Ƙwaƙwalwarsa ce ta shiga juya mishi lokacin da ya shigo cikin falon gidanshi. Akwai bambaci tsakanin fitarsa ɗazu da rana da kuma shigowarsa yanzu bayan sallar isha. Fayau! Babu komai a falon. Babu shakka an yashe su ne. Hatta da labule babu.
Ɗakinsa ya shiga da saurinsa bayan ya saki ledar da ke hannunsa. Laptop ɗinsa da ƴan kuɗaɗensa da ke ajiye yake ta addu’ar Allah ya sa ba’a haɗa da su an sace ba.
A gefe ya ga kayansa a ajiye kamar zama aka yi aka jera masa su. Nan idanunsa suka hau kan jakar laptop ɗin. Yana buɗewa ya gan ta a ciki ya saki ajiyar zuciya. Gaya ma kan sa yake dole ya yi back up ɗin ayyukansa saboda tsautsayi.
Ɗakin Hajja ma fayau sai akwatunanta a jere sai kuwa takalmanta da ya gani cikin kwali. Kan sa duk ya ɗaure. Ga dukkan alamu Nabila ce ta zo ta jera komai. Dama ta kira shi bayan ya fita ta ce mai zata fita. Ƙila da ta zo ta iske satar sai ta tsaya gyaran gida. Amma kuma ina mai gadi har aka shigo aka saka kaya a mota aka fita?
Yana kunna fitilar ɗakin Nabila haske ya gauraye sai ya ganta kwance a kan katifa tare da Hajja. Ganin idanunta biyu ya saka shi tambaya.
“Nabila ina kujeru da kayan ɗakinmu?”
“Na sayar”
Cikin hanzari ya ƙarasa shigowa ɗakin yana ƙara maimaita abunda ta faɗa cike da mamaki.
“Ban gane ba Nabila. Furniture ɗinmu kika sayar? Ɗazu da zan fita fa suna nan.”
“Eh da ka fita na kira masu ƙurƙura suka kwashe. Na ɗauki kuɗi a ɗakinka na basu advance.”
Bai san lokacin da ya ƙaraso kusa da katifar ya zauna yana dafe ƙafafunta ba. Gumi ne ya ji yana karyo masa ba dan zafin da ke gari ba sai dan kiɗimewa da yayi da zancenta.
“Um um Nab.. Nabila kuɗin ɗakina?”
Maganar ta fito da sauri kuma a sarƙe.
“Eh, a yellow da baƙar leda a cikin viva”
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”
Jikinsa ne ya yi sanyi ƙalau yayin da wani abu kamar tsoro ya dirar masa a cikin cikinsa.
“Nabila wallahi wallahi kuɗin mutane ne.”
Ta gyara kwanciyarta tana rufe idanunta.
“To ni dai na bayar kuma ba zan iya komawa na amso ba. Sun ce nan da sati guda zasu kawo kuma zan cika musu seven fifty.”
Hannunsa har ɓari yake yi, ya ɗauke daga kan ƙafarta ya mayar, ya ɗauke ya kuma rasa inda zai saka su. Ba abun ya ɗora a kai ba. Kamar gaske kamar wasa. Da alama wasa take mishi. Nabila ba zata taɓa yi mai haka ba. Ƙila so take ta ɗan kaɗa masa ƴan hanjinsa kuma ta yi nasara. Hakan sai ya saka mishi nutsuwa. Ya tuno da ledar da ya shigo da shi gidan.
“Na kawo miki gasashen kaza. Zo mu je ki ci.”
Da kamar tace ba zata ci ba ko ya je ya saka a fridge sai kuma ta tashi zaune tare da cewa.
“Kawo min.”
Kamar mutum mutumi ya miƙe ya je ya ɗauko ledar ya haɗa da faranti ya kawo mata. Ta buɗe ledar ta baje kazar a faranti ta ci ta ƙoshi sannan ta shiga banɗaki ta wanke bakinta ta koma ta kwanta.
“Idan zaka fita ka kashe min fitila.”
Sai ya tuna da cewar ɗakinsa fa hatta da carpet babu. Tunda ga katifa ai dole nan zasu kwana kafin gobe kuma bayan ta sauko ya ji abunda ya faru da inda ta kai musu kayan gidan nasu. Ya san duk fushi ne ya saka ta cire su.
“Ɗakin ai babu gado kin manta?”
