Skip to content
Part 15 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

A mota ta iske su suna jiranta bayan Hassan ya daddana horn yana nuna tafiyar lokaci. Tun jiya ta gaya mishi yau za’a fara bayar da admission letter na makaranta zata je ta amso kuma ta yi registration.

“Na raka ki ne?”

Tambayar ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba. Girkin Afrah ne amma zai fita da ita. Basu taɓa samun matsala a ka ya fita da wata ranar girkin ƴar uwarta ba saboda bai taɓa fita da Afrah ranar girkin Safina ba.

“Yi haƙuri na bar ma Suwaiba sallahu ne kar mu dawo bamu tarar da abinci ba”

Ihsan suka ajiyewa Hajiya Mama sannan suka biya suka ajiye suran a makaranta. Tun da ta ji labarin zuwa karbar admission take jinta tamkar a gajimare. Ita ma zata zama ƴar Jami’a mai aji da wayewa! Babu abunda kishiya zata nuna mata.

Lokacin da suka isa makarantar goma ta ɗan gota. Da tambaya suka karasa department inda aka nuna musu Faculty aka ce can ake amsar admission.

Layin da suka tarar ne ya saka Safina yin turus! Hassan ya ƙarasa ya yi ma wasu tambaya sannan ya dawo inda ta ja ta tsaya

“Wajen matancan zaki je ki tambayi wacece ƙarshe ki tsaya a bayanta. Ni zan je mota na jira da kin amsa ki zo ki same ni”

Yanda yace haka ta yi. Ganin tsayiwar ba mai karewa bace, ta nemi waje kamar wasu ta zauna a abu mai tudu. Wayarta ta ɗauko tana shiga manhajar whatsapp. Yau take son zuwa wajen Nabila bayan ta amso admission letter ɗinta. Kwanaki huɗu da suka wuce ta kirata tana kuka kan Hussaini ashe baya sonta bai taɓa son ta ba. Ta so ta ɗan yi mata bayani amma Nabila ta ƙi cewa komai. Dan haka haƙuri kawai ta bata ta ɗan rarrasheta gami da gaya mata maganganu masu kwantar da rai.

Bata san lokacin da ta ɗauka tana danna waya ba kafin mutane su dinga miƙewa suna hawa layi. Ta ƙara gyara takardun da aka buƙata. Saƙo ta yi ma Hassan kan cewar an fara bayarwa. Layi ne mai tsayi, ga rashin isowarta da wuri. Suna nan tsaye aka kira sallah amma babu halin tafiya. Ka gama tsayuwar ka je ka dawo na layi su ce ba haka ba. A haka har Safina ta ƙirga mutane shida a gabanta.

“Malam Aminu lokaci ya yi”

Ta ji muryar wani ya faɗa tare da miƙewa yana haɗa kan takardun gabansa. Ya kalle su rai a haɗe ya ce

“Mun tashi sai kuma gobe”

Salati da salallami ya dinga tashi daga inda suke. Safina ji tayi kamar ta fashe da kuka dan tsananin ɓacin rai. Wannan wulaƙanci har ina?

“To mutum goma na gaba su rubutu sunayensu a takarda kuna zuwa gobe mu fara da ku”

Haka suka rubuta sunayensu a kan takarda su goma suka ba mutumin suka tafi

“Har kin karɓo”

Tambayar Hassan kenan

“Ina fa? Wai sai gobe”

Kamar ta yi kuka take ji. Ga yunwa na addabarta ga sallah dole ta haɗa azahar da laasar dan uku ta yi har ta wuce. Wannan jaraba da me yayi kama?

Sai da ta yi wanka ta yi sallolinta kafin ta ci abinci ta kira Nabila tana bata haƙurin cewar sai ta gama registration.

Washegari ma suna ajiye ƴan makaranta suka wuce. Masu bada admission letter basu iso ba sai wajajen goma sha biyu. Sai da suka tsaya jera takardu da kayan aiki a kan tebur sannan suka ce wadanda suka rubuta sunayensu su shigo. Daɗi kamar ta buga tsalle.

