Skip to content
Part 34 of 39 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

A Ranar da Wasila ta bar garin katsina bayan mutuwar Auren ta Kai tsaye ta yanki tikitin jirgi ta wuce birnin tarayya Abuja inda ta sauka a Gidan Shama wacce take a garki. Hakika unguwar tana da tsari haka ma Gidan Shama Babu laifi Yana da kyau sai dai da yake Al Amarin na garin Abuja iya kudin ka iya shagalin ka ne don Abuja Kam ba ta talaka ba ce sai dai yazo ziyara ya koma Amma mazauni Kam in Yana son shi ya tafi arewa itace tasa. Nan kam sai masu kumbar Susa.

Gidan shi ma kam matattara ce ta Yan Duniya inda wasu kan zo su dauki Matan da sukayi mahad’a da su a Nan ko Kuma Wanda shamar ta Kira yazo ya duba irin test din sa a tsadance tunda Aikin Shama kenan kawalci ko Kuma in ka Gano macen da tayi Maka ka Bata kwangilar samo maka ita in Sha Allah kuwa da yake Shama shaidaniya ce ko macen Aure ce sai shama ta samo kanta.

Shama ta Rungume wasila tana fadin, “Kai oyoyo sweetyn honorable Wallahi duk ya Dame ni da maganar ki har nace zan hada shi da wata Amma yace baya so ke yake so ni kuwa meye Sirrin.

“Ke Bama wannan ba Yaya kuka kare da Dan anacen mijin ki? Sai fa kinyi da gaske matukar kina son shakatawa da Rayuwar ki a Hak’ura da Auren Nan Mana tunda ba na zobe bane in Kuma Kuna son juna ya Dan saki kafin ki buga Ron’s din ki in kin shakata sai ku koma tunda kinko yayi Muku Halin nasa.

“Haba Shama ai anyi har an gama takardar na can na Saka a Kaya zuwa gida ban taho ba sai da na kwashe komai na aikawa Goggo kafin na yanki tikitin jirgi nayo nan.

“To tsaya Wasila Goggo ta San Zaki taho? Bana son yin Abinda Babu sanin iyaye don Wallahi faduwa ce karshen Mai Rufewa iyaye don sune koman mu a Rayuwa. Da kin dauko sa a daga gida to Zaki zama gagara gasa Idan kuwa Baki dauko sa a ba to Akwai matsala . Kin Gan ni Nan wasila? Wallahi ban yarda na Fara komai na ba sai da na nemi Albarkar mahaifiya ta wacce a Saudi ma na zarce sai da aka kamo ni ne na yada zango a garin Abuja Kuma ban yarda na hada harkoki na da Aure ba shiyasa ma banyi shi ba bare na keta haddin Ubangiji. Kema shiyasa nace kiyi kokarin Rabuwa da mijin ki don har ki hada taura Biyu . Ina tsoron SHIGA haddin Ubangiji ne don Ina tsoron Allah matuka Gaya. Haka Kuma Ina tsoron hakkin iyaye musamman ma Uwa ta shiyasa komai nake kiyayewa shiyasa ma kikaji nayi Miki shimfida don har ga Allah bana son kuskuren kuruciya in ana Dara fidda Uwa Ake haka Allah ba Abokin wasan mu bane iyaye bamu da kamat su mu duba dai daukar ciki da nakuda. Haihuwa da Kuma Raino Anya kuwa Uwa taci Wani Abu daga danta bayan biyayya? To me muke musu ma Wanda ya nuna mun Yi musu Wani Abu kwatankwacin dawainiyar da Sukayi Mana?…

Jikin wasila yayi sanyi kwarai da gaske don ta San hakikatan maganganun Shama Babu karya Kuma duka a ciki Babu Wanda ta kiyaye ita Kam Ashe kuwa ta jawowa kanta JANHURUN masifa tunda Bata wanye da miji lafiya ba sai da taci Amanar sa a inda Ubangiji ya fallasa ta ya kama ta kuru da kuru. Haka Kuma Bata wanye da Goggo lafiya ba tunda kukan da ta Gani a idon ba zata iya lissfa shi ba. To bare Kuma mutuncin Aure da ta keta Shima sai da Ubangiji ya nunawa danta Abinda take lullube wa. To ita Kam ta Ina ta dauko wata sa a?

