Skip to content
Part 25 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Zamani

01.

Da sunan Rabbi sarki mai zamani, 

Al-Sattaru ubangiji Kai ke da ni, 

Ƙaran basira, ilimi har da imani, 

Ka ninka salati wurinsa sa da ni, 

Kai ne Allah, mahaliccina adali.

02.

Ga zamani kuma ga mu ya akayi?

Gurɓacewar zamani yai ƙamari,

Yaya aka yi laifin wa za a gani?

Mun bar Allah mun kama zamani,

Wai ko kun tuna mutuwa zamu yi?

03.

Lalatar zamani tai yawa a gari, 

Babu budurwa kuma ba saurayi,

Ba bazawara kuma ba bazawari,

Matan banza suna yawo cikin gari,

Shigar baɗala na jawo zina a gari.

04.

Kayan maye a yau ya zam gwari,

Shaye-shaye ya zamo adon gari,

Tsafe-tsafe da tsibbu cikin gari,

Masu canja siffa gasu nan a gari,

To ku faɗa min shin ya za mu yi?

05.

Na sama ba ya tausayin na ƙasa,

Na ƙasa sam baya daraja na sama,

Mata na ha’intar miji in baya nan,

Miji na zaluntar mata ko tana nan,

Anya jama’a kam wannan zamani.

06.

Zamanin da duk ba a haka 

Yanzu me ya sa ake haka? 

Mun zamo tamkar hankaka 

Masu maida ɗan wani naka

Ya kamata mu bar yin haka.

07. 

A ce uwa ba a ganinta da daraja?

Ashe uba yau bai da wata kima?

A yau an ɗau aure tamkar ciniki,

An ɗauki saki kamar kora awaki,

Anya, anya jama’a mu ɗau darasi.

08.

Shugabanni basu faɗi a bi,

Malamai basu faɗi mu bi,

Iyaye basu faɗi mu bi,

Ja’iri in ya faɗi kuma sai mu bi,

Haka muke a wannan zamani.

09.

Kaiconka mutumin zamani,

Musamman mai yin fahari,

Duniya tai maka hanzari,

Da ma ka farga tun wuri,

Ka rabu da ruɗin zamani.

<< Tambaya 24Tambaya 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×