Skip to content
Part 8 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Wane Irin Miji Ne Ni?

Amshi:

Wayyo ni, wayyo ni, 

Wayyo ni, wayyo ni 

Wane irin miji ne ni? 

Wane irin miji ne ni? 

Ya Rabbi na tuba. 

01.

Bismillah sarkina,

Sarkin da yai rana,

Wanda yai yi jikina,

Har ma da ruhina,

Gareka nake tuba.

02.

Ya aiko da Manzona, 

Da saƙon da ba ɓarna, 

Ƙur’ani da ita Sunnah, 

A babin karatuna, 

Ya Hayyu na tuba. 

03.

Don biyayyar iyayena, 

Na auri mai ɗakina, 

Ta daɗe tana sona, 

A raina ko ba ƙauna, 

Akai ba da naso ba.

04.

Ta zarce duk mata, 

Biyayya da nagarta, 

Bani son kallonta, 

Balle in zan huta, 

Wurina ba ta zo ba.

05.

Ta maida ni ɗan gata, 

Shalele ne ni gunta, 

Amma da ta yo wauta, 

Nan da nan na fusata, 

Sarkinmu na tuba.

06.

Wataran na zage ta, 

Wataran na mareta, 

Wataran na haure ta, 

Wataran na duke ta, 

Allahu na tuba.

07.

Haƙuri kamar damo, 

Har in je in komo, 

Bata zuwa yawo, 

Bata ƙwafa in na dawo, 

Fushi sam bata yo ba.

08.

Komai idan na samo, 

Nono tsala ko kindirmo, 

Ko da ice ko ɓawo, 

Murna take na dawo, 

Ƙorafi ba za tai ba.

09

Dariya da oyoyo, 

Yauƙi kamar ayayo, 

Zata mini oyoyo, 

Ta tarbe ni oyoyo, 

Ba tare da fushi ba. 

10.

Girki idan ta yi, 

Ban kulata ko ta yi, 

Ban yabo ko ta yi, 

Gara ma na sha shayi, 

Abincin ba za na ci ba. 

11.

Kwalliya gyaran ɗaki, 

In tai na yo tsaki, 

Wanki idan tai min, 

In ce ta ɓata min, 

Godiya ba za nai ba. 

12.

Shimfiɗarta sai sa’a, 

Ko ta kira in ce a’a, 

Bata taran jama’a, 

Sai dai addu’a, 

Fushi sam bata yo ba. 

13.

Komai idan tai mini, 

Ba yabo sai kushe, 

Hakan yasa ta bushe, 

Kamar rake ya bushe, 

Zuljalalu na tuba. 

14.

Haka dai take haƙuri, 

Wataran ta sha mari, 

Ko ko na sa ta mari, 

Yanzun ta sha ɗauri, 

Tausai ba zan yo ba. 

15.

Magi idan zan bata, 

Ko gishiri zan bata, 

Zan ƙidaya a gabanta, 

Dole ni zan bata, 

Don yarda ba zan yo ba. 

16.

Talabijin sai na kunna, 

Rediyo sai na kunna, 

Bacci idan ni na so, 

Ko da fa bata so, 

Musu ba za tai ba. 

17.

Ana nan fa sai cuta, 

Ta kamata ta ci ta, 

Zuciyarta ta buga, 

Har jini ke ɓubbuga, 

Ba ta hanyarsa ba. 

18.

Ta mace ta tafi, 

Lahira ta tafi, 

Aka barni nan tinƙi, 

Nai jugum ni gwanki, 

Tunani ba za na ƙi ba. 

19.

Zulumi da ya taso, 

Hawan jini ya taso, 

Sai na faɗi kan soso, 

Gani nan kamar soso, 

Alhaki ba zai gudu ba. 

20. 

Babu halin aure, 

Gwauro a cikin zaure,

Jikina ko ya shanye, 

Akira ɗan mai ganye, 

Saiwa ba za na ƙi ba. 

21.

Mugun miji dai ni ne, 

Na sani dai ni ne, 

Cutarta har mutuwa, 

Jinyarta har mutuwa, 

Ba zai wuce kaina ba. 

22.

Wallahi na tuba, 

Sam ban fa kyauta ba, 

Ba zan daina kuka ba, 

Ku yafe ni na tuba, 

Ya Hayyu na tuba. 

23.

Sarkinmu Allahna, 

Albarkacin manzona, 

Ka yafe laifina, 

Ka shafe zunubaina, 

Ba za na ƙara ba. 

24.

Mace in ka samu, 

Sai ka ɗaga hannu, 

Addu’a kai maku, 

Da ku da ‘yan ‘ya’yanku 

Ba wai da wasa ba. 

25.

Mugunta kar kai mata, 

Adalci kai mata, 

Ko faɗa za ka mata, 

Kada dai ka doke ta, 

Hakan fa sam bai yi ba. 

26.

Ni ne naku Haimana, 

Ɗan garin Kaduna, 

Nake ta yin bankwana, 

Cikin watan damina, 

Dubu biyu da bibbiyu. 

<< Tambaya 7Tambaya 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×