LITTAFI NA DAYA
A wani zamani mai tsawo da ya shuɗe, an yi wani babban Sarki ana kiransa Shamsuddini. Ya kasance mai girman iko. Mulkinsa ya watsu cikin ƙasashen duniya, tun daga Kurasana har zuwa Sistani har iyakar tekun hindu. Babban birninsa shi ne Kunaimu Madudu. Yana da Wazirai goma waɗanda ke mulkin wasu jihohin daga ƙasarsa. Ƙarƙashin kowane Waziri akwai hakimai dubu, da dagatai dubu goma, da sauran masu faɗa a ji. Yana da mayaƙa, da bayi, da hadimai, da dukiya mai ɗumbin yawa. Talakawa na sonsa saboda yawan adalcinsa da kyautayinsa gare su. Sai dai duk wannan abubuwa da ya tara ba shi da mata. Ya taɓa yin auren bai ji daɗi ba, don haka ya jinkirta har ya samu wadda za ta yi masa biyayya sau da ƙafa.
Wata rana ya shirya tare da bayinsa suka fita farauta. Yayin da suka gama zagaya daji suka kamo hanyar gida sai suka yi kiciɓis da wani baƙin bawa yana haye bisa alfadara, biye da shi wata taguwa ce ɗauke da darbuka na zinariya yana ta ɗaukar ido. Sannan biye su mayaƙa ne cikin shiri, suna haye kan dawakai, gaba da su wasu dawakan ne ɗauke da jauhari da lu’ulu’u, suna tafiya cikin tsari. Da Sarki Shamsuddini ya gan su sai ya zabura bisa dokinsa, ya isa wajen bawan nan ya ce masa, “wannan matar ina za a kai ta?” Shi bawan bai san Sarki ba ne, sai ya ce, “wannan ‘yar Waziri Yusuf ce, za mu kai wa Sarki Imranu ya aure ta.”
A daidai lokacin da suke magana sai ‘yar Waziri ta leƙo da kanta domin ta ji an tsaya da tafiya, sai kuwa Sarki Shamsuddini ya yi ido huɗu da ita. Ya yi duba izuwa ga ƙirar jikinta, da fararen idanunta, da kyawawan leɓɓanta, nan da nan ya ji son ta ya shige shi. Ashe ita ma yayin da ta yi duba zuwa ga Sarki sai ta ji tana son sa.
Sarki ya ce da bakin bawan nan, “ka sani Waziri Isfahanu a ƙarƙashin mulkina yake. Ni ne Sarki Shamsuddin, ina son wannan yarinyar, don haka ka ba ni ita na aure ta.”
Bawa ya ce, “ai ni ɗan aike ne, ba zan aikata abin da ubangidana bai umarce ni ba.” Sarki ya fusata ya ce, “Kai ɗin banza kai ɗin wofi! Ko shi Wazirin da yake bawan bawanmu bai isa ina son abu ya ki amincewa ba!” Ya daka wa bayinsa tsawa suka kama akalar alfadarar nan suka wuce da ita gidansa. Mayakan nan na ganin haka sai suka juya tare da bakin bawa suka koma wajen Waziri Isfahanu suka shaida masa abin da ya faru. Waziri na jin haka ya fusata matuƙar fusata, ya kawo iyakar wuya. Ya ce, “wannan mugun Sarkin ya bautar da ni, yana son bautar da iyalina ma. Ku sani ban ba shi wannan ‘yar ba, kuma ba zan yarda ya taɓa ta ba. Idan kuwa ya aikata hakan to a bakin ransa.”
Duk da ya faɗi haka sai ya aika da takarda zuwa ga Sarki yana mai cewa, “ka sani ni bawanka ne ɗan bayinka. Kenan ‘yata ma mallakinka ce, sai abin da ka ga dama da ita? Akan haka ba ni da ta cewa.” Da Sarki ya ga wannan takarda sai ya cika da murna da farin ciki, ya sa aka shirya walima mai yawa. Ya aika wa Waziri kyautar bajinta, aka shiga hidimar aure da shagulgula. Bayan an ƙare shagali, Sarki ya shiga wajen matarsa ya tare da ita, babu jimawa ta samu ciki.
Waziri kuwa sai ya riƙa aika wa ragowar waziran wasiƙa a ɓoye yana shaida musu irin abin da Sarki ya yi masa na tozarci. Dama ashe duk suna jin haushin sa. Nan da nan suka taru a wajen Waziri Isfahanu suka shirya yadda za su kashe Sarki kowa ya huta. Bayan sun kare shiri kaf suka durfafi babban birnin ƙasar, duk abin da ake ciki Sarki ba shi da labari. Yana ɗakin matarsa suna cin amarci sai suka ji hayaniyar dawaki, da ihun mazaje, da karar mata da yara.
