Skip to content
Part 8 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

“Kayi min Afuwa Sir na tuba don Allah Kar ka Raba ni da Farida Wallahi na YARDA kayi min komai Kuma Abinda ya faru kuskure ne ban so haka ba don Allah don ANNABI Yaya kar ka ce haka na yarda idan Wani Abu ya Kuma faruwa kayi min komai ma.

“Kar ka kuma ba ni Hak’uri don na gama magana akan ku don na matsu ace kurunkus kan Dan Bera matukar dai ba Hak’ura kayi da zargi ba a Rayuwar ka to Babu Ranar da zaku zauna lafiya Kai da Farida . To kafin kuzo inda ba zan so zuwa ba gara na Raba ku tunda zuciyar ka tafi k’arfin ka har kana tafka Mata Saki Daya bayan Daya kayi sau biyu saura igiya Daya tak ta Rage muku wannan Dukan ma da kayi Mata da Al Amarin yafi haka tsayi da ka cike Mata Dayan to kafin Azo wannan wurin zan Raba ku don na tabbata har ga Allah wannan sauran igiyar ma gata can ka yanke ta tunda ka bari zuciyar ka tafi k’arfin ka . Don haka tashi ka tafi da Ya’yan ka Ina jiran takardar sakin Auren Farida ko Kuma amsa Kiran kotu Wanda duk ka Zaba na shirya.

Hawaye ne kawai suke sunturi akan dakalin fuskar Farida dama ta San haka yake nufi da kawo ta Gidan shi ya ajiye tunda taji Yana fadin a bawa Sameer Ya’yan sa ta San dama Nan wurin yake so a zo.

Tana zaune a wurin ta juyar da kanta tana zurarar hawaye Bata ko tanka ba.

Anty lubna tayi ta Maza inji mata ta tofa da Fadin.

“Daddy don Allah kayi hak’uri tunda ya baka Hak’uri ya Kuma ce kuskure ne Ina Ganin ko don yaran Nan kar ku Saka su a garari kayi hak’uri.

Ya dagawa Anty lubna hannu Yana Fadin “Yara ? Sau nawa iyaye ke mutuwa Kuma Ya’yan su su Rayu? Yana tuna Ya’yan nasu ne idan Yana wulakancin sa? Zargi a Aure haramun ne Amma zuciyar mutumin Nan Babu komai Akan matar sa sai zargi da son ya kamata da laifin da zai jawo Mata JANHURUN masifa. Ni ban San Abinda ya Gani a tare da ita ba Wanda yake zargin ta . Ke wannan mutumin da kike Gani har contacting din Wani ya taba bawa ayi wa yarinyar Nan don ya kamata da laifin ya Bada lambar ta Wani Namiji ya Kira ta don ya Gane shin tana bin mazan da zuciyar sa take Raya Mishi. Ni nafi zargin shine Dan iskan da ke abin fada shiyasa yake zaton ko matar ma tana Abinda yakeyi. Don matukar baka yin Abu ba ka kawowa zuciyar ka Wanin ka Yana yin sa. In da ya yarda da ALLAH Kuma Baya aikata Wani Abu a boye da Bai dorawa matar sa wannan zargin ba. Don haka ni na hada Auren Farida da Sameer Kuma ni na Raba shi duk da Allah NE ya zana Hakan ba ni ba Amma nine sila kuma nine Silar Raba shi don Haka tashi ka je ai ka San kokarin da nayi maka a Auren.

Jiki a Sanyaye Sameer ya Mike Yana Rik’e da Hannun Hanan da Saddam Wanda Suke ta murna Babu abunda ya Dame su.

Ya fice Rike da yaran inda Allura ke shirin motsawa Amma a haka ya figi motar ya fice daga jaji.

Farida ta jima a inda take bata motsa ba har Anty lubna ta dawo ta same ta a inda ta barta ta kamata tana bata Baki.

“Kar kice Zaki Wani bani Hak’uri Wallahi ba zanyi ba Kinga Abinda nake fada Miki ko? Kinga Abinda Yaya dauda ya ja mini? Ni an fada mishi na shirya Rabuwa da Sameer ne? Wallahi ba zan taba Rabuwa da shi ba sai dai Yaya dauda ya zare ni daga cikin Yan Uwan shi tunda na Gane baya kauna ta . In ya zama Silar Aure na Kuma sai ya zama Silar kashe min Aure? Ni fa banzo nace mishi ga Abinda miji na yayi min ba shisshigi ne kawai da son iyawa Kuma yanzu Nan sai anyi Magana yace Yana Sona Amma baya Taya ni son Abinda nake so? To Wallahi na kusa Raba gari da dauda Kuma wannan Hukuncin baiyi mini ba ba Kuma zan dauke shi ba in Yana takamar shi Dan Uwan na ne ai ba shine Uwa ta ko Uba na ba.

