Skip to content
Part 9 of 11 in the Series Su Ne Sila by Aisha Abdullahi Yabo

Janye jikinsa yayi da sauri ya kalli ƙirjinsa da shacin haƙoran ta suka fito, tufa masa yawo ta yi a jikinsa tare da miƙewa tsaye janye idanunsa yayi daga ƙirjin sa ya ɗora su a kanta sosai zuciyar sa ta sosu da abin da ta masa sai dai ya kanne ɓacin ran ya sakar mata murmushi “fatan kin wuni lafiya?”

“Mtsww!!” Ta ja dogun tsaki tare da juya wa a fusace ta shiga ɗakinta ta banko ƙofar da ƙarfi. Ciro hankicef ya yi cikin aljihun rigarsa ya goge yawon da ta tufa masa, ya mayar da kansa jikin kujera ya kwanta tare da lumshi idanunsa. ya rasa wace irin tsana Zainab take yi masa haka, an ya ba yaudarar kansa ya ke ba da har yake tunanin watarana za ta saduda ta so shi. Ya yi maganar a zuciyarsa, ajiyar zuciya ya yi har ya rasa ma ta ina zai ɓullo mata domin shawo kanta.

Hansa’u ta shi go ta durƙusa gabansa “Alhaji an haɗa abinci yana a kan dani”.

Buɗe idanun sa ya yi da suka sauya kala sun yi jawur “sannu da aiki. Zainab ta ci abincin kuwa?”

“Eh tare muka ci” tashi ya yi ya gyara zaman sa ya na faɗin “ya yi kyau.

Fatan babu wata damuwa ko?”

“Eh babu gaskiya” ta bashi amsa ta na gyaɗa kanta. “Shi kenan jeki na gode” bayan tafiyarta ya tashi ya shiga ɗakinsa abincin da bai iya ci ba kenan zaman gidan ma duk ya ji ya fice masa a rai kawai ya ɗauki key ɗin mota ya fita.

*****

Yana zaune gefen gado yana duba wani saƙo da a ka turo masa ta Gmail ɗinsa. Kyakkyawar mace ce ta turo ƙofa ta shi go ɗakin “a she kuwa da gaske take” zama ta yi kusa da shi ya kalleta da murmushi a fuskarsa ya ce. “ke da waye ne?”

“Ilham ce take faɗa mini ka dawo shi ne fa na ƙaryata ta” ajiye wayar ya yi gefensa ya dawo da duban sa a kanta ya ce. “Dan me za ki ƙaryata mini yarinya. Ko da na shi go ba kowa sai ita kaɗai na samu a falon”.

“Na yi mamakin ganinka gidan nan a yau shi yasa. Ina amaryar ta ka ne ta barka ka fito?” Kawar da idanunsa ya yi da ga kanta fuskarsa da murmushi “na yi mantuwa ne shi yasa na dawo ɗauka” ya tashi ya cire rigar jikinsa yana cire wandon idanunta ya kai a kan ƙirjinsa da sauri ta tashi ta je wajan da yake a jiye tufafin ya yi a kan gado ta tsura wa ƙirjinsa idanu kallon wajan da take kallo ya yi da sauri ya janye da ga gabanta ya nufi hanya banɗaki shan gabansa ta yi ta kai hannu a kan ƙirjinsa daidai shacin haƙoran ta sha fa wajan lumshi idanunsa ya yi saboda zafin taɓin da ya ji. “Alhaji cizo nake ga ni fa, me ya faru ne?”

“Oh wai wannan ba wani abun ba ne na ɗan ji ciwo ne” ya shafa fuskarta tare da shige wa ban ɗaki. “Humm ikon Allah cizo tabɗijam to ai shi kenan tun da an ce babu komai, idan tayi wari ma ji” ta faɗa da murmushi a fuskarta ta ɗauke kayan da ya cire ta adana su. Bayan wasu ‘yan mintuta ya fito da ga wajan wanka bayan ya shirya ta ce. “Na kawo ma ka abinci?”
“A’a. Tafiya zan yi kar ta ji ni shiru” ‘ka ji rainin hankali wannan cizon da wankan da kayi a nan ɗin ai ya tabbatar mini da zargina ba wani amarci da kake kwasa sai gasa maka aya a hannu da take. Maganinka kenan muna zaman mu lafiya ka je ka jajibo aure, wallahi daga yanzu na daina damuwa a kan aurenka tun da na gama gane dawan garin’ maganarsa ce ta dawo da ita da ga zancen zucin da take. “ya dai kin mini zuru da idanu?”