Suna karɓa suke wuce dan a basu lamba. Nan suka iske mai bayarwa ya tafi break yai sallah ya ci abinci. Haka suka jira shi ya dawo yace su je su sayi file. Ya taimaka yai musu kwatance suka yi zuga suka tafi. Bayan sun saya sun dawo suka dinga shiga ɗaya bayan ɗayan suka nuna mishi takardu ya basu lambar admission.

“Dole na kai ki muyi celebrating. Zamu je da yara?”

Murmushin jin daɗi ta yi tana juya idanu

“A’a ni da kai kawai zamu tafi”

“An gama ran ki ya daɗe. Dama zan je wani company a China sai mu tafi tare ko?”

Bata san lokacin da ta rungumeshi ba

“Madam kar ki sa steering ya suɓuce min mana”

“Na gode sosai Sweetyna Allah ya saka da alheri thank you very much”

“You deserve it” (kin cancanci hakan)

Tun kafin ya gaya mata ya gaya ma Afrah zai tafi da Safina. Addu’a kawai ta yi musu. Ya ɗauka zata yi rigima ko ta nuna ɓacin ran ta amma sai ya ga akasin hakan. Har haƙuri ya fara bata amma ta katse shi

“Mi amor meye na bani haƙuri? Dama da ita ya kamata ka fara tafiya tunda ita ce babba idan ya so next time in da hali sai a je da ni. Besides… I’m delicate”

Dariya ta bashi kuma ya dara. Ya ɗora hannu a kan cikinta da ke nan a shafe wai babynsa ne a ciki.

“Allah ya sa ki zama mai fahimta irin mamanki”

“Ka san dai kace idan ba girl bace zaka bani ribarka na watan da na haihu ko?

“Ƙwarai da gaske. Because na tabattar macen ce”

“Nima ina fatan hakan. Ko dan kar ka zauna babu kuɗi”

****

Hannunta ya riƙe a nashi yana shafawa bayanshi da babban ɗan yatsansa. Hankalinsa baya wajen saboda yana cikin damuwa.

“Baban Hajja”

Muryarta ta fito a hankali tana kokarin jan hankalinshi. Kallonta ya yi tare da murmushi. Ya ɗora hannunshi a kan goshinta, sai ya ɓata rai.

“Zazzaɓin yana nan har yanzu”

Murmushi ta mayar mishi tana lumshe idanunta cikin siga ta jan hankali

“Ba zazzaɓi bane. Kawai jikin ne yake yin ɗumi. Me ya sameka? Kamar kana cikin damuwa”

Alhaji ne ya ci mishi mutunci daren jiya. Bai taɓa ganin ɓacin ransa irin na jiya ba, bai taɓa mishi irin zagin da yai mishi jiya ba. Ga Hassan ma ya ƙare mishi tanadi a jiyan bayan Alhaji ya ce ya tashi ya bashi waje. Sannan ga Nabila shi bai gane mata ba.

Passport suka je kai ma Alhaji za’a yi musu visa. Wani kampani ne a China zasu je su duba dan su dinga yi musu kayan sakawa na yara. Su tura design su kuma su buga musu shi. So suke su je su duba sahihancin kamfanin da kuma ingancin kayan nasu. Zasu buga musu sample, zasu yi lissafi sannan su duba yiwuwar wani kasuwancin na kayan kitchen. Idan bai musu ba zasu dawo gida. Gabaɗaya sati biyu zasu yi kuma Alhaji ya ce kowa ya ɗauki mace ɗaya ya tafi da ita.

Bai yi aune ba Alhaji ya jefe shi da passport ɗin da ya miƙa mishi tare da ce mishi

“Baka da hankali”

Faɗa ya rufe shi da shi na akan me zai bar Nabila ya tafi da Lawisa? Shi fa a tunaninsa, Nabila ta taɓa fita waje, ta je ta yi aikin Hajji. Sai yaga ita ma Lawisa a bata dama ta ɗan hau jirgi ta bar ƙasar.

“Dan ƙanwar uwarka ba kwance take tana laulayi ba? Saboda rashin adalci ka bar Nabila a gida ita mai lafiya? Me kake nufi?”

