Skip to content
Part 1 of 12 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Gabatarwa

Kirkirarren Labari ne da Bai shafi kowa ba kuskure ne danganta Kai ko Wani da shi Babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarin cikin Labarin Wanda kuka San Babu su fatan za a fahimta Kuma a kiyaye

Sadaukarwa

Wannan littafin Gabadaya na mutanen Gidan iko ne musamman Wanda Suke biye Dani da ayyuka na Allah ta ALA ka Amintar Dasu sani gabadaya.

Kyakkyawa ne Wanda kallo Daya zaka Gane Hakan musamman ma ga Mata Wanda yake Shan kallo saboda tsarin Halittar sa na Namiji ingarma Kuma Mai kyan da ya zamo burin Mata Kuma Mai AZURFA DA ZINARE Wanda ya zamo karshen Magana a wannan Zamanin.

Dogo ne kuma a tsaye . Sai dogon hanci da kyakkyawar fuska tare da gashin saje da na gemu Dan k’arami sai Kuma izza da Jin Kai wacce itace Abinda yafi daukar hankalin mutane akan sa.

Ya Dubi agogon Hannun sa Yana kiyasin Lokacin da ya Saka zai gudanar da BLACK MARKET din sa kasancewar Mai d’akin Nashi ya Kai ta Asibiti ya Kuma ce ta Jira shi zai dawo zuwa karfe Biyu ya dauke ta shiyasa ya dawo gida don yayi daurayar da ya Saka a Gaba wato joint din da ya Kira wacce zata zo ta same shi su sheke Ayar su a D’akin na matar tashi in yaso idan ya sallami Yar iskar da ya gayyato din sai ya koma Asibiti ya dauko matar tashi Farida wacce yayiwa bala in Saka Mata ido don zuciyar sa ta kasa Amince mishi itama tana yin BLACK MARKET din da yakeyi da Matan waje itama da wasu Mazan.

Ya ja tsaki kafin ya sake duban agogon Hannun shi Yana mamakin Abinda wasila ta tsaya Bata K’araso ba gashi har taci Lokaci duk da Yana shakkar kar Farida ta dawo ta samu wasilar a gidan Amma yasan Farida ba zata iya tsallake Umarnin sa ba ko ta gama ganin likitan ba zata taho ba sai Yazo.

Ya Soma zagaye D’akin Yana jiran Zuwan wasila don zuciyar sa tana fada mishi akwai matsala fa . Amma ya Rasa Gane ta inda matsalar zata Fito shin daga wasilar ko kuwa daga Ina? Abinda ya tabbatar dai Babu wata matsala daga Farida sai dai ko haduwar su gidan kowani abu dai.

Ya matsa gaban tagar d’akin Wanda yake a Saman benen ya daga labulen Yana son Ganin Wanda zai shigo Wanda zai shigo din ma Kuma wasila da yake son ta iso suyi su gama ko ya sallame ta ya tafi dauko Farida.

Ya saki labulen ya koma ya zauna Yana shafa kanshi Yana matukar begen wasila da irin Duniyar da ya Gani a tare da ita yake Kuma son yaji shi a jikin ta Yana.

K’arar motar da yaji tana shigowa ne ya dauki hankalin shi ya Mike Yana daga labulen tagar inda yake Hangen motar ta 206 tana shigowa gidan nashi Abinda yazo a Ranshi wasila ce aka kawo a motar? Wani irin matsiyacin kishi ya turnike shi don Allah yayi shi mutum Mai matukar zafin kishi baya son su hada son mace da wani Namiji. Don haka a yanzu ma duk tsananin begen wasila da son yaji ta a jikin shi da yake da ya ga motar nan ya Kuma tabbatar Wani ne ya kawo ta Wanin ma Kuma wata Kil Wanda yayi Abinda yake so yayi da ita yanzu sai yaji ta fice mishi fit a Ranshi don baya son Wani Namiji ya so Abinda yake so don tsananin kishin sa kuwa ji yake kamar zai mutu shiyasa farida Bata fita sai da nikab haka Kuma ko dan Uwa na nesa ne Bata yarda doguwar magana ta hada su don Yanzu ne zaiyi Abinda zai Bada kunya.

Yana tsaye Rike da labulen Yana son Ganin Wanda zai fito a motar Wanda ya kawo wasila idon shi na fidda yajin kishi don ya hango irin Abinda Zaiyi Mata ya yaga ta har son nata ya fasa.

Kyauren motar ya bude idon shi akan motar sai kawai yaga Farida tana fitowa daga motar yayin da yaja baya da sauri tsoro da firgici Mai tsanani ya shige shi inda kishin na zahiri ya bayyana.