“A’a babu komai a sauka lafiya. Ka gaida amarsu ta ango” murmushi kawai ya yi dan ya san magana ce ta yaɓa masa. Har sun kai ƙofa ta ce. “hala banɗakin gidan amarya ya lalace ne?” Kallonta ya yi a ransa yana faɗin ‘kai! Mata! A dole so take sai ta gano matsalarsa’ gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin “a’a ba na faɗa maki nayi mantuwa ba ne, da ga office nan na fara zuwa yanzu ne zan tafi gidan”
“Ta zo mu ji ta”

“Me ki ke nufi da ta zo mu ji ta?” To
“Ba abin da nake nufi” komai bai ce da ita ba ya fice ya dawo gidan dan ya huta sai dai wannan kallon zargin da tambayoyin na ta dole ya fi ce ya bar mata gidan dan ba zai so ta fahimci zaman da ya ke da Zainab ba.

*****
Kwance take a kan gado ta rufe jikinta da bargo kasancewar a na sanyi sosai bacci take cikin natsuwa. A hankali ya turo ƙofar ya shigo cikin sanɗa ya hawo kan gado ya shige bargon ta bayanta ya kwanta ya rungumeta ajiyar zuciya ya saukar ya rasa wani irin so ya ke mata jinta a kusa da shi kaɗai ya kan saukar masa da natsuwa. Juye ta yi ta dawo da gabanta gabansa ta sake lafewa a kan ƙirjinsa, kasancewar tana da nauyin bacci hakan yasa sam ba ta fahimci a ina take ba, farin ciki ne ya rufe shi ji yake kamar su tabbata a hakan. Wani irin yanayi yake ji na ratsa shi tun daga ƙwaƙwalwarsa har zuwa ƙafarsa rigar bacci ne a jikinta kusan komanta a fili ji ya ke kamar ya kai hannunsa a kan dukiyar fulaninta sai dai tsoron kar ya wuce gona da iri ta farka ya rasa ‘yar damar da ya samu yasa ya haɗiye duk abin da yake ji har bacci ɓarawo ya sace shi.

Asubar farin kiran sallah ya doki dodon kunnenta ta yunƙura ta tashi ta ji ta a matsi jikin wani abun da bata san ko me ye ba. Sake yunƙura wa tayi motsinta ne ya tashi she buɗe idanunsa ya yi a hankali ya saukar a kan ta “har kin tashi” ihu tasa tare da fizge jikinta daga nasa “me ye haka? A nan ɗin ka kwana me ka yi mini!!? Wayarsa da take kan lokar gado ya ɗauka ya kunna fitilar wayar ɗakin ya haska tsurawa ƙirjinta idanu ya yi saurin jan bargon ta yi ta lullube jikinta “me ka yi mini na ce!!?”

“Kin ga ki kwantar da hankalinki babu abin da na yi maki. Ki tashi ki je kiyi wanka ki yi sallah tun kan lokaci ya shi ge” filo ta ɗauka tana dukan shi ta na ihu “wallahi Allah ya isa ban ya fe ba ka cuce ni!!” Rungumota ya yi jikinsa tana ta ture shi sai dai ta kasa ƙwatar kanta, kai bakinsa yayi cikin nata yana kising ɗin bakin uhm uhm take da baki da ƙyar ta samu ta ƙwace jikinta ta ture shi ya faɗi rairan kan gadon ya lna mayar da numfashi. Sauka ta yi da ga kan gadon da gudu ta faɗa banɗaki tana yunƙurin amai, ya na jin ta girgiza kansa kawai ya yi ya sauka da ga kan gadon ya fita zuwa ɗakinsa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa.

Tayi burush babu adadi haka ta haƙura ba dan ta daina jin ƙazantar bakin ba sai dan babu yadda za ta yi. Dudduba jikinta ta yi dan ta ƙara tabbatar da babu abin da ya yi mata ganin babu wani can ji da ta gani a jikinta yasa ta yi a jiyar zuciya, wanka ta yi tare da ɗauro alwala sai da ta yi wa ƙofar key.

Wunin ranar a ɗaki ta wuni lemon kwali kawai ta wuni sha da yake cikin firj ɗin dakin. Ko kusa da gadon taƙi zuwa saboda wani irin ƙyanƙamin gadon take ji, Allah ya isa kuwa ta yi masa ya fi cikon kwando. Duk yadda ya so ganinta kafin ya fita hakan ya faskara ba dan ya so ba ya shirya ya fita. Da yamma ya dawo gidan ya samu babu kowa a falon ya tura ƙofarta har yanzu a rufe juya wa ya yi ya dawo falon. “Hansa’u! Hansa’u!!”