Ta kasa motsin kirki don da gaske taji maganar Nan Amma da yake shaidan yayi Mata fitsari a ZUCIYA tun a Ranar Shama ta Kira honorable ta sanar Dashi zuwan wasila. Ba a Rufe awa Biyu ba sai go katuwar motar lumoxin ta iso a kofar gida Shama a garki sakon honorable ne turo a daukar mishi wasila.

Tuni kuwa dama ta shiga Shirin Zuwa amsa Kiran honorable Dan majalisar wakilai Wanda ya gama mutuwa a kan wasila duk ba wani kyakkyawa bane Kato ne na gaske Kuma Bak’i wuluk sai dai akwai kudi a tare da shi don haka macen bariki Bata bukatar Namiji mai kyau a yayin mu Amala Mai kudi dai shine Abokin mu Amala don haka kudi suka fiddo wasila shi Kuma Yana da su.

Tayi Shiri Sosai da kayan Mata irin na Yar Sokoto sai ta Samu wata Anty suby Dake Nan Abuja itama nata kayan masu kyau ne sai anty suby ta kwacewa Yar Sokoto wasila.

Gidan honorable Kam ya bawa wasila mamaki Domin kuwa katon gida ne Mai dauke kayan alatun Duniya Kuma Babu kowa a ciki sai shi Daya don iyalan shi Suna birnin kebbi shine dai yake a Abuja Yana morewa Rayuwar sa.

Don haka a Nan aka Bude wata bariki tsakanin shi da wasila. Tsawon wata Daya da kwana Biyar suke tare a gidan honorable tamkar dai ace iyalin sa ce . Amma bariki ce kawai iyalan nashi suna Can birnin kebbi sai fa yanzu ne zai je gare su kusan tsayin kwana Arba in.

Ya sallami wasila da manyan kudade ya ce idan ya dawo zai Kira ta .

Ta hada Kayan ta a Jakarta Direban shi da zai sauke shi a filin jirgin ya dauke ta idan ya Kai shi Filin jirgin ya kaita garki kafin ya koma da motar Gida.

A filin jirgin aka sauke shi inda anan Wani Abokin honorable don senator Yan doma ya ga wasila a motar honorable ya kuwa zuba Mata idanu Yana fad’in.

“Kai mutumi na Ina ka SAMO wannan furen Mai kama da ZINARE?

“Kai da Babu Ruwan ka da harkar Mata Yan doma meye naka na bin bi ni?

“Ai Kuwa dai wannan ta burge ni ko zaka bari na Ganta mu Gaisa?

“Ba kuwa zan bari ka ganta ba maye ai ni tsoro kake bani Yan Doma Wallahi.

Wasila tayi murmushi tana Fadin, “Haba dai Daga gaisuwa Kuma sai kace zai tafi Dani?

Senator Yan doma ya daga Mata gira Yana Fadin

“Wonder full my flowers. Nagode kaga da yake ni din popular ne.

Da sauri honorable ya tayar da gilashin motar ya Rufe Yana Fadin.

“Kai lurwanu muje ka garki mu Kai dear mu dawo wannan Shegen na San Halin Kaya na maye ne na Sosai.

Lurwanu yaja mota suka fita daga filin jirgin har suka Isa garki suka sauke wasila a gidan Shama kafin lurwanu ya koma filin jirgin ya sauke honorable Wanda ya hau jirgi zuwa birnin kebbi wurin iyalan sa.

Haka wasila ta kasance a garin Abuja. Tunda ta shigo Abuja Bata kuma tunawa da wani shirgi wai shi ISHAQ ba. Amma kuma sagir Yana yawan fado Mata a Rai bare Yusra da Zee Zee. Haka ma tana tunawa da Goggo da Anty murja Amma duk tana ganin Akwai Lokacin da zata mene su .

Senator Yan doma fa ya Rikice da Ganin wasila Amma ya Rasa ta yadda za ayi ya same ta tunda Gona yayi mishi kafar ungulu ya Hana shi Ganin ta.

