Skip to content
Part 6 of 9 in the Series Soyayyar Da Na Yi by Habiba Maina

“Huhh!” ajiyar zuciya tayi sannan ta ce da maliya. “na gode da bayananki maliya, ai Abdul ba kalaman soyayya yake yi ba ko shine soyayyar da kanshi, Ni Bazan taɓa jin ina son Shi ba.” Ta faɗi tana mai jaddada musu har cikin zuciyar ta. 

“to Allah yasa.” inji na’ima ta ƙara da cewa,

“da kuwa kin zama daban a cikin yan’matan da ke makarantar nan.” ta karasa da faɗin haka sai ƙarar wayar na’ima ne ke ta shi, dubawa tayi sannan ta ɗan dago kai ta dube su, sannan ta ce da su,

“malam ne fa… kardai har ya shigo aji?”

“ɗauka mana.” Maliya ta faɗi. Ɗauka tayi da ta ƙara a kunne,

“hello! sir.” Tambaya ya yi mata.

“na’ima kina aji ne ko kina waje?”

“a’a ina waje sir.” 

“to ki sanar da sauranku cewa, bazaku samu lecture da Ni yau ba wani ɗan uzuri ya riƙe Ni… So sai next week. saboda haka baku da lecture yanzu.” ya faɗi dai-dai, lokacida zinat ta tashi ta fice batare da sun ganta ba domin hankalin su duk ya koma kan waya da malamin nasu.

“to sir Allah ya kaimu.”

 “yauwa.”

ya katse wayar, ajiyar zuciya na’ima tayi sannan ta ce da su,

“El mansur ya ce, a sanar da yara cewa bazamu samu lecture da Shi ba Wani ɗan uzuri ya rike shi, sai next week.”

“ke ce class captain?” mamma tayi mata tambaya.

“a’a Ni assistant ce, ina tsammani ya ƙira Captain ɗin be ɗauka bane kokuma switch off.”

na’ima ta faɗi, sai maliya ce ta miƙe ta ce, 

“to ai sai muje ki sanar da su ko! kowa ya watse.” haka suka tashi zasu tafi a yayinda maliya ta tuna da sun bar Zinat a gefe, amma juyawar su ke da wuya suka tarar bata nan sai hango ta sukayi a waje cikin maza, a nan suka dakata. mamma ta ce zata tafi gida domin bata fiye zama a waje ba, babu dalili suma suka shaida mata cewa suna sanar da yara saƙon malamin su, zasu tafi gida nan suka rabu mamma ta koma gida. 

Washe Gari

labarin shigar mamma makaranta ya ɗaga wa rakiba hankali, tayi niyar shiga makaranta amma labarin shigar mamma makaranta ya birkitar da ita a sa’inda ta fito daga wanka, goge jikin ta take da towel sai kira taji wayar ta na ƙara hanzari tayi domin ta ɗauki wayar saboda bata barin kira guda ya yanke mata sai ya zama dole, saboda duk ƙira da za’a yi mata masu amfani ne a wurinta. Ɗagawa tayi sai Zinat ta gani ƙawar ta ke kira bata ɓata lokaci ba, ta ɗauka don zinat ƙawar cin mushe ce ga raƙiba duk ƙiranda zatayi mata to, da bayani don haka ta ƙara a kunne. 

bayan ta amsa ne zinat ta katsar da ita da cewa kada tace ƙala, domin zata bata wani labari amma tana kusa da mutane saboda haka tayi shiru kawai kar tayi mata tambaya don kada mutane su fahimci abinda take faɗa mata. ita dai ta saurare ta kawai, don haka raƙiba ta ja bakin ta tayi shiru domin jin ko mene ne.

Ai kuwa karshen wayar raƙiba sai ya zamo tashin hankali da yasa ta buga wayar Tata a ƙasa sai fash!! Kake ji ya fashe raƙiba duk tabi ta ruɗe cikin minti guda ɓacin rai duk ya bi ya bibiye ta wadda yasa ta fara sake-saken, yadda zatayi maganin duk abunda zai rufe mata gani. Raƙiba wata ce da idan ranta ya ɓace bata hakuri ta bi abun a hankali, ita dai da ranta ya ɓaci to kowa sai yaji, haka kuma da zafin zuciya zata faɗawa mahaifiyar ta, sannan kada ta ce a’a, yadda take so ɗinnan haka take so ayi mata kuma kada ayi mata faɗa idan tayi ba dai-dai ba.

