Mene Ne?
01.
Mene ne, mene ne?
Mene ne ya dame ni?
Mene ne ya dame ka?
Mene ne ya dame ki?
Wai mene ne ya dame ku?
02.
Mene ne ya dame mu?
Mene ne ya same mu?
Wanene ya dame mu?
Mece ce matsalar mu?
Ina ne matsayar mu?
03.
Mene ne cikin ranmu?
Mece ce aƙidar mu?
Mece ce manufar mu?
Yaya ne aikinmu?
Ina ne makomar mu?
04.
Samari juna jina,
‘Yan mata kuna jina,
‘Yan yara kuna jina,
Tsofaffi kuna jina,
Wai ina ne matsayar mu?
05.
Mutane kuna jina,
Ko da ma ba kwa jina,
Sai ku nazarci batuna,
Makomar mu duk mu tuna,
Wai ina ne makomar mu?
06
Siyasa ta ƙasar mu,
Ƙaɓilu na ƙasar mu,
Addinai na ƙasar mu,
Tsarin mulkin ƙasar mu,
Wai mece ce matsalar mu?
07.
Ha’inci a tsakanin mu,
Hassada a cikin ranmu,
Zalunci a ƙasar mu,
Mugunta a tsakanin mu
Wai Mece ce matsalar mu?
08.
Allahu ya sarkin mu,
Kai ke da rayuwar mu,
Kai ne Kasan dukkan mu,
Da abin da ke zukatan mu,
Kai ne kasan matsalar mu.