Skip to content
Part 30 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Sameer yabi bayan Baba Yusha U da kallo tamtar Wani sakarai ko Wanda yaga abin Mamaki.

Tamkar Wanda aka zuk’ewa Jinin jiki haka ya zama sai maimaita Kalmar Baba Yusha U yake ta an daurawa Farida Aure. So yake ya banbance daurin Auren da Wanda ya Sani da Wanda yake son sani a Yanzu.

Farida matar shi aka daurawa Aure? Da wa ? Mai gemu! Zuciyar shi ta sanar Dashi.

Ya Mike da sauri Yana Jin Bai YARDA ba ba dai Faridar sa ba Kuma ba dai Auren Mai gemu gare ta ba.

Idanun shi jajir ya shiga gidan ko sallama Bai iya Samun Yi ba Haj ce ta ganshi ya shigo a Rikice ta ajiye kayan Karin da ta Riko tana Fadin.

“Sameer Kaine tafe?

Ya zube a Gaban ta Yana Gaishe ta Yana Fadin

“Haj da gaske ne Abinda baba Yusha U yake fada min? Yace min an daura Auren Farida a yau.

“Gaskiya ne Sameer kaima Ina Maka fatan Alheri Allah ta ala ya baka mace ta gari ya Sanya Hakan shine Alherin ku. Kai da Farida ai Dole ku karbi kaddarar ku Kuma ku godewa ALLAH.

“Hajiya ba zan iya karbar wannan kaddarar ba wallahi yafi k’arfi na.

“Ai kuwa karbar ta ya zama Dole Sameer matukar dai kace amantu billahi Rabba. Mai Imani baya gazawa Sameer kuma Yana Godewa Allah a duk irin Halin da za ya samu kanshi . In kace ba zaka karbi wannan kaddarar ba ka Kasa imanin ka ne a faifai Sameer. Babu wata Rahama da Ubangiji Bai mallake ta ba in ka Rasa Farida Akwai wacce tafi ta Daga ALLAH don Haka kar ka sake cewa ba zaka karbi Hukuncin Allah ba. Ina so daga yau ka shafe Babin farida a Ranka a yanzu mallakin Wani ce kaima kayi kokari ka mallaki mace zaka rage damuwa Kuma ta debe Maka kewa.

Idanun shi tamkar Rushin wuta sai hadiyar zuciya yake kuka yake so yayi Amma ya kasa samun hawayen da zasu zubo.

Bai iya tankawa Haj ba har ta gama nasihar ta ya Mike ya shiga D’akin Farida wacce ta kife tana kuka saboda tun da taji Abinda baba Yusha U ya fada ta rushe da kuka.

Sameer ya shigo ya same ta tana kuka ya tsaya a kanta har dai ya Gane ba zata dago ba ya Duka Yana tado ta Suka Zubawa juna ido tamkar an Bada musu yaji a idon.

“Ya akayi haka Farida? Bakije gidan baba Yusha U bane ? Da wa aka Daura Auren ki? Kar ki ce min Mai gemun banzar Nan?

“Naje sai dai Babu Biyan bukata sai ma dukan banza da yayi min dubi jiki na har yanzu bai baje ba.

Yabi jikin nata da kallo Yana shafawa.

“Sai dai kayi Hak’uri Sameer Amma Babu yadda zamuyi sai dai tunda an daura da shi Dole ne na San yadda nayi na dawo Amma yanzu kayi hak’uri ka Daina bibiya ta don baba Yusha U ya Soma Gane Akwai Wani Abu a tsakanin mu tunda Yaya basiru ya ganka a jiya don ya fada mishi ya ganka Tare da Wanda kuka je don Haka ka saurare ni zan kira ka.

Kallon da yake Mata ne ya tsorata ta har tayi Shiru tana kallon shi a tsora ce.

“Akwai munafunci a cikin Al Amarin Nan dama na Gane kina son Auren mutumin Nan shiyasa kika yaudare ni da Cewa Baki san komai Akai ba. Sun Isa ne su Aura Miki shi idan Baki ce kina so ? Sai da na fada miki kar Kuma sauraren mutumin Nan don ni na San shi na San kowa ye shi saboda Kinga ya Fi ni kudi ne kika munafunce ni wata Kil ma har Rungume ki yayi ya lash.

