Skip to content
Part 31 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Lokacin da Sameer ya fita Daga Gidan su Farida idon shi a Rufe ya fita Saboda kid’ima don ko a mafarki Bai tab’a zaton Jin wadan Nan kalaman daga Bakin Farida ba sai gashi a yau Farida ce ke Fadin ta Hak’ura da shi idan shine Rayuwar ta ta zabi ta zama GAWA wata Kil idan yaga tudun kabarin ta zai Raka ta da ADDU A Akasin tana Raye.

Bai lura ba idon shi a Rufe sai ji yayi ya afka kwatamin Dake dab da motar shi wacce Mustafa yake ciki Yana Jiran fitowar shi.

Da sauri Mustafa ya fito daga motar ganin Sameer tsullum a kwatami kuma abin Mamaki ya kasa fitowa kwatar sai ma dafe gurbin zuciyar sa da yayi da Hannu Biyu da yayi.

Ya Isa gareshi ya kamo shi Suka fito yaga Sameer din Yana Neman bajewa k’asa.

Ya Rik’e shi Yana Fadin, “Oga Yaya ne?

Sameer Yana dafe da zuciyar shi yace wa Mustafa.

“Kira mini Bello Mustafa bani da lafiya.

Mustafa ya bude motar ya Fara fito da Ruwa a galan Yana wanke mishi kafar da take fal da kwatami har da kakin shi ya samu kwatamin musamman kafafun wandon shi.

Ya wanke mishi kwatar kafin ya dauko wayar shi da take cikin motar Yana Neman layin Bello.

Bello ya amsa kiran Mustafa Kuma ya mikawa Sameer wayar ya karba Yana Fadin.

“Bello kana gida? Don Allah kazo ka kaini Asibiti bani da lafiya.

Suka gama wayar ya shiga motar Yana cewa Mustafa ya mayar dashi gida.

Mustafa yaja motar zuwa gidan Sameer din inda Sameer yake kwance a bayan motar Yana mayar da numfashin Wahala Yana dafe da gurbin zuciyar sa da yake Jin tamkar za a tsinke mishi zuciyar.

Bello ya iso ya kama shi zuwa motar shi Suka nufi Asibiti.

An karbe shi da Bashi da taimakon gaggawa musamman kakin da aka Gani jikin shi da Kuma girman matsayin da kakin nashi yake dauke da shi.

Bello ya Kira Haj ya Sanar da ita Sameer fa Babu lafiya gasu a Asibiti. Hankalin ta ya tashi Amma tayi Mamakin zuwan nashi don ba Lokacin zuwan bane . Sai Kuma taga to ko Ciwon ne ya maido shi?

Tayi Shirin Zuwa Asibitin don ganin Halin da yake ciki.

Yana kwance akan Gadon hannun shi da ledar Ruwan drift idon shi na fidda kwallar kishi musamman da ya Gane Farida gidan wani Namijin zata kwana Kuma Kuma Komai ma zai iya faruwa tunda tayi fushi akan Abinda ya fada Mata.

Haj ta iso hankali a tashe tana ganin Halin da yake ciki ta tausaya mishi matuka Gaya.

Tana tsaye a kanshi tana mishi ADDU AR Allahu yashfeeka Sameer ya baka lafiya.

Ya Dubi Haj Yana Fadin, “Haj kinji an Daura Auren Farida kuwa?

“To ya za a Sameer? Kaddara fa ta Riga fata. Kaima in Sha Allah ka kusa naka Auren ba shikenan ba?

“Haj ba Zanyi tsawon Rain da zanyi Wani Aure ba . Tunda Farida ta bar Rayuwa ta ba zan Rayu ba Dole na bar Duniya. Ta fada min ta Daina Sona ba Kuma zata taba Dawowa gareni na ba Haj meye amfanin Rayuwa ta?

“Kaifa kaji matsalar ka Rashin taihidi Sameer. Faridar Nan ba tare kuka zo Duniya ba . Haduwa kikayi Kuma kuka Rabu. To ita kanta Duniya Da kake Gani mahad’a ce Kuma maraba. Don haka ka sakawa zuciyar ka Aminci ta yuwu Hakan shine Alherin ku akan ace Kuna tare tunda Kai dai ba sauyawa zakayi ba.

