Skip to content
Part 16 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Ni

01.

Ya Rabbana, Kai ne mai ni, 

Na yi addu’a, bisa imani,

Komai zan yo, a bisa izini, 

Nake tambayar wanene ni? 

02.

Ana ta tambaya, wanene kai? 

Jama’a nata tambaya, wanene ni? 

Nima nayi tambaya, wanene ni? 

Wanene ni, wanene ni? 

03.

To nima dai, banda amsar, 

Kuma nima da, ga tambayar, 

Zan yi wa kaina, zan yi miki, 

Zan yi maka, zan yi muku. 

04.

A fagen ilimi, wanene kai?

A fagen ilimi, wacece ke?

A fagen ilimi, wanene ni?

Wanene ni, wanene ni?

05.

A cikin addini, wanene kai?

A fagen addini, wacece ke?

A fagen addini, wanene ni?

Ya jama’a, wanene?

06.

Me na yi, menene zan yi?

Me ka yi, kuma me za ka yi?

Me kika yi, menene za ki yi?

Ya jama’a, wanene ni?

07.

A wurin jama’a, wanene ni?

A wurin iyaye, wanene?

Wurin abokai, wanene? 

A wurin malamai, wanene ni?

08.

Wurin taimako, wanene ni?

Fagen tausayi, wanene ni?

Fagen amana, wanene ni?

Sauke haƙƙin Allah, wanene ni?

09.

A wurin Allah, wanene ni?

A cikin rayuwa, wanene ni?

Yau ina raye, me ake faɗa? 

Idan na mutu, me za a faɗa?

10.

Ya ikiwani, wanga tambaya,

Mu yi wa kanmu ita tambaya,

Mu bada amsar, ita tambayar,

Ga kawunanmu, mu samu amsar.

11.

Ga masu tambaya, wanene ni?

Haiman dai ake kira, ku jini ni,

Jamilu shi ne anka raɗa, tuntuni,

Bn Abdulrahman, ku tuna da ni.

12.

Idan na yi kure, ku yafe ni, 

Na yi muku laifi, ku gafarce ni, 

Ko bayan mai mutuwa, ku yo tuni,

Ku yi mini du’a’i, a tuna da ni. 

<< Tambaya 15Tambaya 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×