Hannun ta Rik’e da Jakarta da Kuma kyallen nikabin fuskar ta da cire Abinda Kuma yayi matukar fusata shi inda yake hango Wani mutum Yana Miko Mata Wani Abu a Leda ta karba tana murmushi ta wuce tana daga mishi Hannu.

Da sauri da wani irin zafi Wanda ya haddasa mishi rikida ya koma Wani Tsoro jijiyoyin kan shi Suka fito Rudu Rudu Babu Abinda zuciyar sa ke fada masa sai Farida tana Neman wasu Mazan a bayan idon shi?

Ya Soma Saukowa daga Saman benen har Yana hada step down biyu uku Yana tsallake wa inda Sukayi taho mu gama a bakin kofar.

Taja baya a tsorace tana kallon yadda ya koma Wani Tsoro shi Kuma ya Dube ta da jajayen idanun shi Yana Kai hancin shi Yana son ya shako kamshin turaren da zai nuna mishi Wani Namiji ya Rungume ta.

Wani Abu ya soki zuciyar ta Domin kuwa Dabi ar sa ce haka matukar ta fita ta dawo sai ya shinshina ta yaji idan kamshin ta ya sauya. Tun Bata fahimci me yake nufi ba har ta Gane ta ko Ina zargin ta yake.

Ta dauke kanta tana Jin wasu kwalla suna ciko idon ta har ya gama shinshina ta Soma Magana cikin wata murya Mai cike da masifa da balaki Yana fadin.

“Wane Dan iska ne kika shigo motar shi? Daga bari naje na dawo ? Dama don ki Samu Damar Kiran yan iskan ki kika ce sai biyu Zaki gama?

Bai k’arasa maganar da yake ba yaji motar da ta kawo ta tana Shirin fita da wani irin sauri ya fita bakin kofar inda ya samu motar tana Shirin fita . Da sauri kuwa ya shiga tashi motar ya fige ta a guje ya Rufa mata baya da wani irin mugun Alwashi.

Aguje yake bin bayan motar da son ya cimmata inda Shima Mai motar ko ya fahimce biye Ake dashi? Oho sai ya Kara malejin gudu suka Soma dibar Fili.

Tafiya Mai tsayi suka dauka kasancewar titi suke bi mike tal tal Babu kwana Babu rawun.

Ya kure malejin gudun motar inda zuciya ke kitsa mishi ya tankada motar a kwatamin da yake Gaban su motar da Mai motar su mutu ko zai huta da zugin zuciyar da yake shirin kashe shi.

Ai kuwa yana cije da Leben shi ya Kara Rarakar motar da karfi ya Kuma kaiwa motar Nan ta gaban shi dauka da karfi ya tankada ta a cikin katon kwatamin Wanda Mai motar yake ta kokarin dauke kan motar Amma Ina ! Da Wani matsiyacin karfi ya danna motar har Yana cije Baki sai da yaga fadawar motar a cikin kwatamin har tana hantsilawa kafin ya juya a guje Yana Sauke numfashi idanun shi jajir har suna kwalla saboda tsabar masifa. Abunda Bai sani ba TANA K’ASA TANA DABO.

*****

Farida na tsaye fuskar ta sharkaf da hawaye tana Jin Wani irin d’aci akan wannan Aure nata da a har yanzu Bata samu yancin da Ake Samu a cikin Aure ba. Aure da zargi fa haramun ne . Babu Ranar Allah da zata fito ta komawa Ubangiji Sameer Bai nuna Mata Alama daya ta Rashin yarda da zargi dubu ba. Ta Gaji ta Gaji da wannan Al Amarin Wallahi ta Gaji Kuma a yau Kam ta barshi kenan har Abada ko bata gaji ba zargin shi ya Isa ya Raba su.

Tana tsaye ta kasa zama ta Kuma kasa matsawa bare da aje kyallen nikabin ko ta ajiye Jakarta sai faman fidda HAWAYE take cikin Rashin tabbacci.

Yaron Dan shekara Hudu ya shigo da gudu kanwar sa na biye da shi abaya wacce Bata cika shekara biyu ba.

Tana tsaye taji Saddam ya Rungume ta Yana Fadin “Mami Ina sweet din da kika ce Zaki kawo Mana.

Ta Dube shi don Bata San sun shigo ba.

Ganin idon ta da Ruwan hawaye yasa yaron yace “Mami Allura akayi Miki ne a hospital din?

Bata tanka mishi ba kamar yadda bata share Hawayen ta ba ta kamo hannun yarinyar Hanan ta Bude jakar ta ta fito da sweet din tana Basu inda Hanan Kam ta Soma Kai sweet din a Baki tana Sha shi Kam Saddam ido ya zuba Mata Yana kallon ta da hawayen idon ta.

“Mami ki Daina kuka Allura akayi Miki ne?

