Janye jikinsa yayi da sauri ya kalli ƙirjinsa da shacin haƙoran ta suka fito, tufa masa yawo ta yi a jikinsa tare da miƙewa tsaye janye idanunsa yayi daga ƙirjin sa ya ɗora su a kanta sosai zuciyar sa ta sosu da abin da ta masa sai dai ya kanne ɓacin ran ya sakar mata murmushi "fatan kin wuni lafiya?"
"Mtsww!!" Ta ja dogun tsaki tare da juya wa a fusace ta shiga ɗakinta ta banko ƙofar da ƙarfi. Ciro hankicef ya yi cikin aljihun rigarsa ya goge yawon da ta tufa masa, ya mayar da kansa jikin. . .