“Na’am!” Ta amsa da ga cikin ɗakinta fitowa ta yi da sauri ta samu yana tsaye tsakiyar falon durƙusa wa ta yi gabansa “sannu da dawowa” “Yawwa sannu, ya gidan? “Lafiya lau”

“Zainab kuwa ta fito?” Tana gyaɗa kai ta ce. “Tun jiya ba ta fito ba na ta buga ƙofar shiru ko motsinta ban ji ba, sai gab da azahar ne na je na sake buga ƙofa sannan ne ta yi mini magana kar na sake buga mata ƙofa ba ta son damuwa.” Zama ya yi a kan kujera ya ja numfashi ya furzar “kenan ba ta ci abinci ba?”

“Gaskiya ba ta ci ba tun da ba ta fito ba” “Shi kenan za ki iya tafiya” ya yi maganar murya a sanyaye. Tashi ya yi ya sake zuwa ya buga ƙofar shiru “na san ki na jina ki yi haƙuri ki buɗe ƙofar nan mu yi magana kin ji?” Jin babu alamar ko motsinta bare har ya sa rai da za ta buɗe ɗin ya ƙara matsawa daf da ƙofar “zan ba ki minti biyar matuƙar ba ki buɗe ƙofar nan kin fito ba zan tafi Kafancan na ɗauko Baba na san shi za ki ji maganarsa ai” ya juya ya dawo cikin falon ya zauna “Hansa’u!” “Na’am!” Jim kaɗan ta fito “ga ni Alhaji” “Me kika dafa ne?”

“Shinkafa da miya na yi”

“Ok. Ki kawo mini anan ɗin”

“To” ta faɗa tana miƙewa tsaye. Bayan ta kawo abincin ta a jiye ta juya za ta tafi Zainab ta shi go falon “sannu da fitowa”. “Sannu” ta amsa mata a taƙaici. Kujerar da take nesa da shi ta zauna ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta na jijjiga ƙafafun. Kallonta ya ke har ya ma rasa me zai ce da ita, a jiyar zuciya yayi kafin daga bisani ya ce. “Ko me zai faru a tsakanina da ke ba na so ya shafi cin abinci ko keɓanta kanki ki zauna cikin ƙunci”.

“Mtsww! Idan har ba ka son damuwar ta wa dan me za ka nace wa aurena, iyayin banza!”

“Shi kenan ki yi haƙuri ki ci abincin sai mu yi magana”. “Ba zan ci ba!”

“A she ba kya son tafiyar” ƙuru ta masa da idanu kar dai burinta ne zai cika ya gaji zai saki ta. Wannan tunanin da ta yi ne ya sa ta yi saurin sauka da ga kan kujera ta zo gaban abincin saukowa ya yi ya zauna a kan kafet ya janyo filet yana faɗin “bari na zuba ma ki da kaina” komai ba ta ce da shi ba ya zuba mata shinkafar ya zuba miya wanda ta ji naman kaji ya tura mata gabanta “maza ki canye sai mu yi magana”.

Babu musu ta ɗauki cokali ta fara cin abincin sai da ta ji ta ƙoshi ta ture filet ɗin ta sha ruwan da ya zuba mata idanunsa na a kanta komai tayi burge shi take yi.

Ganin ta koma gefe ta zauna yasa ya ce. “Kar dai har kin ƙoshi”.

“Eh.” Ta ba shi amsa a taƙaici. Ta shi ya yi ya ɗauki wayoyinsa kallonsa take a tunaninta zai tafi ɗakinsa ne ya ɗauko takarda sai taga ya nufi hanyar fita falon gabaɗaya zuwa waje. “Ina kuma za ka tafi?”

“Akwai wani abun ne?” Ya yi mata tambayar idanunsa a kanta “cewa ka yi za mu yi magana fa” dawowa ya yi ya tsaya gabanta tashi tayi ta tsaya tana kallonsa ido cikin ido, ɗora hannunsa ya yi a kan kafaɗarta kamar ta gunduma masa zagi ta ji ta dai juri kar ta yi wani abun ya ce ya fasa sakin nata “kin ga yanzu Yayarki tana jirana za mu fita unguwa zuwa gobe zan yi tunani sosai idan na dawo sai mu yi maganar ko?” Ture hannunsa ta yi daga jikinta tana harararsa ta ce.

