Mutuwa
01
Sarki Allah, ubangijina mai mutuwa
Ya Mannanu, da sunanKa ni zan fara
Sarkin mutuwa, da duk komai na rayuwa
Allahu gwani, yai duniya kuma yai lahira
Al-ƙaliƙu Ya As-Samadu, Kai ke da rayuwa
Kai ka yi ranmu, kuma kai ne ka yo mutuwa.
02.
Salati ga manzo, Muhammadu Rasulullah
Ɗan lele, a wurin Allah kai ne Nurullah
Kai ne na gaba, a cikin halittun Allah
Ya Manzon mu, ka cece mu a gaban Allah
Ka zamo jin ƙai, a lahira bayan mutuwa.
03.
Allahu gwani, bisa hikima da buwayarSa
Ya yi rayuwa, Ya yi mutuwa bisa ikonSa
Ya sa rayuwa, ta zamo gwaji ga bayinSa
Ya sa mutuwa, ta zam izina ga bayinSa
Domin bayinSa, su sam darasi kan rayuwa.
04.
Amon mutuwa, yana yawo tamkar sauti
Sautin mutuwa, yana yawo har kan titi
Titin rayuwa, mutuwa tuni tai fenti
Fentin mutuwa, ya yi ado a duk rayuwa
Rayuwar kowa, ko ba ka so ka san mutuwa.
05.
Mai yin tafiya, ka bincika ya san mutuwa
Mai saurare, in da hankali yasan mutuwa
Mai karatu, da nazari ka san mutuwa
Mai daraja, da musaki kowa yasan
Mutuwa
Hakanan kowa, in ka tambaya yasan mutuwa.
06.
Ka yi taimako, ka ƙi taimako akwai mutuwa
In ka gyara, ko ka ɓata da akwai mutuwa
Kai zalunci, ko adalci da akwai mutuwa
Ka yi gaskiya, ko ha’inci da akwai mutuwa
Ko mai muka yi, mu dai sani da akwai mutuwa.
07.
Ina tajiri, mai dukiya da samun duniya
Ina shugaba, da anka ba mulkin duniya
Ina malami, da anka ba sanin duniya
Ina manomi, da anka ba ribar noma a duniya
Ko a kasuwa, ko ina kake dai a duniya.
08.
Ina matashi, mai samartaka kana tashe
Ina budurwa, mai budurtaka kina tashe
Ina ɗan yaro, da yanzu yake ƙuruciyarsa
Ina jariri, da yanzu yake fara yin rayuwar sa
Har ma na ciki, mutuwa tana iya samun sa.
09.
Ina talaka, da bai da komai sai ransa
Ina faƙiri, da bai da komai sai tufarsa
Ina mai kyawu, da ke jiji da kyawunta
Ina mai diri, da ke taƙama da dirinta
Ranar mutuwa, wannan ba za a duba ba.
10.
Ko ka shirya, ɗan uwa ko ba ka shirya ba
Ko kin shirya, ‘yar uwa ko baki shirya ba
Ko na shirya, ‘yan uwa ko ban shirya ba
Ko kun shirya, ‘yan uwa ko ba ku shirya ba
Ko mun shirya, ‘yan uwa ko ba mu shirya ba.
11.
Da lokaci yayi, tafiya fa ba mai hanawa
Ko da Ummi, ko Baba ko ko ‘yan uwa
Wane mata, ko ‘ya’ya, basu hanawa
Ba batun maƙiya, masoya ma basu hanawa
Haka za ka tafi, ana kallo ka yi macewa.
12.
Aikin da ka yi, komai kyawu ko muninsa
Shi za ka taras, a yadda ka yi shi da siffarsa
Hali na ƙwarai, ibada da imani ko akasin sa
Kai adalci, zalunci ko makamantansu
Su za ka taras, makwancinka kai ka shirya shi.
13.
Allah ka shirye mu, ka sa kuskure mu gyaggyara
Ka yo afuwa, laifukanmu ka sa a wawwanke
Ka yo yafiya, zunubanmu duka a kankare
Ka yi mana tsari, azaba ta kabari ka tuttunkuɗe
Ka yo rahama, tabbas ita rahamar ai taka ce.
14.
Ranar mutuwa, idan ta zo ka sa mu dace
Kalmar daraja, furtata ka sa mu dace
Da imani, cikin zuciya kar ya kuɓuce
Har Aljannah, mu sam tafiya a cikin dace
Ka haɗa mu, da Manzon mu abin kwatance.