Anty Zainab d’in idanuwanta sun kad’a sun yi jazir! Kafin Umman tace wani abu, taji tace “Sadiya taso mu tafi, kai na ciwo yake yi min”

Suna shirin mik’ewa suka fara jiyo gud’a daga parlourn Madu sai a sannan ma suka lura Shuwa da Baaba Talatu da wasu y’an tsirrun mutane basa wajen a bakin matan wajen suka ji an fara k’us k’us d’in “Ashe tun d’azu mazan gidan Ango suka zo sun kawo lefe yanzu suka wuce da yake falon Madu yana da k’ofar shiga da fita ta waje, shiyasa har suka zo suka tafi ba wanda ya sani. Sai da suka tafi yanzu aka ce aje a fito da shi” Suna ji anata k’usk’us d’in “ai motocin da suka zo da su ma kansu abun kallo ne! Gasu kana ganinsu kaga manyan mutanen da kud’i ya zaunamawa”

Da kyar Umma take iya jan numfashi, dan ji take yi gaba d’aya iskar wajen bata isarta! Ummu ce ta d’an matso su kafin tace “Umma kuzo muje a fito da lefen nan kowa ya gani ko?”

Anty Zainab ce ta iya ce mata “eh”
Itan ma da kyar, daga haka ta mik’e ta d’an dafa Umma kana tace “Muje Sadiya” Da kyar ta iya mik’ewa k’afafun ta suna rawa suka jera ita da Anty Zainab suka bi bayan Ummu suka yi parlourn b’aki.

Mutane kam wasu basu ma samu damar shiga ba dan akwatunan sun cike parlourn tap! Ganin kowa cirko cirko a tsaye iya y’an k’alilan kuma na a ciki suna mik’owa ana fitowa da shi ne yasa suma suka ja suka tsaya a gefe
kai kana ganinsu ka san basa cikin hayyacin su.

Ta gabansu aka fara wucewa da akwatuna nan kuwa suka maida hankali suka hau k’irgawa! Ana wucewa da goma Umma ta nemi d’an dakalin slop ta zauna dan jiri ne taji yaana d’ibarta ba na wasaba! A tunaninta su kenan amman ga mamakinta sai taga ana ta sake fito da wasu! Ganin ta k’irga ashirin da d’aya basu k’are ba ya sanya ta janyo Anty Zainab wadda itama tayi mutuwar tsaye kafin tace, “Zainab zo mu bar wajen nan, tabbas kwakwalwa ta ta d’an samu matsala sannan bana gani sosai! Gani nake yi anata wucewa da akwatuna fa har yanzu basu k’are ba.”
Da sauri Anty Zainab d’in tad’an dafa ta dan yanda take magana da sauri kuma da k’arfi kamar wata zararra ya sanya mutane har sun fara d’an juyowa ana kallonsu. A hankali tace mata “Ba idonki ba ne! Ashirin da hud’u ne cass! Gasu chan ragowar ukun Sai kuma waenchan baskets d’in da ban san na menene ba”.Bata ida rufe bakinta ba aka fara fito da na Gwaggo da Kawu. Ai kuwa Umma bata san lokacin da ta mik’e tsaye ba tace
“Amman dai Maryam sayar da y’ar nan tata tayi ko!? Haba mana wannan abu kuma ai ya zama hauka! Meye hakan? Me suke so su nuna?”

Cikin takaici Anty Zainab ta ce
“Wallahi Sadiya za kiyi hanyarki nima inyi tawa har a tashi daga bikin nan gaskiya! Maganar Allah kenan, haba mana! So kika mu zama abun kwatance? Sai wasu abubuwa kike yi kamar tab’abb’iya? Ki yi controlling kanki mana Haba?” Ta fad’i hakan tana mai wucewa ta barta a tsaye nan dan a yadda take jin zuciyarta yanzu, tsaf zata iya sauk’e ruwan bala’i da fushinta akan matan dake k’ok’arin maidasu telebijin.

Sai da Umma taga an gama fito da kayan an watse daga wajen sannan ta samu da kyar taja y’an k’afafuwanta ta isa harabar tsakar gidan.

Banda gud’a da hayaniyar mata ba abunda yake tashi A lokacin har an bud’e akwatunan farko an fara dubawa.

