Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Son Zuciya by Maryam Ibrahim Litee

Shafin sadar da zumunta na facebook ta luntsuma ta samo lambar Alhajin, da ya ba ta yana ta magiyar ta kira shi ko ita ta ba shi ta ta lambar, ba ko ɗaya da ta yi sai yau da ta so za ta dauka ta kira. Sai da ta dauki lambar ta danna kira sai dai har ta gama burarin ta ta katse ba a ɗaga ba, cikin takaici ta sake kira nan ma ba ta canza zane ba, ta dangwarar da wayar gefen ta tana balla mata harara kamar ita ta je farautar ko ta kashe zomon.

Ba zato ta ji wayar ta dauki ƙara kuma cikin sa’a lambar ce, ta saki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya sai ta saisaita muryarta ta daga tana faɗin “Hello.” “Da wa nake magana? Wata murya mai kauri ta ratsa dodon kunnenta.
“Ni ce “Rali, Alh.” “Oh Baby Rali, sai yau ina ta ba za kunne.”
“Afwan, ina tuba.” Ta fadi murya ƙasa-ƙasa. “Ba kya laifi baby, mene ne labari? “Game da tayin da ka yi mini yaushe za mu haɗu? Ya yi yar dariya cikin shagala da nishadi “Yanzu dai na je Lagos Baby sai jibi zan dawo, zan so kasancewa da ke a gidan shaƙatawata da ke GRA.”

Ta ɗan rike numfashinta “Zan zo in sha Allah. Allah ya kawo ka lafiya Alh.”
Suka ajiye waya ta koma ta kwanta tana tunanin shigar da za ta yi don ta ƙara rikita shi don hotunanta da take ɗorawa a facebook din ba karamin tafiya da shi ta yi ba.

Wajen Zahra za ta ta darzo kaya kamar yadda ta saba. Facebook ta shiga da
wayar Innar ta ta da take kira Ummai, Jummai take amma tun fara maganar Raliya take kiran Ummai shi kenan sai sunan ya bi ta. Tana riƙe da wayar har dare ya fara nisa Umman ta shigo tana faɗin ta ajiye wayar hakanan ta kwanta, ita ma ta gama ƙullin gyaɗa mai gishirinta barci za ta yi. Ta dai ce mata to ta fita ta ja mata kofa ita kuma ta ci gaba da danna wayar.

Misalin ƙarfe takwas na dare ilahirin gidan yawa kowa ya shimfiɗa tabarmarsa a kofar daki don shan iska saboda zafin da ake zambaɗawa, da hadari ya taso da yamma kowa na ta murna za a jiƙa ƙasa gari ya yi sanyi sai kuma ba a yi ba.

Su Hadiza da Innar su ma sun yi ta su shimfiɗar, hankalin Inna ba a kwance yake ba don har lokacin Sa’a ba ta dawo ba, maigidan ya shigo ya wuce su zuwa kofar ɗayar matarsa da ta yi tafiya har da ƴaƴanta.

Takardar balangu da ya zauna ya bude yana ci, yayanshi suka zubo mishi na mujiya daga kofarsu ko a jikin shi, har Ashiru da namiji da aka fara haifar mishi ya shigo ya zauna kusa da shi cikin fushi ya fadi mashi Innar Luba ta hana shi abinci ledar balangun ya miƙa mishi shi kuma ya tafi shimfiɗar su Hadiza “Binta mene ne hujjar ki na hana Ashiru abinci sai ya’yan da kika haifa ko? Ta ƙara sunkuyar da kanta “Ka yi hakuri Malam, amma na ba shi ya ce ya yi mashi kaɗan.”

“To ba dole ya ƙi karɓa ba kin fifita yayanki a kanshi mara adalci kawai.”
Wlh ita kenan.” Ta shiga rantsuwa wani mari ya dauke ta da shi sai da ya dauke jinta da ganinta na wucin gadi bai hakura ba ya ƙara kafta mata wani sai da ta kifa zai ball da ita mijin Maman safiya ya riƙe shi ta baya “Mene ne haka kake yi Malam Sabo? Ai an girma ba kuma a girma a ci ƙasa, kamar matsayin ku da Maman su Luba ai ya wuce haka na faruwa tsakanin ku.”

Ya ja shi har inda ya tashi shi kuma yana surfa bala’in duk garin nan bai ga uban da ya isa taɓa mishi Ashiru ba.

Hadiza da Luba suka kama Mahaifiyarsu suka shigar da ita daki dukkan su kuka suke har ƙananun yaran suka kwantar da ita a shimfiɗarta Luba da ba ta cika magana ba shiru ta yi ta haɗa kai da gwiwa, Hadiza ke kuka sosai tana faɗin Innarmu ki yi tafiyarki garinku wurin yan’uwanki ki ƙyale mutumin nan.” Ta dago idanuwanta sai ta miƙo hannu ta shafa kan Hadizar “Ku yi haƙuri, saboda ku nake wannan zaman ina zan tafi na bar ku? Ya rayuwar ku za ta kasance Allah ya ba ni ku yaya mata dole in hakura da jin nawa dadin don inganta taku rayuwar.”

