Skip to content
Part 18 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Ƙafafunta yake matsa mata duk da cewar ba kumbura suka yi ba. Ya san tana jin daɗin hakan. A yanzu haka ma lumshe idanu take tana murmushi.

“Nan da two weeks (sati biyu) ina saka ran yin tafiya In shaa Allah)”

Ta yi narai narai ta fuska

“Allah sarki Boo zamu yi missing (kewa) dinka”

Murmushi ya yi mata tare da jan kumatunta

“Ban ga alama ba tunda baki fara kuka ba”

Dariya ta yi ta ce

“So kake na ɗaga maka hankali ka fasa tafiya?”

Bayan ya taya ta dariyar ne ya yi gyaran murya

“Tare da Safina zamu tafi”

Nan ma wani murmushin ta yi tace

“Allah ya kaimu lokacin. Yaran ina zasu zauna?”

Har ga Allah idan aka barta ita kaɗai a gidan ba zata ji daɗi ba. Ko da guda ɗaya aka bar mata zata so hakan. Idan bata samu ba kuma gida zata je ta ɗan zauna kafin su dawo.

“Wajen Hajiya Mama muke barinsu idan zamu yi tafiya”

“To dan Allah Boo ka bar ni na tafi gida mana. Bazan ji daɗi ba ni kaɗai gidan”

Bai gaya ma Safina ba sai da ta dawo daga makaranta bayan an kwana biyu. Tana shiryawa zata kwanta ya shigo ya sameta yana mata albishiri. Tsalle ta daka ta ɗane shi tsabar murna. Yana dariya ya ce

“To kika karya ni ai kinga an fasa tafiya”

Washe haƙora kawai take yi saboda ita ya gama mata komai da ya tsallake amaryarsa ya zaɓeta domin su tafi tare. Ashe dai matsayinta bai girgiza ba. Ta yarda wani auren ƙaddara ne amma banda haka ai Afrah bata da waje a rayuwarsu.

“Ina za’a kai yaran?”

“A bar su a nan kaga kaɗaici sai ya yi mata yawa”

Gwara baƙin ciki ya taru ya yi mata yawa. Kina amarya an ɗauki kishiya an yi tafiya da ita, ke kuma an barki a gida ga ciki ga rainon ƴaƴan kishiya ai da takaici. Wani abun ma sai suna can. Sai ta nuna ma Afrah wajenta. Tana da isashen lokaci da zata yi tunanin hanyoyin ƙuntata mata amma bari ta gama jarrabawarta guda biyu da suka rage mata.

Tun a nan ta fara shirye-shiryen tafiya. Waya ta buga ma Nabila ta gaya mata shirin da zasu yi tunda tare zasu yi tafiyar. Ta lura jikin Nabilan duk a sanyaye sai tace zata samu lokaci ta zo ta sameta har gida idan ta gama jarrabawar sati na gaba.

**

“Zan yi kewarka”

Shi ne abunda ta ce mishi bayan ya gaya mata zai yi tafiya. Ta san yana ƴan tafiye-tafiye kafin ta aureshi amma tunda suka yi aure bai taɓa barin cikin garin Kano ba. Ta saba kullum sai ta gan shi ko da ba a gidanta yake ba. Murmushi ta ga ya yi dan haka ta ce

“Ba zaka yi kewata ba?”

“So kike ki ji ta bakina kenan. To na ƙi wayon”

Wannan karon tare suka yi dariyar sannan ta tambayeshi yaushe ne tafiyar.

“Cikin next week In shaa Allah. Dama Safina muka jira ta gama jarawaba a makaranta”

“Oh da Safina zaku tafi kenan”

“Yes. Mu huɗu ne harda Nabila”

Jin maganarsa ta yi kamar saukar aradu. Sai da ta nemi jin ta da ganinta na wasu daƙiƙu ta rasa. Da Nabila zai tafi? Da kyar ta samo muryarta ta tambayeshi

“Wai ba Business dinku zaku tafi ba dama?”

“Business trip ne, amma zamu yi amfani da opportunity ɗin mu tafi da su mu ɗan huta”

Su huta. Banda ma rashin adalci ta yaya zasu tsallake amarensu su tafi da uwayen gidansu? Shekara da shekaru suna tare suna tafiye tafiyensu yanzu an aurosu an kawo ai lokacinsu ne amma ace a bar su a gida.