“Farida kar ZUCIYA ta kwashe ki kiyi Wani Abu fa. A da naga laifin dauda da yake Neman kashe Miki Aure hakikatan don na San doke kiji zafin shi Amma Kuma wannan Yar matsalar da ya karanta mini sai na Gane ba k’aramin gata yake Miki ba Farida . Yanzu har mijin Auren ka ne zai Bada lambar ka ga Wani Namijin don ayi tasar ka don kawai a Gane kana BLACK MARKET a bayan fage Anya kuwa wannan Namiji ne? Gaskiya kiyi Hak’uri Amma zan fada Miki gaskiya in dai mijin ki yana zargin ki wallahi Abinda dauda yayi miki yanci ne ya kwato miki ko don mijin ki ya Gane kina Daraja.

“Haka Ake kwatar yanci dama? Ba gashi ba? Ba gashi ba ya tona min Asiri har Wanda Bai San Halin da nake ciki ba ma ya sani Yanzu? Ni ya kamata a Jira nazo nace na gaji sai a Taya min ko Kuma a taya ni son Abinda nake so Kuma ni naji na Gani akan son Sameer Kuma ni na San Abinda yasa yake zargi na saboda yaga Abinda ya Gani Wanda dole zai Saka shi zargin to Ina Ruwan Wani da Rayuwa ta ? Zan iya Rabuwa da kowa da Komai akan Sameer Banga Dalilin da wani Shege zai shigar min lamari ba.

Anty lubna ta dafa kafadar ta tana fadin, “Farida kar ki zake akan Lamarin Namiji Wallahi tallahi na yabawa kokarin Yayan ku Domin kuwa ya nuna shi din Uba yake a gareku Mai Kuma son ya kare muku mutunci da Kima Farida. Don Allah ki Saka hankali da nutsuwa da lura ki Gane Abinda yake so ki Gane. Shin yanzu saboda Allah Yaya Zakiji a matsayin ki na mace wacce take Jin Zafin Abinda akayiwa wata mace ko da bata San ta ba. Kaddara Baki San ni ba sai kawai kiga Yayan ku ya na auna min duka irin na Shan gishiri Wallahi tallahi na San Abinda zai fara fitowa bakin ki shine zagi kina cewa azzalumi ne . Me ya sa? Ita mace abin lallabawa ce ko Uban ta ne ba dukan ta ya kamata ba irin nasiha da nuni bare miji da in dare yayi Yana iya zuwa yace Miki Gyara. Shin ko Babu komai Baki Jin Wani Abu a Ranki idan kika Gane ana zargin ki ? Zargin ma ga Mijin Aure Wanda yake son yaga Wani Abu ya watsa ki? Dubi don Allah kyau irin naki Amma ace Namiji irin Sameer Yana ware karfi da kwanji ya nad’e ki kamar kurar Roko shin Baki taba Jin zafi ba ? In kuwa Amsar itace Eh Baki taba Jin zafi ba sai nace kirjin ki Babu zuciya Amma Kuma Dan Uwan ki shi nashi kirjin akwai zuciya Kuma Yana Jin zafin Abinda Ake Miki don ya dauki wannan matakin Banga laifin shi ba. Kema ki dawo cikin hayyacin ki ki Gane Abinda yake so ki Gane tunda har mijin ki baya jin Wahalar saki kina zaton ko igiya Dubu ce a Auren ku matukar Bai daina zargi ba zai tsinke iguyoyin du ba? Ki sani kina da gata Kuma wannan shine gatan ki Amma in kin bashi hadin Kai Domin kuwa ni ban hango inda dauda ya Saka son zuciya da son kai ba.

“Dama ta Yaya ke Zaki hango laifin shi? Ba burin shi kenan ya kashe min Aure ba? To Wallahi tallahi in ma Sameer Bai Kai shi kotu ba ni zan kai shi kotun.

“Ina Jiran sammaci Farida tunda har kin shiryawa Hakan Kinga sai ki wakilci Sameer din.

