Tambaya
Da sunan Allah mai duniya,
Ilahu gwani mai duniya,
Sarkin da yayo duka nahiya,
Da duk komai na duniya,
Zan yo waƙe bisa tambaya.
Annabi hasken duka duniya,
Manzona sirrin duk shiriya,
Mijin Hafsat mai juriya,
Abin ƙaunar duka duniya,
Furucin ka dahir ne a duniya.
Jama’ar Hausawa ga tambaya,
Zan yi ta ga duk wanda ya iya,
Shin ana hawa sama da igiya?
Koko sai dai a shiga rijiya?
Shin ta yaya mai shan giya,
Zai yi limanci da safiya?
To wai an taɓa auren gafiya,
Da maciji koko da bushiya.
Waƙa zan yo bisa tambaya
Domin ta zamo manuniya
Ta yo nuni ga duk duniya
Nunin hanyar nan ta gaskiya
Da ilimi har ma da shiriya.
Malam Alaramma ga tambaya,
A ina ake samun walƙiya?
Na san za ka ce a samaniya,
In babu hadari ko a samaniyar,
Sai kuma ina kenan ga tambaya.
Ta yaya zomo zai zama kurciya,
Alade dai ba shi da tsafta ko ɗaya,
Sarakanan tamɓele sai tunkiya,
Sai kuma me masu ƙarangiya?
Baturen da baya son Birtaniya,
Bahaushen da baya son Zariya,
Mahaucin da kasa gane maɗaciya
To ku sani ko da akwai tambaya.
Ka tambayi Tela ya ake tsargiya?
Ka tambayi likita mecece hasbiya?
Ka tambayi zomo ina bushiya?
Raƙumi shi ke cin haki a bishiya.
Ko kare wai ya taɓa jin kunya?
Anya a iya raba kuturu da zuciya?
Makaho kuwa shina iya jan igiya?
Gwauro baya zunɗen ɗan akuya.
Shin malam na cin mushe ne?
Jaki yana cin dutse ne?
Ko kare ya taɓa sallah ne?
Kaza tana ko harbi ne?
Tambayoyin na da dama,
Ga waɗannan a fafata,
Ban dai so a yiwo rigima,
Akan ɗiya mai jar fata.