Sai a sannan ne Aslam ya samu ya tatttaro nutsuwar shi da d’an ragowar kuzarinsa ya mik’e tsaye! Yana mik’ewa Ummu da Mommy suka k’arasa wajensu. D’an b’ata rai yayi kafin yace “Mommy zan wuce
wannan bidi’ar bada ni ba gaskiya”
Murmushi Mommy tayi ta shafa kanshi kafin ta juyo ta cewa Ummu
“Zai iya tafiya?”

Murmushi Ummun tayi kafin tace “eh, zai iya ai an gama komai” A hankali yace mata, “Sai anjima”. Cikin kulawa ta ce “Mun gode kwarai Aslam, mun gode.”

Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e
daga nan ya ajjiye sandar hannunshi a gefe ya juya daidai nan su Sudais suma suka mik’e, Shuraim yana ta b’ata rai shi ala dole ya gaji.

Ummu da Mommy ne suka yi musu rakiya har waje, shi da Sudais da Shuraim bayan ya kira drivern da zai maida Mommy gida yace masa ya taho yanzun. Mutane in banda kallonsu ba abunda suke yi sunata yaba kyawun Angon Gashi bai wani zak’e ba irin yadda Angwayen yanzu suke yi! Instead shi ya kama kanshi matuk’a, hakan kuwa ba k’aramin burge jamaar wajen yayi ba.

Su Mommy suna komawa suka tarar anata ware lefe an yi filla filla ana gani.

Tun daga kan atamfofi Umma ta raina kanta. Zata iya cewa tunda Laraba ta kawota duniya bata taba shiga tashin hankali irin na wannan lokacin ba!
Hankalinta bai gama tashi ba sai da aka zo kan akwatunan jewelry’s
kit kit waenda aka ware guda biyu aka shak’e taff da sark’a da y’an kunne
Na farkon fashion ne Na biyun kuwa gold ne zalla! Matar dake gefen ta ce taji tana cewa. “Ai dama su family d’in MT haka suke lefe duk matan gidan da aka tashi aurar su ko wacce sai da aka yi mata kit d’in gold! Yanzu kuma wannan kinga shine jika na farko da ya yi aure. Kaii amman fa wannan Yarinyar ta tako, gaskiya tayi goshi
Allah yasa y’ay’anmu a danshinta. Zata sha gata ba kad’an ba! Naji ma kamar ance wai k’asar zai bari ma da ita gaba d’aya!”.

Tabbas zuwa wannan lokacin Umma ta daina ganin komai in banda duhu! Maganar ma sama sama ta dawo ji
daga nan kuma jinta da ganinta suka d’auke d’iff!!

Mutanen wajen kowa hankalinshi yana kan kallon lefe mai abun mamaki da alaajabi. Saboda kaff cikin su babu wadda zata ce ta tab’a ganin lefe kwatan kwacin wannan.

Dimmm!!! K’arar fad’uwar Umma ta sa jamar dake kurkusa da ita zabura suka jujjuyo. “Subahanallah! Mai ya sameta!! D’in da aketa maimaitawa ne
ya janyo hankalin mutanen gurin kaff kowa akayi kanta akai mata rumfa.

A zaune Auwal ya tadda shi,
a d’akinsa. Ya jinginar da kanshi a jikin gadon ya lumshe idanuwanshi fuskar shi tayi jajawur! Kana ganinshi ka san yana cikin tashin hankali.

Auwal bai damu da yanayin shi ba dan shi ganinsa ma da yayi a zaune ko shirin tafiya bayayi shi yafi komai b’ata masa rai! Cikin muryar b’acin rai ya ce “Haba Arshaad! Ka sa mutane sun tara jama’a kai kawai ake jira kazo ka wani zauna anan, me kake jira?
Gaka nan dai a shirye tsaf! Mai kuma ya hana ka tafiya tun d’azun? Nace maka ina zan taho karka jira ni.
Ka san yanda hankalinsu ya tashi kuwa? Dagaj in muryar Sakina ka san ba lafiya ba! Taso mu tafi da sauri dallah”

Wata nannauyar ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin a hankali ya samu ya d’an bud’e lumsassun dogayen idanuwanshi, sai da Auwal ya d’an zabura sakamokon had’a ido da suka yi da Arshaad d’in! Da kyar ake iya hango maroon eye balls d’inshi da suka b’uya cikin jajawur d’in idanun nasa. Sai a lokacin Auwal ya lura da yanda jijiyoyin kanshi suka fito sukai rud’u rud’u! Da sauri ya k’arasa ya zxauna a gefen shi kafin yace “Lafiya kake?? Me ya sameka haka?” Ya jera mishi tambayoyin duk ya rikice.