ISHAQ Yana Zaune a gaban Inna suwaiba tana Fadin

“ISHAQ hak’uri kawai zakayi ita dama mace haka take Amma Wata don ba Duka ba Akwai mace Mai halacci akwai mace Mai Rufawa Miji Asiri ta Kuma Yi Hak’uri da Duk babun sa Amma kadan Daga cikin su sune Wanda Basu da halacci da Rashi ya samu Namiji sai kaga suna Neman mafita . Wasila tayi min bazata ishaq iyayen ta Kam sai Sam barka Amma albasa batayi halin Ruwa ba in Sha Allah sai wasila taga yadda Allah zai maida Kai . Hak’uri Kuma shine Arzikin DUNIYA da LAHIRA don haka ka kawo mini su Yusra da Zainab Nan wuri na zaman su ai kamar Babu dacewa Dole sai da Mai nuni tunda Mata ne Kai ko Maza ne yaro sai da Mai nuna mishi in dai ba sangar ta Ake nufin Yi ba Amma kaga sagir da yake Yana da abinyi shi Babu damuwa a Zaman sa ko shi kadai ne a Gidan.

“Babu komai Inna Dukkan Abinda Allah ya Rubutawa bawa Abun Godiya ne wasila Kuwa Wallahi inna ko sunan ta bana son ji . Ya fada idon shi jajir Alamar ya tuna Abinda ya Gani da Wanda ya Dawo Mishi.

A Haka yayiwa Inna suwaiba sallama ya wuce.

Tun daga Ranar Kuma zaman Yusra da Zainab ya koma wurin inna suwaiba wacce take kamawa kuruciyar su ta nuna musu daidai da Rashin ta inda kuma take koyawa Yusra Aikin gida har zuwa girki. Kan kace me ? Rayuwar su yusra ta Dawo irin ta Masu yanci Akasin da can da suke walagigi Uwa na kan hanya su Kuma suna cikin garari.

Tun da ISHAQ ya yiwa Mai Naira dinki sai ya zamo Dukkan dunkunan da za ayi Mishi zai kawowa ISHAQ kuma yayi mishi cikin Lokaci Kuma Babu Saba alkawari shi Kuma yayi mishi Alheri Mai yawa fiye da adadin kudin Aikin sa Kuma yayi ta turo mishi mutane Wanda Duk yayiwa Dunkin sai ya samu Alheri Mai yawa fiye da zaton shi. Don haka yake matukar girmama Mai Naira har Wani Lokaci yayi mishi Dunki ya ki karbar kud’in Dunkin shi yace ba zai karba ba Amma ya Sha mamakin kyautar da Mai Naira yayi Mishi .

Wani Al Amari daga Ubangiji ga ISHAQ shine tamkar Wanda Ake Jiran ya Rabu da wasila sai ga Al Amarin yayi wata irin sauyawa ta ban Mamaki Domin kuwa a yanzu kud’i suna shigowa har mamakin yadda ya same su yake . Wasu daga cikin Mutanen da Basu Hak’ura da camfi a Rayuwar su ba Sukayi ta Yaya ta Cewa Anya wasila ba farar kafa gareta ba? Gashi daga Rabuwa da ita har ISHAQ ya siyi mashin na Zamani kuma ga gidan shi Yana ta gyaran shi Kai shi Kam gobarar titi a jos..

Shi Kam Bai iya duban komai ba sai Allah Mai yawan Rahama ne ya nufe shi da samun ta wata kil Hikimar Ubangiji don wasila ta Gane ita Rahamar Allah Bata nesa Bata kusa ta tafi Rahamar ta sauka.

Kan kace me? ISHAQ ya Soma samun kud’i Wanda ya Soma siyar da huluna na maza irin k’ube zanna bukar da Kuma Dara irin ta manyan mutane. nan ma Allah ya Sakawa kasuwar Albarka mutanen da suke kawo mishi dunkunan suna Ganin hulunan suna Kuma Siya sai ga shagon ISHAQ ya Soma bunkasa da huluna kala kala ya kebe inda yake Dunkin shi sauran wurin kuwa yayi mishi gyara Mai kyau da kawata wurin da gyara irin na Zamani Wanda yake daukar hankali.