*****

Mahaifiyar raƙiba kuwa wata mace ce da ta taso cikin tarbiya duk da iyayenta talakawa ne amma hakan bai sa ta taso cikin rashin karatu ba. a iya ƙarfin iyayenta sunyi mata Sakandire, kuma har ta gama da kwazonta. Bayan gamawarta sandiren ne ta cigaba da zama a gida tana taya mahaifiyar ta, ɗan kulle-kullen, kayan miya. mahaifin ta kuma ɗan kasuwa ne, sai dai kasuwancin nashi ba me ƙarfi bane, a takaice dai na rufin asiri ne wanda zasu samu suna ci.

Mahaifiyar raƙiba bayan sana’a da take taimakawa mahaifiyar ta sai kuma islamiyya da take zuwa asabar da Lahadi. haka aka ɗebi tsawon lokaci tana gida amma duk nutsuwar ta Allah bai bata mijin aure ba kawayenta duk sunyi aure sun barta amma ita kwata-kwata ba alama, haka yasa iyayenta suka dage da addu’o’i amma shuru kamar an shuka dusa. wata rana sai kakar ta, iya talatu tayi rashin lafiya mai tsanani bata iya komai kuma sai aka rasa mai zama a kanta. haka yasa mahaifin ta ya ce, taje ta zauna a kan kakar Tata ta kula da ita, kafin su zo su duba ta, domin ya ɗan sami kuɗinda zai ɗan taimaka, wajen jinyar. sai kuwa ta amince domin zaman gidan ma ya ishe ta, daga nan aka sata a hanya ta tafi kauyen nasu na mahaifin nata wato can kauyen magarya. haka kuwa ta iso lafiya a yayinda ta iske wata mata wacce kawar kakar Ta ce mai koko.

Mai koko ita ke kula da iya talatu kafin zuwan mahaifiyar raƙiba wacce ita ce ma ta sanar da su cewa kakar Tata ba lafiya, cikin ikon Allah kuwa da zuwan ta sai mai koko ma, jinya ta bige ta wadda yasa ake tunanin gajiya ce na kula da mara lafiya, domin ita ma tsohuwa ce tsufa ya bi jiki. Mahaifiyar raƙiba kuma bata taso cikin sanyin jiki ba, mace ce mai kuzari don haka sai ta ɗauki aiki biyu. Duk yadda ta ke kula da kakarta, haka takeyi wa mai koko. tana kula da su matuƙa, cikin yardar Allah ba tare da jumawa ba suka warke, ita mai koko ita ta riga iya talatu samun sauki domin takanyi wani ɗan aikin, amma ita iya talatu bata iya aiki, sai dai da sauki tana iya tashi taci abinci, sannan kuma tayi hira. mahaifiyar raƙiba taji daɗin hakan domin iya talatu mace ce mai daɗin zama indai ka zauna da ita sai ta saka dariya haka kuwa idan suna hira da jikar Tata, tayi tabata labaran mutan da, tayi ta sa ta dariya. mahaifiyar raƙiba taji daɗin kauyen nasu sosai…, ai kuwa dabi’un mahaiyar raƙiba suka birge mai koko, tana yawan faɗin haka, zata so raƙiba ta zama sirkar ta. 

Ba a wuce sati guda ba sai ga isowar jikan mai koko daga birni domin duba jikin kakar tashi, kamar yadda abokinsa idi da ke ƙauyen ya faɗa masa. Mai koko tayi murna sosai da ganin jikanta Muhammad, saboda tana gani burinta zai cika. ai bayan duk wata gaisuwa tsakanin ta da shi sai ya sanar mata da cewa yana samun cigaba a wurin aikin sa don haka yana tunanin tunda aiki ya zauna, yana so ya yi aure. Mai koko taji daɗin wannan batu, tare da godewa Allah, sai kuma ta tambaye shi, shin yana da wacce yake so ne? Sai shi kuma ya sanar da ita cewa bashi da, a halin yanzu. amma in ya Koma zai fara dubawa. a nan ne mai koko tayi amfani da wannan damar ta sanar da shi irin kyawawan dabi’u irin na jikar iya talatu, wato falmata, wato mahaifiyar raƙiba. Don haka ta nemi alfarma su je ya ganta idan tayi mishi falillahi hamdu, indan kuma batayi mishi ba shike nan, baza tayi mishi tilas ba. shi kuma bai ki maganar ta ba sai sukaje ya ganta ai kuwa bai kau da kai ba ya ce, tayi mishi daga nan suka fahimci juna suka je ya ya gabatar da kanshi ga iyayenta akayi duk abunda ya dace aka ɗaura musu aure. cikin so, da kauna da kuma girmamawa.

