Skip to content
Part 18 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Kamata yayi ace ranar Asabar wanke-wanken gidan yafi yawa, saboda ranace ta hutu, kuma yawancin wanda suke makaranta sunzo ko aiki duk suna gida. Sai dai Sa’adatu ta kula ko abinci ba’a cikayi da yawa ba a ranakun karshen mako, kusan duka gidan wannan ne lokacin da suke fita, baka rasa su da wani biki, suna, ko dai wata fitar da ta kula masu kudi ba sai suna da dalili ba.

“Zan dan fita in sha iska.”

Duk iskar da take ciki da wajen gidan

“Zamu ci abinci a waje.”

Sai ta dinga mamaki, ita tana samun irin wannan shagalin a gida, me zai kaita cin abincin waje? Abubuwa da yawa idan ta ga sunyi sai ta dinga mamaki, sai kuma taji da gaske akwai wata tazara mai nisa a tsakanin rayuwar talaka da maikudi, ita dai duk wani jin dadi da take hange baya wuce nama, kaya masu tsada, waya yar yayi, motar hawa, gida me kyau. To su duka suna da wannan abubuwan, shisa take ganin me kuma zasu nema? Me yasa take ganin kamar suna neman wani abu a duk rana, kamar kudin da suke dashi bai isa cikon farin ciki a wajensu ba, kamar kuma akwai wani abu tare da rayuwa daya wuce burikanta. Yau ma kwanonin da ta gama wankewa take gogewa tana jera komai a mazaunin shi. Lokaci zuwa lokaci tana sauke ajiyar zuciyar da bata san takaimaiman dalili ba

“Sa’adatu…”

Taji muryar Nenne, wata matashiyar budurwa da take da tabbacin zata bata kusan shekaru hudu, kuma taji ‘yar uwar suce, kamar abokiyar wasa take a wajen su Hibba, sai dai Sa’adatu na zaton a gidan take zaune, dan zatayi mamaki idan akace mata ba’a gidan take da zama ba, tunda har daki tana dashi da komai. Tana cikin mutanen da suna zuwa waje zaka san sune, mutanen nan da kullum suke cikin nishadi, wani irin nishadi da ko ya kake jin ranarka bata tafiya dai-dai idan kagansu sai kaji murmushi ya kwace maka. Kuma ko da sanyin safiya Sa’adatu batajin ta tana ganin Nenne babu wannan jan janbakin a labbanta, kamar da kwalliya take bacci, ko kuma bayan sallar asuba kwalliyar ce abu na farko da take fara yi.

“Kin iya awara?”

Kai ta jinjinawa Nenne, tana kallon dankunnen da yake kunnuwanta, tana auna nauyin da zaiyi, da yanda Nenne ke yawo da kanta kamar batajin wannan nauyin.

“Ohhh…na taba fada miki ina sonki?”

Ta fadi tana juya idanuwanta da suma suke dauke da kwalliya, wata kwalliya da Sa’adatu ba zatace ga farkonta balle karshenta ba, hakama kalar, kawai dai tasan akwaita tunda gata nan tana gani, batun ko ta taba fada mata tana sonta kuwa ya fara zame mata jiki, ta kula a cikin gidan wannan furucin bakomai bane ba, a wajen duka yan gidan kuwa, musamman a tsakaninsu.

“Dan Allah ki karasa kizo muje gidan Hamma JB tare, Aliya tace zata sameni acan, motarta ta samu matsala ko menene, ko kinyi dare zamu kaiki har kofar gida, I promise.”

Murmushi Sa’adatu ta iya yi tana sake jinjina mata kai cikin amincewa, saida ta sake juya idanuwanta tukunna ta juya ta tafi. Sa’adatu kuwa ta kasa magana ne saboda makoshinta da taji ya bushe, ga hannuwanta da tasan ba lemar ruwan wanke-wanke bane kadai takeji harda zufa, tunda Nenne ta fadi JB. Ga bugun zuciyarta daya karu, a kwanakin nan har haushin kanta takeji, musamman da tayi neman duniya tana rasa dalilin da zaisa ya manne mata haka kawai, sai kace bata da abubuwa da yawa da zatayi tunani akai, sai shi. Tafi tsanar yanda in dai zataji falon gidan a cike saita nemi dalilin fitowa ko zata ganshi zaune a cikinsu, amman sai taga banda shi. Yana da gidanshi ashe, yana da mata, kamar ta mari kanta takeji, ya ma za’ayi ace kamar shi bashi da iyali, ai ko a idanuwanta yayi shekarun da ya kamata ace yana da iyali musamman ma da yake da halin ajiye mata hudu idan yaso.

