Skip to content
Part 13 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

“Ke Nabila, tashi ki bi mijinki”

Ba dan ta so ba sai dan kada Umma ta ga kamar ta rainata ne ya saka ta haɗa kan kwanukanta ta saka a kwando ta yi musu sallama ta bi bayan Hussaini. Lawisa ta riga da ta yi gaba, shi kuma yana tafiya sannu a hankali dan ta ci mishi.

“Motar fa tana can”

Ya faɗa yana nuna mata inda ya ajiye motar ganin ta nufi wani wajen. Tsayawa ta yi ta kalleshi sama da ƙasa kafin ta ce

“Au ka ɗauka bin naka zamu yi? Yanda na hau adaidaita na zo, haka zan hau shi na koma”

Ta ja hannun Hajja suka fita bakin titi don taran adaidaita. Ko ciniki bata tsaya yi ba ta hau tunda yace mata zai je ɗin. Ya san zai ɗauketa a motar tashi ya barta ta taho a motar haya? Wato ta ga ya kawo matarsa shi ne zai wayance ya ce can gida zasu zai rage mata hanya.

Ruwa ta watsa ma Hajja sannan ita ma ta yi wanka sannan ta shiga tana tunanin me zasu ci da dare. Fanke ta yanke tunanin yi musu su sha da shayi su kwanta. Kafin ta yi sallar magrib zata kwaɓa shi dan haka ta je ta zauna tana taya Hajja kallo duk da cewar takan ɗan faɗa tunani wanda ita kadyai ya shafa.

Kamar cikin bacci ta jiyo sallamar Hussaini. Ta tashi daga kishingiɗen da take tana kallon ƙofar falon bayan ta amsa. Ganin Lawisa biye da shi ya saka ta yin kicin kicin da fuska. Ta kalli Hajja ta ce

“Hajja, je kiyi wasa a ɗakin ki”

Kamar yarinyar zata yi magana sai kuma ta fasa. Miƙewa ta yi ta shige ɗakin kamar yanda aka umarceta.

Hankali Nabila ta mayar kan Hussaini da Lawisa da ke ƙoƙarin zama kujerar zaman mutum biyu. Lawisa kamar zata shige jikinshi. Kallon da take aika musu ne ya saka Hussaini fasa zama ya koma kujera mai ɗaukar mutum ɗaya.

Da Bismillah ya fara sannan ya ɗora da jawabin ƙaddara. Banda kallon Hussaini babu abunda Nabila take yi. Mamaki kawai take yi wai Hussaini ne ya kawo kishiyarta kuma aminiyarta a da gidanta, bai ji kunya ba ya zaunar da ita yana magana a kan ƙaddara. Son zuciya dai. Daga nan ta ji yana rokon su haɗa kawunansu a zauna lafiya. Ta tsinci muryar Lawisa ta amsa mishi da

“In shaa Allah”

Ta kalli ɓangaren da take, kan ta a ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta. Abun sai ya nemi bata dariya. Kunyar wa Lawisa take ji? Ta dai san ba kunyar Hussaini take ji ba. Sannan kuma ƙaryar kunya take tunda ta iya aurar mata miji har ta aiko shi neman ƙarin kwanaki a wajenta.

Hussaini na miƙewa ita ma ta mike ta shiga kitchen ta kwaɓa fankenta. Ta zo ta wuce Lawisa na zaune yanda ta barta. Ko ta kan ta bata bi ba ta shiga ɗakin Hajja ta ce ta taso su yi alwala an kira sallah. Suka yi sallah ta ɗan mata karatu suka tashi suka tafi kitchen ta fara suyar fanke.

Gajiya Hajja ta yi da magana ta fice ta barta wai kallo zata yi. A nan Hussaini ya zo ya sameta

“Kin kwashe ki zuba mana?”

“Ai ba da ku na zuba ba”

Bakinshi dai dai kunnenta ya ce

“Ban san ki da rowa ba Beela”

Murya ta gyara tana girgiza kai kafin ta iya cewa

“Ɗan matsa dan Allah. Matarka zata iya ganin mu”

Dariya yayi ba tare da ya matsa ba. Daga shi har ita sun san da gayya yake tsaye a bayanta yana mata raɗa a kunne. Tsikar jikinta duk a tashe yake tana jin yanda ya takureta.

