Sahibar Raina
01.
Ya Sahibar raina,
Ya gimbiyar binina,
Ke ce da mulkin zuciya.
02.
Sanyin idona,
Mai faranta raina,
Ke ce abar son zuciya.
03.
Ya ke mai daɗin murya,
Sannu mai hasken idanu,
Ke ce muradin zuciya.
04.
Sahibar raina,
Ina ƙaunarki mai sona,
Ke ɗai na sa a zuciya.
05.
Kin shige raina,
Ina mararinki mai sona,
Begenki yana a zuciya.
06.
Ke ce da mulkin birnina,
Ke ce abar sona,
Ke ce kaɗai a zuciya.
07.
Rayuwa za ta cutu,
In har babu ke,
Domin ke ce bugun zuciya.
08.
Murmushin Fuskata,
Da fushin zuciyata,
Don ke nake yi masoyiya.
09.
Sahiba saboda ke,
Masoyiyata saboda ke,
Na tabbata zan shiga maliya.
10.
Akan so da ƙaunarki,
Don tsantsar begenki,
Zan wuce judo zuwa ga samaniya.
11.
Sahiba domin na same ki,
Tunda ni dai ina sonki,
Zan iya baki duniya.
12.
Buri na ke ce Sahiba,
Muradina ke ce Sahiba,
Ke kaɗai nake so a duniya.
13
Sahiba na baki raina,
Ruhi, jini da jikina,
Kin zamo mai mulkin zuciya.
14.
Rayuwata tuni ai taki ce,
Kome kike so zana yi,
Ke kaɗai na ba wa zuciya.
15.
Mutuwa ace mini za kiyi,
Na gwammace ai ni na yi,
Da a ce kin bar ni a duniya.
16.
Meye ribar na rayu in babu ke?
Ta yaya za na rayu in babu ke?
Komai na duniyata yana ga ke.
🙏🙏🙏🙏🙏
Shukran