“Kuka kike yi?”

Ta ji ya tambayeta. Bata san lokacin da hawayen baƙin cikin da ta tsinci kanta suka fita ba. Sulalewa ta yi ta kwanta ta bashi bayanta. Tana ji ya bar abunda yake ya karaso kan gadon ya juyo da ita. Lumshe idanunta ta yi dan ba zata iya kallon shi ba

“Meye abun kuka? Uhm?”

Bata iya ce mishi komai ba, hawayen ma ya tsaya. Dama ba da shawararta suka fito ba. Nan ya hau rarrashinta. Duk a tunaninshi kukan rabuwa ta fara tun yanzu. Tausayinta ne ya lulluɓe shi. Da ma zai iya tafiya da ita da ya yi. Nabila bata nuna farin ciki kan tafiyar ba. Kallo kawai ta bi shi da shi. Sai da ya ce mata da Safina za’a je sannan ya ga kamar ta ɗan saki ran ta.

Ya kai hannu ya shafi cikin Lawisa ya ce

“Kai ka hana ni tafiya da mamanka ko?”

Ta ɗan ji daɗi a ranta amma babu abunda zai saka ta farin ciki irin ace an fasa tafiyarnan da Nabila. Bata taɓa tunanin zata ji kishin Nabila irin haka ba. Kusan kullum da hashinta take wuni a zuciyarta. Dama haka kishi yake? A wajenta babu wani abun tashin hankali irin a ce kana da kishiya, Kana da wacca kuke raba soyayya da lokacin miji. Kafin ta kaso aurenta ta taho farautar Hussaini ta dauka damuwarta zata yaye muddin ta aure shi. Ashe abun ba haka bane.

“Tunanin me kike yi?”

Sauke numfashi mai nauyi ta yi ta maida dubanta zuwa fuskarsa. Shi dai Hussaini ba wani kyakyawwa bane ba can can. Ba kuma mugun mai kudi bane. Bai iya zazzafar soyayya ba wani irin soyayya take yi mishi wanda ba zata iya rayuwa babu shi ba. Ita ta san halin da ta shiga da ta rasa shi. Akwai lokutan da ta dinga jin barin duniyar ya fiye mata kwanciyar hankali.

“Tunaninka. Ban san irin son da nake maka ba Baban Hajja”

Hawaye ta ji suna zubo mata. Shi kuma ya zuba mata idanu cikin mamaki. Shi kan shi bai san irin son da take yi mishi ba.

“Nabila ƙawarki ce. Ba kya tunanin hakan zai shafi zumuncinku?”

Wani murmushi ta yi a lokacin wanda har yau bai san manufarsa sai dai ya dinga hasashe sannan ta ce

“Ƙarfafa zumunci dai. Nabila zata fahimceni”

Bai ma san dalilin da ya saka shi yi mata tambayar ba dan ko sama da ƙasa zata haɗe ba zai iya rabuwa da ita ba. Shi ma bai san irin son da yake yi mata ba. Amma ba zai iya gaya mata ba. Gwanda ya bar abun a cikin zuciyarsa ya dinga nuna mata a aikace. Ya kamata yana gidan Nabila yanzu haka dan haka ya mike ba dan ya so ba

“Zan haɗa ki da wani producer ki rubuta musu script din soyayya”

Murmushi ta yi mai tana girgiza kai. Ya sauka daga kan gadon ya ƙarasa shirin da yake yi.

“Zan samu wata ta zo ta zauna da ni kafin ka dawo”

“Hakan ma ya yi. Kafin na tafi zamu je ki yi sayayyar abubuwan da zaki buƙata”

Ta gaya mishi bata buƙatar komai. Dan haka ya yanke zai bata wasu kuɗaɗe ta riƙe a hannunta ko za’a buƙaci wani abun.

**

Tafiyarna ba son shi take yi ba. Tunda ya gaya mata wani abu yake yi mata yawo a rai. Bata taɓa yin tafiya da shi ba duk tsawon aurensu. Watakila fargaba take yi. Sauƙin da ta samu da Safina za’a yi tafiyar. Kullum cikin waya suke yi suna shirin tafiyar kamar masu shirin bulaguro. Har take gaya ma Safina.

