Skip to content
Part 8 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Shekarunta tara lokacin da ta fara haɗuwa da Lawisa. A ƙafa suke dawowa daga makaranta ita da wasu ƴan unguwarsu su da suka haɗa group. Nabila, Safina, Mahmud, Yaƙub sai Salman. kowa yana riga su isa gida. Tafiyar minti goma sai ta kai su mintuna sama da ashirin saboda sai sun tsaya saye saye da ciye ciye. Idan awara suka saya a nan zasu zauna su cinyeta.

Ranar sun sayi fan lolly mai ƙanƙara suna sha suna hirar abunda ya faru a ajujuwansu kasancewa Nabila, Safina da kuma Salman ajinsu daban. Yaƙub ma daban da na Mahmud. Wata yarinya suka lura tana bin su. Da suka tsaya sayen fan lolly ɗin ma ɗan nesa da su ta tsaya.

“Ƴar ajinmu ce new comer.”

Yaƙub yake gaya musu. Yaran ajin dariya suke yi mata saboda bata iya turanci ba. Har wani malami na cewa village girl (ƴar ƙauye) ce ita.

“Bari ku ga wani abu.”

Safina ta faɗa tana juyawa tare da yi ma yarinyar alamun ta ƙaraso inda suke. Sum – sum yarinyat ta ƙaraso inda suke tana sunkuyar da kai.

“Why are you following us.”

Bata ɗago ba yarinyar tana ta kallon takalman ƙafarta sabbi gal sai sheƙi suke yi.

“Ke ba kya ji ne? Why are you following us?”

“Pollo”

Dariya suka bushe mata da shi har Safina na kaiwa ƙasa tsabar dariya. Yarinya kuwa ta fashe da kuka. Lokaci guda dariyar tasi ta ɗauke.

“Kukan me kike yi babba da ke? Cewa na yi me yasa kike bin mu?”

Share hawayenta ta yi sannan ta gaya musu cewar waɗanda take bi ne suka ce kar ta ƙara binsu ita ƴar ƙauye ce. Salman ya ce ta biyo su. Suna tafe suna yi mata tambayoyi. Sai da suka yi mata dariya da tace musu sunanta Lawisa. Wai wani irin suna ne Lawisa. Canja mata makaranta babanta ya yi amma da wajen kakarta take. Tun daga ranar suka fara yawo da Lawisa.

Iyayen Lawisa sun rabu tun tana ƴar shekaru huɗu. Rabuwar da suka yi ba ta daɗi bace sam shi yasa da suka rabu mahaifiyarta ta tafi da ita, ko biyar bai ɗauka ya ba ta ba. Ita kuwa dama ba mai sana’a bace kuma babu boko bata damu da shi ba. Kakar Lawisa ita ke ciyar da su dan haka ma babu maganar makaranta.

Sai da Lawisa ta kai shekaru bakwai sannan mahaifin nata ya soma yin aiken kuɗi. Abunda ya kawo musu canji kenan a rayuwarsu. Ko da ya buƙaci ta je hutu wajensa basu hana ba. Duk da mahaifiyarta ta so ƙin amincewa a cewarta riƙeta zai yi.

Har gida mahaifin Lawisa ya kawota bayan sati guda inda ya nuna rashin jin daɗinsa na rashin zuwa makarantar da Lawisa ke yi. Ya ɗauki kuɗi ya bayar ya ce a saka ta a makaranya. Wata gujari gujarin makaranta aka nema aka sakata wanda ba kullum take zuwa ba. A haka har mahaifiyarta ta yi aure ta dawo garin Kano ta barta da kakarta a Gombe.
Dalilin dawowarta Kano shi ne rasuwar kakarta.  Mahaifinta ya so riƙeta mahaifiyarta ta ce bata amince ta bar ƴarta hannun matar uba ba. Nan mahaifin nata ya saka aka bincika masa makaranta mai kyau ya biya kuɗin makaranta. Kamata ya yi ace tana makarantar sakandire amma tsabar babu abunda ta sani ya saka aka barta a firamare, idan shekara ta ƙare sai a ga ko zata iya coping da sakandire ɗin. 

Gidansu Nabila take zuwa Mummy tana yi mata lesson. Har ta ce Nabila da Safina su dinga yi mata turanci har ta iya ita ma. Cikin ɗan lokaci saboda naci irin na Lawisa ta fara maida musu turancin duk da sukan ɗan ci gyaranta.

