Girarta a hade take kallon wayar data sauke daga kunnenta, tsadaddiyar wayar da Alhaji Danladi ya siya mata, haka ya kawo mata ita a kwalinta saboda yace ya gaji da ganin ta hannunta. Ita kuma ta mikawa Jidda tsohuwar. Har yau kwana biyu, sai dai Jidda ta dauko wayar ta shafa, ta sake bude jakar kayanta ta mayar, kamar ta kasa yarda cewa ta mallaketa, kamar kuma idan ta fito da ita da sunan zatayi amfani, Sa'adatu zata iya canza shawara ta karbe abinta. Ga kuma Abida da bata aminta da kyautar ba, ba rike wayar da Jidda zatayi. . .
masha Allah
muna godiya
Allah sa zamuga karshen sa kusa
I love your books and love reading hausa novels because they interesting 🧐