Banda ajiyar zuciya ba abunda Arshaad yake ta faman sauk’ewa yama kasa yi mishi magana da kyar ya samu yace “Mammy ce ta.” Sai kuma yayi shiru. Cikin firgici da tsoro Auwal yace
“Ta hana ka zuwa?? Lumshe ido Arshaad yayi kafin a hankali yace
“Har ma auren! Ta ce idan aka d’aura sai ta tsine min!”

A zabure Auwal ya mik’e kafin ya ce
“Innalillahi wa innailaihirrajiun!
Shine kuma ka zauna za ka kashe kanka haka? Zama ai bai ganmu ba!
Bara in je in samu su Dad in yi musu bayani, idan ta kama har Granpa sai a sa a case d’in. Mai yasa Mammy zata yi mana haka?” Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.

A hankali Arshaad d’in yace “Ba wanda bai sani ba. Kowa ya san da case d’innan. Har mamanta da sisters d’inta duk an bata hak’uri amman tak’i hak’ura.”

Wata kakkausar ajiyar zuciya Auwal d’in ya sauk’e kafin yace “Ya aka yi Mammyn ta sani? Last time da naje na dubasu naga kamar duk basu san da zancen ba. Na san dama suna iya causing problems shiyasa nima ban yi gigin fad’a musu komai ba! Ko maybe Ummi da aka kawo ce ta kirasu ta gaya musu?”

Da d’an mamaki Arshaad d’in yake kallon shi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace, “Baka had’u da Mom ba hala?
Sun dawo jiya. All of them”

Da mamamki shima Auwal d’in yake kallonshi ya ma kasa cewa komai.

A hankali Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Auwal do me a favour. Ka kira Sakina, ina so kayi mata bayanin komai amman ka ce kar ta fad’awa kowa kawai a san yadda zaai a gudanar da event d’in ba tare da an jira ni ba! Yanzu na san Mammy idonta a kaina yake dan tun d’azu nake lura tana ta turo Aaima tana mata patrol so ba zan iya fita ba. Sakina is smart she’ll know what to do yanzun
In shaa Allah ni kuma anjima da daddare za mu je Ina son ganin Hudan
na san abunda zan yi. For now amman kawai ka lallab’a mun Sakina tayi handling komai, kafin nan da anjima.”

Cike da gamsuwa Auwal d’in ya d’aga kai alamar to sannan ya zaro waya ya fara kiran Sakina. Tun lokacin da aka fara rangad’a gud’a taji dan haka ta mik’e ta lek’a ta windown d’akin Shuwa. Ji tayi kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha sakamokon hango su su biyu a zaune da ta yi! Bata ganin fuskar su especially Huda da har yanzu tata fuskar a lullub’e take sannan windown a rufe ne kuma sun yi mata nesa. Bata san lokacin da hawayen farin ciki suka zubo mata ba!
Tana gani yadda mata suke zuwa suna d’an d’aga mayafin kad’an suna shafa mata da hannuwanta shi kuma a tafukan hannunshi da goshinsa ake shafawa sannan su ajjiye musu gift a cikin d’an kwanon da aka ajjiye wasu kuma kud’i. Ba k’aramin burgeta suka yi ba, banda kalmar ‘Alhamdulillah’ ba abunda taketa nanata a ranta tana mamakin dalilin da ya sanya Aaima karkacewa ta gilla mata wannan uwar k’aryar haka. Wata zuciyar kuma tace maybe an gyara abunne Mammyn ta sauk’o cikin kawar da tunanin a ranta tace “Chan ta matse musu”. Sannan ta hau raya yadda zata yiwa Arshaad in sun had’u na k’in d’aukar wayarta da yayi.

