Ruwan Sama
01.
Bismillah Sarkina Allah,
Kai kaɗai nake yi wa Sallah,
Rabbana ka saitan alƙibla,
Albarkacin Baban Fati, wanda ya koya mana Sallah.
02.
Jama’a ku zo ku ɗan ji ni,
Zan yo batu mai amfani,
Bisa nazari har da tunani,
Ya Rabbana ƙaran luɗufi, ilimi har ma da tunani.
03.
Akan wayi gari ba hadari,
Kafin a wuni an haɗa hadari,
Ruwan sama shi za yaita diri,
Bisa umurnin sarkina, ruwa haka zai ta zuba a gari.
04.
Wannan iko ai sai Lillahi,
Hakan ne ya saka ni mamaki,
Ina ta batu da tambihi,
Akan wannan mu’ujiza, tabbas akwai mamaki.
05.
In ya sauko kan abu mai zaƙi,
Sai ya ƙara mishi yin zaƙi,
In ya sauko kan abu mai garɗi,
Sai ya ƙare shi da yin garɗi, wannan hikima sai Lillahi.
06.
In ya sauko kan abu mai tsami,
Sai ya ƙara mishi yin tsami,
In ya sauko kan abu mai ɗaci,
Sai ya ƙare shi d yin ɗaci, wannan hikima sai Rabbani.
07.
In ya sauko ai ta murna,
Manoma sui ta yin shuka,
Furanni sui ta annushuwa,
Waye zai iya yin haka, wannan aiki sai Allahu.
08,
Ƙasa yanzun ka ga tai laushi,
Furanni sai ka ga sun yi fresh,
Yanayin gari ka ga yi liflif,
Waye zai iya wannan aikin, kasan sai Al-Azizu.
09.
Allahu muna daɗa gode ma,
Bisa wannan tarin ni’ima,
Allah mun ƙara gode ma,
Ba wanda zai iya yin haka, tabbas sai kai Lillahi.