Tayi saurin dakatar Dashi.

“Wai me ya sa ne Sameer duk Wani Abu Da zai fito ta ni abin zargi ne wurin ka? Yanzu Abinda zuciyar ka ta Raya Maka Akaina kenan Kuma ka yarda?

“Kar kice min komai don na gama yarda da ke don haka zan Baki sharadi Wallahi Dole wannan Auren ya kare a cikin sati Biyu ki fito Kuma kar ki sake ya kusance ki idan kika bari akayi Hakan ni da ke da shi Wallahi duk zamu mutu Kuma idan kika wuce sati Biyu Baki fito ba ni da kaina zan zo gidan nashi na fito da ke.

Hawaye kawai yake gudu a fuskar Farida. Ba Don komai ba sai yadda har yanzu da ta barranta da igiyar Auren Sameer Bata fita zargin shi ba ita kuwa me ya kaita yin wannan kuskure Daya tak Mai ban haushi? Da ta sani Kam tayi ta fiye da Shekarun iyayen ta in an hada su wuri Daya. Idan dai haka so yake sai tace so karya ne ba gaskiya ba . Da so gaskiya ne da Sameer Bai kasa Aminta da ita ba kamar yadda ta kyautatawa son shi tayi Abinda yake so son ta faranta mishi Ashe shi kallon da yake Mata ma na kowa ya kalle ta ko ta kalle shi sun Rufe kofa ne.

“Tashi kaje ka na sallame ka Sameer ka Rik’a kallo na kamar wacce ta mutu aka binne ta don na binne ka fiye da binnewar da akewa GAWA. Matukar dai har a yanzu ban barranta daga zargin ka ba to me zan dawo gareka nayi ? Ko na dawo gareka ma Yar gidan jiya zamu koma don Haka sharadin me kake bani? To ka sani zan fadawa miji na dukkan maganganun nan ya Rubuta su ya ajiye ko tari yayi Mai tsanani zan Nemo ka kuma Auren ka bana yin shi son ka ma na Daina in Kaine Rayuwa ta a yau zan mutu tunda son da nake Maka cutarwa ce gareni babu Aminci a tsakanin mu Babu yarda sai zargi da son ka kuntata mini da JANHURUN masifa to ko da ba a Daura Aure na da Abdullahi ba zan Nemo shi don na Gane shine daidai Ni Kai ba kala ta bane sai dai in naso Wahalar da kaina.

Ya zuba Mata ido cike da Tashin hankali Yana Rage murya Yana Fadin

“Farida ni kike fadawa haka saboda Kinga yadda na SHIGA tashin hankali.

“Kai nake fadawa Sameer ! Ba zan taba yarda ka shuga tashin hankali ba sai naga ka bar Duniyar !

Ta fada idon ta fal da masifa Shima ya San ya kaita karshe.

“Fita daga Nan gidan in Kuma Ya’yan ka ne damuwar ka suna makaranta biya ka dauki abinka kar ka Kuma Zuwa gidan Nan don har Abada munyi hannun Riga da Kai tarayya ta da Kai Bata da sauran amfani tunda har yanzu kana Nan a yadda kake to ko Kaine numfashi na na Hak’ura da Kai gara a kira ni marigayiya wata Kil na samu ADDU A daga gareka idan kaga tudun kabari na…

Ya kalle ta cike da Tashin hankali ya juya ya fice Bai ce mata komai ba tabi shi da Kallon Jin haushin yadda ya kasa fahimtar ta duk kokarin ta da kuma dukan wofin da Tasha wurin baba Yusha U Amma bawan Allah Nan zargin ta yake da munafunci har Yana fadar an Rungume ta.

Haj tana Zaune ya fice Bai ko yi Mata bankwana ba . Tayi Mamakin kalaman da taji Farida tana furta mishi na kar ya Kara zuwa gidan su in Kuma Ya’yan shi damuwar shi ya zo ya dauki abin sa. Duk da tayi Mata daidai Amma ba haka Kai tsaye ya kamata ta fada mishi ba.

Farida ta fito daga D’akin tana zuwa bakin famfo ta Tara Ruwa.

“Me yasa kikayi mishi wannan furucin Mai makon ki bi shi a Sannu ku Rabu lafiya? Cewar Haj wacce ta Yi maganar tana Duban Farida da ta Zauna.

