Wariyar Launin Fata
01.
Da sunan Rabbana Allah mai kowa
Tsira da aminci ka ƙara daɗowa
A wurin Mustapha da ya fi kowa
Ƙareni basira da fikira mai yawa
In zamo fasihi abin son kowa.
02.
Tun farko Rabbana kai ke da kowa
Kai ne kai uba da uwa gun kowa
Kai kai yare da al’adu na kowa
Kayi mutane da aljanu da kowa
Kai ke bamu ruwa domin kowa.
03.
Baka rabe ba ka yi ruhi ga kowa
Ga lafiya a wurin jaki har cilikowa
Balle mutum da aljanu samudawa
Hatta ƙwari dabbobi babu ragowa
Baka rabe ba Ilahu ka ba wa kowa.
04.
Kai ne kayi ƙasashe da yawa
Kaine ka yo mutane da yawa
Kai ne kayi harsuna da yawa
Kai ne ka yo kamanni da yawa
Gamu nan birjik muna yawatawa.
05.
Cikin ikonka Rabbana ka yo fari
Cikin hikima Al-Ƙaliƙu ka yo baƙi
Wani dogo wani guntu hakan ka yi
Wani ƙato wani fingi hakan ka yi
Buwayi sarki yadda ya so ake yi.
06.
Ga wasu jajaye wasu ko zabiya
Ga wasu tsaka tsaki kuk dubiya
Ga wasu ‘yan daidai cikin duniya
Ga wasu madalla sun tare hanya
Gwanin sarki haka ya so haka za a yi.
07.
Ga mu nan duk cikin duniya ɗaya
Muna rayuwa, numfashi iri ɗaya
Muna shaƙa da fitarwa salo ɗaya
Muna ci muna sha da baki ɗaya
Bayan gida muna yi duk ta ƙofa ɗaya.
08.
Ga jini nan da jijiya iri ɗaya
Ƙasusuwa da zubin jiki iri ɗaya
Ƙasusuwa da gaɓoɓi iri ɗaya
Harsunanmu suna shige ɗaya
Komai namu suna kama ɗaya.
09.
Launin fata hikima ce ba wasa ba
Kai ka tsara ba don mun nema ba
Haka nan kaso ba za mu raina ba
Baki ko fari ba za mu kushe ba
Tunda Kai ka yi ba za fa mu ƙi ba.
10.
Me yasa kuke ƙyamata ne?
Me yasa kuke guduna ne?
Me yasa ba kwa sona ne?
Shin wai me na yi muku ne?
Amsar ita ce wai ni baƙi ne.
11.
Wariyar launin fata ko ɗai bai ba
Wannan mugun hali sam bai ba
Tir da wannan hali mu barshi dai
Mu so juna kuma mu haɗe kai
Mu zam tsintsiya mu share datti kawai.
12.
Me yasa to muke ƙyamar juna?
Me yasa muke wariya ga juna?
Me yasa muke ƙiyayya ga juna?
Me yasa muke gudun juna ne?
Bayan muna da abubuwa iri ɗaya?
13.
‘Yan uwana mu bar wannan abu
Mu so juna kamar Bukar da Habu
Mu bar rikicin lautin fata a buhu
Mu yasar can mu bar cikin duhu
Mu riƙe juna mu zamo ‘yan uwa.
14.
Allahu ka shiryar da mu duka
Ka sa mu zamo nagari mu duka
Mu zamo masu kyawun hali duka
Mu zamo son kowa mu duka
Cikin gari da ƙasa ai ta yabonmu duka.