Tuni kuwa Allah ya lud’ufa matuka ana kasuwar huluna ga Kuma Dunki a gefe ta ko Ina Alheri Mai yawa Yana shigowa tuni kuwa ISHAQ ya Soma sauyawa hatta da fatar jikin shi ta Soma sauyawa duk da Yana da matsala musamman akan abinci Wanda Inna suwaiba ke ta fama dashi Banda Ma Yana daga kafa baya son Zuwa duk da Dama can shine Mai hidima da inna suwaiba ba wacce in taga Bai zo yaci Abincin ba zata Kira shi tace me yasa Bai zo yaci Abincin ba? Kunya kan Hana shi zuwa sai dai yace Mata yasha fura wacce itace yake Sha tun tana burge shi har ta fita a Ranshi yafi son abinci Mai nauyi wanda baya ganin jagwalgwalon yusra da takeyi haka yake ci Amma yanzu idon shi da kunya ace kullum kafar shi tana hanyar Zuwa gidan Inna suwaiba cin Abinci.

Don haka yake ta hak’uri da cin Abinda ya samu in Kuma yaji Yana son Abincin zai je Gidan Inna yaci .

To wannan ne ya Fara darsa mishi tunanin shi ya fara hango mishi Aure Amma Kuma Yana tsoron Matan don wasila ta Saka mishi tsoron Matan kar ya zamo an gudu ne ba a tsira ba tunda yanzu Matan sun zamo Abin tsoro da shakka.

Tuni kasuwar huluna ta karbu har aka jaraba turaruka Suma aka SHIGA Al Amarin da SA A shima ana samun Alheri har dai aka hada da takama na Maza masu kyau da tsari tuni Kuma ishaq ya fito Allah ya daga Al Amarin inda Kuma sagir ya zama kwararren Mai gyaran mota Wanda aka ya sakawa Hikima da baiwa ta iya gyaran mota ko wace irin matsala ce da ita da ya duba ta kuwa zai tayar da ita da ikon Ubangiji

Shima ya Soma samun kud’i Wanda yake kashe su akan su yusra da Zainab tare da inna suwaiba duk da ishaq Yana yawan fada mishi yayi tattali ya samu ya samu kudin da za a siya mishi floti Amma sai hawaye ya kwacewa sagir ya Cewa ishaq.

“Abba ai ni bani da Wani buri a yanzu sai na ganin Yusra da Zainab Basu nemi wani Abu sun Rasa ba tunda na Gane Mama ma ta Yi Abinda tayi ne don taga Babu a tare da Kai. Bak’in ciki na Abba mama fa har yanzu Babu Wanda ya San inda take don Goggo tace Rabon ta da ita tun Ranar da Al Amarin Nan ya faru Abba Ina cike da Bak’in ciki tunda na Gane hanyar da mama take bi.

Kuka ya kwacewa sagir inda ishaq ya Rungume shi Yana Fadin, “Kayi Hak’uri sagir kayi Mata ADDU A Allah zai yaye Maka Bak’in cikin ka Nima zanyi Maka ADDU A Allah ya maye Maka da FARIN CIKI a Rayuwar ka ya fidda Maka damuwar ka kaji ?

Sagir ya share hawayen shi Yana fad’in, “Abba kayi Aure don Allah don ni Kai nake tausaya wa ko don a Rik’a dafa Maka Abinda kake so tunda yanzu allah ya Rufa Maka Asiri kafi karfin Komai.

“To Sagir ni Matan ne suke bani tsoro shiyasa ban Kuma tuna zanyi Aure ba Kuma ni Yanzu ai ban san matar da zan nema ba Saboda tsoro suke bani.

“Abba ni kuwa da zaka yarda da nace ga Anty maimuna Nan kanwar mama tana da kirki Kuma ba zatayi Maka Abinda mama tayi ba don ba Halin su Daya ba idan Ranka ya amsa zanje nayiwa Goggo Magana.

Da sauri ishaq ya Dubi sagir Yana Fadin, “Sagir maimuna tayi Maka ? In har kaji tayi Maka zan samu Goggo Amma ni da ka barni da kauye zan tafi Can cikin dangi na na Nemo wacce Ra ayin mu zai zo Daya Amma wannan tunanin naka ma yayi don haka idan kaji Ranka ya Aminta da maimuna Nima yayi min sagir don ba zan taba Auren wata mace ba sai wacce tayi Maka tunda ni da Kai ne jigon Ahali na Kaine Uban su ma a Gobe don haka sagir idan maimuna tayi Maka na yarda na Amince sai ka shige min gaba ka nema min Auren ta don kaine waliyyi na.

<< Tana Kasa Tana Dabo 33Tana Kasa Tana Dabo 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.