***** 

Bayan auren nasu ne sai Allah ya albarka ce su da ƙaruwa ta sami juna biyu a nan ne tayi alƙawarin sakawa mai koko takwara idan har ta sami ya’ mace, sai Allah ya amshi addu’ar ta, ta haifu ta sami yar ta aka sa wa mai koko takwara. mahaifinta kuwa ya hana a kira ta da mai koko, ya umurce su da su dinga kiranta da sunanta na asali wato raƙiba.

Wannan shine dalilin da yasa raƙiba ta sami gata matuƙa a wajen iyayen nata biyu tun haifuwar ta har tayi wayo, iyayenta basu son damuwar ta. musamman mahaifiyar ta, duk abunda raƙiba take so to ko ita bata so haka zata danne ayi mata, mahaifiyar ta sam! bata iya cewa raƙiba ki bari balle ta hana ta abunda take so tayi saboda tana kunyar wai me sunan nata mai koko.

Haka take biyewa raƙiba amma sai dai mahaifinta yana da tsauri wajen tsokaci, yana nuna mata abunda ya dace da wadda bai dace ba, amma haka uwar take kau da kai ita dai bazata tsawata mata ba wai saboda mai koko.

*****

Haka kuwa raƙiba taci gaba da rayuwa sai yadda ta so take yi don haka ta nufi ɗakin mahaifiyar ta tana surutai tana cewa,

“Wallahi! bata isa ba.” har ta shigo ɗakin mahaifiyar tata bata san ma ta shigo ba, sai mahaifiyar nata ne ta dakatar da ita da cewa,

” ke…! ke da wa kike wannan surutan? mutun ya yi ta surutai shi kaɗai sai kace mahaukaci.” tana a kishingiɗe a kan gadonta tana riƙe da wayar ta a hannu.

“Umma wai jami’ar da nake baba ya nemawa mamma.” tana faɗi zuciyar ta na bugawa, wani mamaki abun ya bata kuma tare da jin anyi mata bazata ranta a bace tana zazzaro ido.

“Ke wa ya faɗa miki.” Umman ta tambaye ta, ta ƙara da cewa,

“nifa bana son jita-jita, dubi duk kin bi kin rikice. Kuma ke kanki kinsan cewa mamma, A.B.U take so, to Me zai Kaita unimaid?”

Cikin wani mamakin maganar umman nata ta ce, “gashi nan kuwa, Zinat ce ta ƙira Ni yanzu ta faɗa min. kuma Ni gaskiya Bazan haɗa makaranta da ita ba, wallahi!” ta juya baya tare da riƙe kugunta da hannu. 

“Zinat ce ta faɗa miki haka?” umman ta sake tambayar ta.

“Ai kin san bazatayi min ƙarya ba.” ta maida mata wannan amsar ta cigaba da cewa,

“wai kuma da shigar ta ajinsu, kowa ya bi ya ruɗe da ganinta, kamar ita tafi kowa farin jini. Ni bata isa in ja da ita a makarantar nan ba wallahi! kinji na faɗa miki ko? don idan na ɗauki mataki kar aga laifi na.” tana faɗi da gargaɗi sannan zuciyar a bace, babu shakka yadda ran raƙiba ya ɓaci, to zata iya yin komai.

“Ke dakata!” umma ta katse ta.

“Tunkunna ma, wace foculty take?”

Umma ta, ta tambaye ta. Wani far-far tayi da idanunta, ta sauke numfashinda suka makale mata a kirji sannan ta ce,

“wai English and litriture.”