“Ina sane. I need space. Idan kuma ba so kake na fita na bar maka gidan ba.”
Haƙuri ya bata ya kwashi kwano ya kai kayan kitchen. Wanka ya fara yi kafin ya shimfiɗa abun sallah a ƙasa. Kayansa ya dinga ɗorawa a kai daga ƙarshe ya saka zanin gado ya kwanta. Tunda uwarsa Hajiya Mama ta haife shi bai taɓa jarraba kwanciyar ƙasa ba. Duk runtsi duk wuya – balle kuma babu. Sai yau da ya ɗauko auro ƙawar matarsa.
*****
Kwatanta tashin hankalin da Hussaini yake ciki ba zai yiwu. Gumi ke tsatsaffo mishi bayan Nabila ta nuna mishi rasit ɗin wajen kafinta ta kuma rantse mishi kuɗin ɗakinsa ta ɗauka ta biya. Gaya mishi tana buƙatar ciko ba shi ya dame shi ba. Kuɗin yau yake son rabuwa da su.
Akwai kuɗin da zai kai ma Lawisa na hidindimun biki. Ta ce zata gyaran jiki da su ƙunshi. Walimar da zata yi ma duk shi zai ɗauki nauyinsa. Sannan akwai kuɗin masu fenti da na ƙofofi da window ɗin net da kuma masu durowowin kitchen. Yanzu yaya zai yi da mutane?
“Da kin yi shawara da ni Nabila.”
Ci gaba ta yi da murza cin cin ɗinta bata kula shi ba. Dama zaune ya sameta a falon a kan tabarma tana aikinta. Da ya ƙara yi mata zancen kuɗin ta tashi ta ɗauko mishi risit. Ya ɗauka kuɗin zata ɗauko.
“To ina sauran kuɗin?”
“Jiya da Zahra ta zo na bata ta saya min labule da su carpet. Ɗazu ma ta kira ni ta turo min a whatsapp har na zaɓa ma ta koma gida”
Ganin ya dafe kai sai ya ɗan bata tausayi. Da gaske da kuɗin ta yi amfani amma tuntuni Daddy ya aiko mata wasu kuɗaɗen ya ce ta yi gyara da shi. Yanzu da zai nuna ɓacin ransa zata ɗauko kuɗin a banki ta bashi abunshi.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”
Kawai yake ambatawa yana jingine da jikin bango. Baya son bashi ko kaɗan. Da tayi mai magana, bayan biki da sati biyu zai samu wasu kuɗaɗe dan ya saka kuɗi ya sai wasu kaya sun ma taho nan da sati yake saka ran isowarsu. Kuma suna isowa ƴan sari zasu kwashe. Dole ya nemi kuɗaɗe duk inda suke ya kai ma Lawisa ya biya masu aiki.
“Yaushe zaka bada cikon kuɗin?”
Juyowa ya yi ya kalleta daga bakin ƙofa. Babu abunda ya dameta sai aikinta da take yi. Bai san abunda zai ce mata ba sai ya ce,
“Nawa ne cikon kuɗin?”
“Seven fifty na ce jiya ko ka manta har?”
“Wani irin kaya kika saya har haka? Kin san nawa kika ɗauka?”
“Five hundred ce. Komai fa canjawa za’a yi Hussaini. Ko ba komai nima ka shafa min amarci.”
Yanda take maganar tana murmushi sai kawai ya saka kai ya fita. Bata san abunda yake damunshi ba ga dukkan alamu. Kuma zai haɗu da Zahra. Ita ta zo ta zugata ga dukkan alamu. Waya ya ɗauka ya kira Hassan ya nemi ya ranta masa wani abun.
“Kai, ni fifty thousand kawai zan iya baka shi ma na shiga takura.”
Ya san ya yi mishi ƙokari gaskiya tunda shi sabon gidanshi zai tare tunda haɗa su gida ɗaya zai yi. Shi nashi gidan bai gama ba kuma baya tunanin zai haɗa su ko nan gaba. Matsalar wacca zai saka a gidan ne. Mai yawan ƴaƴa ita zata shiga gidan.
Bashi da wani zaɓi dan haka ya nemi kuɗi wajen Hajiya Mama. Idan bai samu ba a wajenta ne dole ya tambayi Alhaji duk da sai ya sha faɗa da zagi kafin ya bashi. Dubu ɗari uku da hamsin ya samu a wajen Hajiya Mama tana ta mita ma kan raba lefen da Alhajin ya yi shi ya saka ta sayi wasu kayan ta yi ciko.