Ta girgiza kanta har sai da ta fara ganin jiri, saboda tana son tunanin shi ya fado daga cikin kanta, yabi iska, koya tsaya kan tayal din kitchen din abi takanshi a wuce, duk bai dameta ba in dai zai bar kanta. Ko da ta fita daga kitchen din ta samu Nenne a falo

“Kingama? Muje?”

Da kai ta sake amsata, tana wucewa ta dauko hijabi da kuma wayarta. Taji dadi da Nenne bata sake yi mata wata magana ba, ko da suke shiga mota ma, wata waka da alamu suka nuna tanajin dadinta ta kunna, tana bi tana tuki har suka karasa unguwar da Sa’adatu bata san ina bace ba, sun dai tsaya bakin wani bakin gate aka bude musu, Nenne ta shiga da motarta. Bata san ya ta tsammaci ganin gidan ba, a tsare, da shuke-shuke kamar gidan da suka baro, sai dai babu alamar bishiya ko daya, sai interlock malale ko ina na harabar gidan, rufin gidan bakine, shikuma gidan kalar ruwan toka mai dan duhu, tunda take bata taba ganin interlock da yake qal-qal irin na gidan ba

“Sa’adatu kinsan menene OCD?”

Kai ta girgizawa Nenne

“Bansan ya zanyi miki bayani ba, cutar kwakwalwa ce dai, to bamu tabbatar ba, amman muna kyautata zaton matar gidan tana fama da cutar.”

Zuciyar Sa’adatu ta doka, abubuwan da suke tsoratata basu da yawa, mahaukata na daya daga cikin abubuwan nan.

“Ki kula, bata so a taba mata komai da batace a taba ba.”

Ita dai da zata iya data juya, amman Nenne na mata maganar suna nufar kofar da zata sadasu da cikin gidan ne, ita kuma tana biye da ita, harta kwankwasa, sanda aka bude kofar sai bugun zuciyar Sa’adatu ya karu, fentin dai ruwan tokane kamar na waje, bambancin wannan mai haske ne, kujeru da duk wani abu da yake dakin ne ruwan toka mai duhu, banda katon agogo kuma babu komai a bangon dakin. A hankali take kalle-kalle kafin ta sauke idanuwanta kan wata siririyar mace da waya makale a kunnenta da alamar tana sauraren abinda ake fada daga dayan bangaren, wandone da ake kira Palazzo a jikinta da wata farar riga, haka hular kanta fara ce, ta dan turata baya har gashinta ya fito, sai gilashi matsakaici da yake manne a fuskarta, sai Sa’adatu taga ya kara mata wani kwantaccen kyau, sai kamshin yan gayu gidan yakeyi tun shigarsu ta shake shi, da matar ta bude musu gida kuma sai taji nata kamshin ya fita daban.

Inda taga Nenne ta cire takalminta nan ta cire itama, sai dai matar tayi murmushi tana nunawa Nenne hanya da hannunta, inda duk ta saka kafa nan Sa’adatu ta mayar da tata, har suka shiga wani daki mai dauke da gado da taburin karatu sai kujera a jikin teburin, nan taga Nenne ta ajiye jakarta da dan mayafin data ratayo, sai itama ta cire hijabinta, suna nan zaune matar ta turo kofar a hankali

“Anty Aisha”

Nenne ta fada, amman yanda ta furta Aisha din saiya fita da wani salo da yan gayu ke amfani dashi wajen kara bambanta kansu da talakawa

“Nenne sannunku…”

Murya can kasa Sa’adatu ta gaisheta, ta amsa a takaice batare data ko kalleta ba, tana cigaba da tambayar Nenne ‘yan gidan, kafin su dora da yawon dasu Nenne din sukaje kasar Turkiyya da kuma kasashen da suka biya, Nenne na dorawa da

“Kun fasa tafiyar ne ku?”

