Hussaini ya zauna kan teburin cin abinci kenan ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofar. Sallamar da aka yi ne ya saka shi ci gaba da abundan yake yi yana cewa,
“Shigo a buɗe yake.
“Hassan ne ya shigo ya maida kofa ya rufe. Nan inda Hussaini yake ya ƙarasa ya zauna. Cokalin zuba abincin ya amshe yana cika kwanon da dankalin da ya sha haɗi. Hussaini na kallon yanda yake afa loma kamar ya shekara bai ci abinci ba.
“Lafiya? Yaushe rabonka da abinci?”
Hassan ya girgiza kai tare da haɗiyar lomar da ke bakinshi.
“Golden morn da cornflakes abinci ne? Ko indomie da ke narkewa minti biyar bayan ka ci shi? Banda madara babu abu mai amfani a ciki na.”
Hussaini ya tashi ya je ya ɗauko wani farantin da cokalin ya zuba abinci.
“Ta yi tafiya ne?”
“Tana nan. Horon ƙarin aure ake min. Da na yi magana ta ce na ƙyaleta zuciyarta bata mata daɗin girki. Ina ƙwaluwa fa.”
Sai da suka yi nisa da cin abincin Hassan ya ce,
“Au, ina mutanen gidan? Hajja na cikin gida ne?”
“A’a sun tafi unguwa uku.”
“Kai, har kun je ka dawo?”
Tambayar ya yi yana kallon agogon da ke jikin bango. Sha ɗaya saura.
“Sun dai ta fi?”
Hassan ya ɗan yi tari, ya dauki lemun citta ya kurɓa, yajin yana yana saka shi runtse idanu
“Wai yaushe rabonka da Hotoro ne?”
Shirun da ya ratsa ne ya ba Hassan amsar tambayarsa.
“Allah ya rabamu da siriki irin ka. Kai tsakani da Allah zaka so mijin Hajja ya dinga maka abunda kake yi? Ko kuwa baka jin dadin yanda sirikan Alhaji ke yi?”
Tsaki ya yi ya tashi ya bar gidan ya wuce gaida su Alhaji tunda dama ya gama cin abincin. Kullum ne sai sun je gida kasancewar unguwar suke. Shi layi uku ne tsakaninsu. Hajiya Mama ta so shi ma ya zauna kusa da su amma ya ƙi. Ta nuna ɓacin ranta a lokacin amma baya sha’awar wannan kusancin. Sai da ya gaida sauran matan gidan bayan ya gaishe da Alhaji sannan ya shiga wajen ta.
Bayan sun gaisa ta ɗauke kai tana danna wayarta. Manhajar whatsapp take kai tana zaɓen wasu kaya a wajen wata ƙawarta da za’a saka a lefen Hussaini.
“Wai Hajiya Mama har yanzu fushin kike yi?”
“Fushin me? Ai kai ɗan kanka ne, dama na daɗe da sallama musu kai.”
“Dama na san kin fi son Hussain. Shi kina murna da aurensa ni kuma ba kya so na yi.”
Ajiye wayar ta yi tana kallonsa. Bata ji daɗin abunda ya faɗa ba kuma bata son hakan ya zauna a ransa tunda ba so take ya fara jin haushin ɗan uwansa ba.
“Ni dukkanku ina son ku dai-dai. Shi ma Hussaini da matarsa bata da matsala babu abunda zai sa na so ya yi aure. Kai kuma fa? Baka fa da wata damuwa. Kuma abunda ya ƙara bata min rai, Hassan ba zaka yi shawara da ni ba? Sai dai na ji maganar aurenka a bakin kishiyoyi?”
Tun da ta fara magana yake kunshe dariya. Ya san halin Hajiya Mama ciki da bai. Ya san abunda zai saka ta saukowa, abunda zai saka ta magana.
“Ni ban gaya musu ba. Kawai Alhaji ne ya je ya gaya musu kin san yanda yake son Inna. Kuma ni ban gaya miki ba dan na san hanawa zaki yi. Amma ki yi hakuri Hajiya Mama.”
Ya san faɗin kalmar Alhaji na son Inna sai ya fi komai ɓata mata rai amma ya faɗa din dan kawai ya kunna ta. Ya maida ita kamar wata kakarsa. Shi yasa ita ma bata ɗaukarsa da gaske, komai nashi ganinsa take kamar na shirme. Mashirirci take masa kallo. Ya fi son hakan. Baya son ta maida shi tamkar Hussaini. Baya son wannan rayuwar.
