Rana Ta Tara
A wannan ranar Wazirai suka kasa samun sukuni, suka taru a wajen da suke tattaunawa suna juya maganar tsakaninsu. Wani daga cikinsu ya ce, “yaron nan ya gagari Sarki ya kashe shi, saboda tasirin sihirin da ke cikin maganarsa. Ban da sihiri, ta yaya har yau kwana tara Sarki bai aika da shi barzahu ba?” Wani daga ciki ya ce, “ko mu haɗa baki da masu tsaron kurkuku su kashe mana shi kurum?” Wani ya ce, “A’a, wannan ba dabara ba ce, domin za a iya ganowa daga baya. Ku zo mu ɓullo masa ta wajen matar Sarki kurum.” Suka amince da wannan shawarar, suka ɗunguma baki ɗaya zuwa wajen matar Sarki. Suka ce da ita, “ke ma dai kin zama kamar ba ki damu da abin kunyar da yaron nan ya jawo miki ba. Sarki kuwa tuni ma ya yi watsi da maganar kullum sai nishaɗi da bushasha yake yi abinsa. Mu muna jiye miki tsoron muddin yaron nan na da rai a garin nan sai an samu lokacin da mata za su riƙa yi miki zambo a waƙoƙinsu, suna cewa matar Sarki tana ƙaunar wani ɗan yaro. Kin ga kuwa wannan bai dace ba. Maganin abin kurum a kawar da shi daga doron ƙasa” Matar ta ce, “ni mace ce, ba ni da abin faɗa game da mulkin waje. Mulkina iyakacin cikin gida ne. Kuma ban san abin da zan faɗa wa Sarki a kan wannan maganar ba.”
Suka ce, “ki je fada ki same shi ki ce masa, yanzu zance yana ta bazuwa a gari kan cewa kin aikata abin kunya. Ki ce masa idan ba zai kashe yaron ba to ke ya kashe ki domin ki huta da takaici.” Ta ce, “haka za a yi.” Lokacin da fada ta cika, duk Wazirai na zaune, sai matar Sarki ta shirya zuwa fada ta yi shigar sarauta. Ta faɗi gaban Sarki tana kuka tana cewa, “Allah ya ba ka nasara haka za a bar yaron nan da ya nemi keta haddin iyalinka? Haka za a bar ni har kullum abin kunya na bi na alhali ba ni da alhaki a kai? Haka za a yi ta zama kullum mutanen gari na yi min habaici suna zunɗe na? Wannan ba al’adar sarakuna ba ce. Na roƙe ka, idan ba za ka kashe yaron nan ba, to ni ka kashe ni, domin na huta da wannan ɓacin ran.”
Zuciyar Sarki ta tunzura, ya ji kamar ya fashe don fushi, ya ce da ita, “na rantse da Allah ba zan bari ki wulaƙanta ba. Ba zan bari wani abu ya ɓata miki rai ba. Koma mazauninki ki saki ranki, wannan yaro a yau zan zartar masa da hukuncin kisa.” Ta tashi ta tafi. Sarki ya sa aka taho da yaron ɗaure cikin sarƙa, duk Wazirai na zaune. Ya dube shi a fusace ya ce, “kai maƙasƙancin wofi! Ranka ya wulaƙanta, ƙasa na jin yunwa tana jiran ta ci namanka.” Yaro ya ce, “ni na san mutuwa ba a bakinka take ba, ko cikin fushinka. Cewa ita ƙaddara ce da aka rubuta bisa goshin kowa, babu makawa ɗan adam sai ya gamu da sababin mutuwarsa. Don haka idan an rubuta cewa kai ne sanadin mutuwata to babu makawa sai hakan ta faru. Babu wani abu na daga tsimi ko dabara da za a iya kauce wa haka kamar yadda ƙaddara ta auku ga Sarki Ibrahimu da ɗansa.” Sarki ya ce, “wane ne kuma Sarki Ibrahimu? Wane ne ɗansa? Me ya faru gare su?” Yaro ya ce, “Allah ya ba ka nasara, bari na faɗa maka labarinsu:
Kaddara Ta Rigayi Dabara
An yi wani babban Sarki da ake kira Ibrahimu wanda ya kasance ƙarƙashinsa akwai sarakuna da dama da suke masa biyayya. Yana da runduna da yawa waɗanda duk garin da suka hara da yaƙi sai sun ga bayansa. To amma duk da kasancewarsa babban Sarki mai faɗa a ji, ya kasance ba shi da magaji, walau mace ko kuwa namiji. Wannan abu na matuƙar ƙona masa zuciya musamman idan ya tuna cewa dukan abin da ya mallaka fa ya zama iska ke nan, zai tafi baitulmali, mulkin kuma wani ya samu wanda ba jininsa ba. Ya nemi auren ‘ya’yan sarakuna da na talakawa da dama, har ya daina aure – auren ya koma sayen kuyangi yana sa su ɗaka domin kwaɗayin samun magaji.