Yayi shiru Yana sauraren Haj da nasihar ta wacce baiji zai iya dauka ba ko Farida na so ko Bata so Dole ta Dawo gareshi. Babu Abinda ke dafa zuciyar sa a yanzu irin ya tuna ga Wani Namijin Farida zata Wanda bashi da tabbaccin ba zai taba ta ba. 

Mai gemu ya kaiwa su Goggo Amu kayan lefen Nan yace a kaisu yanzu ya Kuma taho da Wanda zaija su a motar ya kaisu gidan su Farida ya ce har motar a bawa Farida Duka.

Hajiyar Farida ta Kira Mai lalle da gyaran jiki Saboda ta kula Babu abinda Farida take da niyar yi na game da lalle da gyaran jikin. Don haka Kan kacee me? Gidan ya dinke da yan Uwan Haj da wasu daga dangin Uban su da Matan baba Yusha U sai Kuma ga Anty lubna itama ta iso tare da Yaya Dauda.

Gida cike da yan Uwa da Abokan Arziki sai kuma ga su Goggo Amu dauke da Kaya na garari na lefe

Aka tarbe su da mutunci aka karrama su da Ruwan Sanyi da kunun Aya Mai sanyi tare da Naman kajin da Gali ya kawo ayi Hidima amadu ma ya Siya musu lemun Roba katan katan don haka aka tarbi su Goggo Amu da kayan Arziki

Aka shiga duba Kayan da suka kawo karshe ma sai ga key din mota wai duka kyautar Ango ce zuwa ga Amarya.

Kowa sai Sam barka yake da kayan lefen Nan don ko Auren budurcin Farida Bata samu kamar su ba bare Kuma motar kece Raini da aka Hado ta da ita.

Tukwici Mai kyau Haj ta bawa su Goggo Amu tare da katan katan na lemu suka Yi musu sallama suka wuce.

Anty lubna ta Dubi Farida tana Fadin, “Don Allah ke da kanki Baki ji cewar yanzu ne kikayi Aure ba? Kin kuwa ga motar ? Ke kayan da ya zuba Miki ma ko a Auren budurcin ki baki same su ba . Kuma ni kaina nafi Yi Miki Sha awar Abdullahi ko babu komai so Daya yake Miki tunda ya so ki a budurwa kika Kuma dawo zawarci ya Kuma Dawo kin San Nan dai Kam kinyi balue.

Haka aka yi ta Hidima inda aka yiwa Farida lalle aka Kuma Yi mata dilka da halawa tuni kuwa ta fito Amaryar ta saka.

Karfe Hudu na yamma Baba Yusha U ya sallama gidan inda duk akayi ta Gaishe shi ya Kira Haj Yana Fadin.

“Maza ki fito min da yarinyar Nan na Mika ta gidan mijin ta da kaina ga Nan ya turo mota bana gayyar kowa mutum Biyu ko uku sun Isa daga wurin ki Mai son Zuwa sai yaje daga Baya.

Saddam da Hanan Kam suna wurin Haj ba a yarda Suka ga tafiyar Farida ba inda Haj tayi Mata nasiha da jaddada mata kalmar hak’uri da biyayya itace jigon Aure ko wane iri ne kuwa.

Da haka baba Yusha U da wasu daga dangin Haj suka tafi Mika Farida.

Basma tana tsaye bakin kofar ta tana Hangen yadda garadan ke ta wage baki suna karatun Al Kur ani Wanda Suka kwana suna Yi sun sauke Al Kur ani kafin suka maye da musaffa duk Mai gemu ne ya ce ayi Hakan don baya son wata bidi a.

Tana tsaye ZUCIYA na Mata dukan Tara Tara sai Kuma taga motar Abdullahi wacce ya bayar dom dauko Amarya ta shigo gidan Mai gadin Yana Bude musu kofa suka shigo inda yake nuna musu kofar sashin da aka gyara abinda yazo a Ranta shine yacewa sabon in sun zo ya nuna musu sashin.