“Tir karka sake kiranta da wata Yayata Allah ya tsare Gatari da sarar shuka me ye kuma haɗin kefi da kaska!”

“Allah ya huce zuciyarki ba zan sake ba” ya faɗa tare da juya wa ya fara tafiya ta sha gabansa a fusace ta ce.

“Wai me kake nufi dama raina mini wayo ka yi ba saki na za ka yi ba!?”

Murmushi ya yi kafin daga bisani ya ce. “Ki daina tunanin a kwai saki a tsakaninmu Zainab a rayuwata ko da ban son mace na aureta ba zan saki ta ba bare kuma ke da na ke matuƙar ƙauna. Har abada babu saki a tsakanina da ke, aurena da ke mutu ka raba ne takalmin kaza”.

Idanunta suka ƙanƙance saboda masifa wani irin tururin zafi take ji a zuciyarta tana huce ta ce. “Idan kuma ka mutu kuma fa?”

“Shi kenan sai ki samu ‘yancin ki ki yi rayuwar ki yadda ki ke so. Abu ɗaya dai na sani na mutu da igiyar aurenki a hannuna zan yi farin ciki da hakan”
“Mtsww!!! Wallahi ni ce zan zama ajalinka banza marar zuciya!!” Ta bangaje shi ta wuce ɗakinta bin bayanta da kallo ya yi har ta ɓace wa ganinsa ajiyar zuciya ya saukar haƙiƙa da zai iya tabbas da yau ya rabu da ita kamar yadda ta bukata ba dan kalmar kisan da take yawan jefarsa da ita ba, sai dan ganin tsagwaron tsanarsa da ya yi a cikin ƙwayar idanunta.

Haƙiƙa a rayuwarsa wannan ita ce jarabawa ma fi gauni da a ka jarbace shi da ita son wacce ba ta ƙaunarsa. Ya faɗa a zuciyarsa tare da sake sauki gwarron numfashi jiki a sanyaye ya juya ya fita daga gidan.

Hansa’u da take ɗaki tana jiyo duk abinda ke faruwa a ranta tana jinjina girman tsanar da matar gidan ke yiwa maigidan da kuma rashin sa’a irin na Zainab ka samu kyakkyawan miji ga kuɗi ga soyayya a ce ka dinga bauɗe wa ba ka so kana wulaƙanta shi. Hum Allah bai ba mai wuƙa nama! Ina ma ita ce ta samu wannan damar wallahi da ta rungume shi hannu bibbiyu ta yi wadaƙa cikin dukiya yo ina za ta yi sake.

*****
Da safe su na zaune a dani suna karin kumallo bayan sun gama Ilham ta riƙo hannunsa “Dady alƙawarina” ɗora ɗaya hannunsa ya yi a kan na ta yana murmushi ya ce. “Ban manta ba Ilham motar ki tana hanya cikin satin nan za su ƙarasu In Sha Allah” cikin murna ta tashi ta rungume shi ta wuya “na gode Dady Allah ya ƙara buɗe” ta na gama faɗa ta juya da gudu ta nufi sama tana faɗin “bari na kira Lubna na mata albishir”

“Alhaji kana sarganta Ilham duka yaushe ka saya mata wacan motar da har za ka sauya mata wata”.

“Su biyu ne kaɗai ‘ya’yan da na mallaka duk abin da na ke nema saboda su na ke nema dan haka komai zan iya yi masu domin faranta masu”
“Uhm hakan ne, amma ka daina cewa su kaɗai ne ‘ya’yan ka dan babu mamaki yanzu amarya ta fara laulayi ka ga kenan sun kusa samun ɗan uwa” a zuciyarsa ya ce ‘ina ma hasashin ki gaskiya ne da na fi kowa farin ciki hum sai dai na fara cire tsamani da hakan’ miƙewa ya yi “ni zan fita”
“Au ba ka so mu sani ne to ai shi kenan tun da cikin ma ɓoyon sa a ke mana”
“Ai ba a ɓoye alkhairi, ina fatan hakan ta tabbata” ya bata amsa yana tafiya. Biyu bayansa ta yi tana faɗin “to Allah ya tabbatar ai farin cikin mu ne samun sabon Baby”

“Amin”

“Yawwa ka ga jiya ba mu samu fitar nan ba ya kamata kuma a ce mun je mun duba Baba Nafi har fa an ba su sallama su na gida”.

