Skip to content
Part 6 of 11 in the Series Su Ne Sila by Aisha Abdullahi Yabo

Zuba wa Mama idanu tayi tana magana cikin rawar murya “wa a ka kawo wa kaya Mama?”

“Uhm! Kayanki ne, kayan na gani ina so ne da kuma lefe” hannu ta ɗora aka tana ihu “wayyo na shiga uku! Wallahi Allah bana son shi mutuwa zanyi duk aka au… Mama ta rufe mata baki tana faɗin “meye haka Zainab so kike ki tara mana jama’a?” Janye hannun ta yi tana faɗin “ni duk wanda ma zai zo ya zo amma wallahi ni bana son shi idan har aka yi auren nan sai na kashe shi na kashi kaina!”

“SubhanalLah! Daina faɗar wannan maganar don Allah ki rufa mana asiri, in har ina raye ba wanda ya isa ya maki auren dole.”

“Ai sai na gani tsakanin ni da ke waye yake da iko da ita”.

“Malam abinda kake yi fa sam bai dace ba zamani ya sauya an daina irin wannan auren haɗin, cigaba ya zo mana da ake bai wa ‘ya’ya zaɓinsu” ƙuru ya mata da idanu kafin daga bisani ya ce. “Allah ya waddan wannan cigaban na mai haƙan rijiya, cigaban da yake nuna wa ‘ya’ya su bijire wa iyayensu. To bari ki ji wannan auren babu fashi wata ɗaya masu zuwa ko bayan ba raina in har a ka fasa auren nan ban yafe ba!”

Kallonsa take idanunta suna zubar da hawaye masu zafi wani irin suya take ji a zuciyarta me ta yi wa Babanta ne ya tsaneta har hakan? Me ya sa yake so ya yanke mata farin cikinta. Kalleni da kyau aure babu fashi in har na isa dake, idan kuma kika ce za ki yi mani rashin biyayya za ki bijire wa maganata to bisimillah ga fili ga mai doki ki gani idan har zaki ci ribar hakan” ɗaki ta shiga da gudu tana kuka. “Babu wanda ya isa ya mata auren dole, kamar yadda kake jin ka isa da ita nima haka na isa da ita ni nayi rainon cikinta wata tara har da ‘yan kai na yi naƙudarta ba tare da wasu can sun zo sun tayani ba, babu wanda zai nuna mani ƙarfin iko akan ‘yata, in gaskiya ne ai suna da yara a gabansu su ba shi sai ta wa za su sa wa karan tsana su sa a mata dole!”

“Kar dai ki nemi ki zageni, sannan zan gani tsakanin ni da ke wa ya fi iko da ita. Wallahi a kan wannan auren zan iya rabuwa da ke dan haka ki iya bakinki” ya faɗa ta faɗa ganin abin ba na ƙarewa bane ya fice ya bar masu gidan. Da dare ya dawo ya samu kayan a yashe tsakar gida kamar yadda ya barsu ya kaɗa kai “wato dai so suke su mayar da maganata banza ai shi kenan zan gani tsakanin ni da su waye mai iko” haka ya jidi kayan ya kai ɗakin shi yana ta faɗa tana jin shi ko ci kanka Mama bata ce da shi ba.

“Yau saura sati biyu biki amma kinƙi ki bamu damar fara shirye-shiryen biki”
“Ba wani biki fa da zanyi ke bari ma ki ji kin san Allah auren nan ba zan yadda a yi shi ba, idan har kuma a ka yi shi hum” ta yi ƙwafa daga hakan bata sake cewa komai ba ta mayar da kai ta kwanta a kan doguwar kujera tana latsar waya, “kina da matsala Zainab wai ke wace irin zuciya ne da ke haba! Shin so kike ki bijire wa mahaifinki ne?” Tashi ta yi ta zauna tana kallon Raliya ta ce. “Ai shima ba zaɓin shi bane waɗan can tsofaffin ne suka sanya ma shi abin a ran shi”

“Amma ai ya faɗa ba zai ƙi bin umurninsu ba to ke dan me ba za ki bi umurnin mahaifinki ba ko dan ki nuna wa su tsofaffin ya isa da ke?”

“Saboda ba na son shi, kuma ba aure ne a gabana ba karatu nake son yi” ajiyar zuciya Raliya ta yi kafin daga bisani ta ce. “Amma ai ya ce zai barki ki yi karatun bayan aure ko, sannan ni banga matsalar Alhaji Umar ba yana da kirki mutum ne mai nagarta ko wace mace za ta yi burin samun miji kamar shi uwa uba ga kuɗi”

“Ni na ce bana so a kai kasuwa, tunda har kinji halin shi ya maki ke kije ki aure shi na bar maki” zuba mata idanu ta yi ta fahimci ko me za ta faɗa ba za ta taɓa fahimtarta ba gara kawai ta yi tafiyarta. Tashi ta yi tana sanya Hijab ɗinta “na gode zan tafi In Sha Allah ba za ki sake jin maganata ba in dai a kan auren nan ne, ki yi duk abinda kike ganin shi ne ya fiye maki”.

“Uhm da dai ya fi maki ki gaida gida” ta koma ta kwanta. Ta fita tana ƙara jinjina taurin kai irin na Zainab.

