Skip to content
Part 15 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Girarta a hade take kallon wayar data sauke daga kunnenta, tsadaddiyar wayar da Alhaji Danladi ya siya mata, haka ya kawo mata ita a kwalinta saboda yace ya gaji da ganin ta hannunta. Ita kuma ta mikawa Jidda tsohuwar. Har yau kwana biyu, sai dai Jidda ta dauko wayar ta shafa, ta sake bude jakar kayanta ta mayar, kamar ta kasa yarda cewa ta mallaketa, kamar kuma idan ta fito da ita da sunan zatayi amfani, Sa’adatu zata iya canza shawara ta karbe abinta. Ga kuma Abida da bata aminta da kyautar ba, ba rike wayar da Jidda zatayi bane matsalarta, akwai yarda mai girma a tsakaninta da yaranta, Alhaji Danladi ne bai kwanta mata ba, duk kuwa da a iya binciken Abdallah, ba’ace yana da wani mugun hali daya wuce budurwar zuciya ba. Tun Uwargidan shi, mata ta biyu, ta uku da ta hudun daya aura duka yara ne da ya ba shekaru masu yawan gaske. Dan ta biyun ma ance sanda ya aureta da wahala inta cika shekara goma sha biyar, a yaranshi na wajen uwargidan akwai wanda suka girme mata.

Yanzun da Allah yayiwa uwargidan rasuwa, duka fadin Kano da kewayenta, idanuwanshi sai ya sauka akan Sa’adatu. Gashi ta kafe, duk wata shawara da ake bata tasa kafa ta shure, tun Abida na fada harta koma nasiha, duka sunki aiki, da ta nemi ta kara hadata da Abdallah sai yace mata

“Nayi mata magana Amma, tace har makaranta zai mayar da ita, tace mun duk wani abu da take buri zata same shi a auren Alhaji Danladi, idan kuma ina da wani wanda zai maye mata gurbin shi in kawo, ba zataki amsar shi ba…bani da kowa Amma, bani da kowa da zan kawo mata, idan ma ina dashi aurenta da Yaa Tahir ya gama raunana duk wata yardata akan mutane…”

Data rasa tudun dafawa sai ta wanke kafarta ta nufi gidan Anty Khadi, ta kwashe komai ta fada mata. Ita kanta da alama lamarin ya girgizata, a ganinta akwai cutuwa a irin wannan auren, da kuruciyarta da komai sai ta fadawa tsoho, a ganin Anty Khadi, aiko Abida ce tazo da batun auren mutum kamar Alhaji Danladin ace ta sake dubawa ta samo mai dan kwari-kwari, ba wanda zata shafe sauran shekarunta cikin jinyar tsufa ba. Ashe duk labarin da takeji kan tsofaffi irin shi masu budurwar zuciya, kaddara na gefe tana ce mata zata shaida da idanuwanta, itace dai bata taba hasaso hakan ba.

“Kinsan kafiya irinta Sa’adatu, rayuka ne zasu baci sosai akan maganar nan, sai dai kawai mu dage da addu’a Allah ya zaba abinda yafi alkhairi…”

Kwalla kawai Abida ta share, banda.

“Hmm…”

Ta kasa kwato komai, nan ta wuni suna kara tattaunawa da Anty Khadi din, itace ma ta bata shawarar ko zataje ta samu su Anty Talatu ta fada musu, ko ba komai daga bangarensu za’a karbi auren, idan suka kara nusar da Sa’adatu illar da zatayiwa rayuwarta, watakila taji tasu maganar, daga nan kuwa da Abida ta hau adaidaita sahu sai tayi gidan Anty Talatu, ta samu dawowarta kenan itama daga wajen barka, haka suka gaisa cikin mutunci kafin Abida ta fada mata abinda ake ciki

“In banda abinki Abida, idan ba irin shi Alhaji Danladin ba waye kike tunanin zai aure Sa’adatu? Badan mutuwar Asabe ba da kuma shegen surutu irin na kawarta kina tunanin ko mu dangin Sa’adatu na kusa ba zamu dora ayar tambaya akan dalilin da zaisa miji yayi mata saki har uku washegarin daren farkon su ba?”

Wani abu ya daki kirjin Abida da maganar Anty Talatu ta karshe, har saida ta daga ido ta kalleta. Idan ba son zuciya ba, ai ko a cikin unguwa babu wanda zaiyiwa yaranta shaidar halin banza, balle har akai ga tunaninsu ya hau wannan bigiren

“Cikin dalilan da zasu saka ayiwa mace irin sakin da Tahir yayiwa Sa’adatu kinsan duka zasu iya zama dalilin da zataki auruwa. Ko yanzun din waye za’acewa ai uwar yaron ce tayi musu farraqu ya yarda? Auren kwana daya? Ai mu godewa Allah…inace shi Alhaji Danladin da kudin shi?”