Shiru Hadiza ta yi tana ƙara jin tausayin uwar ta su na cika zuciyarta, in ban da rashin imani ina abin duka a jikin mahaifiyarsu? Ta share hawaye jin innar tasu tana faɗin “Ina kika tsaya Sa’a? Ta ɗago ido sai ta ga tsayuwar Sa’ar a ƙofar daki , don dakin ba wadataccen haske Masari ya gaza ce kuma batirin ya yi sanyi.
Ta ƙaraso ta zauna kusa da uwar “Ƙofar guga na je.” Wata yar’uwar mahaifiyarsu ƙwaya daya da take da ita a birnin Katsina ita ce take a ƙofar Guga.

Don ita din asalinta mutuniyar Kano ce wani kauye da ke ƙarƙashin Ƙaramar hukumar Garun Malam, shi ma mijin nata ɗan can ne.

“Me kika je yi gidan Juma da yamman nan ? Innar ta kuma tambayarta Na je ne ko zan samo kuɗaɗen da zan cika sai ta ce mini ba ta da kudi, yanzu zan shigo Malam Bature ya tare ni, kin gama kudin da ya ba ni.” Ta daga kudin yan dari biyar biyar ne masu dan dama .

Innar tasu ta yi ɗan tari “Ba na son karɓar kudi a hannun Maza Sa’a, kina dai jin shaidar da jama’a ke miki ki kama kanki ga miji ya ƙi samuwa duk wanda ya zo sai a tare shi a ɓata ki ga shekarunki sun fara turawa, ƙannenki kowacce a ka kai daki ta isa.”

Sa’a da kanta ke sunkuye ta ce: “Na ji Inna, akwai wanda muka yi magana da shi ya ce zai zo wurin Baba kuma bai buƙatar a dauki dogon lokaci.” Ta fadi “Alhamdulillahi, sai ki ce ya zo.” Ta ƙara ɗan tari sai ta gyara kwanciya ta yi pillow da hannayenta. Haka suka shiga barci kowa ransa ba daɗi.

Ƙarfe bakwai na safiya Innar Raliya da ke ta kujiba- kujiba a tsakar gida aikin ƙulin saidawa take duk da dai yanzu an samu cigaba sauƙi ya zo musu na injinan markada gyada ta fidda musu man, nasu kawai mulmulawa da soyawa.

Jin shirun Raliya duk da sau biyu tana buga mata ƙofa ta ƙara komawa a karo na uku ta buga mata daga ciki ta amsa ta ce “Ki tashi fa ki yi sallah.” Ta koma kan aikinta.

Raliya ta fito da brush ɗinta a hannu ta dauki buta banɗaki ta kewaya ta jima kafin ta fito ta yi brush din sai ta daura alwala ta shiga daki.

Tana yin Sallah wata guntuwar riga iya gwiwa ta sanya ba ta rufe kanta ba da ta yi ma kitson daure-ɗaure ta fito tsakar gida ba ta ga Innarta ba wani ɗan dutse ta zauna tana ji yo muryar Innar tana magana a zaure da wani yaro da ta aika ya sawo mata koko.

Ta shigo ɗauke da dogon Jug a hannu da ƙullin sugar a kai ta dire gaban Raliya ta wuce ta dauko kofi ta tsiyaya ta zauna tana kurɓa a hankali.

Ganin Raliya ba ta da niyyar zubawa ta ce “Sabon ƙuli na nan mai sugar da na soya ki dauko ki zo ki sha.”

Sai da ta tura baki sai ta harari Jug din tana ƙunƙuni a ranta ita Ummai lokacin da babanta na raye kullum cikin rainuwar abin da yake kawo musu take da hana mashi sukuni, ba ta taɓa jin ta gode ma ƙoƙarin shi ba alhali ba wata sana’a gare shi mai ƙarfi ba, facin keke yake yi ita ga shi nan an bar su su biyu duk da uban sana’ar da take hana kanta sukuni ba dare ba rana ta gyada mai gishiri da ƙuli mai sugar da mai gishiri ba ta sauya zane ba maimakon su koma cin daɗi sai ma ƙara taɓarɓarewa da abin ya yi gara ma lokacin da babanta na nan.

Ita kam ba za ta sha koko ba fitsari daya gara ta haƙura anjima ta shiga gidan su Zarah, a da sammako take musu a karya da ita duk kuwa da fadan da babanta ke mata sai da ta yi hankali take ɗaga ƙafa hantsi ya yi.

Suna nan zaune har tara da rabi na safiya aka rafka sallama daga zaure Ummai ta amsa tana ba da iznin shigowa fuskarta ta washe ganin matar da ke tsaye kanta dauke da faggon kaya.