K’arar wayarta dake kan gado ce ta katse mata tunani dan haka ta isa ta d’auki wayar. Kamar ba zata d’auka ba
ganin sunan Auwal ne sai kuma ta d’anyi murmushi a ranta tace ‘Kar In zama kaza mana’ dan haka ta d’auka ta kara a kunnenta kafin yace komai tace “Gashi chan Ya Arshaad d’in yazo suna zaune ana saka su a lalle.
Thanks for your time” Tana gama fad’in haka ta katse kiran.

Da mamaki suka kalli juna shi da Arshaad dan a hands free wayar take
Shiruu, d’akin ya d’auka chan kuma Auwal yace “Bara inje wajen maybe ko fushi suka yi shiyasa tayi min gatse”

Cikin katseshi Arshaad yace “Kaje wajen Mom mana. Kace bama ka san ta dawo ba bayan a gida d’aya kuka kwana. Kaje wajenta daga nan
ka d’an lallab’ata may be in tasa baki Mammy ta hak’ura.”

Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo yace, “Su kuma fa?”

“Kar ka damu na gama tsara komai, zuwa anjima da daddare za muje in shaa Allah. Zan sameka a gida.”
Cewar Arshaad yana mai maida kanshi da lumshe ido dan kanshi ba k’aramin ciwo yake yi ba amma kuma har ga Allah y’ar maganar da ya samu suka yi da Auwal ya d’an ji sassauci a ranshi.

“Allah ya kaimu”. Shine kawai abunda Auwal yace yana me fita daga d’akin
da waya kare a kunnen shi still yana sake kiran Sakina sai dai har ya tsinke bata d’auka ba.

A tsakiyar main parlourn suka kusa yin karo da Aaima, kasancewar hankalinshi naga wayarshi yana turawa Sakina message. D’agowa yayi yana kallonta itam ma shi take kallo kafin da kyar ta iya cewa “Ya Auwal Ina wuni”. “Fine” kawai yace yana me wuce ta. Da sauri ta sha gabanshi kafin tace “Am dan Allah gida zaka je?”
Maida hankalinshi yayi a wayar kafin yace “Eh” A hankali tace “Owk, d’an jirani plss Mammy ta bani sak’o wajen Mom ina so zan kai mata. Bara in d’auko vail d’ina”. Ba tare da ya kalletaba ya k’arasa kan d’ayan daga cikin kujerun parlourn ya zauna still yana danna wayarshi. Ta fahimci yaren kuramen nashi dan haka ta wuce sama da d’an sauri…

Bayan 5 minutes ta sauk’o! Ta chanza kaya daga atamfar ankon dake jikinta
ta d’aura bak’ar abaya tayi rolling, ta sanya lipstick da powder. Ta yi kyau kuwa ba laifi. Gabanshi tazo ta tsaya sannan tace “muje”. Tun kafin sauk’owarta daman ya san ta taho sakamokon k’amshin turarenta da ya karad’e parlorn! Tana sauk’owa kuwa ya lura da ita amman sai ya kawar da kai. Wai me Aaima take nufi ne?
Ya kasa gane kanta kwana biyun nan! Har magana take mishi ta WhatsApp yanzu. Yana tunawa lokacin da suke tare yasha gaya mata yana matuk’ar son yaga mace da black abaya tayi rolling abun yana burgeshi shiyasa
kusan duk lokacin da zasu fita tare takan yi irin wannan shigar kuma ta san baya son native cloth kwata kwata
Inba riga da wando ba to abaya. “Mu tafi, na shirya”. Muryarta ta katse shi.
Kallonta yake yi tun daga sama har k’asa! Hakan kuwa ba k’aramin dad’i yayi mata ba. A hankali taji yace
“Ina sak’on??” Diriricewa tayi kafin da kyar tace “Yana cikin purse d’innan”
Tayi maganar tana nuna mishi purse d’inta wadda ta saka iya wayarta da lipstick a ciki.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya mik’e yayi gaba. Shi fa har ga Allah kunyar ta yake ji a halin yanzu idan ya tuna irin yadda ya fito mata k’iri k’iri ya fad’a mata abunda yake buk’ata daga gareta da kuma yanda ya furta mata kalmar ‘ba ya k’aunarta’ Wasu abubuwan da yawa da ya yiyyi idan yana tuna su a yanzu sai ya dinga ji kamar k’asa ta tsage ya shiga! Tabbas Daddy yayi gaskiya daman ya tab’a gaya mishi
‘’Akwai ranar dana sani!Ranar da zaka ji inama ana yin reverse ayi maka domin ka samu ka aikata alkhairi ka kuma goge duk wani abun da kayi marar kyau. Ranar tana nan zuwa, ko bayan raina za kace na fad’a maka‘’.
Tabbas kuwa tun kafin aje ko Ina gashi ranar ta zo Ya san dalilin da ya sanya Sakina take gudunshi ta kuma k’i sa! Bai wuce akan tunanin da take yi na alak’ar shi da cikin jikin Jalila ba ne…bai san wanne kalar kallo zata yi masa ba idan taji tabbas cikin nasa ne!
Ballantana kuma azo kan maganar halayyarshi da baya fatan Allah yasa Sakina ta sani! So yake ya gyara komai
ya zama mutumin da ta ambata tana son kasancewa tare da! Gashi already yana da competition, yanzu ahaka ma ta riga ta nuna mishi ta zab’i Ashraff a kansa ina kuma ga idan taji wata magana akanshi! Ya kenan? “Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Itace kalmar da ya ambata yana mai dafa motar shi dan har sun iso bakin motar.

