“Mamma…!”
“Maganar da naji, gaskiya ne?
To idan naji maganar nan daidai, idan har kunnuwa na gaskiya suka jiye min. Babu gargad a ciki. Idan zancen da na saurara haka yake, wato babu aljanu” Mama tana faɗin haka tazo ta zauna a bakin gado na kusa da ni ta ci gaba da cewa,
“Wato babu abinda ya hana samari zuwa wurin ki balle ya hana ki aure?Ina tambayar ki kinyi shuru?” Mama ta daka min tsawa. Ta ci ga ba da cewa,
“Kina so ki ce min kece kika yanke wa rayuwar ki zama a haka, kika hana kowa zuwa neman auren ki?”
“Mamma..!”
“Baki ce min komai ba? Wannan itace tambayar da mama tayita min tana kallon cikin idanun na.”
“Eh! Mama. Duk abunda kika ji haka ne.” Na amsa mata na ƙara da cewa,
“Sanadiyar Abdul ne yasa na yanke wa kaina wannan rayuwar. Domin muyi rayuwa iri ɗaya tare.
Da so samu ne. zan so ace hatta abicin da yake ci, ita nake ci. Haka idan ya Kwana da yunwa. Nima in kwana da yunwa.”
Tun ranar da na tsinci labarin soyayyarda Abdul yake yiwa Raƙiba tawa ce, daga ranar nayi alƙawarin shiga irin halinda yake ciki.
Na maida kuka abinci na. Watarana ma sai nayi kuka nake fitowa ki ganni. Haka kuwa bana iya barci. yarda naga rana haka nake ganin dare.
Wata rana nakan fito kiyi ta bincike na meke damu na. Ince miki babu. To wannan shi ne dalili.”
Na ƙarasa ina kuka.
“Ya Salam! Mamma…! Menene mafarin haɗuwar ki da Abdul? Sannan mai ya jawo ɓatar sa?
Don na ƙasa gane wannan abun. Kuma ma idan na canki Abdul dinnan dai-dai. Kina nufin Abdul Nams? wannan yaron da yayi suna wajen kalaman soyayya? Kalamai masu ƙarya zuciya?” (Love poem)”
Tambayar da mama tayi min kenan da mamaki a fuskar ta.
“Shine mama.” Na Amsa mata na cigaba da cewa,
Na haɗu da Abdul ne tun kina gidan Baba. Bayan gamawa ta (secondary school).
Ranar Baba ya ƙira ni domin yayi min albishir.”
*****
Mamma…! ta Fara Basu labarin mafarin haɗuwar ta da Abdul tun farkon rayuwar su, har zuwa yau.
******
Ranar naje karɓo littafi. Wayata na ƙara amma ban ji ba domin littafi nake karantawa kuma nayi zurfi cikin karatun.
Ina tafiya sai wani dishi-dishi nake gani da ya rufe min gani tamkar mai ciwon ido da yasa na dakata don ganin mai ke gaba na.
Sai wani bango na gani wadda taku na da isowar shi bai wuce taku uku ba. Kallon mamaki nayi masa nace a zuciya ta,
“Da na bugu da bangonnan, naji ciwo mai zance a gida?”
Sai karar wayata naji na tashi da ya maida ni cikin haiyaci na. Ka fin in ɗau wayar ma ta yanke.
“Kai! baba…! Har three missed calls? To ya akayi banji ba?”
Tambayar da nake yi wa kaina kenan saboda mamaki. Sai wani ƙaran ne yasa ke tashi wadda yasa na hanzarta ɗaukan wayar.
“Hello Baba…!”
Sai baba ya amsa min da cewa,
“Ina kike ne yanzu haka mama na?”
“Ka ganni a hanya. Amma gani cikin unguwa na kusa gida.”
Na ammsawa baba. Sai baba yace da Ni,
“To ki hanzarta. Domin yau nazo miki da albishir.”
Jin haka daga bakin Baba ne yasa nace,
“Wani albishir ne wannan Baba? Ka faɗa min yanzu mana”. Na ɗan haɗa da magiya. Sai baba yace,
“A’a sai kin iso gida.”
“Wai sai na iso gida? Baba ka faɗa min don Allah?” Kafin ina ƙarasa har ya katse wayar tasa.
Na dakata na minti ɗaya na dubi littafin da ke hannu na. Duk yarda nake son karatun littafinnan, albishir ɗin da Baba ke son faɗa min yafi shi. Don haka nasa gudu. kuma babu ruwa na da wanda ke kallo na. Sai Muryar wata naji na ƙira na da bansan ko wa cece ba. tana ƙwalla min ƙira.
Tsabar hanzari da nake yi, ya hana in waiga bare in saurare ta.
