Yaushe Ne?
01.
Yaushe za mu gode Allah,
Yaushe za mu tsaida Sallah,
Yaushe ne, Yaushe ne, Yaushe ne?
02.
Yaushe zan ɗau addini,
Yaushe zan bar kafirci,
Yaushe ne, Yaushe ne, Yaushe ne?
03.
Yaushe za mu kama sunnah,
Yaushe za mu ƙyale bidi'a,
Yaushe ne, Yaushe ne, Yaushe ne?
04.
Yaushe zan ɗauki ilimi,
Yaushe zan bar jahilci,
Yaushe ne, Yaushe ne, Yaushe ne?
05.
Yaushe za mu daina gulma,
Yaushe za mu bar haɗama,
Yaushe. . .