Skip to content
Part 12 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Tambaya Mabudin Ilimi

01. 

Tambaya mabuɗin ilimi,

Tambaya sirrin ilimi,

Tambaya aikin ɗalibi,

Amsawa aikin malami,

Ɗauka kuma aikin mumini.

02. 

Tambaya tushen ilimi ,

Tambaya maganin jahili ,

Tambaya ƙaton makami ,

Tambaya kofin ilimi,

Tambaya ruwa na ilimi. 

03. 

Tambaya tilas ga ɗalibi,

Tambaya jidali ga jahili,

Tambaya jiki ga mumini,

Tambaya ruwan shan malami,

Tambaya makamin ɗalibi.

04.  

Tambaya bata wuce ɗalibi, 

Tambaya ta fi ƙarfin jahili, 

Tambaya na ƙara ilimi, 

Tambaya na canza zamani, 

Tambaya mabuɗin ilimi.

05. 

Tambaya tana da adadi,

Tambaya tana da ladabi,

Tambaya tana da madadi,

Tambaya tana da jalabi,

Tambaya mabuɗin ilimi.

06.  

Tambaya na canza jahili, 

Tambaya na sauya ɗalibi, 

Tambaya na ɗaga malami, 

Tambaya na tona malami, 

Tambaya na tona jahili.

07. 

Tambaya ɗaya na iya kai hari ,

Tambaya ɗaya na iya cin gari,

Amsa ɗaya na iya kare gari,

Amsa ɗaya na iya rusa gari,

Tambaya mabuɗin ilimi.

08. 

Tambaya bata son jinkiri,

Tambaya na tona makiri,

Tambaya na samar da rai,

Tambaya tana da cin rai,

Tambaya mabuɗin ilimi.

09. 

Tambaya mai tsawon zamani,

Tambaya kan ba da lamuni, 

Tambaya ke kawar da jahili, 

Tambaya ke samar da mumini, 

Tambaya mabuɗin ilimi.

10.

Tambaya tushen ilimi ,

Tambaya sirrin ilimi,

Tambaya na ƙara ilimi,

Tambaya na ɗaga malami,

Tambaya ruwa na ilimi.

<< Tambaya 11Tambaya 13 >>

8 thoughts on “Tambaya 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.