Wajen Inna ya je ya aro sauran ɗarin dan baya so mutuncinsa ya zube idanun Lawisa da ƴan uwanta. Baya so ta ga gazawarsa ko kaɗan. Masu aiki ya fara biya kuɗinsu sannan ya wuce wajen Lawisa.
Ta ƙara haske, fuskarta sai wani sheƙi yake yi ta ƙara cikowa. Wani daɗi ne ya baibaye shi dan Lawisa matar da zaka shiga ko’ina ne da ita. Mata ta kere ma sa’a. Godiya ta dinga zuba mishi tana kwararo masa addu’o’i waɗanda suka saka zuciyarsa yin sanyi. Bai jima ba saboda ƙamshin da ke fita daga jikinta ya saka shi wani tunani na daban.
*****
“Hassan magana fa nake yi maka ka min banza.”
Inda take bai kalla ba ya ci gaba da danna wayarsa. Tunda ta bi shi har shago ta rufe ƴar mutane da duka yake jin haushinta. Ɓacin ran da ta haddasa mishi har yanzu ya tuna sai ya ji kamar ya rufeta da duka ita ma.
Bayan ya ajiyeta kai tsaye ya wuce gidansu Afrah. Ta yi mamaki da ta ga kiranshi. Lokacin tana duba fuskarta a madubi, akwai inda farcen matarsa ya karce mata fuska har fatan wajen ya ɗan ƙwarzane. Kasancewar mahaifiyarta ma’aikaciyar jinya ce, ba sa rasa akwatin bada taimakon gaggawa a gidan. Ta ɗauko auduga ta dangwala a spirit, ta shafa shanshanbale ta rufe wajen da plaster ta fito.
“Subhanallah kin ji ciwo ko? I’m so sorry dimples.”
Murmushi ta yi tana girgiza kai.
“Lah Boo ba komai fa.”
“Ba haka Safina take ba. Ban san me ya faru ba.”
Wani murmushin ta kuma yi. Kullum cikin faɗin halayen ƙwarai na matarsa yake yi. Bai taɓa zancenta ba tare da ya yabe ta ba.
“Safina bata da matsala.”
Wannan kullum shi ne furucinsa. Abun yana taɓa zuciyarta amma haka taka daurewa.
“Boo, ko ni na ganka da wata zan iya haɗawa da kai na zane.”
Ƴar dariya ya yi yana girgiza kan shi. Ya ji daɗin yanda ta fahimci halin da ake ciki.
Abunda ke ɓata mishi rai shi ne, ya san mutuncin da take da shi a idon Afrah, wanda ya ɗauki sama da shekara yana nuna ma Afrah to idan bai rushe dukka ba to rabinsa babu.
“Kana ji ina maka magana amma dan wulaƙanci ka ƙi amsa ni.”
“Ke kar ki dame ni kin ji ko?”
Hawaye ta ji suna sauko mata. Ita bata saba wannan rayuwar ba. Tsakaninta da Hassan babu kyara babu hantara sai tsantsar nuna soyayya da kulawa gami da tattalawa. Babban ɓacin ranta ma a kan wata mace ake yi mata hakan. Haƙuri kawai zata yi har zuwa lokacin da za’a yi auren tunda an gano cewa akwai rabo. Idan ta yi yunƙurin hanawa to zata rasa ran ta.
“Ka yi haƙuri Hassan”
Fashewa ta yi da kuka mai cin rai. Abun yayi mata yawa. Sai zuciyarsa ta karaya. Shi kan shi ba daɗin zaman da suke yi a yanzu yake ji ba. So yake ya nuna mata kuskurenta kuma zuwa yanzu yana ganin kamar ta gane.
“Na haƙura. Zo ki zauna”
Ta samu waje ta zauna tana share hawayenta tare da jan majina.
“Dan Allah Nabila ki guji yin abunda zai taɓa mutuncinki. Abunda zai janyo miki raini bana son shi ko kaɗan. Ki ja girmanki a zauna lafiya.”
“In shaa Allah. Ka yi haƙuri bazan ƙara ba. Sharrin zuciya ne, ban san lokacin da na biyo bayanku ba.”