Tsaki ta yi ta ɗauki wayarta tana ci gaba da abunda take yi a waya. Sai jin shi ta yi a gefenta yana leka wayar har yana kare mata.
“Lah Hajiya Mama kayan lefen namu ne? Nawa zamu bayar?”
Ta ture kan shi ta ce,
“Na Hussaini dai. Je ka haɗa naka ai ka fi shi sanin kan kasuwa.”
“Ai shikenan. Na san Inna ba zata ƙi haɗa min ba.”
Duka ta kai mishi yana kaucewa. Ficewa ya yi yana mata dariya ita kuma tana raka shi da harara.
*****
Nabila na shiga cikin gidansu ta tarar da Daddy zaune a kan farar kujerar roba a tsakar gida yana karatun jarida. Yana ganinsu ya fara sakin murmushi.
“Amarya ta taho nan na biya kuɗin kwaliyyar nan.”
Hajja bata bi ta kan shi ba ta wuce cikin gida ta bar Daddy yana mita kan zasu haɗu ne. Nabila ta sunkuya ta gaida shi tana dariya. Ko zama bata yi ba, Hajja ta fito hannunta cikin na Mummy suka wuce kitchen.
“Yanzu tsakani da Allah Nabila sai ki fito da yarinya baki bata abinci ba? Sai ki je ke ma ki ɗiba ki ci.”
Sai da suka kara gaisawa sannan ta tashi ta zubo wainar gero da ya sha kuli da kuma kunun tsamiya. Tana ci suna hirar duniya kafin a taɓo harkar kasuwancin Daddy. Yana taɓa harkar canji sannan yana aiki a nan Sakateriya ta Audu Bako.
Sai da Hajja ta ci ta ƙoshi sannan ta je tana tsokanar Daddy. Dariya ya yi ya dauko alawa daga aljihunsa ya bude mata sannan ya bata. Nan hirarsa ta koma kan ta su kuma Mummy da Nabila suka wuce kitchen.
Abubuwan da ke cikin zuciyar Nabila game da damuwa ta dinga gaya ma mahaifiyarta tana sharce hawayen da ke sauko mata lokaci zuwa lokaci. Ita kuma Mummy take tausarta tana bata hakuri da kuma ƴan shawarwari. A haka suka gama abincin rana, lokacin Hajja har ta yi bacci shi kuma Daddy ya fita.
Duk lokacin da Nabila ta je gida, la’asar na yi zata fara shirin tafiya gida. Kafin magrib ta isa gida. Amma yau sai ta kara sakin jiki. Sosai zuciyarta ta washe zuwa da ta yi ta ga iyayenta sannan suka yi hira. Su ma a nasu ɓangaren sai suka ɗan kyaleta tunda sun san tana cikin damuwa. Amma Daddy yace ma Mummy idan akai Isha’i zai kai su ya ajiye.
Tun bayana sallar magariba wayar Hussaini ta fara shigo mata amma sai ta danne shi. Yana katsewa ta danne wayar ta kashe shi. Duk wani abu da zai haɗa ta da Hussaini a yanzu bata son shi. Bata son ganinshi ko ɗaya.
Daddy ya dawo daga sallar Isha’i tare da Hussaini. Ya fita zashi masallaci ne ya gan shi zauna a kan mota yana ta latsa waya. Shi ne yake gaya mishi ai wayar Nabila yake gwadawa ta ƙi shiga.
“To banda abunka sai ka zauna a waje ba sai ka shigo ba? Da ban fito ba haka zaka yi tama ko ka haƙura ka tafi? Kai ta abu sai ka ce baƙo? Mu yi sallah sai mu dawo.”
Nabila ta murtuke fuska ta ce ita bata ma san inda wayar take ba. Nan kuwa cikin jaka ta jefa shi bayan ta kashe. Daga nan bata ƙara cewa komai ba sai sauraren hirar da suke yi. Ita haushi ma abun ya bata, sai wani sakar masa fuska suke har suna hira suna dariya bayan baƙin cikin da yake ƙunsa mata. Ran nata bai ƙara ɓaci ba sai da ta ji suna mishi Allah ya sanya alheri na auren da zai yi. Ji ta yi kamar ta kurma ihu. Shi kuma sai wani sunkui yake da kai wai ya ji kunya.