Sarki ya dubi matarsa wadda ke da tsohon ciki ya ce mata, “wace dabara za mu yi?” Ta ce, “kai ke da gani duk abin da ka gani shi za mu aiwatar.” Ya ce, “babu sauran zama a nan, mu tsere da ranmu.” Suka tashi suka shirya dawakai biyu, sannan suka ɗauki jakankunan kuɗi masu yawa suka bi ta bayan gida suka gudu su biyu kaɗai. Cikin duhun dare suka yi ta tafiya cikin ƙungurmin daji basu san inda suke tafiya ba.
A wannan daren naƙuda ta kama matar saboda wahala da fargabar da ta shiga. Nan ta durƙusa ta haifi ɗa namiji. Sarki Shamsuddini da kansa ya yi mata hidima, babu ruwa, sai tufafi suka sa tsumma suka goge shi sannan ta soma shayar da shi. Suka samu wani kogo suka ɓuya a ciki bayan sun ɗaure dawakansu a wuri mai nisa yadda babu wanda zai gan su.
A cikin gari kuwa, fitarsu ke da wuya ‘yan tawaye suka shiga gidan, Waziri Asfahanu ke kan gaba da zararren takobi, duk wanda ya samu sai ya fille masa kai, suka zagaye ko’ina kaf babu Sarki babu matarsa. Waziri ya sa aka tara mutanen gidan kaf ya shiga tuhumar su inda Sarki ya shiga suka ce basu san inda ya yi ba. Da ya ga ba za su ba sa ba shi amsa mai daɗi, sai ya sa aka yanka su gaba ɗayansu, mutum fiye da ɗari biyu maza da mata.
Daga nan ya haye bisa karagar mulki, ya riƙa aiwatar da zalunci da kama karya. Duk abokansa da suka taimaka masa sai da ya kashe su ɗaya bayan ɗaya. Wannan kenan game da al’amarin Waziri wanda yanzu ya koma Sarki Asfahanu.
Sarki Shamsuddin kuwa da gari ya waye, suka shirya za su tafi, sai ya ce da matarsa wadda yanzu ta zama mai jego, “ni ina ganin makiya na nan biye da mu, kuma a gaskiya wannan jaririn zai zame mana matsala har a kai ga cim mana. Don haka na hore ki da ki ajiye shi nan, idan da rabon ganawarmu Allah zai sadar da mu a nan gaba.”
Matar ta fashe da kuka, saboda tana tsananin son ɗanta duk da bai ɗauko kamanninta ba. Amma da ta duba irin hatsarin da suke ciki sai ta haƙura ta ajiye shi. Ita da uban suka yi ta kuka amma babu yadda za su yi, haka suka yi masa shimfiɗa suka ajiye jakar dinari dubu kusa da shi suka tafi.
Suka yi tafiyar kwana goma sha uku a ɓarauniyar hanya cikin tsoro da firgici suka isa wani babban birni. Suka isa wajen Sarkin garin suka kwashe dukan labarinsu suka shaida masa. Sarki ya karɓe su da kyakkyawar siffa ya basu masauki, ya yi musu goma ta arziki. Bayan sun huta ya tattara rundunarsa mai dakaru masu yawa suka tafi tare da Sarki Shamsuddin zuwa birnin Kunaimu, suka auka masa da yaƙi. Sarki ya kashe Wazirinsa Asfahanu da hannunsa, ya ƙwace mulkinsa ya koma kan karagarsa. Mutane suka yi ta murna saboda azzalumi ya tafi adali ya dawo.
Bayan an natsa, sarki Shamsuddini ya aika dakaru zuwa daji inda suka ajiye jaririnsu, amma suka dawo ba su same shi ba. A nan Sarki ya zauna yana ta baƙin ciki tare da addu’ar samun saduwa da ɗansa. Shi kuwa jaririn nan da aka ajiye yana barci har rana ta soma zafi yunwa ta farkar da shi ya soma kuka.
A daidai lokacin kuwa wasu ‘yan fashi sun zo wucewa sai suka ji kukan jariri, suka isa wajen suka tarar da jakar kuɗi kusa da shi kuma yana cikin mayafi irin na sarakuna. Suka ɗauko shi suka kawo wa babbansu. Shugaban ‘yan fashin na ganinsa ya ji son sa ya kama shi. Ya sa aka tatso nonon taguwa aka ba shi. Nan da nan ya sha ya koma barci suka tafi da shi wajensu. Aka miƙa shi ga mata suka yi ta rainon sa.
Ana nan yaro ya girma har ya iya tafiya da magana. Ya koyi karatu da dabarun yaƙi, ɓarayin suka riƙa ƙoƙarin shigar da shi cikinsu, amma ya ƙi yarda, kullum sai wa’azi yake musu da nasiha da gargaɗi. Da shugaban ‘yan fashin ya ga lalle yaron nan ba zai yarda ya zama tamkar su ba, sai ya shirya wata dabara yayin da za su fita wani hari. Ya kira yaron wanda suka raɗa masa suna Kabiru, ya ce masa, “gobe za mu kai ziyara ga wasu abokanmu, ina so ka shirya ka tafi tare da mu.” Kabiru ya ce, “Allah ya kai mu, ziyara tana da daɗi, kuma tana da ɗimbin lada.”
