Ina Ma
01.
Da sunan Ilahi gwani gwarzo da yai min basira
Sarki Ilahi da yai kowa ka daɗan basira
Salati ga manzo Mahmudu da ya zo da bushara
Ina ma na ganka manzona in gode in ƙara
Ina ma ace zan samu cetonka da ba batun ƙara.
02.
Ina ma ace ni tsuntsu ne in yunƙura in tashi
Ina ma ace ni zomo ne in ta gudu ba fashi
Ina ma ace ni kifi ne in ta iyo babu fashi
Ina ma ace waliyyi ne ni in yi rayuwa babu fushi
Ina ma ace ni jariri ne in ta bacci ba fashi.
03.
Ina ma ace ni tajiri ne in ta kece raini
Ina ma ace ni manomi ne in ta noman rani
Ina ma ace Soja ne in ga mai min raini
Ina ma ace tuni na shahara ai ta ma nuna ni
Ina ma ce mace ce ni ai ta faman ririta ni.
04.
Ina ma ace dogo ne ni in fi kowa nisan sauti
Ina ma ace sirri ne a daina ce min lukuti
Ina ma ace ɓarkeke ne ni ƙato uban ƙarti
Ina ma ace ni direba ne kullum ina kan titi
Ina ma ace bani da kowa in ta sheƙe aya kan titi.
05.
Ina ma ace ni malami ne in ta karatu
Ko ace ni ɗalibi ne in ta faman ɗaukar karatu
Ina ma ace ɗan kasuwa ne in je makarantu
In ɗauki nauyin yara na ƙasa fannin karatu
Ina ma dai ace plumber ne masani na bututu.
06.
Ina ma ace tunanina zai samu ya ɗan gyaru
Ina ma ace halayyata za ta samu ta ɗan gyaru
Ina ma ace ɗabi’una za su samu su ɗan gyaru
Ina ma ace fa ƙalbina za ta samu ta ɗan gyaru
Da na fice matsala na daina raɓe a jikin garu.
Allah ya ƙara basira.