Da sauri Aaima tace “Subahanallah Ya Auwal mai ya faru?” Tana mai matsowa inda yake.

Sai da ya d’an runtse idanunsa kafin ya dawo dai dai tukunna ya samu yace mata “Ba komai, shiga mu tafi” Yana mai zagayawa ya bud’e mazaunin driver ya zauna. Tana shigowa ya tada motar yaja suka fita.

Har suka isa mansion d’in nasu babu wanda ya samu damar furta kalmar ‘a’ a cikin su. Shi ya fara fita daga nan itama ta fito suka nufi ciki.

Suna shiga parlourn suka tarar da Jalila ta d’aura k’afa d’aya kan d’aya ga remote a hannunta tana ta chanja channel. Lumshe idanuwanshi yayi a hankali ya shak’i iska ya furzar sannan ya bud’e idanuwan nashi a hankali a fili yace “My worst regret!!” Ya kasa gaba ya kasa baya.

Aaima ce tayi k’arfin halin k’arasawa tsakiyar parlourn inda Jalilan take
tana kallon ta da d’an mamaki dan kamar bata tab’a ganinta ba.

Fitowar Mom daga kitchen ne ya katse mata tunani har shi Auwal d’in
Uwa mai dad’i suna had’a ido yaji wani sanyi a ranshi. Takawa yayi har inda take yana zuwa ya sa hannu yayi hugging d’inta. Tun a cell Mom take aiyyana kalar abubuwan da zata yiwa Auwal kala kala In Allah ya maidota gida lafiya dukda kuwa tana shakkarshi, babu yadda bata yi mishi shi da Arshaad akan su basu kud’i su samu su fito ba amman suka hana su
saboda suna shakkar Granpa sannan basu san darajar su uba and sun rainasu! Sannan ta dawo amman tun jiya take zuba ido but bataga k’eyarsa ba. A hankali yace “welcome home“
Ta manta rabon da Auwal ya nuna wani affection a kanta irin haka, ba ta san lokacin da wata kwalla ta zubo mata ba, a hankali tasa hannu ta share
tana jin duk wata wutar masifar da ta shirya juye mishi tana sauk’a daga k’irjinta. Muryar Jalila ce ta katsesu jin da d’an k’arfi tace “Adama ina shayin nawa??” Da mamaki Aaiima take kallonta sai kuma ta juya tana kallon su Mom.

Da sauri Auwal ya cika Mom ya yunk’ura zai yi wajen yaji ta rik’e mishi hannu yana juyowa ta girgiza mishi kai daga nan ta koma kitchen ta d’auko tea d’in daman ta gama had’awa waya take so tayi shiyasa ta manta ta fito d’aukar wayar. Zata nufi wajen Jalilan amma ga mamakinta sai taga Auwal ya tare, yace “Ba zata kaiwa Jalilan ba wallahi! Idan tana son sha to tazo ta d’auka anan d’in!”
Ya fad’a hakan yana mai karb’ar tea d’in ya d’aura akan dining sannan yaja hannun Mom d’in za suyi sama.