Allah da ikonsa kuwa sai wata kuyangarsa ta samu ciki, Sarki ya yi ta murna ya sa aka riƙa kula da ita ana ba ta magani da abinci iri – iri. Yayin da watan haihuwarta ya matso, sai Sarki ya sa a ƙara kula da ita, ya kirayi masana ilmin taurari da masu bugun ƙasa suka riƙa duba masa halin da take ciki. Da lokacin haihuwar ya zo, aka zauna ana jiran zuwan jariri. Bayan wani lokaci sai kuyangar ta haihu. Ta samu ɗa namiji kuwa. Sarki ya cika da matuƙar farin ciki, ya sa aka buga masa taurari domin su gano sha’anin rayuwar yaron a duniya.
Malamai suka duƙa suna haɗa alƙaluma suna tattaunawa tsakaninsu. Bayan wani lokaci babbansu ya duƙa gaban Sarki ya ce, “Allah ya ba ka nasara, hangen gaba ba shi da amfani, ya fi kyau a bar kaza cikin gashinta.” Sarki ya ce, “ku faɗa min ko mene ne babu komai.” Suka ce, “Ranka ya daɗe muna tsoron rayukanmu bisa ga abin da muka hango.” Sarki ya ce, “na yi muku alƙawarin ba zan muku komai ba komai rashin daɗin bayanin.”
Bayan sun gamsu da kuɓutar rayukansu sai babban ya sake duƙawa ya ce, “abin da muka gano shi ne, bayan shekara bakwai ɗanka zai gamu da tsautsayi na harin zaki zai kashe shi, amma idan ya kuɓuta daga harin to nan gaba zai zama sanadin mutuwar ka.”
Da Sarki ya ji haka, sai yanayinsa ya sauya. Ƙirjinsa ya ƙuntata. Duk da haka ya kanne kamar bai ji zafin komai ba, ya ɗebo kyauta ya ba wa malaman ya sallame su. A ransa ya shirya yadda zai kauce wa faruwar wannan al’amari kamar yadda aka ce masa zai faru. A kullum ya tashi sai ya ji maganar na damun sa duk da cewa a karon farko ya ƙaryata malaman. Bayan an yaye yaron sai ya sa aka gina wani gida a can saman dutse, ya hana kowa zuwa wajensa daga shi sai mai rainon sa. Duk mako yake sawa a kai musu abubuwan da suke buƙata na daga abinci da sutura da sauran kayayyaki. Shi kuma Sarki ba ya zuwa sai bayan wata guda, sai a maƙala tsani ya taka ya hau, a kawo masa yaron ya yi masa wasa yana daga kan tsanin, sannan ya sauka.
Hashim ɗan Sarki Ibrahim ya riƙa girma, yana ƙara wayo yana fahimtar al’amura. Sannu a hankali har tsoron nan ya fita daga ran mahaifinsa, ya sakankance maganar nan da aka faɗa game da ɗansa duk shifcin gizo ne. A lokacin kuwa shekararsa bakwai a duniya, saura wata ɗaya ya cike shekara ta takwas. Sarki ya ƙudure cewa zai dawo da ɗansa gida da zarar ya cika shekara takwas, domin hasashen da aka yi kansa bai tabbata ba.