“to ke da kike science and technology, me ze haɗa ki da ita?” Tambayar da umman nata tayi mata sannan tana kallon ta cikin jiran amsa.

“Umma…, department nasu fa ɗaya da abdul, saurayinda na ke so…, kuma ke kin san yadda mamma ta ke a wurin mutane, ni bazan ɗauki yar da za ta zo ta zama a idanun abdul ba.” raƙiba na faɗin haka kamar zata yi kuka, kuma babu kunya a idanun ta, sai tashi umman tayi ta gyara zamanta kan gadon sannan ta miƙa hannu ta ajiye wayar ta akan drawer da ke kusa da gadon nata, sannan kuma ta jawo raƙiba kusa da ita ta ce, 

“zauna a nan ɗiya ta, bana so kina tada hankalin ki akan abunda bai kai ya kawo ba, duk nima sai ki ɗaga min hankali.” tayi shiru na ɗan secons sannan ta ci gaba da cewa,

“nasan yadda kike son abdul, amma ai kin faɗa min cewa, abdul ɗin har yanzu bashi da wacce yake so, sannan kuma babu wacce yake kulawa a makarantar duk kyan ta kuwa. Haka ne?” umma ta tambaye ta.  

“Eh! haka ne, amma ai kinsan yadda mamma take…, na rasa wani irin kwar jini take yi wa mutane?” ta faɗi jikinta a sanyaye.

“dakata!” umma ta katse ta.

“ina yarinyar da kika ce min ‘yar shuwa ce, ga kyau, ga gashi, gata fara sol! amma duk da kyannan nata, abdul ɗin ya ki ta, Haka ne?”

umma ta sake tambayar ta.

“eh haka ne umma.” raƙiba ta amsa.

“to ina so ki kwantar da hankalin ki, mamma bata da duk wani abunda abdul zai so…, karshe dai ke ɗin ce wcce zai ji yana so. ke ce kika dace da shi raƙiba ta.”Umma tana faɗin haka, raƙiba tayi wani dariyar farin ciki, sannan ta ce,

“Allah! umma na?”

“sosai ma kuwa.” inji umman.

“ai ki kwantar da hankalin ki kawai, tunda kuna abota, to karshen ta soyayya ce. Domin kuwa a sannu, in sabo ya yi sabo kawai ji zai yi, ke kika dace da shi.”

ai umma bata ƙarasa maganar ta ba, sai ji tayi cap! raƙiba ta rungume ta, tana matukar murna ji take kamar ranar auren ta da abdul ne aka yanka. wannan batu na umma ya sanya raƙiba matsanan cin farin ciki, wadda babu misaltuwa, domin bata da wani buri da ya wuce ta auri abdul. sai dai kash! shi abdul ɗin bai san tana son shi ba, ya zata abota ce kawai tsakanin su, domin ita raƙiba wayon tsiya ne da ita, da abota ta je masa a maimakon soyayya, tana bashi duk wata gudumawa na abota, amma sai dai abdul ɗin abokiyar mutunci ya ɗauke ta kuma fan! amma da yasan tana son sa, to baza su shirya ba. 

Raƙiba ta riƙe ummanta ƙam-ƙam, taki sake ta. umma tayi murmushi sannan ta ce, 

“To yanzu tashi ki je ki gama shirin ki, ki tafi makaranta abin ki.”

“a’a! ai bazan je makarantar ba, dama bani da class yau, Assignment ne zai kai ni. amma yanzu na fasa zanyi a gida.” Ta faɗi.

 To shike nan…, Tunda haka ne, yanzu sai muje kitchen ki taya ni girkin rana, yau zan yi girkin da ban taɓa yin shi ba a gidannan. saboda haka kema sai ki gani ki koya, matar abdul.” umma ta faɗi tana hura wa raƙiba kai. Raƙiba jin ta, take a sararin samaniya, tsabar farin ciki, haka suka miƙe, umma na gaba ita kuma rakiba na binnta a baya. su ka isa falo, sai wayar raƙiba umma ta gani a ƙasa a watse.

“raƙiba…! wannan ba wayar ki bace a watse?”

