Skip to content
Part 17 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

A fuskokinsu Abida take ganin mamakinsu duk safiya idan ta tashi ta shirya da nufin tafiya wajen aiki, ta san mamaki sukeyi yanda akayi bata gaji ba har yanzun

“Muje in rakaki dan inga gidan da kike aikin nan yau.”

Abdallah ya fada lokacin da yaga ta hada sati biyu, kamar shakku ya fara shigarshi akan aikin. Dariya kawai tayi tana daga masa kai, adaidaita sahu suka hau har kofar gidan, ya fito ya tsaya, sai da yaga ta shiga tukunna ya koma cikin napep din ya juya dashi. Kullum da abinci take komawa gida, wasu ranakun harda kayan marmari da lemuka na roba, kwali ko kuma gwangwani. Saboda kaf gidan babu mai kyashi hana mata duk wani abu da za’a shigo dashi. Wani lokaci sai tazo tafiya za’a dauka a bata, kuma kullum naira dubun nan sai an bata tayi kudin mota. Ta san daga Abida har Fa’iza zuwa yanzun sun dauka wannan kayan dadin da take komawa dasu ne dalilin da yasa take tashi da karsashin fita aiki kullum. A halinta na son jin dadi tabbas wannan din dalili ne mai girma, amman tafiyar da take ci daga gidan kafin ta samu abin hawa wajen komawa kadai ya isa yasa aikin ya fita daga ranta.

Balle kuma azo batun tarin wanke-wanken gidan, kullum kamar mutanen karuwa sukeyi, yawansu da take gani duk rana yasa ta daina mamakin girman gidan da yawan dakunan yanzun. Girkin gidan kuwa wasu a cikin ‘yan matan da kuma masu aiki har guda uku ake haduwa ayi, harma da Hajiya Hasina wata rana, itama idan ta gama nata aikin, in har ta shiga kitchen din, daya a cikin yaran suna nan, to basa rasa wani abin da zasu saka ta kama musu. A yan satikan da tayi ta kula duk ranakun juma’a gidan yafi cika, wata irin cika harda kananun yara da a hasashenta take tunanin jikokin gidan ne. Sai dai duk shige da ficen da zata dingayi, harta gama bata ganin ko da giccin shine, shi din da tun ranar da idanuwan shi suka shiga cikin nata suka samu waje suka manne mata.

Shi din da haka kawai yanzun ya zama farkon abinda yake fado mata data bude idanuwanta da safe, kuma yake zama karshen abinda take tunanin lokacin da zata rufe idanuwanta da daddare, kusan da nashi idanuwan take rufe nata. Shi din da yanzun yawan ‘yan uwanshi da ta gani yasa kamannin shi sun fara bace mata, saboda sai harhadasu takeyi dashi tana rasa abinda ya bambanta su, sai ta fara tunanin ko bata ganshi da kyau ba. Duk wadanda ta gani, maza da mata, akwai farare, akwai bakake, akwai kuma wasu a tsakiya, wanda ake kira wankan tarwada. Amman shi din kamar duka kalar uku aka dibi kowanne a ciki aka samar da tashi kalar, ta kuma rasa wadda zatace tafi rinjaye, ko duhun yammaci ne da kuma na motar da yake ciki suka sa ta kasa tantance ainahin tashi kalar.

Ta ma rasa dalilin da yasa takejin tambayoyi masu tarin yawa a zuciyarta game dashi, take son samun amsar tambayoyin kuma, ta sha gwada bude bakinta da nufin tambayar Hibba, sai taji harshenta ya nade, da gaske tana da tambayoyi da yawa a zuciyarta, amman ko ita kadai idan ta gwada furtasu sai ta kasa, kamar hade mata sukeyi suna saka kwakwalwarta cikin rudani. Batare da ta dorar da wani abu ba kwanaki talatin suka zo suka wuce kamar basu faru ba, dan saida aka danqa mata kudin aikinta a hannu mamakin saurin da kwanakin sukayi ya dirar mata. Sai taji bata dokin kudin sam, haka taje dasu ta mikawa Abida

“Amma ki ware dubu biyar, na Lami din nan ne data samo mun aikin, ki dauka idan zakiyi amfani dasu, sauran saiki ajiye mun”

Albarka Abida ta saka mata, sai dai idan tace ma tana da bukatar da saita taba kudin Sa’adatu zatayi karya. Rayuwar ta fara yi musu sauki, in ba wani buri zasu sakama kansu ba, dai-dai gwargwado suna cikin rufin asiri. Washegari da Sa’adatu ta tashi har Abida saida ta tambayeta ko batajin dadine

“Lafiyata kalau Amma, me kika gani?”