Da yake ƙaddara ta rigayi dabara, a wannan daren sai wasu mafarauta suka raraki wani zaki. Suka yi masa rauni a allon kafaɗarsa na dama da kibiya. Ya ji zafin harbin sosai, amma ya jure ya gudu domin neman mafaka. Mafarautan nan suka bi shi da gudu, sai ya tsere musu ta hanyar faɗa wa gidan nan da ake kula da Hashim ɗan Sarki Ibrahim. Yana shiga ya yi arba da Hashim yana wasa. Ya daka tsalle kansa ya yakushe shi a kafaɗa. Yaro ya ƙwalla ƙara mai firgitarwa ya faɗi sumamme. Uwar goyonsa na ciki ta ji ƙararsa, ta fito da gudu a gigice, zaki na ganinta ya ƙyale yaro ya daka tsalle ya banke ta. Nan take ta faɗi matacciya ko shurawa bata yi ba. Masu farauta suka iso wurin suka tarar da yaro kwance magashiyyan ga zakin ya kashe wata yana cin namanta. Yana ganin su ya yi gurnani ya juyo kansu a fusace. Nan da nan suka hau harbinsa da kibau sai da ya faɗi matacce. Suka binne ragowar naman uwar goyon Hashim, shi kuma suka tafi da shi tare da mushen zaki zuwa garinsu. Sai da suka gyara masa raunin da ya zakin ya ji masa a kafaɗa sannan ya farfaɗo, inda ya tsinci kansa a wani wuri dabam.
Haka dai Hashim ya zauna a wurin mafarautan nan waɗanda ba farauta kaɗai suke yi ba, suna yin noma da kiwo, wani lokacin kuma suna fita hanya su yi fashi su koma ƙauyukansu kamar ba su aikata komai ba. Yana nan wurinsu har ya kai shekara goma sha biyu. Ya koyi hawa doki da sukuwa da jefa mashi da wasa da takobi, da harbi da kibiya, sannan ya soma fita farauta da tare hanya tare da mariƙansa.
Wata rana suka fita farauta ba su kamo komai ba, sai suka wuce kan hanya domin tsare hanyar fatake. Nan ma ba su samu nasara ba, domin kuwa ayarin da suka gamu da su jarumai ne, suka auka musu da yaƙi suna sara da sukan su, har suka karkashe su baki ɗaya. Hashim ne kaɗai ya rage wanda shi ma ba su lura da shi ba ne amma sun yi masa rauni mai yawa. Bai samu kansa ba sai da sanyin asuba ya doke shi, ya tashi ya ga cewa shi kaɗai ne ya rage cikin mutanensa. Ya rarrafa ya tafi bai san inda za shi ba. A hanya ya gamu da wani mutum, ya tambaye shi abin da ya same shi. Ya faɗa masa komai daga farko har ƙarshe. Da mutumin ya ji zancensa sai ya tausaya masa, ya ɗora shi kan jakinsa ya tafi da shi garinsu ya yi ta jinyarsa har ya warke. To shi mutumin nan aikinsa shi ne tono ma’adinan ƙarƙashin ƙasa yana kaiwa garuruwa masu nisa yana sayarwa.
Da ya lura Hashim ya warware, ƙarfinsa ya dawo masa, sai ya rarrashe shi kan ya riƙa bin sa suna harkar tonon tare. Hashim ya amince suka tafi da jakuna biyu zuwa cikin ƙungurmin daji, sai da suka shafe kwana biyu a dajin sannan suka samu wurin da suke buƙata. Wani waje ne a tsakanin duwatsu inda suka sami wata rijiya take zururu amma babu ruwa a cikinta. Bayan ya yi ‘yan karance – karancensa sai ya zura igiya da guga cikin rijiyar, sannan ya ɗaura wa Hashim igiyar, ya zura shi cikin ramin. Da farko ramin ya kasance mai zafin gaske, har iska na ƙoƙarin wuyata ga numfashinsa. Amma a can ƙasa sai ya zamana da yalwa da iska mai daɗi tana huro masa ta ko’ina. A gefe guda kuma wasu irin duwatsu ne masu daraja manya – manya. Yaro ya riƙa ɗiba yana cikawa a guga mutumin yana ja yana juyewa a mangalar jakuna. Da ya cika managalolin ya ga sun ishe shi sai ya turo igiyar cikin ramin, ya yi tafiyarsa ba tare da ya fito da Hashim ba.