Dariya ta yi

“Ai wannan babban bulaguro ne. Idan muka tafi da zuciyoyinsu ai ba zamu dawo musu da shi ba balle su sam ma wasu”

Ita ma dariyar tayi. Lamarin Safina dariya yake bata yanzu. Nabila ta dawo daga rakiyar soyayya. Ta yi ta bata amfana mata komai ba sai bacin rai. Me za’a yi da auren wanda baya sonka? Gaskiya son maso wani ƙoshin wahala. Sama da shekaru 7 tana zaune da wanda babu ita a zuciyarsa. Sai kwanan nan fa abubuwa suke zuwar mata haske. Abubuwa da yawa wanda a da bata fahimcesu ba, yanzu ta gane su sarai.

Babu ita babu soyayya. Ta dawo daga rakiyarta. Masu yi su yi amma Nabila ta sallama. Babu komai a zuciyarta sai jini da jijiyoyi. Babu so, babu ƙiyayya, babu komai! Bata jin soyayyar Hussaini kuma bata jin tsanarsa. Wayam!

“Kullum kullum zan ta kwana a can?”

Hajja ta dawo da ita daga tunanin da ta shiga. Kaya take haɗa mata cikin sati zata koma wajen Umma saboda ba’a yi hutun makaranta ba. Idan an yi hutu kuma a kai ta can gidansu ta kwana biyu

“Eh a can zaki ta kwana har mu dawo”

Ta juya ta dauko wani takalminta

“Zan tafi da wannan idan zamu je strolling da Alhaji na saka”

Haka ta dinga fito da kaya tana bayanin abunda zata yi da su

“Ya isa Hajja kar mu kwashe dukka kayan”

Takan tuna lokacin da Hajja ke ƴar ƙarama. Tana son yara a lokacin da suka fara zama zuwa lokacin da suka fara guje guje. Zata so ace ta ƙara haihuwa. Murmushi ta yi ma Hajja da ta kafa mata idanu. Ta janyota ta rungumeta tana mai sumbatarta

“I’ll miss you” (Zan yi kewarki)

Ita ma ta rungume wuyarta

“Kar ki yi kuka mamana”

Dariya ta yi ta fara mata cakulkuli ita kuma tana kyakyatawa tana kokarin guduwa. Sai ta ji zuciyarta ta yi mata daɗi. Farin ciki mara misaltuwa na lulluɓeta.

Gyaran murya ya yi bayan ya gama daukarsu bidiyo a cikin wayarsa. Ashe har yanzu tana dariya? Da shi ne kadai bata yi kenan. Hajja ta tsagaita da dariyarta sannan ta tashi ta je ta rungume shi. Ya dauketa yana maida kallonsa kan fuskar Nabila da ta riga ta haɗe fuska.

“Kun shirya?”

Ɗaga mishi kai ta yi tana mai miƙewa. Gida zai kaita su yi sallama. A can zata wuni zuwa dare sai ya je ya ɗaukota saboda tafiyar tasu gobe ce. Ta ƙarasa jera kayan Hajja ta zuge ƙaton akwatin sannan ta gyara fuskarta ta saka hijabinta suka fita. Sai da suka fara kai akwatin cikin gidan sannan suka wuce.

**

“Yanzu ba zaki zo ki raka mu ba?”

Girgiza mishi kai ta yi

“Haka kawai ka saka ni kuka cikin mutane”

“Ashe yau za’a sha kallo dan kato da ni kuka zan yi”

Daurewa take yi tana murmushi amma tana ji yanda kewarsa ke cikata tun kafin su tafi ɗin. So take ma ya tashi ya tafi kar ya karya mata zuciya.

Dai dai lokacin aka ƙwanƙwasa ƙofa a shigo tare da sallama. Safina ce ta shigo yara na biye da ita sun yi shirin rakiya tashar jirgi.

“Amarya mu zamu wuce. Sai mun dawo”

“Allah ya tsare hanya ya dawo da ku lafiya”

Miƙewa Hassan ya yi ya zura wayoyinsa a aljihu ya yi ma Afrah sallama ya fice. Bata iya zuwa ta raka su mota ba ta yi zamanta.

Sai da suka biya gida dan ƙaninshi ne zai dawo da mota. Basu jima a gidan ba suka kama hanya harda Nabila dan Hussaini ya mai waya ya ce su je zai taho daga baya. Nan kuwa Lawisa ce ta ce zata rako shi kuma bai san yanda Nabila zata dauki hakan ba. Kila ma ta fasa tafiyar tunda ba so take ba.

