Tsaki ta ja, a karo na ba adadi, na yanzun yafi duka sauran tsayi da kuma fito da asalin takaicin daya cunkushe mata zuciya, tana duba takalminta daya tsinke, saboda duwatsin da yake hanyar, ga wani tudu da sauka, sunyi tafiya kenan ta kusan ta minti talatin daga inda mashina suka saukesu, amman ita banda fili bata ganin komai
"Yanzun haka zan taka duwatsun nan babu takalmi kome kike nufi?"
Ta tambaya kamar zata kaiwa Uwani duka saboda bacin rai
"Tun dazun kike mun masifa kamar bake kikace in rakoki ba, Asabe in kin fasa ne mu juya, amman ni. . .
HasbunAllahu wa ni’imal wakeel 😭 Allah ka rabamu da muguwar zuciya, asabe anyi tafiyar zomo kasuwa. Allah ya yafe miki kurakuran ki ya gafarta wa iyayenki
Allah ka yaye mana son zuciya
Allah ya kara mana imani.
Dagaske na tsorata
Ke Duniya ina zaki damu rayuwa baki da tabbas ya Allah ikon iya tanƙwara zukatan mu ka tsaremu da sharrin zuciya
Gsky babin nan ya taɓa ni ya tuna min da nima ina zaman jiran tawa mutuwar Allah kasa mu cika da kyau da imani