Da ya fahimci abin da mutumin ya aikata masa, sai baƙin ciki ya kama shi ya yi ta kuka yana cewa, “na kuɓuta daga halakar zaki, na tsira daga sharrin mahara amma ga shi nan zan mutu cikin rami a wofi, babu wanda ya damu da ni.” Daga bisani dai da ya fahimci kuka ba zai masa magani ba, sai ya miƙa al’amarinsa ga Allah mai girma. Ya sa hannunsa yana cire duwatsun nan masu daraja yana ajiyewa. Kwamfa yana wannan aikin da zummar ko zai samu wata ƙofa da za ta fitar da shi, ashe a jikin wajen kogi ne. Nan take ruwa ya shigo da ƙarfinsa. Ya yi awon gaba da shi inda ya riƙa buga jikinsa da sassan garun duwatsu, ya jefa shi can wani wuri a waje a sume. Haka ya kasance a yashe har kwana sannan ya farfaɗo. Ya tashi ya ci gaba da tafiya bai san inda ya nufa ba. Bai jima ba ya isa wani ɗan ƙauye a galabaice, suka rirriƙe shi, suka kwantar da shi, suka yi ta ba shi magani suna lura da shi har ya samu kansa. Bayan ya warke suka tambaye shi labarinsa ya ba su. Suka yi ta mamaki, musamman irin haɗurran da ya tsallake a rayuwarsa. Daga nan suka tambaye shi mahaifinsa ya ce musu, “iyakar sanina da shi yana zuwa gare ni lokacin da ina saman dutse, amma ba zan iya shaida shi ba.” Mutanen garin nan suka so shi sosai musamman da suka gane irin jarumtakarsa da kuzarinsa a wurin farauta.
Game da Sarki Ibrahim kuwa, yayin da gari ya waye, ya tafi domin ya ɗauko ɗansa, aka sa masa tsani kamar yadda aka saba. Ya hau ya yi kiran matar nan amma ya ji shiru bata amsa ba. Ya sake kira bai ji motsin komai ba, sai ya sa aka shiga ciki. Babu kowa sai dai ga jini nan ko ina faca – faca babu kyawun gani. Mai dubawa ya dawo ya faɗa masa. Sarki ya shiga da kansa ya gani. Ya sauko yana mai baƙin ciki. Ya tafi wurin masu binciken taurari suka duba. Suka ce masa, “zaki ne ya cinye su kai kuma ka kuɓuta daga mutuwa ta dalilinsa. Da ma haka aka ƙaddaro babu makawa. Kuma bincikenmu ya nuna cewa sai da zakin ya raunata shi a kafaɗa kafin ya kashe shi.” Sarki ya zauna yana mai baƙin ciki da mutuwar ɗansa. Aka yi makoki na mako guda sannan aka watse, aka manta da wannan abu.
Hashim kuwa ya girma sosai a wajen mutanen ƙauyen nan har ya balaga ya isa munzalin mutum. Ya zamana duk wani abu da za a yi na gangami da nuna jaruntaka shi ne a kan gaba. Wata rana wasu ‘yan fashi suka je birni suka yi ɓarna sannan suka taho da wani babban attajiri. A hanya suka kashe shi, suka jefar da gawarsa a wannan ƙauyen da Hashim yake. Sarki Ibrahim ya aiko da wasu dakarunsa domin su ƙwato wannan attajiri. Da suka iso ƙauyen nan sai suka tarar da gawarsa, lokacin kuwa alfijir na daf da ketowa, jama’ar ƙauyen ba su san abin da ke wakana ba.
Ba tare da bin bahasi ba dakarun nan suka yanke hukuncin cewa ɓarayin a wannan ƙauyen suke. Suka shiga kisan mutane suna ƙona gidaje, suna lalata dukiya. Hashim da abokansa masu tsaron gari suka ji labari, nan fa suka yi shirin yaƙi suka gamu da dakarun Sarki suka yi musu fata – fata. Babu wanda ya tsira sai mutum biyu da suka kai labari shajara – majara. Sarki ya fusata ƙwarai da wannan aika – aika. Nan da nan ya yi shiri da kansa ya tafi zuwa ƙauyen da dukan askarawansa. Hashim na cikin matasan da suka nuna jarumtaka ƙwarai da gaske, domin kuwa shi ya taɓe kwari da baka ya harbi Sarki a gadon baya.
A ƙarshe dai aka kame dukan mutanen garin aka tafi da su. Harbin da aka yi wa Sarki ya yi masa rauni mai yawa. Duk da an yi masa magani amma raunin na ƙara yi masa ciwo ƙwarai. Ya aika aka zo da masu bugun ƙasa ya ce musu, “kun ce mutuwata na hannun ɗan da na haifa na cikina. Kuma kun sani a halin yanzu ba ni da magaji. Yaya aka yi mutuwar kuma ta faɗo hannun ɓarayi?” Suka ce, “wannan kam yana daga hukuncin Allah wanda bugun ƙasa bai isa ya gane komai kan haka ba. Amma iyakacin nazarinmu shi ne mutuwarka na da musabbabi daga ɗan da ka haifa.” Sarki ya ce, “a yadda nake ji a raina, wannan ciwon ba mai warkewa gare ni ba ne. A zo min da ɓarayin nan duka.” Aka shigo da mutanen ƙauyen nan dukansu a ɗaɗɗaure.