Ya san Alhaji na ƙaunar Nabila. Wani lokacin ma ya yi wani abun a kan ta sai ka ɗauka ita ce ƴar shi. Kullum maganarsa amana aka bashi. Ita Lawisar ai amana ce ita ma. Bai ga laifi dan an tafi da ita ba. Da Alhajin ya gaji da ce mai shashasa, lusari kuma sahorami da nau’ikan zagin da ya iya sai yace ya fita ya bashi haƙuri.

Yana fita Hassan ya biyo shi ya ke kara nuna mishi rashin dacewar abunda ya yi

“Ka taɓa tafiya tare da Nabila?”

“Dalla na ga ita ta je Saudiyya”

“It’s not the same thing (ba abu ɗaya bane ba). Wannan ita kadai ta tafi. Nan da Abuja baka taɓa tafiya da ita ba. Ka gwammace ka tafi kai ɗaya da ka je da ita. Amma ita wannan daga zuwanta zaka haɗa tafiya da ita? Ni tafiya nawa na yi da Safina? Ka ji nace zan je da Afrah? Ko dan kar Safina ta ji ba dadi a ranta, ta ji kamar dan Afrah ta zo na yarda ita ai ban ce da Afrah zani ba. Why? Me yasa kake haka? Ba ka son ta ne?”

Ita kuma Nabila ya kasa gane me ke damunta. Komai nata a sanyaye. Idanunta sun yi ja, fuskarta a kumbure sannan bata zama inda yake. Ya so suyi magana ma ta ce a’a. Ya so ta yi mishi bayani a kan abunda take nufi da ya ƙi gaya mata gaskiya a lokacin ba.

“Ka yi shiru”

Ɗan murmushi ya yi

“Tunanin tafiyarnan nake yi. Hankalina bazai kwanta ba na bar ki a nan baki da lafiya”

Wani murmushin ta ƙara yi

“Babu matsala, akwai waɗanda zasu taya ka kula da ni ai”

Bai samu damar magana ba aka tura ƙofar ɗakin aka shigo. Bai saki hannunta ba, ya saka ma ƙofar idanu yana jiran wanda zai shigo.

Hajiya Mama ce da kanwarta Mama Nafi. Mama Nafi na ɗauke da kwandon abinci. Tunda aka kwantar da Lawisa kullum sai ta kawo abinci. Da kanta take shiga ta dafa ta zo ta lallabata ta ci shi. Mahaifiyar Lawisa sai dare take zuwa ta kwana da safe ta tafi idan ya zo.

Tashi ya yi ya basu waje dan zai koma gida ya ɗan huta. Wataƙila ya samu ya yi bacci. Gidan shiru kamar babu kowa dan Hajja na wajen Umma. Ya tarar da abincinsa a kan tebur sai ya wuce dan neman inda  take. Bata cikin gidan, a baya ya ganta. Tana kwance a inuwa tana kallon shuke shuke.

Gefenta ya zauna shima yana kallon shukokin. Yanayin ya yi masa daɗi, ya ji zai iya samu ya kwanta a nan ya yi bacci.

“Ban tafi kasuwa ranar dan ban damu da ke ba. Na san yanda kike son cikin, na ga yanda ya canza ki. You were so happy”

Yana iya ganinta a cikin kansa. Kullum tana cikin murmushi. Ya kan ganya ta ɗora hannunta a kan cikinta tana dariya ita kaɗai. Da alamu tunani take yi, gaba take hangowa. Ya kan yi murmushi ya girgiza kai ya ƙyaleta ta yi ta tunaninta. Bata taɓa fita ta dawo gidan nan bata saya ma abunda ke cikinta wani abu ba.

Akwai ranar da ya tashi da asuba ya ganta kusa da inda take sallah a kan gwiwowinya tana manna abu a bango. Calendar ce da ya fara daga watan da suke ciki zuwa watan da aka yi hasashen zata haihu. Kullum ta tashi sallah kafin ta yi alwala sai ta soke rana ɗaya. Shi ma kafin ya fita masallaci sai ya kalla, ya ji sanyi a ran shi.

“Bana so na kalli idanunki. Bana so ki tashi ki gan ni.”

Lokacin da likita ya bashi haƙuri ya ce cikin ya zube ji ya yi kamar shi kaɗai ne a duniya. Bai san yanda zai ji ba.  Kawai ya san ba zai iya kallon cikin idanun Nabila ya kalli yanda duk wani mafarkinta ya rushe ba. Ba zai taɓa iya gaya mata ba. Dan haka Mommy na zuwa asibiti ya gudu gida.