Da sauri suka daga kansu ita da Anty lubna Ashe Yana Nan sama Yana Jin duk abinda suke fada Kuma Yana kallon su sune Basu San Yana Nan ba sun zaci Yana d’akin shi.

Ya Soma Saukowa har ya iso inda suke ya Soma Fadin,

“Yanzu Farida har nayi lalacewar da kike fadar maganganun Nan a Kaina? Har kinyi kwarin kan da Zaki tsaya Dani a kotu? To Ina jiran sammaci Kuma duk yadda zuciyar ki ta zana miki ni a tsakanin makiyi da masoyi ki dauki Wanda kika gamsu akan sa gareni Amma Ina Mai tabbatar Miki da akan Sameer dai sai dai ko ki mutu Amma yadda Nasha wannan Alwashin Banga Mai Saka ni janye shi ba ko a kotun kuwa Zaki Fadi ne Idan nace akan zargi na Raba Auren don zargi a cikin Aure haramun ne Kuma Raba Auren yake Kinga ke da shi Kun fado.

Ya kama Hannun matar sa Yana Fadin,

“Kyale ta lubna Dabba ce wannan yarinyar Bata San Abinda yake mata ciwo ba muje Rabu da ita Ina jiran sammaci kowace kotu ai na Isa na tsaya ayi Shari a Dani.

Farida ta Raka su da ido tare da wata matsiyaciyar harara ta Mike zuwa d’aki inda Sameer ya bar Mata Daya Daga cikin wayoyin shi don su Rik’a waya.

Ta dauki wayar tana kiran Haj Sai dai wayar haj a kashe don haka ta zauna tana jijjiga kafa tana tunanin wane hali Sameer yake a yanzu? Sun Kai gida ko kuwa Yana hanya? A yadda taga tashin hankali a fuskar sa ADDU AR ta kar yaje ma ya buga motar ta shiga UKU ta lalace.

Sameer.

Tafe yake a motar a guje tamkar Mai Shirin tashi Sama ta bakwai. Gaba Daya jijiyoyin kan shi sun fito idanu jajir tsabar tashin hankali. Baka Jin kotsin komai sai hayaniyar Saddam da Hanan Wanda Suke ta wasa ya Kuma Siya musu kayan tabawa suna ta Kaya kayar su shi Kam cike yake da Tashin hankali. Ya iso marabar hunkuyi ya taka burki zai fito yayi sallar la asar sai Kuma ya tuna bashi da tsarki tunda ya tab’a Farida Abunda ya matukar faranta musu har suka kwashe lokaci Mai tsayi a haka.

Dole ya tashi motar ya wuce inda tafiya tayi tafiya har su Saddam sukayi bacci ya Rufe gilas din motar ya sakar musu AC yayi ta auna Uban Gudu har ya shigo katsina ya Kuma yanke shawarar zarcewa gidan Hajiyar shi inda yaran suka tashi Saddam Yana fadin, “Daddy zanyi fitsari.

Ya juyo Yana fadin, “To bari mu Isa gidan Haj sai kayi .

Haj ta ganshi da yaran da magarubat fari inda Saddam ya Isa ga Haj Yana Fadin.

“Haj ba kice min ni mijin ki ne ba…

“Kai maraba da Mai gida sannu da Zuwa ga Hanan Nan ita Kuma me kike ce mata ma ? Tace
“Kishiya ta ce ai ita wannan. “Yauwa to ga ibon din da Daddy ya kawo min haj Kisha daya ki aje min sauran Amma ki bani Abinci kiyi min wanka.

Haj ta dubi Sameer da Rudanin da yake ciki tace, “Daga Ina kake da yaran Nan haka ? Ina Uwar su ne da kake kwaso su da magarubar fari.

Ya sauke AJIYAR ZUCIYA Yana zayyane wa haj duk abinda ya faru tsakanin sa da Yaya dauda.

“Auhoo shine ni ka kawo min yaran ka saboda Bak’ar zuciyar ka ta zuga ka kayi Abinda aka karbe Yar mutane shine don ka Raina ni ko kuwa Rashin Imani shine zaka nufe ni da Ya’yan ka nice zanyi Maka Wahalar su ? To tafi da Ya’yan ka ka Kai su duk Ma inda zaka kaisu Kuma ni nayiwa wanda ya kwace yarinyar Nan daga gare ka ADDU A don ya nuna ya haihu Kuma ko da Bai Baiyi hakan ba ni Ina Dab da mayar da yarinyar Nan ga Ahalin ta don na tabbata Bak’in cikin ka take hadiya ba Dan kadan ba tunda ka Soma kafa Mata kahon zukar zargi . Don haka duk abinda kayi yayi maka daidai.