A’a shigo mana Tani.” Tana fadi tana mikewa ta tura mata kujerar da take kai ta sauke kayan ta zauna ta dubi Raliya da sauri Raliyar ta fadi “Ina kwana? Cikin fara’a ta amsa tana faɗin “Yau Lahadi ba makaranta ? Raliya ta daga mata kai za ta fara kwance faggon Innar Raliya ta tsayar da ita “Kin ga Tani kar ki kwance ba kuɗi.” Ba tare da ta fasa kwancewar ba ta ce: “Bari dai a kwance Innar Raliya da gani akan yi saye.” Da ma ai ba ba a so ba garin ne da yake ta ƙara damalmalewa.” Tani ta gyaɗa kai “Abin fa sai godiya kawai Allah dai ya ba mu mafita.”

Tana ta yamutsa kayan Raliya da ke ta shafa magen su tana kallon kayan gwanjon karaf idonta ya faɗa kan wata yar farar riga ta miƙa hannu ta ɗauka tana ɗagawa yar ƙarama ce da ko cibi ba za ta kai ba, gaban ta kuma a buɗe yake igiyoyi aka yi mishi a maimakon butura tana ta kissima yadda za ta yi da ita idonta ya faɗa kan wani baƙin wando da Tanin ta ɗaga mai kama jiki zaraf ta miƙa hannu ta karɓe shi “Nawa rigar nan shi ma wandon nawa? Tanin ta dubi abin da ta ɗauka wando dari takwas riga dari bakwai. Raliya ta zaro ido “Haba dai gaskiyar su nan fa kike kawo su Naira sittin tamanin.” Tani ta riƙe haɓa “Shekara nawa yar nan? Ba dai yanzu ba da komai ya yi tashin gwauron zabi.”
To a dai rage mini Baba Tani.” “Shi kenan ba da dubu daya duka ala amfana. Saboda Ummai ai ko kyauta na ba ki.”

Zan bayar idan kika dawo Lahadi mai zuwa.” “Lahadi bai yi nisa ba? Ki ba da wani abu idan na dawo sai ki cika.” Raliya ta shafa cinyarta “Yau dai ba ni da kudi Baba Tani, amma kika dawo zan ba ki kudinki duka “Innar Raliya na jin su ba ta tsoma baki ba duk da sanin halin yar ta ta ba ƙaunar biyan bashi take ba sau tari ta ciyo bashi wurin masu shago sai dai ta biya, amma saboda shiga rai irin na ɗa ɗaya tilo da kuma wani zamani da muka riska iyaye ba sa son bacin ran ya’yan su sai ta yi shiru.

Tani ta ƙulle kayanta kafin ta miƙe har Raliya ta riga ta ta watsa kayan a bokiti ta zazzaga omo ta wanke su tas ta shanya can inda rana ta fara fitowa.
Ta dawo ta zauna uwar na cewa “Anya Raliya ba za ki karya ba ? To zubo tuwo na yi ɗimame.”

Ta daƙuna fuska don ji ta yi kamar ta kwaɗa mata duka “Ni dai Ummai kin san na tsani tuwo ballantana wani abu ɗimame.”
Uwar ta miƙe “Ki dauko dari biyu ki sawo Indomie. Ta ce: “Yawwa Ummai.”
Ta nufi ma’ajiyar uwar ta zaro dari biyun sai ta koma dakinta waya ta ɗauka don ta riga ta gama da cajin, ta fito ta taɓa kayan sun fara shan iska ta koma ta zauna ta ƙara masu mintoci sai ta kwashe su ta ce ma Ummai bari ta sawo Indomie ta ce “Sai ki tafi da wayar ki kai caji gidan su Zarah.” Ta ce To.

Da fitar ta ba ta nufi shagon ba gidan su Zarah ta shige zuciyarta fal murna ta samu kudin motar da za ta fita gobe.
Duk da ta san mai wuya ta samu Zarah don ba a isa tashi hadda ba, ita dai tuni ta zare kanta da zuwa hadda Hadiza da Zarah ke zuwa.

Ta yi sallama ƙofar dakin, Nene ta amsa sai ta cusa kai su biyu ke zaune Nene sai jikanta na wajen Baba mai mota, ta gaida Nene sai ta gaishe shi kafin ta shaida ma Nene guga za ta yi ta ce ta shiga ciki.

A bedroom ɗin suke guga sai da ta sanya wayar caji ta jona Iron din ta tsinkayi sallamar Zarah ba ta fito ba har ta shigo ta same ta liƙab ta zare da hijab din ta ɗora saman gado sai ta zauna gaban Raliya “Kin ƙi hadda dai Raliya ga shi nan har mun haɗa hizif goma.” Ta ce: Allah ya taimaka ashe za ku yi mana walima? Ta ce “Ba za mu yi ba sai mun haɗa talatin.” Suna ta hira Raliya na jin kamar ta tambaye ta ba su da abinci sai ta ga ta mike ta kwaso kayan shayi ta yi musu hadin kauri suka sha da suka kammala suka fita falo Nene ta fita dubiya don haka labaran samarin su suke yi wadanda suka kasance abokai Jamilu na Zarah abokin Shamsu ne shi Jamilu bai zurfafa karatunsa ba kasuwa ya shiga yana kuma samu.

Sai da aka kawo abincin rana Raliya ta cika cikinta wayarta kuma ta cika sai ta dauki kayanta da ta goge ta yi ma Zarah sallama ta tafi gida.

<< Son Zuciya 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×