“Haj mutumin Nan babu wani Alheri a tarayyar mu tunda maimakon ya gyara sai ma k’ara lalacewa da yayi. Wai Bai ma yarda da Abinda da na fada mishi ba zargi na yake akan bance bana son Abdullahi ba Wai har Kira na yake da munafunci idan acan ya zarge ni Ina da igiyar Auren shi yanzu Kuma fa da Babu igiyar Kuma yake zargi na? Nayi Aure na Shima yaje yayi nashi ko Ina so ko Bana so bashi da hurumin Komai a kaina bare ya tutsiyeni Yana fada min Abinda ya ga Dama.

“Shiyasa duk Mai Kaunar ki Farida zaiyi Miki murna da Auren Wani ba Sameer ba. Domin kuwa duk Nisan jifa k’as dai zata dawo Kinga kenan gara ki sabunta don ki Gane banbancin Mazan . Ni Kam Ina Mamakin yadda zuciyar yaron Nan take cike fal da zargi Wanda ya kasa Aminta da ke sai ya danganta ki da Neman maza ko Rashin Aminci. Sai kace Wanda ya kama ki da kwarto ko Kuma ya same ki ba a budurwa ba…

Hawaye ya kawowa Farida Bata share ba taji Ina ma zata iya sanar da Haj makasudin zargin Sameer akan ta? Ina zata iya fadawa haj itace da kanta ta bawa Sameer Damar ya zarge ta ya Kuma kasa Aminta da ita. Amma Kash idon ta da kunya ba zata iya fadawa haj Al Amarin da ya faro tun daga samartaka ba Wanda shine mabudin da ya Bude Mata kofar kowane Balaki da ta gamu da shi a gidan Auren Sameer har ya Zame mata garnakaki har yayi Dalilin Rabuwa . Amma duk yadda ta iya kawar da Kai daga laifin shi Dubi shi sakamakon da yake nufin Yi Mata.

Tayi Shiru Bata tsinka ba don ta San ba zata iya sanar da Haj kuskuren da tayi ba har ya bude Mata kofar zargi . Amma Kuma a yanzu sai ta Gane sau tari kuskuren kuruciya shi ne yake bibiyar mutum ya Kuma zame mishi damuwa kamar dai ita da ta Gane har da Kuruciya a cikin Abinda tayi ba kamar yanzu da tayi hankali ba ko Gani tayi wata mace zata kwata irin kuskure ta zata Hana ta Bakin Rai don taga irin Abinda kuskuren yake jawowa wanda har ka mutu ba zaka Daina hadiyar Bak’in ciki ba da na sani kuwa fiye da shurin masaki.

*****

Gyaran gidan da Basma taga Abdullahi ya tashi Yi da Rana tsaka shine ya tayar Mata da Hankali don taga kamar wahayi ya tashi Aikin gyaran a Ranar da aka fara Kuma a Ranar ne ya tafi Hado kayan Auren Farida

Duk yadda Basma taso taji Wani Abu daga Bakin shi Bai yarda ya tofa ya dai ce mata Yana son ya gyara su ne.

Hankalin Basma fa yayi masifar tashi don a Duk Duniya idan Akwai Abinda yake tada Mata hankali to zuciyar ta ta Raya Mata wata Rana Abdullahi zai iya karo Aure musamman ya samo macen da ta mallaki abubuwan da yake so wacce ba fara ba Kuma ba doguwa ba Mai cikar kirjin da yake so.

Ta Soma safa da marwa tana karyata Kanta akan Abinda zuciyar ta take Raya Mata Amma kuma bata gamsu ba irin taji daga Bakin Abdullahi.

Kwanan shi biyar da tafiya wanda ya yi daidai da Shekaru Dubu d’ari biyar a idon Basma inda ya dawo ya samu sashin yayi matukar kyau fiye da yadda ya tsara . A Ranar da ya dawo ne Kuma ya samu Kiran dauda Wanda yace baba Yusha U Yana Neman shi inda ya rage kwana uku a Daura Auren ya Kuma je Kiran baba Yusha U yaji ya maido Auren Gobe Da Asuba inda akayi gangamin daurin Auren tun a Daren don haka Bai samu zuwa ba Mai gemu sai dai a washe gari ne kayan da ya siyo suka iso tare da katuwar motar da zai bawa Amarya wacce a cikin ta za a Mika lefen da ya tsaro Mata.