“Eh shi ne, da rai na ya ɓaci ne na buga ta a kasa.” tana faɗi tana kakkau da kai cikin tsarguwa.

“haba raƙiba ke wai me yasa idan ranki ya ɓace, bakya iya controlling ɗin kanki ne, dubi fa! wayar nan be kai wata biyu da aka sai miki ita ba, ki matsa abban ki ya saya miki. amma kika rugurguza shi ko a jikin ki? to shike nan idan abban naki yazo sai ki faɗa mishi da kan ki. amma ni, babu ruwa na.” inji umma.

“kema faɗa kike, amma nasan baza ki ya ba. you always defending me.raƙiba ta faɗi tana murmushi tana wani ɗan shagwaɓa. 

“to shike nan, bana dai zaki ga canji. ni nayi kicin in kin gama kya same ni.” umma ta faɗi sannan ta wuce kicin, raƙiba kuwa ta durkusa tana stince wayar tata.

*****

Wani abun mamaki shine mamma ta zamo kamar wata halitta da ɗaliban makarantar nan basu taɓa gani ba, duk da’ma, mamma ‘ya ce da bata raina kowa, tana da lafazi masu daɗi, sannan tana kokari wajen ibada, to ko wannan ya ishe ta rigar kallo. amma kuma, ai gaba ma da gaban ta. akwai wa’yanda suka fita da wa’yannan qualitys ɗin, to me yasa sai ita ake kallo? wannan abun, ya ɗaure wa mamma kai.

Da shigar ta makaranta kuwa, sai ta tarar da abokan karatunta duk a waje, domin ba a shigo musu lecture ba, samarin ajin ne ta fara tarar wa ƙarƙashin bishiya da sukayi kane-kane, kamar za su rufe hanyar wucewa, sai wani ɗan hanya suka bari ɗan sirir,i wani stinkewar zuciya mamma taji da ganin su, shigar ta ke da wuya kuma kowa idanun sa a kanta, wani cijewa tayi wuri guda, taji kamar ta koma. zuciyar ta na bugawa domin tun tana ƙarama bata son idanu, wani tsarguwa taji da suka rife mata idanu. Sai ɗaga kai tayi ta dube su sannan ta saukar da kanta ƙasa, ta ci gaba da tafiya ta ratsa tsakanin hanyar da suka bari ta wuce, amma hankalin kowa na kanta. kaɗan daga cikin samarin ne ke hira amma da yawa sunyi shiru kamar masu kallon wata, mamma kuwa, ta cika da fargaba da sak-sake, a ruhin ta. wani dishi-dishi, take gani domin zuciyar ta na bugunda ke taɓa jijiyar da ke haɗe da idanu. Sai wani karo na bazata tayi da abdul a yayin da ya fito a library zai je wajen abokan karatun sa, maza. ita kuwa ta zo wucewa domin ta isa wurin aboka karatun ta mata. Amma tsabar yadda idanun ta suka toshe mata gani, bata ga fitowar abdul ɗin ba, hanyar kawai ta ke gani, wurin shi kawai ta nufa bata kauce ba, ganin yadda mamma ta ɗauki hanya baji ba gani ya sa abdul ɗin ya dakata da tafiyar tasa, don gudun kar su yi karo. amma duk da haka bata ganshi ba sai da ta ƙure masa, domin a tsakiyar flawar cikin makarantar suke

Sai buguwan su kawai ta ji da takardunda ke hannunta suka zube, tsayawa tayi cikin tsoro da fargaba. ɗaga kai tayi cikin tsoro domin ganin da wa, tayi karo. babu wanda yazo mata a rai face abdul… ta ce a ranta, 

“kaddara ce ƙaɗai zata iya haɗa ni da abdul, na roke ki don Allah…! kada ki haɗa ni da shi.” Amma inna! Kaddara ta riga fata. Duk Idanun ta sun cicciko da hawaye, daurewa tayi da yasa ta ɗago kai domin ta ga wane ne, sai dai ɗago kanta da tayi, bai mata daɗi ba domin kuwa ,da abdul ɗin tayi ido huɗu. yana tsaye a kumbure kamar zai dake ta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayyar Da Na Yi 5Soyayyar Da Na Yi 7 >>

4 thoughts on “Soyayyar Da Na Yi 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×