Kalaman soyayya babu irin wanda Lawisa bata gaya mishi a mota ba. Zuciyarsa wasai babu wata damuwa. Ji ya dinga yi dama da ita zai yi tafiyarnan. Sam baya son rabuwa da ita.

Ko da suka isa can ɗin, yi tayi kamar zata shige mishi. Sararta ce in dai suka shiga cikin mutane ta dinga yi kamar mai tsoron jama’a. A gaban Alhaji ne kawai bata iya wannan abun. Dama gaban Hajiya Mama ba’a magana. Har farin ciki take ana ririta mata ɗa ana ji da shi. Sai yanzu ta san ya yi aure. Yanda take lallaɓa Lawisa ko ƴaƴan cikinta sai haka.

Ƙwafa Safina ta yi da ta ga abunda Lawisa take yi. Ta ce

“Aikin banza. Ki yi na ƙarshe. Lokacinki ne yanzu”

Hassan da Hussaini kaɗai ke magana. Bata ce musu komai ba suma babu wanda ya bi ta kanta. Safina sai cika take tana batsewa sai kace mijinta ake shigema ita kuwa Nabila idanunta na kan wayarta tana lalubo adduoin da zata yi idan jirginsu ya fara yawo a iska. Banda ganganci ma da saida rai mai ya kai mutum hawa jirgi? A iska fa. Zuciyarta a wuya take. Ko Saudiyya da ta je bata shaƙi numfashi mai daɗi ba sai da ta ji ƙafafunta na taka ƙasa.

“Wai ni me aka miki ne kike ta kumbura?”

Hassan ne ya tambayeta ganin halin da take ciki

“Wannan banzar ce. Bana sonta Hassan. Ta ci amanar Nabila, ta ci amanar ƙawancenmu”

Girgiza kai ya yi yana jinjina hali irin na Safina.

“Yi haƙuri toh. Kar ki bari ta ɓata miki rai ke da zaki tafi honeymoon”

Sai nan ta ɗan saki ranta. Amma Hussaini na karasowa ta ce mishi

“Wai me Lawisa ta ɗauki kanta ne? Ta zo ta samu mutane babu sallama balle tai mana sannu”

“Ke kuwa ki yi haƙuri”

Hassan ya faɗa yana jan hannunta gefe. Nan suka wuce inda za’a auna kayansu

Gani ya yi Nabila bata ma san me ake ba dan haka ya ƙarasa inda take ya yi mata magana. Tayata riƙe ƴar ƙaramar jakar hannunta ya yi suka karasa inda ake awon.

Ko da aka gama basu yi zaman cikakken mintuna goma ba aka kira lambar jirginsu aka ce su fara shiga. Irin firgicewar da yaga ta yi ya saka shi tambayarta lafiya

“Hmn, babu komai”

Sai da ya ɗan yi jim sannan ya yi tunani ko tsoro take ji

“Ko ba komai cewa za’a yi ita da masoyinta suka mutu. Romeo and Juliet”

Turo baki ta yi

“Ni dai na bar iyayena da ƴa ta”

Dariya ya yi

“Ba komai in Allah ya yarda. Ki yi addu’a ki bar komai a hannun Allah. Tsoron nan ba zai taimaka miki ba. It’s a long flight” (tafiya ce mai tsayi)

Shi ya taimaka mata ajiye jakarta a saman inda zasu zauna. Ce mishi ta yi bata son kujerar da ke jikin taga saboda jiri ne zai kwashe ta idan ta kalla. Suka zauna ta dinga karanto adduointa. Ta yi azkar kafin su taho amma ta kuna yin wani. Adduarta kawai su isa lafiya su dawo lafiya.

Basu jima sosai ba maikatan jirgin suka zo suka soma bayanansu. Hakan ya saka cikinta ƙara kullewa. Suma fa sun san jirgin bashi da tabbas amma suke shigarsa har wasu su yi yawo idan ana tafiya. Harda masu cin abinci dan karfin hali.

Hussaini ya taimaka mata wajen saka madaurin kujerar. Ya rike hannunta lokacin da jirgin ke gudu lafin ya kai ga tashi…

A ƙara haƙuri bayin Allah. 

<< Soyayya Da Rayuwa 17

5 thoughts on “Soyayya Da Rayuwa 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.