Yana cewa zasu tafi bata ɓata lokaci ba ta ɗauko jakarta ta rataya. Tana ganinshi yana ƙoƙarin ɗaukar Hajja ta yi sauri ta sunkuceta ta saɓa a kafada.
“Da kin bari na ɗauketa tana da nauyi.”
Fakar idanun iyayenta ta yi ta watsa mishi harara kuma murya ƙasa ƙasa ta ce,
“Ban roƙe ka ba. Da can baka san zaka dinga ɗaukar min ita ba sai yanzu.”
Ta san da Mummy ta ji ta faɗa zata mata sosai. Amma ai ba ƙarya ta yi mishi ba, sau nawa yana kallo zata kinkimo Hajja tun daga cikin gida ta kaita nasu gidan amma bai taɓa kwatanta taimaka mata ba? Sai dai ma idan samarin na gidan na nan a ce su taimaka su ɗaukar mata amma shi yana nan zaune yana latsa waya.
Sallama suka yi ma iyayen nata suka fita. Kafin ya buɗe motar su shiga yake ce mata.
“Akwai kaya a boot za’a shigar musu da shi.”
“Ba sa buƙata”
Ta bashi amsa ta shige mota ta bar shi nan a tsaya mamakinta na ƙara lullube shi. Sai da ya yi dan jimmm kafin ya zagaya shi ma ya shiga motar ya tayar. Bai tabya damuwa da shirun da ke gittawa tsakaninsu ba sai yau. Ya rasa dalilin da ya sa hakan ke damun shi.
“Wayar taki babu caji ne? Dan da farko na kira ta shiga daga baya ne na ji a kashe”
“Da caji”
Ta bashi amsa a taƙaice.
“Ta samu matsala ne? Gobe sai.. “
“Ni na kashe”
Ta yi saurin katse shi. Juyawa ta yi gabaɗayanta tana ba shi baya dan bata son ya ƙara yi mata wata magana. Ta takure sosai saboda Hajja na jikinta amma hakan ya fiye mata duk wani kame kamenshi.
Jin abunda ta faɗa, ya san bata buƙatar magana da shi ne ta kashe wayar. Sannan kuma ta juya mishi baya. Nabila ta fara botsare mishi. Dama Hajiya Mama ta gaya mishi za’a yi hakan, sai ya kauda kai. A lokacin bai ɗauka Nabila tana daga cikin irin matan nan ba saboda haƙurinta.
Suna komawa gida ko ta kan shi bata bi ba ta yi shigewarta ɗaki. Bai yi tunanin zata kara fitowa ba amma sai ya samu kan shi da zama falon yana jiranta. Ya fito da wayarsa dan rage lokaci daga nan kuma ya ɓige da chatting da sabuwar amaryarsa.
Washegari da safe wajen karfe goma sha daya na safe Daddy ya kira Nabila yana ce mata a ƙara yi ma Hussaini godiya yanzunnan ya ajiye musu kayan abinci ya tafi. Bai wani ɗaɗata da ƙasa ba dan gani take ba dan Allah ya yi ba. Farkon aurensu yakan musu lokaci lokaci amma ko shekaru biyu ba’a rufa ba ya daina.
Amma Alhaji yana musu. Iyayenta ba mabuƙata bane da rufin asirinsu. Hakan bai hana Alhaji tunawa da su ba idan ya tashi alheri. Suna cikin jerin mutanensa ko ba dan komai ba ko dan kyautatawar Nabila gare shi. Sannan su kan su iyayenta mutanen arziki ne masu mutunci. Buhun shinkafa, katan ɗin taliya, garwar man gyada, kayan shayi duk baya yanke musu. Idan Daddy ya kira yana mishi godiya yakan yi masa wasa ya ce,
“Ni fa so nake ka hakura ka bar min Hajjan nan dai shi yasa. Duk cikin takara ne.”
Anko kuwa, ko da a wani gari ne da ba zata samu zuwa ba to sai ya yi mata. Tun bikin Zahra da aka yi, Inna ta dinga surfafa faɗa a kan abunda Hajiya Mama da Hussaini suka yi, ya ɗauki nauyin share mata hawaye.