Tsayawa ya yi ya na kallonta ya ce. “Hakan ne gaskiya abubuwa sun yi mini yawa ki tafi da Ilham ku duba ta idan na samu lokaci zan yi ƙoƙari na shi ga da yardar Allah”.

“Shi kenan, idan mu ka dawo za mu biya mu ga amarya tun da ka ƙi kawo mana ita” shiru ya yi ya ma rasa me zai ce ya fahimci Hafsat so take ko ta ya ne sai ta gano matsalar da ya ke ciki da amaryarsa. “Ka yi shiru idan har ba ka so ka haɗamu ne ai shi kenan sai ko wacce ta zauna a in da take tun da hakan ka zaɓa”

“Saboda me zan ƙi haɗuwar ku. Ba damuwa Allah ya tsare sai kun dawo” ya sa kai ya fita. Dariya ta yi ta koma ta zauna a kan kujera tana faɗin “yau sai na ga dalilin da yasa kake ɓoye mana ita.”

******

Tana zaune a kan kafet uwar ɗakinta tana shan shaye tana waya da Raliya “wai me kuke nufi ne da ni tun da na zo babu wanda ya zo wajena sai ka ce ban da kowa a duniyar nan”.

“Ki yi haƙuri Zainab wallahi na so na zo kamar me Baba na gidan ku ne ya hana ya ce sai kin yi hankali kin natsu ko za a fara zuwa gidan ku”.

“Humm ai na sa ne Baba ya jima da daina sona hakan fa ya hana Mama zuwa, sannan Mama ta ce shi ne ya hana a barni na je gida tsawon watanni nan”

“Kema dai har da laifin ki ya kamata ki haƙura komai ya wuce hakan tun da an riga da an ɗaura wata uku da auren ku fa”.

“Mtsww! Ni don Allah mu bar wannan zancen me ye labari”?”

Murmushi Raliya ta yi kafin daga bisani ta ce. “Ke ƙawata ba ma wannan ba hoton da kika turo mini kin ga yadda ki ka yi kyau da fari anya ba jinjirin ciki ne da ke ba ƙawata?”

“Idan ban gunduma ma ki a shar ba Raliya ki ce ba Zainab ne sunana ba! Banza ni kin ma ɓata mini rai wallahi” ta tsinki kiran ta jefa wayar kan gado tana yin tsaki “Allah ya isa na Raliya wai ciki wallahi ta ma raina mini wayo Allah ya kiyaye.!” Cikin sa’a ya na turo ƙofa ya ji ta a buɗe shi gowa ya yi “Assalamu alaikum” kallon ƙofar ta yi ta kawar da kanta tare da jan dogun tsaki ba tare da ta amsa masa sallamar ba ta ci gaba da shan shayen ta.

Ƙarasa wa ya yi ya zauna gefen gado “ko ba komai ai kya amsa mini sallamar ko” “Ai ban ga amintaccin ba ne bare har na ta ya shi neman aminci” ta yi maganar ba tare da ta kalle ko gefen da ya ke ba. “Fatan kin tashi lafiya”. “Da ban tashi lafiya ba za ka ganni hakan ne” gyaɗa kansa ya yi kafin ya ce “hakan ne. Dama na zo na ga yadda kika tashi na kuma nemi wata alfarma a wajan ki” ya yi shiru yana kallonta ganin ba ta da niyar cewa komai yasa ya ci gaba da faɗin “mai ɗakina da ‘yata za su zo an jima ku gaisa, ina roƙun ki alfarma da ki ɓoye duk wani abun da kike ji a zuciyarki ki yi masu tarba ta ƙwarai don Allah ki ɓoye sirrin zaman mu a idanun duniya domin mutuncina da kuma naki don Allah” ya ƙarasa maganar cikin magiya. Shiru ta yi tana tunanin murmushin gefen baki ta yi kafin daga bisani ta ce.

“Allah ya kawo su lafiya”. “Kin karɓi wannan alfarmar da na nema a wajanki ba za ki nuna masu komai ba?” Shiru ta yi na ‘yan daƙiƙo har ya fidda rai da za ta yi magana can ta gyaɗa masa kai tana faɗin “eh” cikin farin ciki ya ce. “Na gode Allah ya yi miki albarka” tashi ya yi kasancewar yana sauri ya mata sallama.

<< Su Ne Sila 8Su Ne Sila 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×