Da kyar mamakin Auwal ya barta ta iya ce mishi. “Ban ci abinci ba, bara in na gama sai muyi saman dukkanmu ko?”

Ajiyar zuciya ya sauk’e ya watsawa Jalilan wata uwar hararar da sai da y’an hanjin cikinta suka kad’a! Daga nan ya cika hannun Mom d’in ya wuce sama.

Tabbas Jalila ta d’an sha jinin jikinta kuma it’s like kamar akwai abunda yake damunshi sannan tana da buk’atar kud’i daga hannunshi da kuma alfarmar ya barta ta je wajen Umma dan she can’t afford to loose Arshaad, duk da kuwa Umman tace mata akwai nasara amman tana son zuwa yau ta bita ta je da k’afafuwanta, shiyasa ta barshi kuma bata sake yiwa Mom wani yunk’uri ba ta hak’ura kawai ta barshi akan idan ya d’an huce kamar nan da 20 minutes haka zata kirashi ta zayyane mishi buk’atun ta.

Hira sosai Mom da Aaima suke yi, Jalila kuwa tana gefe tanata hura hanci. Chan Mom ta cewa Aaiman tazo suje suci abinci. Haka suka mik’e suka isa dining d’in sukai lunch d’insu cikin kwanciyar hankali. Sai a sannan Aaima take tambayar Mom wacece jalila? Murmushi kawai Mom d’in tayi sannan ta ce mata “no one”, kawai, daga nan tace “Ta mik’e ta je ta jirata a parlourn sama.

Hakan kuwa akayi, Mom na ganin wucewar Aaima ta mik’e itama tayi kitchen. Dama tun d’azu ta sallami cooks da masu goge gogen gidan! Tace musu “su tafi part d’insu In akwai wani abun zata neme su!” Har ta shiga ta d’auko abunda zata d’auka ta fito
hankalin Jalila yana kan kallo.

A daidai stairs na bakwai ta tsaya ta zuba abunda zata zuba tayi sama abunta da cup d’in cikin sand’a.

Kamar minti biyu ta dawo bayan ta ajjiye abun hannunta a d’an gefe kad’an a nan saman ta tsaya a saman bata sauk’o ba kafin ta d’an fara sauk’owa sai kuma ta tsaya tana lek’en parlourn k’asan kafin tace “Jalila ga Ummanki tayi miki message, ungo wayarki, tunda na hau nake ta jin k’arar wayar shine na duba d’akin naga misscalls da messages Za ki zo ki karb’a? Ko kuma ma kawai bara in karanto miki kina daga zaune dan na san mik’ewa yanzu aiki ce a gareki saboda yanayin da kike ciki.” Ba tare da b’ata lokaci ba Mom ta fara karantowa “Aslm Jalila ya gidan, yau banjki..”

A zabure Jalila ta mik’e tayi hanyar stairs tana masifa “Adama ba na son rashin mutunci! Yanzu ke inda ace uwarki ce tayi miki message zaki yarda a karanto miki.?” A fusace take maganar tana tahowa da d’an cikinta wanda ya d’an fara tasowa! K’arfen stairs d’in ta kama cikin sassarfa ta fara taka stairs d’in har da d’an gudunta, tana zuwa kan na bakwai kuwa ta zulme santsi ya d’ebeta a take ta hantsila ta gangara ta koma k’asa ta fad’a ruf da ciki a kan cikinta! Wata azababbiyar k’ara ta saki daga nan ta saki jiki bata sake motsi ba!.

Da sauri Mom wadda daman da tsummanta har biyu ta ajjiye a gefe farkon stairs d’in dan haka ta d’an juya ta d’auka ta sauk’o, daidai wajen na bakwai d’in ta saka wet one d’in da ta jik’a a ruwan omo ta goge wajen tass kafin ta saka dry one d’in ta goge wajen sosai shima. Daidai nan Auwal da Aaima waenda k’arar Jalilan ya janyowa hankali suka taho a tare.