Ai Abida batama iya dora komai ba, tayi mata sallama kawai ta koma gida. Da dare yayi taga ta kasa bacci sai ta rayashi da salloli tana nemarwa Sa’adatu zabin abinda yafi alkhairi. Amman zuciyarta sam taki natsuwa da wannan auren. Amira ma ca tayi.

“To Amma ita Sa’adatun nawa take da zatace ba’a isa da ita ba? Tsayawa za’ayi a biye mata? Kibari zan kirata.”

Kiran nata kuwa tayi

“Tunda ni nace naji nagani ba sai abarni da zabina ba Yaa Amira? Da kuka kawo mazajenku Abba ya tabbatar basu da wani mugun hali ba aura muku su yayi ba? Ko yace baku da hankalin da zaku zabama rayuwarku abinda ya dace?”

Tanajin numfarfashin bacin ran da Amiran takeyi ta cikin wayar

“Rashin kunya zakiyi mun Sa’adatu?”

Kai ta girgiza

“Ni ba rashin kunya nake miki ba, so nake ki gane Alhaji Danladi nake so, da tsufan shi da komai, ku bini da fatan alkhairi ko ku zare hannayenku daga kaina kubarni da zabina”

Ta karasa tana sauke wayar daga kunnenta ta kashe. Ranta idan yayi dubu ya baci, akan wanne dalili zasu dinga mata haka? Shi saurayin me zai tsinana mata? Ina ma ta ganshi? Kamar suna manta ita ba budurwa bace ba yanzun, a layin zawara za’a sakata, zawaran da kaddarar aurensu na farko zai iya zame musu katanga da sakeyin wani. Ba zata yaudari kanta bama, ko taso saurayin tasan yayi mata nisa, kuma yanzun bata soyayya takeyi ba tunda ta dawo hayyacinta.

“Matar Yayaa nifa na bar muku soyayya, hankalina kuma ya koma kan kudi.”

Ta cewa Fa’iza itama da tazo mata da wani zance, sai da Fa’izar tayi dariya sosai kuwa.

“Wato hankalinki ya koma kan kudi.”

Itama dariyar tayi

“Kudi ai abin sone Matar Yayaa, tun kafin in shiga cikinsu baki ga yanda na canza ba, dan Allah kamshin da nake badawa idan na wuce kawai baya burgeki?”

Dariya suka sakeyi tare

“Hajiya Sa’adatu…”

Ita kuwa tayi far da idanuwa

“Jakarki ta tsaraba daban zanyo miki”

Dan a cikin alkawurran da Alhaji Danladi yayi mata harda kujerar Makka, yace da an fara biya zai biya musu tare, dole suje ya godewa Allah daya bashi kyautarta. Wasu kalaman nashi tun suna bata kunya, harma ta fara sakewa tana biye mata yanzun, musamman ma da in dai zaiji dadin kalaman sai yayi mata wata babbar kyauta. Ta kula shekarun ne kawai, amman juya shi ba zai mata wahala ba. Hankalinta bai kwanta ba sai da taga ya aiko tambayar aurenta, an kuma ce an bashi, in dai Abida ce tasan zata huce idan taga da gaske auren babu fashi. Ga Alhaji Danladi ya sakar mata bakin aljihun shi sosai yanzun, abinda duk tace tana so sai ya siya mata, kudi bata da matsalarsu, shagali kawai takeyi. Tayi dinkuna sababbi sunfi a kirga, haka tayiwa Jidda itama, tunda bata ga fuska a wajen Abida ba balle tace zatayi mata.

Yau dinma shiri ta gamayi tace wa Abida zataje ta karbo wasu dinkunanta da ta bayar

“Allah ya tsare”

Abida tace tana cigaba da ninkin kayan da takeyi, jiki a sanyaye ta baro dakin Abidar, yanzun kuma wannan shariyar ta Abida ta fara damunta, ko hira sukeyi da Fa’iza idan ta tsoma baki sai Abidar tayi shiru, zaman gidan ya fara isarta. Ga Alhaji Danladi yayi tafiya Abuja, yace sati biyu zaiyi, yana dawowa sai a tsayar da lokacin aurensu, ba za’a saka ya wuce wata biyu ba, bangaren da zata zauna kawai ake dan kara gyarawa, shi baya son komai, har kayan daki shine zaiyi, ita kadai yake so akai masa. Gara yayi ya dawo ko a daura auren tabarwa Abida gidan kowa ya huta. Tana sako kafafuwanta kofar gida taji kamar iska ta mayar da ita baya, jinta ya dan dauke na wucin gadi, akwai sauran hasken rana tunda yammace, hasken dai data gani ya gilma mata irin na an kunna fitila ne a cikin duhu.

