Haka Yakubu ya amshi kuɗaɗen sannan ya shiga ɗaki. Shi abun da zai iya cewa ya mora a wannan auran shine kawai ciyar da gida da suke yi, amma bayan haka babu komai wallahi. Haka yana wanka yana tunanin to ko dai ya hana su yin aikin ne gaba daya, to amma kuma ai da aikin suke riƙe da gidan, to ko dai ya saki ɗaya ne a cikinsu, nan ma ya tuna da yadda aka yi auran da sharaɗi. Haka dai ya cigaba da wankan ba tare da ya samo mafita ɗaya da ya yi na'am da ita. . .