Kallonta Abida tayi sosai

“Naga fuskarki kamar ta kumbura”

Hannu Sa’adatu takai tana taba kumatunta

“Kila baccin dana shane, amman babu komai”

Babu inda yake mata ciwo, banda kanta da ya danyi nauyi, sai kuma yanayin da gabaki daya batajin dadin shi. Sallama tayi da Abida tana ficewa daga gidan, sai dai kafin taje titi yanda zuciyarta ta tsananta bugawa har jikinta na mata bari yasa ta juya ta koma gida, data shiga soron gidan hatta da kafafuwanta sunyi wani irin sanyi, ko sallama ta kasayi haka ta shiga. In da tabar Abida a zaune nan ta sameta, sai dai ta hada kanta da gwiwa, da sauri Sa’adatu ta karasa tana tabata

“Amma lafiya?”

A wahalce Abida ta dago

“Cikina ke ciwo Sa’adatu…”

Sai zufa take hadawa

“Ciwon ciki? Tun yaushe? Ba yanzun na fita lafiyarki kalau ba?”

A kidime Sa’adatu ta kamata suka shiga daki, ta fito tana shiga dakin Fa’iza da take ta fama da zazzabi kwana biyu itama

“Amma ce bata da lafiya”

Ta fadi muryarta na rawa tana taba Fa’iza din da tayi wata irin mikewa tana dirowa daga kan gado. Sanda suka shiga dakin banda juye-juye babu abinda Abida takeyi a cikin dakin. Ba karamin tashi hankulansu yayi ba, musamman Sa’adatu da tunda tayi wayau bata taba ganin Abida a cikin yanayi irin wannan ba

“Ki fita ki samo adaidaita sahu mu tafi asibiti, ki fara mikomun wayata in kira Yaa Abdallah”

Wayar ta fara daukowa Fa’iza tukunna ta fita, taci sa’a wani mai napep ya sauke wata mata, ta taro shi, daga ita har Fa’iza a rude suke, dan mai napep dinne ma ya tuna musu basu rufe gidan ba. Da suka rufe, gudun kar rudu yasa su yadda mukullin yasa Fa’iza tace ta kai gidansu Haulatu a ajiye. Aikuwa Maman Kamal ta tsame hannunta daga wanke-wanken da takeyi tana salatin jin Abida bata da lafiya. Ta leko, tana fadin duk yanda ake ciki Sa’adatu ta kirata ta fada mata

“Akwai kudi a hannunku dai ko?”

Maman Kamal ta tambaya, mukullin Sa’adatu ta karba taje ta bude gidan, ta san inda Abida take ajiyarta, duka kudin data gani ta zuba a jakar da tayi niyyar fita wajen aiki da ita, ta fito ta sake kulle gidan taba Maman Kamal mukullin suka tafi, kai tsaye Aminu Kano suka nufa, mai adaidaitadin nan ganin halin da Abida take ciki da suka tambaya nawa za’a bashi haka yace

“A’a ku barshi, Allah ya bata lafiya”

Yaja adaidaita sahun shi yayi gaba yana barinsu da kara tabbatar musu da mutane nagari basa taba karewa, sai dai kawai idan bakayi dacen haduwa dasu ba. Wajen tambayar inda zata siyi kati wata Nurse ta gani data dago tana mata wani kallon raini, kuma da alama bahaushiya ce, amman sai tayiwa Sa’adatun turanci, mamaki karara kuma ya bayyana a fuskarta lokacin da Sa’adatu ta mayar mata cikin turancinta da lokaci da kuma naci yasa ta koya, tunanin shiga yan gayu yasa bata gajiya da kokarin ganin ta dai-daita harshenta wajen bawa kowanne harafi hakkin shi

“Ina son yanda kike turancinki Sa’adatu, akwai yanayin yanda kike furta wasu kalmomin da ace bansan kiba zan iya rantsewa kinyi rayuwa da wasu turawa ko da na kankanin lokaci ne”

Tahir ya taba fada mata, yana kuma kara mata kwarin gwiwa wajen sauraren labarai a gidan Radio tana baza kunnuwa wajen jin yanda suke turancin su, tana gwada maimaitawa ita kadai a daki. Ko yau din badan halin kidimar da take ciki ba, tabbas sai tayi alfahari da kanta, dan bata tsaya kan tambayar wajen siyen kati ba kawai, ta hadane da yi mata bayanin marar lafiya suka kawo da kuma yanayin da take ciki. Sai ga Nurse din ta zagayo tana raka Sa’adatu, da alama ta burgeta ne, ita kuma ta taimaka musu har inda zasu ga likita, tana ta faman zubawa Abida sannu, akwai layi ba laifi, amman ganin ko zaman ma Abida ta kasa yasa mutane da yawa akan layin sukayi musu alfarmar su fara shiga. Ko bata lokaci ba’ayi ba yace kwantar da ita zasuyi.