Aka fito Baba Yusha U Yana Rik’e da Hannun Farida wacce yake cewa ta karanto wasu ADDU OIN da yake biyawa tana maimaitawa suka wuce ciki Matan da suke tare Kuma Suka Rufa musu baya.

A cikin kayataccen gidan Suka samu su Goggo Amu suna musu maraba tare da taryen Amarya da kayan Hidima irin na girma.

Baba Yusha U ne ya bawa su Goggo Amu Amanar Farida yace su bawa Abdullahi. Suka karba suna fadin in Sha Allah zasu isar

Baba Yusha U ya nemi ganin matar Abdullahi wadda Goggo Amu ta fita ta Kira ta Suka dawo tare baba Yusha yayi musu nasiha Sosai tare da Cewa su Zauna lafiya ta yadda hankalin Wanda ya Tara su zai kwanta

Basma dai ido ne nata don gaskiya a Rude take matuka Gaya Bata fahimtar duka manufofin Baba Yusha U ta dai amsa ne har ya sallame su inda take Ganin an so ci Mata fuska ne da aka Kira ta sashin Farida maimakon a Kai Mata ita can a matsayin ta na Babba.

Inno ce kafin su ta Fi ta ce da baba Yusha U ya bari a Kai Farida ga Uwar gidan ta don haka Al adar take tunda ma kowa wurin sa da ban Kuma Dole ne a Bata girman ta.

Haka aka Kai Farida sashin Basma Nan ma dai nasiha ce da bawa Basma girman ta aka juyo da Farida.

Da haka dai sukayiwa Farida sallama suka wuce Suka barta dafe da kumatu. Kewar Saddam da Hanan take ji tamkar sun Rabu kenan. Taja waya tana Kiran Haj ta dauka tana Fadin

“Yaya aka yi?

“Haj Saddam Yana Nan kusa Dake?

“Wani Abu ne? “Kewar sa nake ji Haj ni kadai a gidan shine nake son Naji muryar shi shi da Hanan.

“To yanzu dai baya kusa kakar su tazo Yi Miki Allah ya Sanya Alheri tace Uban su Yana Gadon Asibiti Babu lafiya shine ta tafi dasu ni Kuma na san sun karbe kayan su ne Hikima dai tayi don Kar tace tunda kowa ya kama tsagin sa sun karbi kayan su ni Kuma naga duk yadda Sukayi ai ikon su ne.

Wani Abu ya daki ZUCIYAR Farida . Sameer Yana gadon Asibiti itace Kalmar da tafi komai tayar Mata da Hankali Akasin wacce Haj ke zaton zata tada mata Hankali ta karbar su Saddam da Hanan wacce ta tabbatar da Duk Nisan da sukayi Dole ne su neme ta .Amma meye Dalilin Zuwan Sameer Asibiti? Bata ko shakka Dalilin ba zai Wuce ita da kanta ba ko Auren ta ko maganganun da ta fada mishi.

Ta kashe wayar tana cike da alhini.

Ta Mike tana Duba kayan da su Goggo Amu suka Tara Mata Wanda Suka iske ta da shi tana kuryar daki su Goggo Amu suna falo.

Bata iya cin komai ba sai lemun Roba Tasha tana zaune inda take jiyo firar su Goggo Amu jifa jifa duk da kallon da aka kunna musu Wanda Suka mayar da Hankalin su akan shi.

Ana dab da sallar magaruba Abdullahi ya shigo su Goggo Amu suka Rattaba mishi Abinda akayi da Amanar da aka Basu duka suka danka mishi kafin Sukayi nufin wuce Farida ta fito sukayi sallama itama sai da ta bisu da kwalbar turare Mai kamshi sukayi Godiya suna Kara Bata hak’uri da kawar da Kai . Zasu fita ne yace su bari ya mayar da su gida .

Ya aje musu jakar da ya Sako musu Abinda zai Basu kafin ya hada musu da kudi ya Kuma dauke su ya mayar gida suna ta mishi fatan Alheri da Samun zama lafiya.

