Skip to content
Part 7 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Barka Da Zuwa

Barka da zuwa zamaninmu, Zamani mai ban mamaki.

Zamanin da uwa ke ƙaunar,

Kuɗi sama da ‘ya’yanta.

Zamanin da uba ya ke cinikin,

Ɗiyarsa kamar haja abinsa.

Zamanin da ‘ya’yaye

Ke gudun iyayensu.

Zamanin da malami,

Ya ke cutar ɗalibansa.

Zamanin da ɗalibai

Suke raina malumansu.

Zamanin da mutane, 

Kowa ke ta kansa. 

Barka da zuwa dai, 

Barka da zuwa baƙo. 

Barka da zuwa zamanin 

Da ake ado da cuta. 

Zamanin da mutane, 

Suke fahari da zamba. 

Zamanin da malamai, 

Ke ciniki da malanta. 

Zamanin da shugaba, 

Ke fahari yayi cuta. 

Zamanin da ‘ya mace, 

Ke sakin mijinta. 

Barka da zuwa dai, 

Barka da zuwanka. 

Barka da zuwa zamanin,

Da aka raina marubuta.

Mutane sun kama Shaiɗan,

Sun bar Allah Rabba.

Kowa ta kai kawai ake,

Jama’a mu yi duba.

Hoɗijam! Akwai aiki Babba,

Aradu akwai aiki ja.

Ɗan uwa ke sa a sace nashi, 

Wani ma ka ji ya ce a kashe shi. 

Uwa da ɗa wata sai ta yada shi, 

Wata ƙunzugunta ta saida shi. 

Fatana Ilahu ka duba mu, 

Kada ka barmu da wayonmu. 

Ka tsare mu shiriya, 

Duka gamu.

Albarkacin Annabi dai, 

Wannan mai sonmu. 

<< Tambaya 6Tambaya 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.