“Don Allah Haj ki fahimce ni ni fa babu wani Bak’in ciki na da Farida take kunsa kawai dai Yana son ya wulakanta ni ne don yaga Ina kawar da kaina Ina Jin nauyin shi.

“To ka Daina jin nauyin shi din Mana kawai sai ka kwaci hakkin ka. “Ba zanyi Hakan ba Haj don Ina kunyar mahaifiyar su Amma dai don Allah ki tausaya mini ki karbi yaran Nan har naga Abinda zai yuwu…

“Ai in na karbi yaran Nan na daure maka kugun kayi abinda yafi haka gara kaje da su ko hidimar kwana bakwai kayi musu don ka Kara girmama Uwar su da kokarin dawainiyar su kadai ta ci kayi mata Alfarma ta haka zaka Gane kimar ta da mutuncin ta.

“Haj Gobe zan koma Aiki ba zai yuwu na tafi da su ba.

“Ai kuwa tafiya kake da su don a Gane kakin ne kawai da Kai Amma Sam baka da wata jarumta sai akan matar ka wacce take rufa maka Asiri don haka tashi kuje naga bacci suke ji

“In kikayi min haka haj Asiri na zai Tonu dama haka Ake so shiyasa aka maido min su don Allah don ANNABI ki barsu Nan na yarda In na dawo zanzo nayi musu komai.

Ta Mike tana Rik’e da Saddam da Hanan zata Yi musu wanka. Ya sauke AJIYAR ZUCIYA ya Mike Yana Fadin.

“Sai da safe zanzo Haj ko akwai Abinda kuke so? “Babu “

Shi kadai ta ce ta ci gaba da yiwa Yaran wanke ta Basu abinci suka ci suka kwanta sai bacci dama a Gajiye suke.

Da safe ya tashi yayi shiri ya Saka kakin sa ko Ruwa Bai Sha ba don jiya Kam yayi kwanan takaici don haka ya zarce gidan Hajiyar Farida inda ta ganshi ta tarbe shi Suka gaisa tana fadin.

“Za a wuce Aikin ne? Ya amsa a ladabce tayi mishi fatan Alheri da ADDU AR dacewa

Yayi shiru ya kasa cewa komai har sai da ta ce, “Yaya ne Sameer? Ko Akwai matsala?

Ya tado kanshi Yana fadin,

“Akwai matsala Haj jiya naje jaji saboda kince sati Daya Farida zata dawo Amma Yaya dauda yace Auren mu ma zai Raba har ya bani su Saddam yace na taho da su Kuma na Kai mishi takardar sakin Auren Farida. Ni Kuma na bashi hak’uri Haj na San nayi kuskure Amma Yaya dauda ya kasa Yi mini Afuwa.

“Subuhanallahi shi daudan ne ya Fadi haka? Ban sani ba Sam Wallahi Sameer Amma kayi hak’uri ai ba shine mai yanke wannan Hukuncin ba in lokacin k’arewar Auren Farida yayi sai dai ya samu Labari ba zan san Yaya akayi ba. Don haka tashi kaje Aikin ka sati Daya yace ya Kuma Dawo yace sai tayi biyu yau kwanan ta goma to in Sha Allah Nan da kwana Hudu Sameer zaka ga Farida ta dawo ka barni dashi meye nashi na wannan cika bakin ? Shi mutuwar Aure har Wani Abun nemawa Kai JANHURUN masifa ne? Tashi ka tafi Aikin ka ka barni da shi…

Yayi murmushi Yana Kara dukar da Kai Yana fadin,

“Nagode haj Allah ya Kara lafiya ke kadai kike fahimta ta Nagode Allah yaja da Rayuwa.

“Ameen ya Rabb Sameer lokaci dai wata Rana sai dai a nuna tudun kabari na mun wuce kamar yadda magabatan mu suka wuce Allah yayiwa Rayuwar ku jinkiri Mai Albarka ya Raya muku ZURIAr ku da Imani kuyi ta hak’uri dai wannan Rayuwar cike take fall da kalubale in Sha Allah Nan da kwana Hudu Farida zata iso tashi kaje Aikin ka kar ka makara.

