Yana ɗaga wa aka ce masa yanzu-yanzu yazo ana nemansa a jam'iyyar su. Haka kuwa bai tsaya sanarwa Zinaru ba ya fita da sauri. Sai da yaje zai shiga mota ya tuna babu hula a kansa, hakan yasa ya dawo gidan da sauri yana jin yadda Zinaru take amsa waya tana kuka da ƙarfi kaman wanda aka yi mutuwa. Sosai wannan videon ya tada ƙura a cikin garin na Yalwa mutane ke ta yin sharhi akan maganar da yayi. Ɓangaren Saif kuwa hankalinsa kwance sai dai ya na ta samun suka daga abokansa da kuma ƴan uwa, hakan. . .