Kafada Aisha ta dan daga

“Kinsan aikina, kuma Jay ma baya karfafa mun gwiwa kan tafiyar shisa abin duk ya fita daga kaina.”

Hira suka dan karayi, Sa’adatu na jinta a takure, gashi haka kawai ta kasa ko danna wayarta.

“Ga Sa’adatu ita zatayi miki awarar.”

Duk da taji idanuwan Aisha akanta, bata ko motsa ba.

“Na fito da komai a kitchen ai, kuma ta iya?”

Aisha ta karashe tambayar tana kallon Sa’adatu sosai, batayi mata kama da wadda zata iya yin awara ba, tana son abin sosai, sai dai ta gwada tana rasa abinda takeyi ba dai-dai ba take mata gardama, ita kuma tana da tsantsanin da baya barinta cin abinda bata yarda da ingancin shi ba. Shisa take sa su Nenne suna dauko mata hayar mutane azo ayi mata a gida saita saka a fridge, data tashi zata dauko abinta ta soya. Daga dakin kitchen suka nufa su duka, kicin din da komai yake a tsare da kuma wajen zaman shi, dan taga da Nenne ta sha ruwa ta ajiye robar, sai da Aisha ta dauke tana bude wani abu da Sa’adatu take zaton wajen zuba shara ne ta jefa robar duk da akwai ruwan kusan rabi a ciki, taji dadi da Nenne ta mika mata robar ruwan itama, dan makoshinta ya bude, sosai tasha, sai ta ajiye sauran a kusa da ita, duk abinda takeyi kuwa idanuwan Aisha na kan robar nan har saida ta dauketa tukunna ta samu natsuwa.

A darare takeyin aikin, har wani numfashi ta sauke lokacin da Aisha ta fita daga kicin din, sai taji ta samu natsuwa kuma tafi sakewa. Da Nenne ma ta fita saboda taji zuwan Aliya. Sai taga aikin yafi mata sauri, tunaninta ne dai ba zatace ga inda yake ba a lokacin. Taji dadin dauko wayarta da tayi, kawai earpiece ne da yake cikin jaka, da ko waka ta saka. Tunawa tana da wani littafi na saurare da Fa’iza ta tura mata sai ta rage sautin dai-dai kunnenta tana fara saurare, shiya debe mata kewa harta kammala, aikin awara ba abu bane mai sauki, kwanonin duk data bata ta wanke, ta gyara ko ina tukunna ta dauki wayarta tana tsayar da littafin da take saurare sannan ta fito, muryarta dauke da wani sanyi da bata san tana dashi ba tace

“Nagama…”

Yanayin fuskokinsu ya nunawa Sa’adatu sunyi mamaki, gabaki dayansu suka tashi suna shiga kitchen din dan su tabbatar, saita tsinci kanta da bin bayansu itama, sai lokacin kuma taga Aisha ta kalleta, sosai, kallo na mamaki da alamar ta burgeta

“Nagode…”

Ta fadi da dan guntun murmushi, itama Sa’adatu saita mayar mata da murmushin

“Ai da an soya mana munci munji…”

Cewar Aliya, dan yanda Sa’adatu ta yanka awarar yayi mata kyau sosai. Hakan kuwa akayi, tun kwashin farko duka suka zagaye filet din suna dauka, yanda tayi kyau, ga laushi duk sai suka kasa jira, ana soyawa suna dauka suna ci

“Ke ba zaki ci ba?”

Nenne ta cewa Sa’adatu da tayi dariya tana girgiza mata kai, duk kwadayinta bai kai wajen awara ba, dan ko siyowa akayi ko a gida sukayi zai wahala ta iya cin guda biyar. Dauka sukayi kunyace ta hanata ci, shisa da ta gama soyawa, Aisha da kanta ta samu wata roba ta zuba mata, bataki karba ba, Fa’iza zataci ta sani, su kadaine a gidan yanzun, Nabila na laulayin cikin da yake bata wahala, tazo ta dauki Jidda, daga kwana biyu gashi nan sun fara bace lissafi, kuma da yake kowa saukin radadin mutuwar Abida yake nema, sai babu wanda ya daga mata maganar. Kamar yanda Nenne tayi mata alkawari, sunayin sallar Magriba suka fito, har kwanar gida suka sauketa bayan Aisha ta bata dubu biyar din da taketa shafa jakarta tana mamaki. Suka juya, ita kuma tayi kwanar da zata kaita gida.