“Dan Allah Hussaini ka matsa kar ka sa na ƙone”

Yanda ta yi maganar a marairaice ya saka shi yin dariya. Ya ɗauki fanke guda daya ya saka a baki. Ya yi masa daɗi sosai dan haka ya ɗauko faranti ya ƙara ɗiban gudan huɗu. Ya so ɗiban fiye da haka amma Nabila ta hana. Nan kan dandamali ya zauna ya cinye sannan ya goge hannunsa yace zasu wuce. Kai kawai ta ɗaga mishi ya fice. Baya son takura mata. Ya san tana buƙatar lokaci dan haka zai bata lokacin.

Juyawa ya yi ya kalli Lawisa da ke zaune a gefensa ta yi shiru tana kallon hanya.

“Tunanin me kike yi?”

Ya tambaya yana juya kan sitiyari yana shiga kwanar hagu. Ya san akwai abunda yake damunta

“Nabila ta tsaneni”

Murmushi ya yi wanda ya ɓoye dariyar da ta zo mishi. Da kamar ya ce mata

“To da me kike tsammani?”

“Na san na yi mata ba dai dai ba. Ko da ka nuna kana so na, bai kamata na amince ba. Amma Baban Hajja ina son ka. Na kasa danne zuciyata a kan ka. Na bari son da nake maka ya rufe min idanuna. Na yi tunanin Nabila zata min uzuri saboda ita mai haƙuri ce. Na manta irin son da take yi maka duk da bai kai wanda nake maka ba”

Shiru ya yi yana nazari maganganunta. Gaskiya ne Nabila tana da haƙuri kuma ya san ta so shi. Yanzu ne dai bashi da tabaccin soyayyar na nan ko kuma baya nan. Babu wani abu da yake nuna akwai soyayya a tsakaninsu. Ko me ya sa?

**

Wajen sha ɗaya na safe suka dawo gida. Tun tara aka sallame su amma saboda cike ciken takardu da haɗa kaya basu samu shigowa gida ba sai sha ɗayan. Ajiyeta ya yi sannan ya tafi maida Umma gida.

Ɓangaren nata a share a goge. Ta shiga banɗaki ta yi wanka dan so take ta rage warin asibiti da ke tattare da ita. Ta yi tunanin inda Ilham take, amma ta jira ya dawo tukunna sai ta tambaye shi.

Turaren wanka ta dauko ta saka cikin ruwan wanka sannan ta ɗauko sabulu mai kamshi ta yi wanka da shi. Doguwar riga ta saka shima bayan ta feshe shi da jikinta da turaruka masu sanyin ƙamshi.

Masu aiki suka shigo suka gaisheta da jiki suka fita sannan Afrah ma ta shigo. Hijabi ne burgujeje a jikinta kamar bata jima da tashi daga bacci ba. Tana kuma ɗauke da Ilham.

Ta gaisheta da jiki sannan ta fita ko zama bata yi ba. Ilham ta haye cinyar Safina tana yi mata surutu na yara. Ita kuma tana murmushi tana shafa kanta.

Suwaiba ta dawo ta tambayeta abunda za’a dafa

“Me muke da shi a fridge?”

“Ai tun da kika tafi Alhaji ya sa aka kwashe ana amfani da su saboda lalacewa. Abunda kike bukata sai a bada kudi a saya kafin a kawo”

Ɗan gajeren tunani ta yi ta ce a yi musu tuwon shinkafa da miyar taushe sai a yi mata ɗan farfesu na naman rago dan ta ƙara jin daɗin bakinta. Ta ɗauko kuɗi da take tunanin zai isa ta bayar. Bata san lokacin da bacci ya daukesu ita da Ilham ba.

Bayan sallar azahar suka ci tuwonsu ita da Ilham sannan ta dinga bata naman cikin farfesun har ta ce ta ƙoshi. Ta zuba nata tana ci ta ji dawowar su Iman. Farin ciki sosai ta ji ya lullubeta. Ba wai daɗewa ta yi bata gan su ba dan ko jiya sun je asibiti. Kawai wata kewarsu take ji ne.