Da sauri Mom ta d’ago ta kalle shi a rikice kafin tace, “Yauwa Auwal zo ka duba inaga jiri ne ya kwasheta kaga ta fad’i kamar ma ta suma bara in d’ebo ruwa.” Ta fad’i hakan tana mai sake duk’unk’une tsummokaran a hannunta Yayin da su kuma gabad’aya hankalinsu ke a kan Jalila. Idan idanuwansu ba gizo suke musu ba kamar jini ne yake fitowa ta k’asan ta!
Shiyasa ma kwata kwata basu lura da Mom d’in ba suka fara sauk’owa har suna y’ar rige rige, ita kuma ta wuce wuff!! Tayi kitchen tana mai cewa “bara in kawo ruwan”

Hankalin Aaima ba k’aramin tashi yayi ba ganin kamar ma ta mutu ne! Ga kuma jinin da taga yana ta kara b’ulb’ulowa, shi kanshi Auwal duk da cewa babban burinshi a halin yanzu yayi getting rid of Jalilan ne amman sai da ya firgita ba kad’an ba.

Suna a haka Mom ta fito, ruwan da ta zo da shi a jug gaba d’aya sai da ta juye mata shi amman ko gezau Jalilan bata yi ba!

Ganin haka yasa Auwal yin sama da gudu ya je ya d’auko makullin motarshi ya dawo ya zo ya kinkimeta yayi waje su Mom suna binshi a baya….
Yana gama sakata a bayan mota motocin su Dad na shigowa
ganinshi a d’an firgice yasa suka tsaidashi suka hau tambayarshi..
Da kyar ya iya ce musu Jalila ce ta fad’o a bene ta suma
ya shige ya tada motar ya fice a 70 ya bar su Mom suna sake yi musu bayani
“Allah ya sauwwak’e” suka ce.
Shi kam Dad bai ma san wacece suke magana akai ba
daga haka suka nufi side d’in Abba
dan Dad yad’an yiwa Daddy bayani a mota
So ya kamata su sameshi ya maida Ummi first kafin granpa ya tsine mishi, sannan kuma ayi maganar ta yanda za a b’ullo wa haukar Mammy
dan sun yi alk’awarin in dai sune mazan mt masu fad’a aji
to tabbas gobe sai an d’aura aure bi izinillahi!
Babu fashi…..

GANDUN ALBASA
“Ku bata iska mana ya duk kuka lullub’eta haka ne??!!”
Cewar Baaba Talatu wadda take k’arasowa wajen da kyar.
Da sauri duk aka fara matsawa gefe.
Hansai da Anty Zainab da wasu mata
Baaba Talatu ta umarta da su d’auketa a kaita parlourn
da ga nan ta cewa Maryam “ta kirawo Likitan da take zuwa tana dubasu.”

Hakan kuwa aka yi
Nan tace mata “gata nan zuwa tana ma kusa dama, su bata nan da minti goma.”
Ko da Likitan ta zo da kyar ta samu Umma ta farfad’o
amman ta bada shawarar a kaita emergency a take dan jininta ba k’aramin hawa yayi ba!
A motar Abba k’arami wanda suka iso yanzun nan shi da iyalinshi da Mahaifiyarsa da Baban sa aka kaita asibitin.
Duk da halin da take ciki da suka had’u da Ya Jamilu a waje bakin motar sai da ta tambayeshi “ina Baba?”
“Yana nan”
kawai ya iya ce mata daga nan ta shige ita da Anty Zainab wadda ta zauna a gaba suka wuce asibitin.

Da kyar Mama ta iya tsayawa aka gama kallon lefen da ita
daga nan ta wuce ta shige tayi sama…

Tun a corridor d’in d’akin Shuwa ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa. Da sauri ta tura k’ofar ta shige tana wani matsanancin kuka a tunaninta ba kowa amman tana shiga suka yi ido biyu da Sakina. K’ok’ari take yi ta danne kukan ta wayance amman ta kasa dan haka kawai sai ta durk’usa ta sake sakin shi a wajen da dukkan k’arfinta tanayi kamar ranta zai fita………

BULAMA ✍️

<< So Da Buri 52So Da Buri 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×