Basma ma ya siyo mata kayan fadar Kishiya don haka ya danka mata akwati Biyu Mai cike da Kaya Lokacin da yake Shirin fita ya kaiwa su Goggo Amu wadan da zasu Kai kayan Matan kanin mahaifinsa wato Baba Isuhu.

Ta Dube shi a matukar Rikice tana fadin, “Wannan kayan fa?

Ya Dube ta Yana gyara gashin gemun shi da kum Yana Fadin

“Au ! Wai ban fada Miki kwanaki Farida tana Gaishe ki ba? “Wace haka? Ai in dai wannan ce wacce ko mutuwa ta ban tsana irin tsanar da nayi Mata ba ka taimake ni ka Daina Ambata min sunan ta don Wallahi Ina Jin sunan ta tamkar kana zagin Uwa ta da Uba na Kuma a na me zata gaishe ni.

“To ki yi Hakuri Basma na zaci na Sanar da ke Al Amarin da yake Shirin faruwa a tsakanin mu kin San Auren ta ya mutu.

“In Auren ta ya mutu kana Shirin Auren ta ne? To kar ka fara Abdullahi don zan iya zama da kowace mace Amma Banda wannan da tajawa Mai irin sunan ta ma bana kauna Wallahi.

“To Yaya za ayi yanzu kenan tunda gata Nan Zuwa ma a matsayin kanwar ki ? Wannan kayan da na Baki na fad’ar KISHIYA ne itama ga nata a mota yanzu zan kaiwa su Goggo Amu su Mika musu.

Wani irin tsalle da Basma ta Daka tana dafe kirji tana fadin.

“Da gaske kake mini ? Na SHIGA UKU na lalace Wallahi ban yarda ba ba kuma zan yarda ba gara ka dauko min Mata UKU a lokaci Daya zanfi gamsuwa Akasin kace min Farida zaka auro mini. Ai Tunda naji kana sambatun bacci da matar Nan hankali na kuma ya ke a tashe nayi ta mugayen mafarkai Ashe kuwa JANHURUN masifa kake shirin jawowa a gidan Nan don na Rantse Maka da Allah ba zan taba zama da wata Farida a gidan Nan ba gara ka sauwakewa kanka Balakin da kake Shirin jawowa don Wallahi yadda na tsani matar Nan har Ajalin ta zan iya.

“To amshi Nan Basma Wallahi tallahi kinji na Rantse Miki ? Wallahi akan Farida Babu Abinda ba zai faru ba a ciki kuwa har da tsinke igiyar Auren ki don ke kin San Rayuwa ta ma zan iya fansar da ita ga Farida don haka duk Abinda kika Shirya kar ki fasa ni Kuma zanga kokarin ki Amma in Sha Allah Nan da Gobe Farida tazo Gidan Nan Kinga na Baki satar Amsa.

Ya fice daga gidan inda ta leka taga ya fice a motar da ta shawa Alwashin sai ya Siya Mata irin ta.

Ta dawo tana share zufa inda Kuma ta jawo jakar ta ta fice daga gidan ta nufi gidan kawar ta lawisa wacce ta ganta wurjanjan.

“Ke Kuma fa? Lafiya?

Sai kawai Basma ta Rusa kuka tana kankame lawisa tana Fadin

“Na shiga uku na lalace lawisa Abdullahi ne yake fada min Auren shi da Farida.

“Wace Faridar? Lawisa ta tare ta.

“Tsinanniyar da ta kama mishi kurwa.

“Amma kuwa kin bani Mamaki Basma kina nufin Faridar ce ta tsorata ki haka har kike kuka? To Wallahi ba Zaki iya da ita ba tunda har kike Mata kuka ta gama firgita ki da kin ji a Ranki Bata Kai mace ba a wurin ki Wallahi da Babu Abinda zai tayar Miki da Hankali Amma yanzu tun Bata shigo ba tana Saka ki zubar hawaye Ina Kuma ga ta zo gidan ki ai Kila Kuma sai ta hautaka ki tunda a yanzu kike kuke kuka daga Jin zata shigo.