Sarki ya ce musu, “ina so ku faɗa min gaskiya babu ɓoyewa, a cikinku wane ne ya harbe ni da kibiya?” Gaba ɗaya suka nuna Hashim. Aka matso da shi gaba ga Sarki. Duk da ya yi baƙi, kammaninsa na asali kusan sun ɓace amma sai da Sarki ya ji wani irin abu game da shi. Ya ce masa, “wane ne mahaifinka? Ka faɗa min gaskiya, ni kuma na yi alƙawarin yafe maka laifinka.”
Hashim ya ce, “bisa gaskiya ya shugabana, ban san mahaifina ba, domin kuwa a gidan saman dutse na girma har na yi wayo. Daga bisani zaki ya kashe mai raino na, na shiga hannun wasu mutane.” Ya ba shi labarinsa kaf, tun daga farko har ƙarshe. Sarki na jin wannan labari sai ya yi kururuwa ya ce, “wallahi wannan shi ne ɗana!” Mutane suka dube shi da mamaki, shi kuwa ya ce da Hashim, “yaye kafaɗarka mu gani.” Ya yaye sai ga tabon inda zaki ya raunata shi, ya yi daidai da yadda masu bugun ƙasa suka shaida masa.
Sarki ya aika aka zo da kuyangarsa wadda ta haifi Hashim, tana ganin sa ta shaida shi, ta rungume shi tana kuka tana cewa, “dama ban fidda ran zan sake ganin ka ba. Yau ga shi Allah ya haɗa mu.” Da wannan Sarki ya haƙiƙance ɗansa ne. Ya aika aka kirawo dukan manyan fada da attajirai da masu bugun ƙasa da talakawa. Ya ce da su, “ku sani Allah ya rubuta ƙaddara ta rigayi dabara wala fata. Yadda Allah ya tsara babu makawa sai ya tabbata. Komai dabarar mutum bai isa ya kauce mata ba. Kasancewar an ƙaddaro dalilin mutuwata na hannun ɗan da na haifa, to ga shi bisa hukuncin Allah hakan ya tabbata. Amma ku sani na yafe wa ɗana bisa aikin da ya yi bisa kaina cikin rashin sani. Kuma na gode wa Allah da zan bar duniya a cikin gidana gaban jama’ata ba a wani waje da za a mance da ni ba.” Da ya kawo nan sai ya cire kambin sarauta ya ɗora wa Hashim, ya ce, “daga yau na mayar da ɗana ya zama Sarki gare ku.” Jama’a duka suka ce, “mun yi biyayya!” Hashim kuwa sai kuka yake yi bai samu bakin magana ba.
Sarki Ibrahim ya kwanta jinya, ɗansa na kula da shi, a kullum yana wajensa. Shi kuma ba abin da yake masa sai nasiha game da al’amarin sarauta da sha’anin jama’a. Bayan kwanaki tara Allah ya karɓi ran Sarki Ibrahimu. Hashim ya miƙe ƙafa a matsayin Sarki, ya mulki jama’a bisa gaskiya da adalci.”
Yaro ya ci gaba da cewa, “to ka gani ya Sarki, idan Allah ya ƙaddara bisa goshina cewa kai ne ajalina, to babu makawa komai wayona da dabarata ko ƙarfina, ban isa na guje maka ba. Ballantana ma ni da yanzu nake hannunka, sai yadda ka yi da ni. Amma ka sani aiki bisa adalci da daidaito shi ne sirrin tabbatar al’umma cikin mulkinsu.”
Da Sarki ya ji wannan labari sai zuciyarsa ta kaɗa ya shiga ruɗani. Ya yi shiru yana tunani. Can an jima ya ce, “ku mayar da shi kurkuku, yanzu dare ya kawo jiki, sai gobe ma duba al’amarinsa. Nufina na aikata masa mummunan kisa, ta yadda zai zama darasi ga masu surutu irinsa, su gane cewa hujja dabam labari dabam.”