Skip to content
Part 14 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Sanadi

01.

Allahu sarki adali, 

Kai ne ka yo ilimi, 

Kai ne ka yi jahili, 

Kuma kai mai ilimi. 

02.

Tsira da aminci ga sahibi, 

Manzona Abus-Sabri, 

Haɗa dukka sahabuna, 

Cikinsu haɗa da Mujaddadi. 

03.

Duniya akwai hargitsi, 

To menene sanadi? 

Manzo ya zo da gargaɗi, 

Sai muka watsar cikin gari. 

04.

Mun shure koyarwa tasa, 

Da ta Allah Wahidi, 

Mun ɗau wayo da dubara, 

Mun bar Allah masani. 

05.

In ka ce kai wane ne, 

Wani zai ce shi wane ne, 

To mu ɗin ko wanene, 

Me muka yo a cikin gari? 

06.

Me muka zamo a cikin gari? 

Salihi ko ja’iri? 

Malami ko jahili? 

Kuma hakan meye sanadi? 

07.

Sadaka da yin zakka, 

Halaye ne nagari, 

Sata da yin zamba, 

Babu mai son su a gari. 

08.

Fitina ta zamani,

Wai menene sanadi? 

Talauci a cikin gari, 

Yawan saɓo ne sanadi. 

09.

Yaranmu duk ga su nan, 

Suna ta yawo a gari, 

Talauci ya zamo sanadi,

Mata na ta yawo a gari. 

10.

Kar ka zamo uban sababi, 

Ka zamo uban haƙuri, 

Maimakon rashin ladabi, 

Haƙuri ya zamo madadi. 

11.

Mun zamo masu rigima, 

Zuciyar mu sam ba haƙuri, 

Mun zamo kamar mujiya, 

Muna ta gudun juna a gari. 

12.

Kowanmu dai ya dudduba, 

Ya samu ya yo nazari, 

Me za mu zam gyarawa, 

Mu samu sauƙi a gari. 

13.

Wanda duk ya shiga Wuta, 

Tabbata akwai sanadi,

Wanda ka gani a Aljanna, 

Tambaya akwai sanadi. 

14.

Menene, menene, 

Wai menene sanadi? 

Sanadi, Sanadi, 

Kowa ya yo nazari. 

<< Tambaya 13Tambaya 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×