Anty Hinde tayi dariya kawai ta na kallon Abida. Abbati ma ya ce "Anty ko ni wallahi bana so ki aihu da wannan mutumin, ko kin san abun da yamin a police ranar?" Ya Tambaye ta abun da ya faru na dawo masa. "Mai ya faru?" Anty Hinde ta yi maganar duk da kuwa tasan komai, domin a washegarin ranar duk da irin halin da take ciki bai hana ya faɗa mata ba, kuma ya ɗora mata laifin komai. Nan Abbati ya sanar mata da irin dukan da yayi masa da kuma abun da ya faɗa. Haka Anty Hinde ta. . .