Gidan da mahaifiyar Lawisa ke aure, gidan Malam Tasi’u irin rayuwar da kowacce ke ciyar da kanta da ƴaƴanta ne. Malam Tasi’u zai kawo masara da gero da ajiye shikenan ya gama. Sai jifa jifa zai ɗauki kuɗi ya ba mace domin yin wasu hidindimun. Uwar gidansa Mama Harira ƴaƴanta biyar. Ya yi ƴan aure aurensa amma matan basa zama saboda halinsa na rashin kulawa.

“Wallahi bazan ɗauki nauyin ƴar wani ba. Nawa ƴaƴan ma sun ishe ni!”

Abunda ya faɗi kenan lokacin da amaryarsa Atika ta dawo daga rasuwar mahaifiyarta tare da ƴarta. Tijara ya kafa mata kan sai dai ta mayar da ɗiyarta ita kuma tana bashi haƙuri tana magiya. Ga yarinya nan a raɓe a ƙofar ɗaki tana jinsu sai hawaye take yi.

“Ai kuwa dai zama ya kama ta”

Cewar Harira daga tsakar gida inda take tankaɗe garin masara. Da shiru ta yi musu tana jin su, bata da niyar magana amma yarinyar ta bata tausayi matuƙa.

“Ida ba’a riƙe agola ai kai ma da gidanka babu masaka tsinke. Daina roƙonsa, ke kike mai alfarma da kike zaune da shi da mugun hali irin nasa. Ƙarƙari yai ta kumfar baki fa.”

Harira mace ce mai kirki. Bata da lokacin yin kishi a kan Tasi’u. Abunda ke gabata shi ne sana’arta na sai da su daddawa, kuka da kuɓewa. Sai idan ana neman ma’aikata a manyan gidaje na unguwa.

Farkon zuwan Atika gidan, duka abunda Malam Tasi’u ya samo nan ɗakinta yake zuwa su yi ƙurmusunsu sai dai da safe Harira ta ga takardar tsire ko ta balangu. Idan ma doya da ƙwai ne da gangan take barin ɗan ƙwaya ɗaya da safe ta ba autan Atika wai duk dan ta ji haushinta. Ranar nan ta ka da baki ta ce,

“Atika tausayi kike bani. An yi ni kuma an yi dubu kafin ke. Lokaci ne zamu zama ɗaya da ke.”

Bata gane zancen ba sai da ta haihu da watanni huɗu. Gabaɗaya ta kasa gane kan Malam Tasi’u. Ta zabge, ta lalace, ta shiga damuwa.

“Yanzu kika fara gane dalilin da yasa matan Tasi’u ke barinshi. Masarar nan dai ita zaki dawo kina ci. Idan kika ga kin ci mai daɗi to guminki ya saya miki ko kuma Allah ya tsaga da rabonmu a wajen Tasi’u. Yanzu zaki fuskanci rayuwa. Idan har kina son zamanki a nan gidan ya ɗore, to ki cire shi a zuciyarki ki tashi ki nemi na kan ki.”

Tun tana ganin abun kamar wasa, tana ɗauka kishi ne irin na Harira kuma ita ta shiga tsakaninsu. Sai daga baya ta ga ba haka bane. Gashi ita ba mai sana’a bace. A wannan halin aka kawo Lawisa.

In dai Harira zata ba ƴaƴanta abinci, to kuwa zata ba Lawisa. Atika ce dai zata san abunda zata ci. Hakan ba ƙaramin sauƙi ya sama ma Atika ba amma ta san muddin Shehu ya kai munzalin da zai fara cin abincin shima to tallafin da Harira ke bayarwa, zai kau.

“Kitson da kikai ma Lawisa ya yi kyau. Me zai hana ki mayar da shi sana’a ko ba komai kya dinga samun ɗan canjin ki?”

Tunda bata da wani zaɓi, sai ta amince. Duk inda Atika ta ji ana neman mai kitso sai tace a kishiyarta ta iya. A hankali ta fara samun mutanen da take yi ma har wasu matan kan aiko a kirata har ta yi musu. Sai Atika ta sauke kai suka haɗe kawunansu suna zaman lafiya.

Ranar wata Laraba, Lawisa bata je makaranta ba shi ne abokan tafiyarta suka yi shawara su biya ta gidansu su duba ko lafiya. A tsakar gida suka tarar da ita kwance, zazzabi take yi. Nabila ta bata awarar da ta saya mata. Kullum da safe Daddy zai bata kuɗin makaranta sai ya haɗa da na Lawisa saboda ta bashi labari ita bata zuwa da kuɗi. Ko abincin break, duk abunda za’a zuba mata to tare da na Lawisa ake zuba mata. Da wuya ka ga Lawisa da kuɗi. Har Lawisa ta yi sati kullum sai sun biya sun kai mata abunda suka saya.