“Ya wuce. Yanzu zubo min zoɓon nan da kika yi jiya. Raina ya biya kawai daurewa nake yi.”
Murmushi ta yi mishi ta miƙe dan zubo mishi. Ta samu zai sha abunda ta girka bayan ɗan lokacin nan. Sai da ya sha kofi biyu sannan ya fara jan ta da hira irin wacca suka saba.
*****
Ta ɗaga wani leshi daga cikin lesukan da ke gabanta tana kuma magana a cikin waya,
“Eh yanzu aka kawo min nake dubawa. Color combination din sun yi kyau. Kin dai tabattar masu tsada ne ko?”
A ɗayan bangaren aka bata amsa,
“Wallahi Hajiya Safina masu tsada ne. Sababbin kaya ne ma.”
“Shikenan, idan na zaɓa sai na turo miki. Ki zabo min takalmi da mayafi idan an zo karɓa miki sauran kayan ki bayar a kawo min.”
Kayan take kallo, babu na ƙasa da dubu tamanin. Wani ja da baƙi ta ɗauka ta san kalar na yi mata kyau kuma yana cikin wadanda suka fi tsada. Bikin Hassan take yi ma shiri. Akwai dinner da aka gayyace ta. Sai ta saka yarinyar ta raina kanta. Kwaliyya zata yi na kece raini. Tana da kayan da ta tanada na ɗaurin aure, Anko zata yi da Hassan su sha hotuna.
Yanzu shirin na dinner take yi. Ta sayi sabon gwal danƙarere bayan ta saida ɗaya a cikin filayen yaranta da Alhaji ke bayarwa. Da ragowar kuɗin take sauran hidindimu sannan gwal ɗin da aka saka mata a lefe ma ta sayar.
Tunanin Nabila ne ya faɗo mata. Ko me take ciki yanzu? Bayan sun yi waya ta tabattar da cewa Lawisar da ta sani ce zata auri Hussaini ta buga mata waya. Zageta ta yi tas! Da farko ta so ta yi mata bayani amma bata saurara mata ba. To bayanin me zata yi mata? Ai babu wani bayani a wannan lamarin. Amana ce ta riga da ta ci shi.
Kiran Nabila ta yi ta tambayeta lafiyarta da kuma shirin da take yi kasancewar bikin sauran kwana tara.
“Shirin me zan yi Safina? Auren Lawisa ko na Hussaini? Ni babu abunda ya shafe ni da wani aurensu. Can su je su karata.”
“To ki zo namu event ɗin mana. Ni zan je dinner din su. Baki ga shirin da nake yi ba.”
Murmushi Nabila ta yi ta ce,
“Um um Safina. Idan nace zan je ma ƙarya nake yi. Bani da karfin zuciyar yin duk wata walwala da kike tunani. Ba kuma zan iya faking ba. Bani da jarumtarki.”
Da gaske kam ita jaruma ce tunda ta ji ta kuma gani zata je wajen dinner ɗin mijinta da sabuwar matarsa. Kishiyarta! Ba dan ƙwarin gwiwar da Hajiya Bilki ke bata ba, da bata jin zata iya ci gaba da zama da Hassan ma.
“Ki tsaya a nan wata ta raba ki da mijinki.”
Cewar Hajiya Bilki,
“Ƴaƴana biyar da mijina na fari ya zo ya yi min kishiya. Yarinya ce ƙarama. Na ɗauketa da zuciya ɗaya muke zaman tsakani da Allah. Ashe ita bata da babbar maƙiyiya irina. Bayan baƙar wahalar da ta bani, baƙin cikinsu da na ƙunsa, da ƙyar ta shekara a gidan aka sakoni. Ban ci ba ban sha ba. Wallahi, wallahi kika yi sake wannan yarinyar da kike ganin bata kai ki komai ba sai ta jefa ki a mummunan yanayi.”
Faɗin tashin hankalin da ta shiga ba zai yiwu ba
“Saboda haka, ki tashi ki nemi tsarin jikinki da na yaranki. Duk wani mugun nufinta ya ƙare mata a kanta. Kar ki bi bokaye su saka ki a halaka. Kissa da kisisina ya ishe ki.”
Shi yasa ta je ta karɓi magunguna wajen Malam mai almajirai. Sannan ta zauna Hajiya Bilki ta karanta mata duk wata harka ta rike miji, duk wata dabara ta dawwama a Mowa.
Kamar anyi mistake