*****
Take na buɗe kofa kamar wacce aka koro da sanda. Nashiga falo na bankaɗe ƙofa. Wanda yazo dai-dai da shigowar mama falo. A yayinda tazo dai-dai da zama, na shigo a fizge. Mama ta razana bata zauna ba ta miƙe tsaye.
“Mamma…! Lafiya kika shigo a gaggauce, kamar wadda aka biyo…? Wa kika Tsokana?”
Mama ta jero min tambaya cikin fargaba zuciyar ta na bugawa. Nace mata,
“Kin Sanni da tsokana ne mama? Ai da tsokana nayi, Bazan shigo gida da gudu ba. Sai dai in’na ƙaraci masifata a waje, sai in shigo gida baki san ma anyi ba.”
Naƙarasa mata bayanin cikin tsarguwa. Sai tace da Ni,
“To faɗa min mai ya koro ki haka?” Mama ta tambaye Ni.
“Baba ne ya ƙira Ni a waya wai yazo min da albishir. Shine nace, ya faɗa min a wayar sai yace a’a sai na iso gida. Kuma ina so inji mene-ne. shiyasa na zaɓi inzo da gudu, domin inyi sauri.”
Na bawa mama amsa na sake cewa,
“Kin san kuma fa, idan Baba yace, albishir. To kyauta zaiyi maka mai nauyi.” Da na matso kusa da mama ina faɗa mata haka cikin raɗa.
Sai wani murmushi naga mama tayi mai tattare da farin cikin kasancewar ta da iyalinta.
“Mamma! Maman Baban ta. Wai dama ya ƙira ki?” Mama ta tambaye ni.
“Ya ƙira ni.” Na bata amsa.
“Wai mai yake son faɗa minne?” Na tambayi mama cikin dabara.
“A’a. Bazan faɗa miki ba don kar aji mutuwar sarki a baki na. Kuma, ma. ai waƙa a bakin mai ita, ta fi daɗi.”
Mama na faɗin haka tana murmushi wadda hakanne ya nuna min lallai Baba yazo min da albishir mai daɗi. Tace da Ni,
“Kije ki same Shi Yana daƙin sa.”
Ai bata ƙarasa ba na sa gudu kamar zan fire. Mama ta sake tsorata tana min tsokaci,
“Ke! Mamma…! So kike Ki ji wa kanki ciwo Ko?…. Kai wannan yarinya da hanzarin tsiya kike.”
Da isowa ta banyi wata-wata ba na buɗe labule amma sai na ƙasa shiga kana kuma, na ƙasa motsi. idanuna duk sun kakkafe da ma sansan jiki na.
Sai wani murmushi naga Baba yayi a yayinda ya ɗago kai ya dube Ni.
“Sallamar ta gagara ko mama na?”
To ki shigo ki sami wuri ki zauna.” Tambayar da baba yayi min ganin na gagara shiga kuma ban ce komai ba.
Jin haka ne daga gare shi yasa na saki numfashi da ya dawo dani haiyaci na. Sai nayi mishi sallama.
“Salama’alaikum.”
Sai baba ya amsa min da sallamata bayan ya haɗiye dabinon da ke bakin sa.
“Wa’alaikummussalam.”
Sai na shigo na zauna a damar sa. kaman yarda ya umurce Ni da in dinga zama a damar sa. Saboda a ko da yaushe yana faɗa mana Ni da mama na cewa, mahaifiyar sa ita ce a damar sa. Don haka, sai na zauna a daman sa.
“Mama na… Har kin iso kamar wanda aka wurgo a sama?”
Yayi min tambaya cikin mamaki.
“Eh Baba ai dama nace maka na kusa.”
Na bi shi da idanu ina bashi amsa. Ni dai na ƙosa a bani wannan albishir ɗin.
Sai baba ya buɗe drowar da ke jikin gadonsa, ya ciro wasu takardu, ya buɗe ya duba.
Wani ɗan karatu naga yayi da bai fice layi ɗaya ba. da halamu dai, karanta takardar yayi domin yasan wace takarda ce daga ciki. Domin takardun suna dayawa. a drowan,nasa.
Sai yayi murmushi yace dani,
“Karɓi takardannan ki duba.”
Na karɓi takardar, hannu na. na kakkarwa. Sai na dubi takardannan, cikin sauri. Duk da jikina yayi sanyi domin ban san takardar mece -ce ba. amma sai (admission) nagani na samu, a (University of Maiduguri) .
Wani ƙas! Naji kamar zuciya ta aka datse da almakashi. sai gumi ne ya yanko min a jiki na cikin minti ɗaya, kamar wanda akayi wa sirace.
Baba baiga murna a fuska ta ba sam.!Haka yasa ya dakatar da murmushin da ke fuskarsa. sai kuma wani mamaki da ya baiyana a fuskar tasa.