Washegari suka shirya suka tafi, ashe aikin fashi za su je. Dabarar shugaban ita ce, idan yaron ya ga yadda ake gumurzu da fatake zai yarda cewa sana’ar fashi da makami ma babban jidali ne, domin kuwa kafin a samu abin da ake nema sai an sha fama. Suka isa wata babbar hanya inda wasu ayari suka taho da dukiya mai yawa za su birnin Kunaimu, suna kuwa ɗauke da dukiya mai ɗimbin yawa. Ɓarayin sun samu labari sai suka yi niyyar tare su su karkashe su su ƙwace dukiyar. Suka shirya suka samu wajen da za su tare su.
Ashe su ma wannan tawagar akwai mayaƙa, samun labarin ‘yan fashin ya sa suka yi kyakkyawan shirin ko ta kwana. Suna gamuwa kuwa yaƙi mai tsanani ya kaure tsakaninsu, Allah ya ba wa ayari nasara a kan ‘yan fashin nan. Suka yi musu mummunar ɓarna, har shugabansu ya arce da ƙafafunsa. Suka kama mutane da dama ciki har da yaro Kabiru suka tafi da shi.
Yayin da suka isa fadar Sarki suka yi gaisuwa, sai suka shaida masa labarin karonsu da ‘yan fashi, suka nuna masa waɗanda suka kama daga cikinsu. Sarki da ya ga yaron nan bai gane cewa ɗansa ba ne, amma sai ya ji yana ƙaunarsa. Ya ce da shi, “kai yaro me ya kai ka cikin ɓarayi?” Yaro ya ce, “ubana shi ne shugabansu, amma ni bana sha’awar sana’arsu.” Sarki ya ce da mutanen da suka kawo shi, “ku bar min wannan ya zauna a wajena.” Daga nan Sarki ya shigar da shi cikin hadimansa ya ba shi kaya na alfarma kuma ya amince masa.
To kafin a yi haka kuwa, Sarki na fama da matsalar masu kula da dukiyarsa, musamman yadda waziransa su goma suke shiga ciki suke wadaƙa son ransu. A hankali ya auna wannan yaro ta hanyoyi da dama ya amince da mutuncinsa da hankalinsa da amanarsa. Sai ya tuɓe ma’ajinsa ya naɗa shi, ya zamana ba ya rabo da shi a ko da yaushe. Da haka ya magance matsalar Wazirai da ke shiga dukiyarsa suna yin abin da suka so.
Wannan mataki bai yi wa tsohon ma’aji da aka sauke da ragowar Wazirai daɗi ba. Sai suka shiga ƙulle – ƙullen makircin yadda za su karya lagon yaron, sai dai sun rasa yadda za su yi da shi. Daga bisani dai suka shirya a kan za su kashe shi kowa ya huta. Hakan ma bai zama dabara ba, domin kuwa sun rasa lokacin da za su same shi a keɓe su iya aiwatar da mugun nufinsu a kansa. Bayan tsawon lokaci sai suka zartar da cewa za su shirya masa makirci yadda Sarki da kansa zai kashe shi.
Ana nan wata rana yaron ya halarci wani shagali inda aka yi sha mai yawa, har barci mai nauyi ya kwashe shi a can. Bayan an tashi ya taho gida yana cikin magagi bai san inda yake tafiya ba ya shiga gida. Maimakon ya wuce ɗakinsa sai ya wuce makwancin Sarki inda yake keɓewa da matarsa. A ranar kuwa Sarki ya yi nufin kwanciyar aure da ita, ya sa an gyara gadon an ƙawata shi, an fesa turare, ƙamshi na tashi. Yaro na zuwa, da yake yana cikin mamagi, sai ya yi tsammanin gadonsa ne aka gyara masa. Ya yi murna da haka, ya haye kan gado ya shiga barci mai nauyi yana munshari.
Yayin da Sarki ya kammala cin abinci da matarsa sai ya kamo hannunta ya tafi da ita ɗakinsa. Suna zuwa sai ga yaro kwance kan gado yana ta munshari. Sarki ransa ya baci, ya dubi matarsa a fusace ya ce, “na tabbata ke ce kika gayyace shi nan wurin domin ku ci amanata.” Matar ta ce, “wallahi ban san komai game da haka ba, kada ka ɗauki alhakina. Ni makuɓuciya ce daga zarginka.” Cikin fushi Sarki ya kirawo bayi suka zunguri yaron nan ya farka, ya daka masa tsawa ya ce, “me ya kawo ka gadona!” Da jin muryar Sarki nan da nan maye ya sake shi ya durƙusa yana mai gaisuwa. Ya ce, “wallahi ban san cewa nan na zo na kwanta ba.” Sarki ya ce, “ƙarya kake yi maci amana! Allah ya kama ka!” Ya daka wa bayi tsawa ya ce, “ku kai shi kurkuku zuwa gobe!” Aka tasa ƙeyar yaro aka kulle. Matar ma ya sa aka kulle ta a wani kurkukun dabam. Ya kwana yana mai matsanancin fushi.
Wannan labri ya anfani jama,a .muna jiran sauran littafi nagaba.