Ya Mike Yana ajewa Haj kudi tace ya dauki kudin shi ta gode Amma ya Bata hak’uri ya fice Yana Jin ita kadai ce tabbaccin sa

Farida Bata iya runtsawa ba a wannan Daren Saboda kwanan Bak’in ciki tayi. Haka tayi ta kiran wayar Haj Amma a kashe . Haka ta kwana ido Biyu cike da takaici da Bak’in ciki tana tunanin Halin da Sameer yake ciki

Washe gari kuwa tana Kiran wayar Haj ta same ta inda ta fashewa Haj da kuka inda Haj ta taka Mata Burki…

“Waye ya mutu Kuma kike fasa min kuka ne Haka?

“Ba gara ma a mutun ba Haj da dai ni kisan da Yaya dauda yake shirin Yi mini?

“Da akayi me to?…

“Haj Yaya dauda fa kashe min Aure yake son yi har Yana fadawa Sameer wai takardar sakin Aure na yake so a kawo mishi Kuma fa ya bashi su Saddam da Hanan ya tafi da su.

“To yanzu Yaya kike so ayi? Kuma shi daudan Bai Isa yace ga yadda za ayi ki yarda ba ko kuwa Yaya za ayi?.

“Haba haj ki fahimce ni Mana cewa fa yayi a kawo min takardar sakin Aurena ni nace mishi a sake ni ne?

“To yadda dauda yake so haka za ayi don Hukuncin da uban ki zai zartar Miki shi dauda zai zartar miki don Haka Babu Ruwa na da Abinda ya ga Damar Yi Miki tunda kuma Baki iya siyasa ba kar ki Kuma Kira na in haka dauda yake so Dole kibi Hakan in Kuma kin Isa to ki tunkare shi tunda ke Sam na lura Baki da mutunci gara na barki da shi ya koya Miki Hankali.

“Haj ke kadai Zaki mishi magana don Allah Haj kar ki bari ya kashe mini Aure Wallahi in ya Raba ni da Sameer ya cuce ni.

“To kin bari ne Kinga Abinda zanyi da kike son fada mishi magana ke tabbatacciya? Kuma in ya cuce ki sai menene ? Mutane nawa aka cuta ko sai kece ba za a cuta ba? Wallahi in kika cika ni Wallahi Zanyi shiru ne da Baki na in barki da kaifin harshen ki naga Zaki iya da daudan ? Tunda akayi Hakan kamata yayi ki same shi cikin lalama ki nuna mishi ko ki Kira ni Amma ke akan Sameer yanzu ne za a Gane sakarai ce ke. Na San Abinda dauda yake hango Miki Wanda Daraja ce yake son sama Miki Amma Kuma ai kin San ba zan bari ya jirga Sameer din ba tunda duk Rashin mutuncin da yayi Miki ni Yana girmama ni Kuma ba zan bari ayi Mishi Wani Abu na danne hakki ba Amma tunda kina da kokari sai ki gwada.

“A a Haj don Allah Kar ki barni da shi Amma don Allah kafin kwanaki hudun da ya fada kiyi Wani Abu Haj.

“In kinbi yadda yake so ne Zanyi Hakan Amma in kika ce Bakin ki ba Zaiyi shiru ba ni Kuma zan Zuba muku ido.

“Zanbi yadda yake so Haj Amma wallahi na Gaji da garin Nan da Gidan Nan don Kar in Bata miki ne yasa ban taho ba Amma Wallahi da Nayi tafiya ta.

“Ai zabi Yana gareki yadda duk kika Zaba haka za ayi.

“Yadda kuke so Haj haka zanyi.

“To kinyiwa kanki kiyamullaili in Kuma kika Kuma tunkara ta da wata Banzar magana na tsame Hannu na naga kina iyawa.

Da haka sukayi sallama haj ta kashe wayar ta Amma Farida kam ta Rufe yiwa kowa magana a gidan hatta da Anty lubna Bata ko kallon ta bare da tanka Mata. Bare Kuma Yaya dauda da take daukewa Kai sai ma tazo ta shuda shi ta wuce Bata ko kallon shi sai dai ya bita da ido Yana kallon ta da Mamakin yadda take mace akan son Sameer Amma Yana gallaza Mata Kuma wai ita shine abin so a wurin ta. Sai ya Gane dama Abinda kake so shi yake Wahalar da Kai Amma Kuma yayi Damara Raba su don yaga irin k’arar da zata Kai shi.

<< Tana Kasa Tana Dabo 7Tana Kasa Tana Dabo 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.