Gantalalliya
01.
Da sunan Rabbana sarki,
Allah kai daɗin tsarki,
Ga wanda ya zarce tsarki,
Habibu ka wuce mamaki,
Shugaban masu shiriya.
02.
Haiman yau na yo niyya,
Zan yo waƙar la’ananniya,
Koko ku ce mata mujiya,
Tana yawo tambaɗaɗɗiya,
Wannan ita ce gantalalliya.
03.
Yau na taso zan yi bayani,
Akan wata ‘ya mai muni,
Aikinta shi ne mafi muni,
Tana cutar da addini,
Allahu ka sa ta sam shiriya.
04.
Ita ce matar da tai aure ,
Tana nan zaune gidan aure ,
Tana neman mazan ƙyaure ,
Kunyarta fa duk ta ture ,
Wannan ita ce la’ananniya.
05.
Ja’irci sai ja’ira,
Makirci sai makira,
Kwartanci sai kwartuwa,
Jahannama can dai ba ruwa,
Wannan zance ne na gaskiya.
06.
Ta bar mijinta gida zaune,
Tana can yawo ba aune,
Tana ta cin amanar aure,
Imanin tuni ya ware,
Wannan ita ce tsinanniya.
07.
Ƙwaya tare da yin maye,
Tana ta layi kamar ganye,
Idanu duk sun jujjuye,
Bata gane ko waye,
Wannan ita ce makakkiya.
08.
Shagiɗaɗɗiya maras kunya,
Karkatacciya tana hanya,
Ba ta Kano ba ta Zariya,
Kullum dai tana kan hanya,
Wannan ita ce gantalalliya.
09.
Ita dai da zarar ta ga kuɗi,
Kwanyarta shaiɗan yai ta kiɗi,
Tana lissafa gyaɗa da riɗi,
Tana sauran kayan haɗi,
Wannan ita ce karkatacciya.
10.
Bata ɗakin gwauro a yau,
Na tuzuru zata biɗa a yau,
Tana nema amma fayau,
Ba albarkar ko ta miyau,
Wannan ita ce wahalalliya.
11.
Komai ya bata ba ta yabo,
Ita dai idonta idon kwabo,
To yanzun ka sha yabo,
Komai nata tana baka,
Wannan ita ce tambaɗaɗɗiya.
12.
Namiji ɗai bashi isarta,
Naira ɗai ce ƙawwarta,
Ta manta da auranta,
Ta yar da duk kimarta,
Wannan ita ce firgitacciya.
13.
Gata ƙyamas tamkar rake,
Idanu duk sun rarake,
Kutushi duka duk ya molaƙe,
Ƙafafu duk sun shagiɗe,
Wannan ita ce busasshiya.
14.
Sai ta bari ba mai gida,
Ta kawo gardi har gida,
Su hau aikata masha’a,
Ba imani ko ɗa’a,
A wurin Allah mai duniya.
15.
Gata can jemammiya,
‘Yar bishiya busasshiya,
Ta fi kama fa da muciya,
Koko ku ce makauniya,
Wannan ita ce watsattsiya.
16.
Ya dai kamata ki zam gyara,
Tun kafin ki je lahira,
Aita bugun ki kina ƙara,
Ba mai ceto ko kin ɓara,
Kina ihu wahalalliya.
17.
Ki tashi ki zam gyaran hali,
Ki zam tuban munin hali,
Ki gyara ki koma mumina,
Ki bar layin ‘yan sintiri,
Ki hau hanya managarciya.
18.
Ya Allahu ka shirye mu,
Da mata har da ‘ya’yanmu,
Maƙfta har da danginmu,
Ka sa ilimi a ƙwaƙwalwa,
Wannan shi ne dai gaskiya.
19.
Ka sa imani a zukatanmu,
Da shiriya a ruhinmu,
Da ƙarin son ManzonKa,
Habibu da ba ya shi gunka,
Shi ne hasken duka duniya.
20.
Haiman ne ke sallama,
Na barku tare da salama,
Ku kasance cikin ni’ima,
Da walwala banda hamma,
Har ranar barinta duniya.