Aa halayen Lawisa, akwai naci. Naci mai ban haushi ma kuwa wanda ka kan ji kamar ka kai mata duka. Atika na yawan dukanta a kan hakan amma ko a jikinta. Idan tana son abu duk wulaƙancin da zaka mata ba zata haƙura ba.

“Ke wallahi Lawisar nan baki da zuciya.”

Safina ta faɗa tana harararta. Wani yaro ta maƙale ma suna Js2. Babu irin wulaƙancin da baya yi ma Lawisa amma kullum tana maƙale da shi.

“Ku yara ne. Baku san soyayya ba.”

Shekaru biyu ta basu amma ji take kamar shekara goma ta basu. Yaron nan sai da ya dawo yana kula Lawisa ko dan ta ƙyale shi. A komai take da naci shi ya sa ma take ɗan ƙoƙari a makaranta.

Lawisa ta na da baƙar wayo. Ko mahaifiyarta ba zata gaya mata wayo ba. Idan ta je wajen mahaifinta hutu, ya kan haɗota da ƴan kuɗaɗe saboda wani sha’ani tunda ba waya suke yi ba sai dai idan ta samu Daddy yana nan ya kira mata shi. Duk binciken Atika haka take haƙura bata ganin kuɗin. Shigowa gidan ne ba sa yi. Idan tana son raba Nabila da abunta, cikin ruwan sanyi take sakata ba ta. Ta san yanda zata bi da ita ta. Abu ɗaya ne ka kasa saka ta bata.

Daɗin baki, iyayi, kwaliyya, shiga rai duk Lawisa gwana ce. Akwai ta da kirki da son jama’a. Ga ta aron halaye na gari. Wuyarta ta zauna da mai halin ƙwarai bata kwashi halayensa ba.

Ita ta saka ma kanta Suna Wisa Wise saboda wayewar da ta yi, a cewarta. Da tsokana suke kiranta sunan, lokacin suna ss1. Lawisa kyakkyawa ce dan mahaifiyarta ma ba baya ba. Hasken fata wajen mahaifinta ta ɗauko shi. Shi yasa take nan kamar buzuwa.

Ta yi aure a Zaria in da ta auri wani ma’aikacin banki. Su Nabila sun rigata aure da watanni goma sha uku.

“Mum ɗina ta takura min nai aure, kullum sai ta min magana. Gashi Dad ɗinmu yana so na samu na haɗa degree ɗina tukunna.”

Ba maganar bace ta ba Safina haushi ba, wani Mum da Dad da take ambato ne ya ƙular da ita ta kasa bata amsa. Lokacin ta zo yi mata barka ne bayan ta haifi Ilham.

Watanni biyu bayan nan ta yi aure aka kaita Zaria. Haihuwarta biyu, na farkon ƴan biyu ne amma macen ta koma. Shekara ɗaya cif bayan haihuwar farko ta yi na biyun. Auren bai cika shekara uku ba ta dawo gida. Duk ta lalace saboda rashin kula na mijin nata da tashin hankalin ƴan mata. Gudowa ta yi bayan ya kawo mata mace har ɗakinta ta yi magana ya lakaɗa mata duka. Haka ta dawo gidan mahaifinta da takalmi wari da wari. Kuɗin mota ma sai biya mata aka yi bayan an haɗa mata a tashar kuma direba yai mata ragi. Duk wanda ya ganta a lokacin sai ya koka mata.

Mahaifinta ya ga babu dalilin da za saka a kashe masa ƴa tunda dai auren nan babu dole a cikinsa. Ana yi ma mijin magana ya kawo mata takardarta da ƴaƴanta. Nan gidan mahaifinta ta baro su ta dawo gaban mahaifiyarta. Da cewa tayi ta bar mishi kayan ɗaki amma Atika ta yi tsalle ta dire ta ce sai an amso su. Haka ya yi musu kuɗin mota aka kawo. Ta ɗauki ɗaya ta saka a ɗakinta ɗayan kuma ta ba Harira ta saka a nata ɗakin.