Ya taho a hanya ya tsaya mansho suya yayi oder kaji da kayan fruit ya taho gida.

Basma Kam sai safa da marwa take ta kasa zaune ta kasa tsaye musamman da tayi ido Biyu Da Faridar Da sunan ta kawai take ji har tayi Mata tsanar da ko mutuwa Albarka sai gata yau ta Gani ganin idon ta Kuma Ashe duk yadda take zana Faridar a zuciyar ta ta wuce tunanin ta don sai ta Gane ta rage ta Sosai akan yadda ta zana ta . Faridar zahiri Rayayyace akan wacce ta zana da ta Zana ta a nakasasshiya don Haka sai Rudewar ta ta linka don ta San ba Zata iya kishi da wannan Faridar ba Wallahi.

Sai Uwar Zufa take sharewa saboda firgici.

Ya shigo sashin nata Hannun shi cike fal da ladodi Wanda Suke nuna Mata na siyen bakin Amarya ne.

Ta Yi saurin Duban shi kafin ta Mike tana Fadin, “Dama an shirya wulakanta ni ne da wani fak’irin Uban matar ka zai Wani Saka Goggo Amu ta Kira ni yayi Mana wata shegiyar nasihs? To kar ka sake ka hada ni da matar ka ta tsaya wurin ta na tsaya wuri na bana son Abinda zai hada ni da ita Wallahi bana Kaunar yarinyar can bana kamar Ina Kaunar ta.

“Ni ai Ina Kaunar ta Basma Kuma bana Neman mataimaki a son nata kice yau kinga Farida ta ?

Ya dauki Leda UKU daga cikin Wanda ya shigo dasu ya Mika Mata Yana Fadin

“Ke da su Najwa da Nabeela. Wannan Kuma na Farida ne Ina fatan Babu wata matsala?

Tayi Maza ta Mike tana Fadin, “Yo me kenan? Daga Zuwan ta zaka fara Rashin Adalci? To Wallahi ba zan yarda ka matsa ko Ina ba sai kayi min kwanaki na Biyu kafin kaje gare ta tunda ai yaushe Rabon da kayi min kwana na? Tun da ka Soma zancen auren Nan Shekaran jiya ma ai ce min kayi kanka na Ciwo shine zaka kwashi kwana na ka kaiwa wata? Wallahi ban yarda ba ko zaka je ga Amarya sai kayi min kwanaki na Biyu ciff Babu coge Babu dosane in yaso kaje gareta.

Tayi Maza ta Isa ga kofa ta mayar ta Rufe tana murza key ta datse Kafin ta zare key din ta dawo kan kujera ta Zauna.

Ya Dube ta da mamaki Amma sai yayi murmushi Yana Fadin, “Basma kar ki fusata ni har Nayi Abinda zai baki haushi ko mamaki . Idan fa kika ce kin Gaji da zama da ni a yanzu Babu ko ja zan sallame ki . Haka Kuma ki Rik’e a Ranki Farida fa tazo kenan Bata zo don ta fita ba ko Wani haukan ki ya rage komai Babu Abinda Hakan zai jawo miki sai matsala don haka Bude min kofa na fice ai kin San tunda Bakiyi kokarin Hana Farida shigowa gida na ba Babu Abinda zai Hana mu kwana a kan gado tare da ita na san dai Abinda kikewa kenan?

“Ta yau dai Kam Wallahi ba Zaku kwana a tare ba sai na Bata muku wannan Daren Abdullahi Kai Zakayi kwanan falo ita kuma sai dai ta Rungumi filo Amma wannan Daren Kam akan idon ku zai Kare Kai kana katsina ita tana Daura ni Naci girma ma na yafe.

Ta Mike da sauri ta shige Uwar d’aki ta maido kofar tana murza makulli ya zama ta Rufe kofofin na fita waje da Wanda zai Kai ka dakin ta ta barshi a tsakiyar falo Babu shiga Babu fita kena ya bita da kallo yaji ta mirza key.

<< Tana Kasa Tana Dabo 30Tana Kasa Tana Dabo 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.