Kasancewar buri na ne shiga jami’a. sai dai yau, fuska ta tazo da canji. mai alamar tambaya. sai dai baba ya gagara tambaya ta dalilin hakan.
Nima kuma na gagara cewa komai. duk magana ta maƙalƙale min na rasa yarda zanyi. domin magana biyu ce cikin ɗaya. gamsuwata da shi, ko-ko rashin gamsuwa ta.
kuma duka ya kamata in furta su. to amma ta yaya zan baiyana wa Baba rashin gamsuwa ta da wannan jami’ar. bayan burina kenan, a ko da yaushe. Kuma shi Baba, amsa ɗaya kawai yake jira.
dole na, na jiure na yi magana. amma sai tambaya ce tazo min farko, a maimakon godiya.
“Baba….University of Maiduguri Kuma?”
Na tambaye shi da sanyin murya.
“Eh mama na University of Maiduguri saboda nasan wannan shine burin ki. shiyasa nayi miki bazata. Sannan yar uwar ki na can. Kinga, zaku haɗa kanku nasan zakiyi murna sosai haka kuma itama zatayi farin cikin ganin ki.”
Baba ya karasa da faɗin haka ya kuma ƙara da tambayata,
“Ko baiyi miki bane mama na?”
Ba makarantar bace bana so. Haɗuwa da Raƙiba ne bana so. saboda Raƙiba bata sona. kusan ma gaba take yi da Ni. sai dai kuma, munafuka ce. domin a ko da yaushe tana nunawa mahaifin mu tana so na.
Rashin haɗuwar mu gida ɗaya ne ya kawo min sauki. amma da gidan mu ɗaya, ban san iya rashin mutuncin da Raƙiba zata sauƙe min ba.
Duk da haka, bana tsoron haɗuwa da ita a makaranta ɗaya. sai dai tashin hankali ne bana so.
“Wani irin tarba zata yi min ranar da aka ce na shiga makaranta. Gaskiya ni da Baba A.B.U ya nema min, da hankali na ya fi kwanciya amma baba sam bazai gane hakan ba.”
Maganar da na furta kenan a raina. Sai nace da shi,
“Baba na gode sosai. Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta min.”
Ina faɗin haka a yayinda na saki wata murmushi na dole a fuska ta.
Baba yace dani,
“Babu komai mama na. Amma sai dai kaman bakiyi farin cikin ganin admission ɗinnan ba? ki faɗa min mene ne? Idan akwai wani damuwa ki faɗa min?” Baba ya tambaye ni.
Duk abunda nake so shi Baba yake yi min don haka yazama dole nima in faranta mishi. Haka yasa na kauda duk wata damuwa da ke fuska ta na ce,
“A’a Babu komai. kawai dai nafi son A.B.U ne shi yasa. amma tunda an sami wannan ɗin ma, shikenan.” Na ƙara da cewa,
“Yaushe ne zan fara registration Baba?”
Na tambaye shi cikin dabara domin kar ya fahimci da wani abu a raina. Sai yace da ni,
“Monday nan zaki fara insha Allah! Sai Ki shirya.” Ya faɗa min haka tare da murmushi a fuskar sa sai wani farin ciki ne ma ya sake cika shi fal! Ganin,na faɗi dalili. kuma dalilin nawa ma, ba mai ƙarfi bane.
Jiki na yayi sanyi matuƙa da ganin farin cikinda mahaifi na ya shiga a yayinda ya ga walwala ta.
Lallai, iyaye na na so na. basa son damuwa ta sam! Nima kuma Yakamata in, saka musu da alkhairi.
Haka yasa naci alwashin shiga jami’ar nan babu ruwa na da raƙiba. zan shiga makarantar nan ne kaman yarda ko wani ɗalibi ke shiga. zanyi karatu kamar yadda iyaye na suke bukata. Nace da Baba,
“Baba na…! Na gode Allah ya saka da alkhairi.”
na ƙara da cewa,
“Yanzu dai inje in fara shiri kenan?”
Na tambayi Baba cikin raha sai shima yace da Ni,
“Kije ki fara shiri mama na.” Muna dariya na fice a ɗakin.
Bayan Sati Daya
Ranar Litinin. Ranar da na Shiga jami’a. Bayan na kammala duk bukatun makarantar. Tare da taimakon wani malami abokin mahaifi na. wadda shine kulawar raƙiba ke hannun sa a makarantar. haka kuma, nima aka sa Ni a hannun shi. Don haka, sai malam Kabir yasa aka nuna min aji na.
A nan, na nufi aji na. amma sai dai ban isa ajin akan lokaci ba. domin da isa ta ajin, sai na tarar da malami.
Ganin Ni sabuwar ɗaliba ce. tarar da malami a ajin bai sa naji tsoro ba. don haka, na nemi izinin shiga. kuma sai malamin ya bani izini, na shiga.
