Wata Rana
01.
Da sunanKa Rabbu Azizu
Wanda yai dare yayi rana
Subhana Jalla Jalalu
Mai yi wa kowa komai
Allah Ka ninka salati
A wurinsa Baban Fati
Alihi haɗa da sahabu
Da ulama’u gaba ɗaya.
02.
Wata rana zan yi bayani
Ba don ina da sani ba
Wata rana zan zama ba ni
Ba don ina da nufi ba
Wata rana za ku guje ni
Ba don na yi laifi ba
Wata rana za ku tambaye ni
Kuma ba zan iya amsawa ba.
03.
Wata rana za ku tunani
Ba domin kewa ba
Wata rana ku so ku ganni
Ba don ba hoto ba
Wata rana za ku soni
Ba tare da na nema ba
Wata rana za ku yabe ni
Ba don ganin ido ba.
04.
Wata rana tana ga Allah
Ko wai ba haka ne ba
Ku zamo kula da sallah
Wata rana za ku ci riba
Wata rana za ku ji daɗi
Ko da maƙiya basu so ba
Watarana za ku yi nasara
Ko da ace ba za na gani ba.
05.
Duniya tana da daɗi
Ba sai kana da kuɗi ba
Duniya tana da azaba
Ba don talauci ɗai ba
Rayuwa makaranta ce
Ba sai ga ɗalibi ba
Tambaya ita kau sila ce
Ba sai ga wanda ya yo ba.
06.
Kalmar so na da tasiri
Ba sai ga mai yin so ba
Ƙauna tana da sihiri
Ba sai ga mai tsafi ba
Rayuwa tana da sirri
Ba sai ga mai laifi ba
Mutuwa ƙarshen darasi
Babu wanda ba zata hau ba.
07.
In ka so ka zamo na kirki
Ba wanda ba zai so ba
In ka so ka zamo na banza
Ba wanda za ya yabe ka
In kin zamo ta kirki
Ba wanda ba zai zo ba
In kuma kin zamo ta banza
To nagarin ko ba zai zo ba.
08.
Allahu muna roƙonKa
Ka yafe zunubanmu
Mun yi tuba a gareka
Ka shafe laifukanmu
Albarkacin Baban Fati
Manzo Muhammadu namu
Wanda duk bai ƙaunarsa
Tabbas ya zama garwa.