Wane Irin Uba Ne Ni?
Amshi:
Wane irin uba ne ni?
Wai ni wane irin uba ne ni?
Wane irin uba ne ni?
Wai ni wane irin uba ne ni?
01.
Jama’a ku saurara, zan yo batu babu ja-in-ja
Zuciya ce ta ruɗe ni, gashi yau na taɓo danja
Ina son ɗiyata ce, kun ga na ko jawo jarfa
Riga ta gaza hana aikin banza, wa ke batun ma jamfa.
02.
Ɗiyata da na haifa, ita zuciyata take ƙauna
Tsantsar nuradinta, yasa na kira ta sanyin raina
Gashi nan fa ta girma, komai dai masha Allah
Ga ɗiyar akwai ladabi, halayyarta sai madalla.
03.
Na kori dukkan samarinta, don bani so su yi min cikas
So nake da na sam dama, in tsinci haja a ɓagas
Bani so kowa ya raɓeta, don ni kaɗai ke muradinta
Ko aike ban so a tura ta, don bani so tai ta ragaita.
04.
Na zamo tamkar kare, ɗiyata nake ta farauta
Kullum ina tunaninta, na manta ni na haife ta
Tunani a har kullum, yaya zan same ta
Burina a har kullum, idanu sui ta kallonta.
05.
Hancina a koyaushe, so yake ya ji ƙamshinta
Na sha in ta mafarki, wai ina tare da ita
Na riga fa nai nisa, banjin kira ku bar mini mita
Shaiɗan ya min huɗuba, kan lallai na nemeta.
06.
Tunda har ta kira ni Uba, dole ne in umurce ta
In ce ta ɗan duba, ta taimaki Abbanta
In ta so ta min tababa, wai kawai sai na shaƙeta
Haka shaiɗan yai ta riya min, zuciya har fa ta aminta.
07
Watarana ina ɗakina, kawai na kirawo ta
Dama a loton nan, na aiki babarta
Na ce ta je can ƙauye, don ta dubo iyayenta
Ita ɗiyata na ce ta zauna, akwai makaranta.
08.
Na riga fa na shirya, tabbas yau zan same ta
Ta shigo ɗakina, sai na ce ta sakki jikinta
Kafin ta ma zauna, na riga fa na sa sakata
Na kulle ƙofar gam, babu hanya bare mafita.
09.
Da ta nuna tababa, ai nan da nan sai na shaƙeta
Ashe na taɓo Nepa, akwai aljanu a kayinta
Aljanin da ya tashi, ji kake titim sai duka
Kafin ka ce mene, tuni har na fara yin kuka.
10.
Jikina ya yi talata, domin ko na sha duka
Ina yin shesheka, neman afuwa ina kuka
Ina ta faman ihu, neman agaji na maƙwafta
An shigo cetona, ƙofar ko na sa sakata.
11.
Kafin a ɓalle ma, tuni na riga na fa jigata
A taƙaice dai malam, da ƙyar aka ƙwace ni
A sa’ilin nan ma, jikina duk rauni
Ko’ina sai tabbai, sai assibiti aka kaini.
12.
A loton ga na farka, na ji ni ina gurnani
Zufa tana karyo min, kamar a kogi aka tsamo ni
Takaici nan ya sarƙeni, na zauna ina ta tunani
Ashe mafarki na yi, damuwa ta aure ni.
12.
Allahu na tuba, Allah ka yafe ni
Sharri na sheɗani, Allah ka kare ni
Tunani ma mai muni, Allah ka kiyaye ni
Ruɗi na zamani, Ya Rabbana ka kare ni.
13.
Ka shirye ni shiryawa, daga duk baɗala ta zamani
Ko da ina kogi, ko bayan na haye tsauni
Albarkacin Manzo, shugaban masu imani
Na tuba na bika, Ya tabaraka Mannani.
Allah ya shirya mana zuri’a.
Ya mana kyakkyawar ƙarshe.
🙏
🙏🙏🙏🙏
Amin.
#haimanraees