Shiga na ajin, duk daliban ajin da ke gauraye maza da mata. kowa na kallo na. a yayinda wasu ke yaba kyanda Allah yayi min.
Wasu ƴan’matan kuma, na son suyi ƙawance da ni.
Ni dai babu wanda nake kallo. sai wani benci da na hango a baya da babu kowa kanta. sai na nufi baya, domin in zauna.
Bayan zama da nayi ne. sai malamin ya bukaci kowa da yayi shuru. domin ajin duk ya kurme da surutu da gani na. sai ya ce dani, in fito in gabatar da kai na a matsayi na, na sabuwar ɗaliba ga abokan karatu na. Ya kuma sanar da mu cewa, gabatar da kai ga sabon ɗalibi ga abokan karatu, na da matuƙar amfani.
Amma sai da, zuciya ta ta tsinke ganin yarda suke da yawa a ajin nan. ta yaya zan fara tsayawa agaban dubunnan jama’a haka? gashi bana son idanun mutane.
Amma haka na daure, na je na tsaya a gaban ajin. sai na fara da,
“Da farko suna na Ramlat Muhammad Ali. Nayi nursery, primary and secondary school dina a International school. Daga nan ne, na samu admission a wannan jami’ar. Ina fatan zaku karɓe ni da hannu biyu a matsayi na na sabuwar ɗalibar ku?”
Na ƙare jawabi na cikin ƙarfin hali. Duk wanda ke ajin kuwa, sai da ya tafa min. Kuma da amsar, sun karɓe ni. Sai mutum ɗaya ne da bai tafa ba. Hasali ma, ya naɗe hannuwansa yana kallo na.
Tafinda sukayi min ne, yasa Ni farin ciki. kuma yasa na saki zuciya ta. Na dai na jin duk wata bugun zuciya. domin kowa na haba-haba da Ni. Wasu daga matan. na ɗago min hannu, Nima haka.
Duk da na bar gaban ajinnan bayan gabatar da kai na. amma saurayin nan bai dai na kallo na ba. ya kuma naɗe hannuwansa har na iso inda ya ke.
Cikin bazata kuwa, sai idanuna suka sauƙa akan shi. har nayi tunanin kaf cikin ajin shine baiyi farin cikin gani na ba. idan ba haka ba. maiyasa yaƙi tafa min? kuma kallon mene-ne yake min?.
Haka mamma ta koma ta zauna. a yayinda wasu yan mata da ke gefen karshen bangon ajin na zaune. Na’ima, Zinat da Maliya.
Sai maliya ta ɗaga wa mamma hannu gami da kiran sunan,ta. mamma ta juya ita ma ta ɗaga mata. haka ma, na’ima . Zinat ce kaɗai bata ɗaga mata ba.
Daga nan lecture dai ya ƙare sai suka fita break.
*****
Daga nan ne mamma ta fice a ajin ba tare da tayi wa kowa magana ba. sai ta nufi inda ɗalibai ke cin abinci cafeteria.
Mamma na zaune a yayinda aka kawo mata abin ci tana ci.
Haka kuwa Na’im, Zinat da Maliya suma suka zo cin abinci sai suka zauna su uku.
Mamma na cin abinci. babu zato ba tsammani sai Abdul ya shigo inda suke. Abdul ya kalle ta. sai ya ja ɗaya daga cikin kujerar da ke gaban ta, ya zauna. yana kallon ta har cikin idanu, ita ma haka.
Cikin mamaki mamma ta dakatar da lemon da take sha. tace da shi,
“Waye kai? Kuma mai ya kawo ka?”
Tambayar da tayi mishi ya bashi mamaki haka yasa shima ya tambaye ta da,
“Mai ya ɓata miki rai game da ni kike yi min irin wannan tambayar?”
“Saboda bani da halaƙa da maza shiyas na tambaye ka. kuma ma, yau ne na fara shiga makarantar nan. kaga bani da halaƙa da kai.”
Ta bashi amsa ta kuma sake tambayar sa da,
“Mai ya kawo ka wuri na?”
“Nazo inyi miki gargaɗi ne. kuma idan kikayi amfani da shi, zaki ji daɗin ta.” Ya faɗa mata.
Mamma tace,
“Gargaɗi kuma? Gargaɗin mai ni kuwa zakayi min?” Ta tambaye shi da mamaki.
“To ina so ki sani bana soyayya kuma babu wacce nake so a makarantar nan saboda haka ki cire tunanin ni, zan so ki.”
Wannan maganar ta Abdul ta ɗaure wa mamma kai. shin, a zahi take jin zancennan? ko a mafarki? idan a zahiri take jin zancennan, to lallai saurayinnan yana da tabun hankali.
Madallah nice ba yaxanyi in sami labarin offline na godi
Ki tuntubi bakandamiya domin samun labaran