Kafin mintina talatin har ruwa an saka mata an kuma yi mata allurar bacci dan ta samu saukin ciwon. Sai lokacin kuma Fa’iza ta kira Abdallah ta fada masa, dan kafin su fito din ta kasa samun shi. A rude kuwa ya karaso asibitin yana tsare su da tambayoyin da basu da amsarsu. Ya fita wajen likitan dan ya kara samun cikakken bayani kan gwaje-gwajen da aka rubuta. Kafin yamma har su Nabila duk sunzo, sun kawo abincin da babu wanda ya iyaci saboda yanda Abida ta farka kamar an kara mata ciwon akan wanda suka kawota cikin shi. Amira da aka kirata aka fada mata kuka ta dingayi, dakyar Abdallah ya lallabata ta hakura karta biyo hanya a ranar tunda yamma tayi, tabari sai washegari tukunna. Yaita ma su Sa’adatu fadan sun kira sun daga mata hankali.

Zuwa washegari da Magriba kuwa dukansu sun hadu sun tare a asibitin kamar zasu iya bata lafiya. Maryam har kusan marin wata Nurse tayi, akan tayi musu ihu

“Ai da kin banni na koya mata hankali Nabila, yara marassa kunya, da sun saka farin kayan nan sai su dinga jin kamar sunfi kowa, aini basa burgeni har sai sun hana nasu iyayen da iyalin kwanciya ciwo tukunna”

Abdallah ne ya tattarasu ya saka a napep daya, yace babu wanda zai kwana sai Sa’adatu, duka su koma gida tunda Abidar ma bacci takeyi. Da Hibba bata kira Sa’adatu ba sam ta manta da wani aiki da takeyi saboda tashin hankalin da suke ciki. Ta fada mata dalilin da yasa batazo ba, fatan samun sauki tayiwa Abida sannan sukayi sallama. Cikin dare Abida ta tasheta, tasa ta kira mata Nurse ta cire mata karin ruwan

“Amma bafa kida karfi a jikinki…”

Sa’adatu tace tana taimaka mata taje bayi

“Barni dai in rama salolin da suke kaina tunda naji dama-dama…”

A zaune tayi salolin duka, Sa’adatu ta hada mata ruwan shayin da take ta kurba a hankali kamar tana shan magani

“Babu lemon zaki?”

Kai Sa’adatu ta girgiza mata, Nabila ta kawo, amman kwanan shi biyu babu wanda ya sha, dazun Amira ta kwashe su da kuma biredin har biyu da babu wanda yako taba su

“Lemon kike son shane Amma? Gobe idan Allah ya kaimu sai a siyo miki”

Murmushi ta danyi, fuskar nan tayi fayau da ita

“Kin tuna Abbanku idan wani bashi da lafiya”

Yar dariya Sa’adatu tayi

“Tashi ga lemon zaki, kina sha zakiji kin fara samun sauki”

Abida ce tayi dariya wannan karin

“Shifa Abba koma meya faru to idan kansha lemon zaki zakaji dama-dama, kuma kinsan Yaa Nabila ita da yake ta yarda, tana shan lemon zakin zakiga ta fara yin kwari”

Hira suka dingayi kamar ba dare ba, dan har itama Sa’adatun sai da ta hada shayin ta sha, duk wani gwaji da akayi ma Abidar lafiya kalau, babu wani abu da yake da matsala a cikinta, likitan dai yaita tambayoyin shi, me taci na karshe, to abinda dai taci shi sukaci suma kuma gasu nan garau, kawai dai Allah idan ya dorowa bawa ciwo sai kuma fatan samun sauki. Ita cuta bako yaushe take da dalili ba. Har akayi asuba idanuwan su biyu, sai da sukayi sallah, aka sake mayarwa Abida da karin ruwanta, itama Sa’adatu ta kwanta akan tabarma bayan da suka gaisa da matar da take can gadon jikin bango. Tunda dakin gado takwas ne a ciki, kuma sanda aka kawo Abida akwai mutum hudu, an sallami ukune ni washegari, a jiyan ma an kawo wasu biyu da safe, sai dai duka wajen Magriba aka sallame su, basu kwana ba, su biyune kadai a dakin. Matar kuma matashiyar budurwa ce take jinya, taji ana cewa sikila gareta.