Rabon da taji zafin mari irin wannan tun wani da Maryam ta tabayi mata, shima dan Maryam din bahagguwa ce, kuma irin cikin rashin tsammani tayi mata shi tunda lokacin fadan ma bada Maryam din takeyin shi ba, yanzun dai kafin ta gama wartsakewa taji an shako wuyan riganta ana jijjigata

“Sa’adatu ko?”

Sai lokacin ta samu ta kalli matar, fara sol da ita, fuskar nan kamar ana wankewa da madara, tayi kyau harta gaji cikin doguwar abayarta, ko da Sa’adatu bata taba ganin zinari ba, tasan shine a kunne da wuyan matar nan, dankareren zinari ma

“Wanne tsautsayi ya gifta dake ta gaban mijina?”

Tayi maganar tana janta zuwa cikin gidan hadi da watsar da ita a tsakar gida kamar kayan wanki. Itace matar Alhaji Danladi ta uku, ko ace ta biyu a yanzun, itace tafi kowa zafin kishi da kuma buri akan dukiyar shi, lokacin daya karo aure bata waye haka ba, burinta bai karu ba. Gashi tunda tazo gidan yara biyu ta haifa mata. Ana kawo mata amarya harta haifi namiji, shisa tayi asiri da aka juye mahaifar amaryar dama ta dayar matar duk ta tsaida musu haihuwar, Uwargida ta rigada ta shammaceta tunda ta zuba kwayaye kafin shigowarta, amman tabbas lissafin dukiyar Alhaji Danladi zai tsaya iya sune, ita da take shirin yanda zatayi ya fara mallaka mata dukiyar shi a hankali a hankali kafin sauran su farga, sai yace zai maida mata hannun agogo baya ta hanyar jajibo wani aure?

Yanzun da Bokanta bai buga kasa ya hango mata auren nan ba ai da an shammaceta. Shiya fada mata akwai hasken dake kewaye da yarinyar, zai wahala jifa daga nesa ya kamata, kuma ma ba zatayi asarar makudan kudade akan Sa’adatun bane, saita fara zuwa tayi musu barazana ita da iyayenta, ta dai bayar a kauda hankalin Alhaji daga kanta

“Ba dake zanyi ba, ina uwarki?”

Hajiya Baturiya kamar yanda ake kiranta ta fadi cikin daga muryar daya fito da Abida daga daki babu shiri

“Kece uwarta?”

Kallonta kawai Abida takeyi, harta karasa tana tabata

“Na tabaki da alheri baiwar Allah, ba jimawa zanyi ba, gargadi dai nazo inyi miki, idan har kina son rayuwae ‘yarki, kina kuma son zaman lafiya, to kiyi mata magana ta fita harkar mijina. Wallahi har zaman garin Kano zan iya sakawa ya gagareku…”

Tana karasawa ta juya ta fice, banda bari babu abinda jikin Abida yakeyi

“Kingani ko Sa’adatu? Da nace miki babu komai tare da masu kudin nan banda tashin hankali baki yarda ba ai…”

Sa’adatu kuwa banda hawaye babu abinda yake zubo mata, bama na zafin marin da Hajiya Baturiya tayi mata ba, maganganunta da suke nuna kamar so takeyi ta rabata da Alhaji Danladi, tayi mata bakin cikin shiga tarin daular daya haska mata. Har Abida ta kamata ta shigar da ita daki kuka takeyi, duk wata nasiha ba karasawa kunnenta takeyi ba. Fa’iza bata gidan, taje kitso lokacin da abin ya faru, data dawo Abida take fada mata, ita kanta saida ta tsorata

“Allah ya karemu ya shiga tsakanin nagari da mugu”