Zahra ita ce autar Inna. Kuma ta wajenta ne Hussaini ya ga Nabila. Tun Js2 da aka saka ta a Islamiyyar Tarbiyatul Umma da ke Hotoro suke ƙawance. Ankon bikin Zahran a hannun Hajiya Mama yake duk da cewar daga wajensu Alhajin aka samo. Su suka shigo da shi kuma basu da yawa.
Kowacce, Hajiya Mama ta ɗauka ta bata amma banda Nabila. Ganin biki ya matso ta ka da baki ta yi ma Hussaini magana yace mata ai Hajiya Mama na sane zata bata. Ganin dai bata da niyyar bata tace ya bata kuɗi ta sayi na ƙawaye tunda kafin ta zama matarsa ai ita ƙawar Zahra ce. Nan ya hau ta da faɗan babu gaira babu dalili, ta bashi hakuri ta kama bakinta ta yi shiru.
Ko da aka zo biki Inna ta ganta babu anko ta tambayeta yanda aka yi, bata ce mata komai ba sai dariya ta yi mai ciwo. Inna bata yi ƙasa a gwiwa ba ta je ta samu Hajiya Mama take tambayarta yanda aka yi sai take ce mata
“Lah, kin ga shaf na manta. Kuma ita ma bata tuna min ba. Haba, ni fa na dinga ganin kaya a ɗaki na rasa waye ban bawa ba.”
Dan haushi Inna bata iya ce mata komai ba. Kai tsaye ta je ta gaya ma Alhaji. Shi ma a lokacin bai ce komai ba.
“Tunda kai Hussaini shashasha ne kana da kuɗin amma ba zaka kashe ma matarka ba, ni zan yi ma ‘ya ta. Ba za’a ba mu amana ba mu watsar”
Hussaini da Hajiya Mama yake gaya ma hakan. Tun daga wannan bikin, babu wani abu na rabo da ya ƙara biyowa ta hannun Hajiya Mama.
Ko da Hussaini ya dawo, bata nuna mishi sun yi waya da iyayen nata ba. Bata ma yi mishi magana ba balle ya saka ran wata hira zata shiga tsakaninsu.
Kwana biyu bayan haka, duk wata hanya da zai bi dan wata magana ta shiga tsakaninsu ta ƙi. Bayan gaisuwa babu abunda take ƙara ce mishi. Lafiya ƙalau idan ta gaishe shi, amsarsa bata wuce lafiya. Yanzu kuwa, ƙarawa yake da
“Kun tashi lafiya? Ya Hajja ta kwana? Tana bacci sosai?”
Dauke kai take yi ta yi gaba abunta dan bata ga amfanin bashi amsa ba. Da ya shigo gidan ma, bata wani bi ta kan Hajja balle ta fiya magana. Ita ma kuma dama ba mai saka magana bace. Barta dai idan bata da abunda zai ɗauke mata hankali. Ta dinga ɓarna kenan ko kuma tai ta maka hira.
Yau dirowarta take gyarawa ta haɗa Hajja da aikin goge mata takalma, Hussaini ya shigo. A leɓɓanta ta amsa masa sallama ba tare da ya ji ba
“Hajjata, me kike yi ne?”
“Mimi ce ta ce na goge mata shoes ɗin ta.”
Ya kalli Nabila da ta yi kamar bata san yana nan ba ya ce,
“Uhm, Mimi ba dai kaya ba. Har ta fi mu kaya fa ni da ke.”
“Eh kullum kullum Alhaji yace Mimi, ga kayanki. Ta bashi ya ajiye mata ne?”
Kafin ya bata amsa Nabila ta juyo tana kallonta,
“Yi sauri Hajja dauko min bottled water a store.”
Ta ajiye tsumman da take goge takalman ta ruga dan dauka ruwa. Nabila ta kalli Hussaini
“Ina so zan nemi aiki”
“Aiki? Wani aikin kuma?”
Ya tambaya a mamakance
“Aiki dai wanda ka sani?”
“To ban yarda ba”
Kai tsaye ya gaya mata saboda shi har ga Allah bashi da ra’ayin matarsa ta yi aiki. Ita ma ya yi tunanin bata da wannan ra’ayin tunda bata tabya yi mishi maganar aikin ba. Kawai ya gane rigima take nema.
“Za mu gani”
Shi ne abunda ta ce da shi da ya sanya shi zuba mata idanu. Me take nufi da za su gani? Raina shi ta fara yi dan kwana biyu yana sakar mata fuska?
Masha Allah
Allah Ya Kara Basira