Sun ɗan ɗauki lokaci kafin su shigo su rungumeta. A baki ta dinga basu abinci ko kayan makaranta bata ce su cire ba tukunna. Tana kallo suka ciro littafansu na makaranta suka yi hanyar waje

“Ina zaku je ne?”

Iman ce ta bata amsa

“Wajen Aunty Afrah zamu je ta mana homework”

Hana su tafiya ta yi ta ce su zauna zata koya musu. Babu musu suka dawo suka zauna. Suna gamawa ta ce su yi bacci kafin lokacin Islamiyya ta yi dan su huta kwakwalwarsu.

Ko da suka tashi, shirin Islamiyya suka yi suka tafi. Duk da Ilham na nan sai ta ji gidan ya yi mata shiru. Gashi bata ji ɗuriyar Hussaini ba sam. Tana tsoron kiranshi kar ya amsa ta zo tana ɓacin rai a banza.

Bai shigo ba sai bayan Maghrib.

“Yauwwa”

Shi ne abunda ya ce da ita bayan ya amsa sallamarta. Ya zauna ta yi mai tayin abinci yace ya ƙoshi. Ya tambayi yara ko sun yi aikin makaranta ya ɗan yi wasa da su sannan ya tashi ya fita.

Ganin shiru har tara ta wuce bai shigo ba ga yara ta saka su bacci sai ta kira wayarsa. Kira biyu ta yi mishi bai amsa ba. Ran ta ya ɓaci sosai kan hakan. Take haushin Afrah ya turnuketa saboda babu makawa ta san ita ce ta riƙe shi ta hana shi dawowa. Ai dai duk abunta sai ta hakura ta sakar mata shi tunda dai ta dawo. Ta ɗauko hijabin da ta yi sallah da shi daga kan sallaya ta saka. Zuwa zata yi ta sako shi gaba su dawo.

Bata kai bakin ƙofa ba ya murɗa ya shigo ɗakin. Sai ta ji kuma duk haushin da take ji ta huce shi. Dan haka ta yi murmushi ta amsa sallamarsa tana cire hijabin ta linke shi.

Ɗan nesa da shi kaɗan ta zauna tana wasa da ƴan yatsun hannunta. Tambayarta ya yi ko lafiya ya ga kiranta. Ta yi mishi bayani a kan cefanen da basu da shi ya ce ayyuka ne suka mishi yawa a kasuwa amma zai bayar a mata sayayyar. Idan kuma ta fi so ya bata kuɗin sai ya bata ta aika da kan ta.

“A’a ka bayar ɗin a kawo min”

Ganin bata da abun ce mishi sai ya tashi yai mata sai da safe.

“Ina kuma zaka je?”

“Bacci zan je na yi”

Nan da nan ta harzuƙa, ɓacin ran ta ya fi na da. Kirjinta kamar ya fashe dan yanda take jin iska na cika ta yana son fita ko ta halin ƙaƙa.

“Wallahi bazai yiwu ba. Sati nawa kuna tare ni ina kwance a asibiti? Bai ishe ku ba? Sai an ɗauki kwana na an bata kuma ina nan? Bazan yarda ba gaskiya”

Murmushi Hassan ya yi ya ce

“Kwananki? Baki ji me likita ta gaya miki ba? Ko har kin manta?”

Ji ta yi kunya na neman mamaye ɓacin ran da take ji. Ya ci gaba

“Ko ma dai yaya ne, ni bazan iya haƙuri ba. Maganar kwana kuma, baki da shi sai ranar da likitoci suka tabattar da warkewarki suka baki pass. Amma yanzu, ki maida hankali wajen kiyaye dokokinsu da samun sauƙi. Zai fiye miki”.

Kuka? Ihu? Ta rasa wanne zata yi. Tana dai nan zaune inda ya barta bata ma san a wacca duniya take ba. Ita Hassan zai ce ma ba zai iya haƙuri ba? A kan wata macen yake gaya mata haka? Kafin ya kara aure ya yake yi? Ko dan … Sai a wannan gaɓar ta ji hawaye ya sauko mata. Bata da wani amfani kenan har sai ta warke? Kusan watanta guda a asibiti. Sannan ana saka ran ta kuma yin a kalla wani watan tukunna kafin ma a fara tunanin za’a barta ta ci gaba da haɗa shimfiɗa da mijinta. Har wannan lokacin bata da kwana?