Taketa maimaitawa, nan suka hadu sunata ba Sa’adatu baki, amman taki daina kuka. Zuciyarta kuma tanata kara karfafarta akan ta dage, barazana ce kawai, data samu ta shiga gidan Alhaji Salihu shikenan, sai dai kamar wata almara, haka ta dinga kiranshi baya dagawa, karshe ma sai ta daina samun shi gabaki daya. Ta gane ya rufe layinta ne saboda ta gwada kiranshi da sabon layin Jidda ta shiga, bai dai daga bane ba. Tayi kuka sosai, ta tsinewa Hajiya Baturiya yafi a kirga. Balle da kudaden data samu a hannun shi suka gama karewa, fiye da rabi tayi dinkuna dasu, dan kayan dadin da bakinta ya fara sabawa dasu suka yanke, sai wani irin kunci na daban ya mamayeta. Tana ganin murna a fuskokin Abida da Abdallah, tunda ba auren suke so ba. Anty Talatu ce kawai tazo har gida tayi mata jaje, ita kadai kuma ta tayata jimamin rasa Alhaji Danladi

“Daman matan masu kudin nan ai sun kwashe kayansu daga gaban Ma’aiki, sufa suna cikin daula, amman mugayen yan bakin ciki ne, ko kadan basa son suga wani ya rabo ya dangwali arziki…kici gaba da addu’a tunda Allah yayi ke din mai kashin arziki ce, In shaa Allah sai kin samu wani hamshakin dayafi Alhaji Danladi”

Amin dinta a fili ta furtata babu ko kunya, dan kuwa hamshakin take buri, Alhaji Danladi kuma ya haska mata wata rayuwa da zata jima tana aunawa da duk wani wanda zai sake zuwa mata da sunan soyayya ko kuma da tayin aure ma gabaki daya. A cikin wannan dan tsukin da komai ya hade matane ta samu Abida da fadin

“Ni makaranta nake son komawa Amma…”

Kallonta Abida tayi

“In ba shekaruna zan zabtare in siyar da wasu ba ina naga halin daukar dawainiyar komawarki makaranta Sa’adatu?”

Anzo dai-dai wajen da take so, dan tunda suka dawo unguwar, gida daya take dan shiga, yarinyar gidan Haulatu da zasuyi sa’anni da Sa’adatu kuma itama tana dan shigowa jefi-jefi. Suma marayune da suke fadi tashi da mahaifiyarsu, sai dai ba kamar su Sa’adatu ba, su gidan da suke ciki nasu ne, ba su da tashin hankali tunanin kudin haya. Abida ma bata damu da kawancen nasu Sa’adatu ba, saboda mahaifiyarsu Haulatu da ake kira Maman Kamal, tana da kirki sosai, tsaye take kan yaranta, zumunci sukeyi sosai

“Sai inyi aiki in tara kudin, amman zaman hakan ya isheni, ni ba auren ba kuma ace ba karatun…tunda jarabawata tayi kyau”

Da mamaki karara a fuskar Abida take kallonta

“Aiki kuma? Wanne irin aiki”

Zama Sa’adatu ta gyara, a wajen Haulatu ta samu wannan dabarar, don ita Haulatun dama yayyenta da sukayi aure, aikatau sukeyi a gidajen masu kudi, tace wata kawar Mamansu ce take samo musu, da yake sana’ar da takeyi kenan, inda Haulatun take yanzun ana biyanta dubu talatin ne a wata, kuma da yake akwai sanayya, sai bata karbar komai a cikin kudin, gashi ita gidan da take tayi sa’a basu da matsala, ita daga safe ne zuwa yamma takeyi, can zataci abincin safe, taci na rana, harma wata rana su bata ta taho dashi gida

“Ai kinga irin abincin dana dawo dashi rannan, wallahi ko kaji sukaci nima ina da kaso, ke ko banma san anzo da abu ba, sai kiga an kirani an bani…kema idan kina so wallahi da nayiwa Mama magana za’a samo miki, yafi miki wannan zaman…”

Haulatu tace mata adashi takeyi na dubu sha biyar, sauran kuma sai su kara a hidimar gida, ko yanzun duka kayan kitchen na alfarma an gama sai mata, ko yayyenta da haka suka tara kudin kayan dakinsu. To ita Sa’adatu bama ta kayan daki takeyi ba, dan burinta ta samu mijin da zaice ya dauke musu duk wannan. Yanzun dai taji dadi a bakinta, tayi kananun hidindimunta, kuma in da hali ta koma makaranta, ko da bata samu mijin aure ba, da karatun saita samu wani aikin ta tsaya da kafafuwanta

“Kinga Haulatu tanayin abincine a wani gida da su shara haka, suna biyanta, tace idan inaso nima sai a samo mun…albashi…”

Bata karasa ba Abida ta katseta

“Ba girki ba, aikatau zakice Sa’adatu, aikatau takeyi a gidan masu kudi…”

A hankali Sa’adatu ta daga mata kai, sosai Abida take kallonta tana son tabbatar da cikin hayyacinta take. Ita bata da matsala da aikatau, duk da da yawa suna kallon abin a matsayin aiki mafi kaskanci, a wajen Abida sana’ace halastacciya kamar kowacce sana’a, wanda kuma duk kagani yanayi halalin shi yake nema, kudin da zai rufawa kanshi asiri yake nema. Bata kuma taba kallon masu aikatau da wata fuska ba, ko ita da ace bata da wata sana’a lokacin da Habibu ya rasu, idan ta samu aikatau din zatayi, ko dan kar yaranta su zauna da yunwa.