Wanda duk yazo dubata a ranar zaka ga walwala a fuskar shi na ganin saukin data samu, zuwa la’asar jikin ya sake rikicewa, tanata suma. Cikinsu kuwa babu wani mai karfin halin hana dan uwanshi kuka, Abdallah da yake namiji, kuma ake tsammanin zai lallashe su, shi yafi kowa kuka. Kasa tafiya yayi, a masallacin asibitin ya kwana. Washegari kuwa tun kafin bakwai duk sunzo asibitin, suna nan likita ya shiga round din farko, Sa’adatu ta fito, tunda asuba da aka sake yi mata allurar bacci, bata ko motsa ba. Dan Sa’adatu na kallon fuskarta da kuma fitar numfashinta, tana jin wani tashin hankali yana kawo mata mamaya. Ko yanzun ma da ta fito haka take ji, yanayin harya fi na dazun, tsugunnawa tayi nufin yi sai Abdallah ya rigata yana hade hannayen shi ya dafe goshin shi dasu

“Ko ruwa ka sha Abdallah, kaima sai wani ciwon ya shigeka”

Amira ta fadi cikin sigar lallashi

“Yaa Amira zuciya rawa takeyi, gabana na faduwa”

Hannu takai da nufin kamo nashi, in tayi magana kuka zatayi, lokacin ne kuma likitan ya fito, hakan yasa Sa’adatu shiga dakin, ta karasa wajen Abida taja kujera ta zauna, ta kamo hannunta da yake dauke da karin ruwa, sai taga ruwan na fitowa ta gefen dan bandejin da aka saka, ga hannun ya kumbura kamar ruwan baya shiga jikinta, mikewa tayi nufin yi sai taji Abida ta riko hannunta, ta kalleta taga ta bude idanuwa, a tunaninta Sa’adatu take kallo, amman kuma wani waje take kallo daban, kamar idanuwan nata sun juye. Sai Sa’adatu taji wani yanayi da ba zai taba misaltuwa ba ya lullubeta, ta window din ta kira su Nabila

“Ku shigo…yanzun…”

Aikuwa su dukansu suka wuce, suna manta gargadin likita akan a dinga shiga da bibbiyu. Wata Nurse ta taso tana rufo musu baya, sai dai ganin yanda suka zagaye gadon Abida sunata kuka yasa jikinta yin sanyi, musamman da Abdallah ya zagaya ta gefenta yana rike dayan hannunta, muryar shi na rawa ya fara fadin

“Laa Ilaha Illallah…”

Kamar kuwa Abida taji shi saita fara maimaitawa, yanda su duka suka hada baki wajen fadin

“La Ilaha Ilallah Muhammadur Rasulillah…”

Da wani amo mai cike da rauni da kuma mikawa Allah lamurransu sai da tsikar jikin Nurse din nan ya tashi, gashi ta kasa juyawa. Kallonsu takeyi, duk yawansu, duk kukansu, duk kuma tsananin bukatar kasancewa da mahaifiyarsu da yake shimfide a fuskokinsu bai hana Allah yin Ikon Shi akanta ba, kaunar da suke mata bata hana mutuwa daukarta suna kallo ba. Ita kanta ta tsorata, ba karamin tsoro ba, shikenan fa, rayuwar da duniyar gabaki daya. Yanzun zuwa zasuyi ana gaggawa ayi mata wanka ayi janaza, duk wata kewarta da zasuyi daga baya ne, ita dai a zaman duniyar iya abinda ta dibo kenan. Sai dai sune abin tausayi tunda ita da kalimati shahada a bakinta ta cika. Tasan tunda ta zabi wannan aikin na ma’aikaciyar asibiti zata dinga cin karo da mutuwa, ko da ba kullum ba kuwa. Sai dai tana da yakinin wannan na daya daga cikin mutuwar da ba zata taba mantawa da ita ba

“Me zamu cike mu tafi gida? Ta rasu”

Abdallah da bata ga tasowar shi ba sai zuwan shi yace mata, yana kuma kai hannuwan shi a lokaci daya ya share kwallar data zubo masa, tabi hannuwan nashi dake rawa da kallo zuciyarta na kara karyewa fiye da waje daya. Haka tayi masa jagora, ta kuma yi tsaye tana nemo daya daga cikin direbobinsu, ita tace ya kaisu gida ya dawo zata sallame shi. Gidan suka nufa kuwa, wata tafiya da ba zasu manta da ita ba, wata tafiya da tsayinta ba zai misaltuwa a wajensu ba. Fadin kaduwa da kuma tashin hankalin da duk wani makusanci Abida ya shiga da rasuwarta ma bata lokaci ne. A wajen yaranta kuwa babu wanda zai fahimta sai wanda ya taba rasa mahaifiya, koya za’a fada, in dai baka dandani abinda sukeji ba, hasashenka ba zai taba kamanta maka kwatankwacin abinda suke jiba.