Tana zuwa cikin soron gidan nasu ta tsaya daga bakin ƙofar shiga cikin gidan tana riƙi ƙugo “ga ni meye” ɗago kansa ya yi yana faɗin “ki zauna mana” kallon banza ta watsa masa kafin daga bisani ta ce. “Ba wannan ne ya kawo ni ba ka fadi abinda yake tafi da kai ko kuma na ƙara gaba dan ina da abin yi” komai nata burge shi yake ya rasa wani irin so yake mata yana ji a ransa zai iya jurar komai da za ta yi masa ya sani watarana za ta daina ƙurciya ce yanzu take ɗawainiya da ita. Miƙewa ya yi tsaye yana murmushi “tunda gimbiyar tsayuwa take so ya na iya bayan nima na bi umurni”

Tsaki ta yi tare da hararar shi, bai damu ba ya cigaba da faɗin “fatan kin wuni lafiya?”

“Da ban wuni ba za ka ganni ne?”
“To Allah ya ba ki haƙuri, dama na zo ne na ji dame-dame kike buƙata da za ki yi hidimar biki”.

“Mtsww!!! Aikin banza kai har tunani kake za a yi wannan auren? To wallahi ka daina ma wannan mafarkin dan aure nan ba za a taɓa yin shi ba, idan kuma kaga anyi to ka rubuta ka a jiye ajalinka ka auro!” Fuskar shi da yalwataccin murmushi ya ce. “Ai gaskiya kika faɗa mutuwa ce kaɗai dama za ta rabamu. Ni ban damu da duk abinda za ki yi ba, na sani ƙurciya ce a tare dake komai zai wuce bayan aurenmu”.

“Humm! Yaudarar kai kenan, har abadan abada ba zan taɓa sonka ba gara ka daina yaudarar kanka!” Tana gama faɗa ta juya tayi shigewarta gida. Wani irin gwarron numfashi ya furzar har ma ya rasa tunanin da zai yi. Abu ɗaya ya sani ba zai iya haƙuri da ita ba.

Gida ya fara cika da ‘yan’uwa daga ɓangaren Baba, Mama ta ce kowa ba za ta gayyata ba. “Ke Mairamu wannan wani shashanci ne gobe ɗauren aure amma amarya ba kitso ba ƙunshi duk tabi ta fige ta zama kamar mahaukaciya sabon kamu!”

Gwaggo Hari ta yi maganar tana mai janyo hannun Zainab da ta zo fita gidan, “to ta ce ba za ta yi ba zan sa ta yi dole ne”

“Oh rashin kunya za ki yi mani so kike ki nuna mana kina goyon bayan ‘yarki ko? To kar Allah yasa ta yi ɗin, da yinta da rashin yin duk ɗaya babu abinda za a fasa ai!” Mama za ta yi magana ‘yar’uwarta ta yi saurin janyeta suka ƙule uwar ɗaki.

Zainab ta fizge hannunta daga riƙon da Gwaggo ta mata ta kama hanya za ta fita tana magana ciki-ciki sake janyota ta yi tana faɗin “ba gidan uban da za ki je wa ya faɗa maki Amarya na fita ana gobe aurenta!”

Sake fizge hannunta ta yi ta nufi ɗakin Mama tana magana ciki-ciki “oho sai dai a yi magana ƙasa-ƙasa amma ba a isa a yi a fili ko a dakeni ba yarinyar banza! Aure ne dai babu fashi”.

“Ai ni wallahi gani nake har da laifin Yaya shi ne ya basu dama daga ita har uwarta suke yin abinda suka ga dama, wai ko ruwa matar nan kasa bamu ta yi abinci wannan maƙota yasa a ka yi komai kafin mu zo”

“Barsu da mugun halinsu da babu abinda suka isa su hana a yi, maza ku tashi ku fara ɗora girkin dare sannan a fara haɗa na ‘yan ɗauren auren gobe.”

Suna shiga ɗaki Yaya ta ce. “Na ce dake ko me za su faɗa karki ce dasu komai amma sam kinƙi ji”.

“Uhm! Wallahi na kasa riƙi kaina ne Yaya ina jin haushin yadda ƙiri-ƙiri suka sa malam ya rufe idanu yake shirin yi wa yarinyar nan auren dole, ji nake kamar na rufesu da duka wallahi!” Zama suka yi gefen gado Yaya na faɗin “ba daɗi amma ba yadda muka iya bayan mu yi haƙuri da fatan Allah yasa hakan ya zama alkhairi tunda dai sun fi mu iko da ‘ya. Kinga saboda rigimar nan yasa ‘yan’uwa kowa ya tafi sai ni ce kaɗai na tsaya don Allah ki yi haƙuri a gama komai ba tare da an samu matsala ba”.

Shiru ta yi bata iya cewa komai ba Allah kaɗai ya san irin tunanin da yake ranta.

“Zainab ki shirya mu je a yi maki kitson da ƙunshi” za ta yi magana ta yi saurin tarar numfashinta “bana son jin komai” kuka tasa ba tare da ta yi magana ba. Da dare Mama ta sace jiki ta bar gidan tare da Zainab da dawowarsu kenan daga wajan ƙunshi.

<< Su ne sila 5Su Ne Sila 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×