*****
Tana shawo kwana ta hango motar Hussaini. A lokacin magariba ta kunno kai. Cikin unguwa ta faɗa ɗazun da ya biyo ta. Tafiya take bata san inda take zuwa ba. Ƙwaƙwalwarta ta kasa haɗa Hussaini da Lawisa a waje ɗaya. Dakalin wani gida ta samu ta zaune ta dafe kai tana ta kiran sunan Allah har ta samu nutsuwa. Ta ɗan jima a zaune kafin ta miƙe ta nufi gida.

Bata son Hussaini ya gan ta. Bata son ganin shi dan haka ta shige gidan wata maƙociyarsu tace ta zo Mummy bata nan. Kan kujera ta samu ta kwanta ta yi shiru dan bata son magana. Babu abunda idanunta suke yi sai tsiyayar hawaye.

Sai da aka yi sallar isha’i sannan ta tashi ta fita. Lokacin babu motar Hussaini da alamu ya gaji ya tafi gida. Dama me zai ce mata? Kawai gulma ce irin tashi.

A daren Mummy ta so kiran Hussaini ya zo ya ɗauketa amma Nabila ta fashe mata da kuka.

“Bana son ganinshi Mummy. Kamar na tsaneshi nake ji.”

Mummy bata hana ta kukan ba. Tabarta ta yi mai isarta sannan da kan ta ta yi shiru. Kulle gidan Mummy ta yi kasancewar Daddy ya kira ya gaya mata sai asuba jirginsu zai sauka kasancewar an ɗaga lokacin tasowar jirgin nasu daga birnin Ikko.

Sun raba daren Mummy na tausarta tana kwantar mata da hankali. Tare suka je ɗauko Daddy suka dawo gida.

“Allah ya kyauta.”

Kawai ya iya cewa jin Lawisa ce wacca Hussaini zai aura amma kana gani ka san ka san ran shi ya yi matuƙar ɓaci. Dama can dannewa yake a kan maganar auren tunda dai Allah ya hallata kuma bai isa ya ja da ikon Allah ba kuna daɗim daɗawa ba huruminsa bane yin magana ama yanda yake ji a ransa kamar ya ci ma Hussaini mutunci.

Wanka ya yi ya ci abinci ya shiga ɗaki ya kwanta. Ko mintuna biyar bai yi ba sai ga Hussaini dan Mummy ta riga ta kira shi. Bai iya shigowa gidan ba ita ma bata buƙata ba. Mota ta shiga ya ja suka wuce gida. Shiru babu mai cewa komai. Tun jiya yake ta tsara abunda zai ce mata idan ya ganta. Da ƙyar ya yi bacci jiya kasancewar bai san inda ƴar mutane take ba. Yanzu ma yana ganin wayar Mummy sai da gabansa ya tsinke. Jin tana gida ya bazamo ya taho ɗaukarta.

Har suka isa gida bai samu abunda zai iya ce mata ba. Sai a jiyan ya yi tunanin halin da Nabila zata iya shiga idan ta san ƙawarta zai aura. Sai a jiyan ya tuna ana iya barin halas dan kunya. A jiyan ya san bai yi ma Nabila adalci ba.

Yana kallo ta buɗe ƙofa ta fita daga motar ta yi cikin gida. Tausayinta yake ji haka kawai na saukar mishi. Ko da ya shiga falo bata nan. Ya murɗa ƙofar ɗakinta ya ji a kulle. Abunda bata taɓa yi ba sai sau ɗaya. Wannan ne na biyu. Baya so ya takura mata dan haka ya wuce nashi ɗakin. A nan bacci ya yi awon gaba da shi.

Wayarta ta gani a kan gado a kashe. Da dukkan alamu mutuwa ta yi saboda an kira bata ɗauka ba har cajin ya mutu. Ga mamakinta tana saka caji ta ga akwai har ya fi rabi. Babu tantama Hussaini ne ya kashe ta. Ta duba ko an kira ta sai ta ga Safina ce ta yi mata kira ya fi talatin dan haka ta biyo kiranta.

“Haba Nabila ina kika shiga tun jiya na kasa sukuni. Wacece Lawisa Salisu? Ni mutum ɗaya na sani da wannan sunan Wisa Wise. Amma a tunanina Lawisa ba zata miki haka ba.”

“Hm”

Shi ne kawai abunda Nabila ta iya faɗa tana share hawayen da ya gangaro mata. Safina bata jira wani ƙarin bayani ba ta lailayo zagi ta aika ma Lawisa tare da kashe waya. Bata san dalili ba amma sai ta tsinci kanta da kiran Zahra.

“Zahra zaki iya zuwa?”

<< Soyayya Da Rayuwa 7Soyayya Da Rayuwa 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.