Kamata yayi ace ranar Asabar wanke-wanken gidan yafi yawa, saboda ranace ta hutu, kuma yawancin wanda suke makaranta sunzo ko aiki duk suna gida. Sai dai Sa'adatu ta kula ko abinci ba'a cikayi da yawa ba a ranakun karshen mako, kusan duka gidan wannan ne lokacin da suke fita, baka rasa su da wani biki, suna, ko dai wata fitar da ta kula masu kudi ba sai suna da dalili ba.
"Zan dan fita in sha iska."
Duk iskar da take ciki da wajen gidan
"Zamu ci abinci a waje."
Sai ta dinga mamaki, ita tana samun. . .