Ta Sani yaron Yana damuwa da damuwar ta.

Ta zauna tana kamo yaran ta Rungume sai Kuma kuka ya kwace Mata tana tausayin yaran Amma Kuma Dole ta Hak’ura da Uban su don matukar suna tare Kam shine Ajalin ta.

Saddam Kam Kuka yake ganin kukan Uwar sa Akasin Hanan da take Shan sweet din ta Babu Abinda ya dame ta.

Da karfi ya shigo Gidan har Yana dukan kofar get din da motar Amma Bai damu ba burin shi kawai ya kai ga Farida da take son Kashe shi da wannan Aikin na cin Amana da keta haddi.

Ya faka motar ya fito ko kofar bai Rufe ba ya nufi cikin Gidan Yana warware belt din Dake kugun shi irin na kakin SOJA.

Bai iya kula da yaran da take Rungume da su ba saboda son ya yaga ta don haka idon shi ya Rufe ya Kai Mata wata irin damuka ya Figo ta har Yana take Yan yatsun Saddam Wanda ya kwallara wata Razananniyar Kara saboda Balakin da yaji a Hannun. Sai a sannan ya kula da Saddam din Amma duk da haka Bai bi ta kan yaron ba sai Marin da ya kaiwa kyakkyawar fuskar Farida hagu da dama kafin ya shake ta Yana Fadin.

“Dama Abinda kikeyi kenan ? Dama Abinda yasa na kasa yarda da ke kenan? Ni kike wa wannan wulakancin? To zan kashe ki kafin ki kashe ni da Bakin CIKI.

Da duka karfin shi ya shake ta idanun ta Suka fito waje ganin kamar Bai Yi Mata yadda Zata ji azaba ba yasa ya sake ta ya Soma Kai Mata Duka da Bakin belt tamkar dai ya samu Kato. Tun tana kuka har ta kasa kukan inda kukan su ya hade da kukan Saddam Wanda a yanzu Hanan ma ta mara musu baya wata kil Kuma watsin Karan mahaukaciyar da akayi da ita ne.

Wasila Kam da Napep ya kawo ta ta dubi gidan ta tabbatar da Nan ne sai kawai ta sallami Mai Napep din ta tunkaro gidan tana Jin Yar shakka irin ta marar gaskiya Amma a haka ta danna kanta inda ta Soma jiyo hargagi da k’arar saukar Duka.

Idon ta ya sauka akan Sameer da yake jibgar wata mace wacce ta gama yarda matar sa ce.

Da sauri ta Isa tana karbar Farida da yayiwa jina jina duk ya fasa Mata jiki da karfen belt.

Wasila ta Dube shi ya Dube ta inda yayi sak . Farida Kuma da ta gama ficewa a hayyacin ta Bata San Abinda ke faruwa ba.

Maman Umar makociyar Farida wacce a gidan ta Farida ta Kai Saddam da Hanan lokacin da zata tafi Asibiti da Kuma ta dawo yaran suka dawo itace taji kukan da Ake yayi yawa don haka ta fito don taga Abinda ke faruwa…

Sai kawai ta iske Farida ba a yadda take ba ga Kuma wata mace da bata San wacece ba sai Kuma baban Saddam din da belt a Hannu wanda Hakan ne ya nuna shine Mai kokarin dukan dama Kuma ba yau ne farko ba.

Da sauri ta Isa ga Farida tana fadin
“Haba baban Saddam in Rai ya Baci sai hankali ya gushe? Shi fa Rai karau ne Allah NE kadai ya San inda yake.

Jikin shi yayi sanyi kalau inda wasila Kam sai ta sulale ta bar Gidan don shims Kuma ba son zuwan nata yayi ba a yanzu…..

Yana tsaye wayar shi tayi Kara ya dauko ta inda yaga nomber Haj mahaifiyar su ya dauka da sauri inda ya juyo kukan Haj tana fadin

“Sameer don Allah taho yanzu aka Kira ni da wayar bello wai Wani marar Imani da tsoron Allah ya tankada shi da motar a kwatami ya gudu don Allah taho muje na ga halin da bello yake ciki wai har an Kai shi Asibiti taho don Allah.

Ta fada da rushin kuka inda jikin shi yayi Wani irin Sanyi kar dai kanin nashi ne bello ya Kai makasa?

Ya fice ya nufi gidan Haj inda maman Umar Kuma ta kira mahaifiyar Farida tana kuka ta fada Mata Abinda ke Nan tuni sai ga mahaifiyar Farida ta iso da Napep ganin yadda Faridar take bats San Wanda ke kanta ba ya tayar Mata da Hankali Dole ta kwashi Farida suka nufi Asibiti…

Tana Kasa Tana Dabo 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×