Tun misalin ƙarfe bakwai gidan na marayu ya fara ɗauka harama, duk wani ɗan gidan wanda yasan yayi katin zaɓe to ya iso ko dai ya na kan hanya ko kuma shirin zuwa gidan. Wannan dalilin yasa yau gidan aka dafa abinci mai yawa domin ƙaruwar da aka yi. Ko ina ka leƙa al'umma ne kaman ana yin wani gagarumin bikin. Misalin ƙarfe takwas na safe kuwa kowa yazo, suma jagororin yin zaɓen sun iso har sun gyara ko ina an fara hawa kan layi. Manyan gidan ne a gaba haka aka dinga zaɓar jam'i ɗaya a cikin. . .