“Wai Baki ji Abinda nake fada Miki ba lawisa ? Nace Miki Faridar Nan wacce ta Rik’e mishi kurwa yanzu haka maganar da nake Miki yace an daura Auren su me kike so Nayi ? Tun tana Gidan Wani ma ban Zauna lafiya ba bare kuma ya Auro ta? Ni Kam ba zan iya ba Wallahi Dole sai Nayi Abinda nake Ganin shine nake Ganin mafita Amma Wallahi ba zan iya zama da yarinyar Nan ba a matsayin KISHIYA Dole ko ni ko ita ya zabi Daya ko Kuma.

“Ko a yi Yaya? Ke kinji matsalar ki hauka kike ba haka Ake yi ba kin tashi kina ta bare b’are kina kuka wai don Allah bakiji kunya ba ace yadda kike din Nan kina kukan za ayi Miki KISHIYA? Yanzu idan kika ga wata na kukan kishin Nan Anya ba Zaki ce mata wani Abu ba? Ni Wallahi Dariya kike bani wai kuka kike za a auro Miki Farida ni kamar Faridar ki biyar ko goma ai sunyi karya Wallahi su furgita ni bare su Saka ni kuka har da hawaye haka har da Shan Alwashi matsoraci fa baya zama gwani ko wanene kuma ko Dan waye.

“Lawisa Wallahi ba zan iya yin Abinda kike nufi ba saboda tuni yarinyar Nan ta gama firgita ni tun a waje bare kuma ace gata Nan Zuwa. Ban fada Miki kwanaki da sunan Farida yake Kira na ba? Tuni ya gama fallasa min yadda ya mutu a kan ta har na shuga fafutukar Neman yadda za ayi na koma irin ta Amma a banza a wofi lawisa kwanaki yake fada min tana Gaishe ni Ashe duk suna tare sai a yau fa yake fada min Auren ta ya mutu har ya shiga an daura Auren su bana ko shakka lawisa shine ya kaso mata Auren ta don ya kawo mini ita gashi Kuma Yana dab da Hakan Yaya Zanyi lawisa ke kin San yadda nake son Abdullahi ban shirya Raba shi da wata mace ba bare Farida wacce na San ba Raba shi zamuyi na kwace mini shi zatayi tunda ta mallaki Abinda yake so.

“Kinji kuskuren ki Basma da kike Bata tabbacci da hakika . Ni nafi son kike karyata ta ki dauka kema Zaki iya fin ta ta haka Zaki zama jajirtacciya Amma kina sarewa da ita ai har Abada babu ke Babu nasara akan ta Amma ki dauka kinci Uwar ta shaidanci Wallahi sai ta bar Miki mijin ki Amma irin wannan kuka kamar wacce ta Rasa iyaye ? Ai ko ni ke bayar da tabbaccin Nan Basma ba zan Baki shi ba saboda kin nuna kasawa ba Kuma Zaki iya ba. Zata Kuma fiki nesa ba kusa ba don na tabbata ita ba raguwar zuciya gareta irin Taki ba. Don haka Abinda nake so da ke ki zama jaruma ki ji a Ranki karya KISHIYA take ta furgita ki bare ki zubar mata da hawaye idan tazo da Abu Daya ki tanadi goma idan tana da Rashin kirki Daya ki tanadi balaki goma . Don haka yanzu ki bari kiga da me tazo kafin na Dora ki akan irin abinda tazo Miki da shi Alheri da mugunta duk wanda tazo dashi sai mun karyata ta don haka yanzu ba zamu yanke Mata Hukunci ba tunda bamu ga takon da ta shugo da shi ba sai tazo munga kamun ludayin ta ta haka zamu shirya Mata Amma yanzu ai ihu bayan hari kike Basma wata Kil ma fa ita bakwa gaban ta Amma ke sai Neman zarewa kike.

Basma ta sauke AJIYAR ZUCIYA tana fadin

“Ai yanzu dai kawai bari naga shigowar ta ta Lawisa Amma duk yadda Baki zato yarinyar ta gama firgita ni Saboda na San yadda ya gama mutuwa a kanta itace first love din sa.

<< Tana Kasa Tana Dabo 29Tana Kasa Tana Dabo 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.