Ko’ina ya kalla a gidan sai ya tuna abunda ya rasa. Ya ji baya son zama shi kaɗai, baya son ya yi tunani dan haka ya wuce kasuwa ko zai samu hankalinsa ya ɗauke. A can ɗin ma shirme ya yi. Ya yi ɓatan lissafi.

Zai ci gaba da magana wayarsa ta yi ƙara. Ya saka hannu a aljihun gaban kaftaninsa ya ciro ta ya amsa ya saka a speaker. Wata yar sa ce

“Mun zo asibiti duba Lawisa, Hajiya Mama ta shiga banɗaki ta zame ta faɗi”

Nan take ya rikice

“Subhanallah lafiya dai ko? Bata yi rauni ba ko?”

“Alhamdulillah da sauƙi kaga an ma dubata ɗan tsagewar ƙashi ne”

“Bari yanzu zan dawo”

Ya kashe wayar ya maidata aljihu tare da kallon Nabila da ke kallonshi.

“Mu je ki raka ni sai mu dawo tare.”

Girgiza mishi kai ta yi. Ba dan a inda taje tsautsayi ya rutsa da ita ba, Hajiya Mama bata sonta bata ƙaunarta. Ta daɗe da yanke ma kanta hukuncin raba kanta da inda Hajiya Mama take. Idan sun haɗu zata gaisheta amma ba zata dinga kai kanta inda ba’a ƙaunarta ba. Har yau ta tuna irin gorin haihuwar da Hajiya Mama ta mata sai ta ji wani ɗaci a ran ta. Gori ne kashi kashi a lokuta mabanbanta kuma babu ruwanta a gaban kowa ma yi mata take yi. Babu irin kyautatawar da bata yi mata ba. Shekaru uku da suka wuce, an kwantar da Hajja a asibiti, yarinyar kamar ba zata kai ba. Har suka gama jinya suka dawo gida, bata kira ko ta je duba su ba. Daga ranar ta ƙullaceta saboda ta san bata da wani dalili na ƙin zuwa.

Hannunta ya riƙe ta sigar lallashi

“Ba zan daɗe ba zan dawo. Me zan taho miki da shi?”

Murmushi ta ƙirƙiro ta girgiza mishi kai. Tana kallonshi ya tashi ya tafi. Ta yaya bata gani ba? Ta yaya bata gane ba? Hussaini fa Hassan ya dinga rakowa wajen Safina. Gefe suke matsawa su basu waje. Yawancin tambayoyinsa a kan Lawisa ne, ta tuna. Banda ƴan kwanakin nan bata taɓa zama ta yi tunani ba. Yarinya ta ce ko me?

Ta san sun yi soyayya. Ta ɗauka sun yi soyayya dan a wannan gaɓar komai nata hasashe ne. Bata da tabbas ma abunda ta yi tunanin ta sani a baya dai dai ne ko ya faru. Tana tuna wasu lokuta ya kan ce mata yana sonta. Ta yarda a wancan lokacin. Ta yarda a shekarun da suka gabata. Amma yanzu? Ko a rashin Lawisa ya kulata?

Lawisa bata taɓa raka su ba. Bata taɓa raka Safina ba. Zancen samarinsu ƴan biyu ma bata so. A lokacin ta lura ta ja baya da su har take yi ma Safina maganar

“Toh idan bata son kawancen da mu ba shikenan ba?”

Har gida ta bi Lawisa take tambayarta abunda ke damunta. Ko sun yi mata wani abun ne. Yatsina fuska ta yi

“Yarinta ce bana so. Kun kasa girma har yanzu”

A lokacin ta ji haushin Lawisa dan ta ki jinin wannan girma da take nuna musu. Shekarun da ta basu bai wuce uku ba amma ta dinga kiran du yara ne. Ashe da gaske take. Yarinta ya kaita cusa kanta idan ba’a sonta, ya saka ta raba masoya biyu. Bata jin haushin Lawisa ko ɗaya. Tausayin kanta take ji.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 14Soyayya Da Rayuwa 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.