“Ke zaki iya aiki a karkashin wani? A sakaki shara, a sakaki wanke-wanke da wankin bayi…”

Ta sake tambaya tana yar dariya saboda ko ita idan ta saka Sa’adatu wani aikin da bai kwanta mata ba sai tasan yanda tayi ta zame sukayi musaya da wani. Kai Sa’adatu ta sake daga mata, dariya Abida takeyi sosai, saboda idan ta hango Sa’adatu a matsayin yar aiki a karkashin wani, ana bata umarni sai abin ya sake bata dariya, bata da matsala da aikatau tabbas, ko da tana da matsala dashi ma ba zai dameta ba tunda Sa’adatu ce tace zatayi, tasan ko kwana biyu ba zatayi a gidan aikin nan ba gayyar zata watse, idan su basu korota bama ita zata dawo da kanta

“Waye yake samo aikin?”

Sa’adatu mamakin da takeyi ya hana taji haushin dariyar da Abida takeyi mata, ko kadan bata hango abubuwa zasu zo mata da sauki haka ba

“Kawar Maman su Haulatu, ita take samo musu”

Kai Abida ta jinjina da murmushi a fuskarta har lokacin

“To zan shiga muyi magana sai ta samo miki…”

Wani sanyi ya ratsa zuciyar Sa’adatu

“Kinga Amma sai in shiga adashi nima, yanda zan dauki kudin a dunkule”

Dariya Abida ta sakeyi

“Hakane…”

Ta fadi, Sa’adatu ta mike

“Bari inje in fadawa Haulatun to, sai ta gayawa Maman yanda zasu san da zancen kafin ki shiga”

Tana fita daga gidan Abida ta fito take ba Fa’iza labari, dariya sukayi sosai. Ko Abdallah daya dawo ta bashi labari dariyar yayi

“Amma muna da kudin beli kuwa? Kinsan masu kudin nan ba kirki garesu ba, nasan halin Kanwata, karta dauko mana maganar da za’a kullemun ita…”

Dariya Abida tayi

“Aifa ni fatan alheri ne nawa, ba ita tace zata iya ba? Ai Maman Kamal din tace za’a dubo mata gidan da basu da matsala tunda tanaso, ni kawai matsalata karta sakani a kunya…an fara mutunci da mutane, ko kowa zaiyi aikatau banda Sa’adatu, son jikinta yayi yawa”

Kai Abdallah ya jinjina

“To Allah dai yasa hakan ne mafi alkhairi…bari inje muyi magana da ita”

Da farin ciki a fuskarta take bashi labari

“To banda dai daukar magana, kuma ki kula da kanki sosai, idan wani ya nemi yayi miki wata magana da bata kamata ba cikin yaran gidan, ki saka takalma ki dawo gida, kina jina?”

Kai ta daga masa

“Da adashi ma zan shiga na cewa Amma, yanzun kam na fasa naji ance sai an dauki wani kaso cikin kudin, zan dinga baka kana taramun kawai”

Kallonta yakeyi da zumudin da yake cikin muryarta

“Idan na kashe kuma fa?”

Dariya tayi

“Bakomai, ai kaine…”

Shima sai yayi dariyar yanajin kaunarta har cikin ranshi, hira suka dan karayi kafin yayi mata sallama. Ta kwanta tana bude wani littafi da Fa’iza ta tura mata tun rannan bataji walwalar zama ta karanta ba, sai da ta kara tsinewa Hajiya Baturiya, tana kuma godewa Allah, ko bakomai dai ta samu riba a soyayya da Alhaji Danladi, ko wayarta ta kalla ta isheta alfahari. Littafin ta bude mai suna Dan Adam na Rufaida Umar. Data nutsa sai taji kamar marubuciyar tasan cewa tana da shirin zuwa aikatau, shisa tayi wannan littafi

Karatun ta cigaba dayi cike da nishadi, batare da tasan kamar bude sabon shafin littafin da takeyi, haka kaddara ta bude mata wani sabon shafin da mafarin shi zai fara ne da aikatau…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.6 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 14Tsakaninmu 16 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×