Mutumin ya ce "Kaga bari ni na raba wannan matsalar, akan ɗari biyar dai ai ba kayi faɗa da Mace kuma yarinya ba". Ya fara ƙoƙarin saka hannu ya ɗauko kuɗin Abida ta ce "Malam barshi kawai, idan ma cutata yayi Allah Ya isa ban yafe ba, kuma in sha allahu sai wannan shagon naka ya lalace, mugu kawai mai halin mugaye". Ta na faɗa ta ɗauki ɗari biyun da Fantasy ɗin ta, tayi waje, tana jin yadda mutumin nan ke kiran ta akan ta zo ya bata ɗari biyar ɗin amma sai ƙara sauri take. A bayan gidan su. . .