Sai dai hakurin da suke hangowa da nisane suka matso dashi kusa saboda Abdallah da ranar sadakar bakwai ya mike da nufin tafiya masallaci sallar la’asar ya yanke jiki ya fadi. Likita kuma ya hausu da fadan ya akayi aka bari jininshi ya hau har haka? Yana dorawa da fada musu yanda Allah ya tsare shi da ya samu babbar matsala. Kuka suka fita wajen dakin da aka kwantar dashi sukayi suka wanke fuskokinsu sannan suka koma, da yake wani asibitin kudine suka kaishi da yake nan kusa dasu, sai ba’a hanasu shiga su duka ba, an daice kar suyi hayaniya saboda yana bukatar hutu. Ko daya farka Nabila ce ta dinga masa nasiha, bai koyi kokarin goge hawayen da suke zubo mishi ba

“Maraici akwai ciwo Nabila, inajin wani irin kadaici yana mamaye ni…”

Itama kwallar ta share

“To ya zamuyi da Ikon Allah? Ya kamata mu gode masa, ko baka ga jama’ar da tayi bane ba? Baka ga tarin mutanen da suke ta zuwa tayamu jimami ba har yau? Ko ka manta da Kalimati Shahada a bakinta ta cika? Kewarta bai kamata ta hana mu tayata murna ba, kuma itama zata so mu cire wannan damuwar…musamman kai”

Cije lebenshi na kasa yayi yana kauda kai, hawaye na sake zubo masa. Dukansu ba zasu taba gane irin abinda yakeji ba, Asabe haihuwar shi kawai tayi, shisa ko da ta rasu ya rasa mahaifiyane kawai, amman yana da Uwa, yanzun ne yakejin maraici ta kowacce fuska. Kwanan shi biyu, ciwon shi da son ganin ya kwantar da hankalin shi yasa kowa ya aro hakuri ya sakama ranshi, ko da aka sallame shima kowa saiya cigaba da kokarin komawa dai-dai. Matan duk suka koma gidajen auren su. Shima ya tattara hankalin shi ya mayar kan karatun da saura kadan ya kammala, cike da burin ba zai tsaya iya NCE ba, duk wahalar da zai sha sai yaga yayi karatun nan ya cikama Abida burin ganin ya samu ilimi. Sa’adatu ma da Hibba ta sake kira dan tayi mata gaisuwa sai tunanin ta koma aiki ko zai rage mata damuwa ya fado mata.

Dan tayi mamaki sosai da taga Hajiya Hasina da Hibba sunzo mata gaisuwa, harda buhun shinkafa suka kawo da kuma dubu biyar ta bata. Da tayiwa Abdallah magana tana son komawa shima baiyi mata musu ba. Fa’iza ce dai bata iya ce mata komai ba, duk ta karayin sanyi, ga laulayi daya sakata a gaba, ga kuma rasuwar Abidar da itama ba karamin dukanta tayi ba. Haka tayi shirinta tsaf ta tafi

“Sa’adatu sannu kinji, ai da kin zauna kin kara hutawa”

Hajiya Hasina tace mata, tayi murmushin karfin hali batare data furta komai ba. Tana kula har sauran masu aikin ma tayata sukayi bayan sun kara mata gaisuwa cike da tausayawa. Sosai aikin ya rage mata damuwa, duk da akan mutuwar Abida take karyata cewar lokaci zai iya tafiyar mata da ciwon rashin da tayi. Sai dai ta saba a hankali, amman wannan filin ai bata da abinda zata cike shi dashi. Ranar wata alhamis ta fito daga kitchen kanta a kasa tayi karo da shi, ta dago a razane da kalmar hakurin data makale mata, sai dai baiko kalleta ba ya raba ta gefenta ya shige kitchen din, ya fito da robar ruwa a hannun shi yana wuce ta inda ya barta a tsaye duk wani tunani nashi daya bace mata na dawowa sabo fil.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 16Tsakaninmu 18 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×