Dama bata da niyyar kaucewa sharruɗan likita amma ko ba komai ko hira sai su yi ai ya tabattar mata har yanzu akwai soyayyarta a tattare da shi. Amma ya tsallaketa ya tafi wajen kishiya? Me zata yi tunani? Ta san yanzu yarinyar na can tana yi mata dariyar mugunta a zuciya. Tana ganin bata da wata ƙima ko daraja. Ta rasa Hassan kenan?

Tsabar kukan da ta kwana tana yi, ga saƙa da warwara, ta tashi da matsanancin ciwon kai na ɓari guda ɗaya. Suwaiba ta kira ta ce ta shirya yaran bata jin daɗi. Sannu ta yi mata ta kuma tambayi ko a yi ma maigidan magana ya maidata asibiti. Wani ƙululun baƙin ciki ya kara turnuƙeta. Wato ma har masu aikin gidan sun san bai kwana ɗakinta ba a na kishiya ya kwana.

Ɗakin ya shiga ya gan ta kudundune cikin bargo. Ga shi babu wuta balle ya yi tunanin ko na’ura mai sanyaya ɗaki ta kunna. Karasawa bakin gado ya yi ya kira sunanta yana ƙoƙarin yaye bargon amma irin ƙudundunar da ta yi ya saka shi kasawa

“Safina lafiyarki kuwa? So kike sankarau ya kama ki ko me? Buɗe mu gani”

“Dan Allah ka fita ka kyale ni Hassan. Ka rabu da ni”

Sauke ajiyar zuciya ya yi ya zauna gefenta ya yi kasa da murya

“Na ƙyale ki? Ai kin san hakan ba zai yiwu ba. Buɗe na ga fuskarki sai na tafi”

Ji yayi ta fashe da kuka dan haka ya saki baki yana kallonta. Girgiza kai kawai ya yi ya nemi waje a gadon ya kwanta yana murmushi

“Yanzu ke Safina dan nace miki baki da kwana shi ne kike kuka? Na dauka kin san mijinki fiye da kowa. Kin san dai ni mai adalci ne ko?”

Shiru ta yi ta daina kukan tana saurarenshi. Ta san kawai daɗin baki yake kokarin yi mata kuma hakan ya fara tasiri

“Kawai haushinki nake ji shi yasa na ce haka amma wallahi a part dina na kwana ni kadai. Ki yarda da ni”

Tashi ta yi zaune bayan ta yaye bargon tana goge hawaye

“Ni baka min adalci ba Hassan. Ka san yanda ka kuntata min kuwa ina gadon asibiti? A lokacin da nake bukatar kulawark ka yi watsi da ni. Da haka kake min? Dan ka samu wata ka fara wulakanta ni?”

Haƙuri ya bata tukunna

“Raina ne a ɓace. Na kasa gane abunda ya sa kika yi abunda kika yi har ya kai ki da ja ma kan ki jinya”

“Saboda kai na yi”

Girgiza kai ya yi

“Ba saboda ni bane. Na miki wani ƙorafi ne? Ko kuma na janye daga gareki? Ko wani canji kika gani a tare da ni? Ko ma dan me kika yi, na san ba dan ni bane”

Baki kawai ta turo dan ta ga kamar so yake ya saka ta dogon tunani. Ko ma dan me ta yi ta san dai shi janyo musu tunda tana zaman zamanta ya je ya ɗauko aure ya ruguza mata lissafi. Yanzu gashi ya sa ta jangwalo ma kan ta jangwam

“Ai dai ba dan kaina zan yi ma kaina wannan azbar ba. Ni ma magani ai wai zan maka gwaninta”

“In dai irin wannan gwanintar ce bana so. Yanzu tashi mu je mu ci abinci dan yau ma aiki ne da ni”

****

Kada a manta a yi liking da comment. Abun ma raguwa yake maimakon ya ƙaru. Menene matsalar?

<< Soyayya Da Rayuwa 12Soyayya Da Rayuwa 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.