Aisha kuwa sake gyara kitchen din tayi tana maida komai muhallin shi, sauran awarar ta saka a fridge, wadda aka soya da basu cinye ba ta samu roba ta juye da nufin ta saka a fridge itama, taji shigowar Jabir

“Meke kamshi haka?”

Ya tambaya yana takawa cikin kitchen din zuwa inda take

“Awara ce fa akayi mun, zakaci?”

Kai ya girgiza mata

“Indomie nake so, da shrimp”

Dariya tayi

“Angama…jeka zan kawo maka idan nagama”

Ta karasa maganar da murmushi ganin gardamar dake cikin idanuwan shi

“Dan Allah…yanzun zan gama, ba dadewa zanyi ba, kayi kallo ko wani abin”

Kallonta yakeyi har lokacin, kuma gardamar yakw son yayi. Ta san burin mata da yawa kenan, ace suna aiki a kitchen miji yazo ya tayasu hira ko da bai taimaka da komai ba, balle kuma Jabir da zaita damunta da me zaiyi, sai dai ita bata cikin jerin matan nan, ko ba aiki takeyi ba tafi son komai a kammale, cikin ka’ida, balle kuma idan tana aiki, har cikin kwakwalwarta take ji ka taba mata wani abin ka kauda mata shi daga inda take son ganin shi, ka’ida da Jabir kuma basa zama a layi daya sam. Ya bude bakin shi da nufin magana ta karasa tana sumbatar shi a kunci

“Ina sonka nima”

Dariya yayi, har kumatun shi na gefen dama ya lotsa sosai yana bayyana dimple din da bata gajiya da tsokanar shi akai, saboda bangare dayane yake dashi, hakan yasa shi fasa magana ya juya ya fice daga kitchen din zuwa falo, ya karasa kan doguwar kujera yana kwantawa hadi da sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Ba zama shi kadai bane matsalar shi, a kwanakin nan ne bayason kadaicewa haka, in zai zauna shi kadai, to tabbas tunanin da bayaso ne zai kawo masa ziyara kamar yana son debe mishi kewa. Lumshe idanuwan shi yayi, da a fim ne ko littafi da yanzun matsalarsu ta kare, da yanzun mafitar da suke nema sun sameta cikin sauki, ko fim din da Aisha ta kalla satin daya wuce cikin sauki kadddara ta mikowa jaruman maganin matsalarsu

“A haka kamar abu mai sauki ko?”

Ita da kanta tace masa tana gyara kwanciyarta a jikin shi, numfashi kawai ya iya saukewa yana sake riketa, saboda baisan me zaice mata ba, itama da alama batayi maganar dan ya amsa ba tunda bata sake cewa komai ba har suka kwanta. Shekara daya suna abu daya, shekara daya suna bulayin amman sun rasa ta inda zasu fara, anya zasu iya kuwa? Duk wata alama ta gama nuna musu ba zasu iya su kadai ba, shekara daya ba kwana daya bane ba

“Da kikayi tunanin nan, saina dauka karshen matsalar mu yazo, ranar na kwanta ne zuciyata kamar an sauke mun dutsen da ya danneta, amman yanzun nauyin ya dawo, tare da wani na daban…”

Yanda ta kalle shi a lokacin sai da zuciyar shi ta kara yi masa nauyi

“Ni kaina sai yanzun nake ganin a fim ne abin yake da sauki, ko a kasashen ketare, amman anan, Jay wa zaka tara kace ya ara maka mahaifa zaka ajiye kwai? Ina zamu samu wadda zata yarda da yarjejeniyar mu?”

Babu kuma abinda yake kara masa damuwa sai kasancewar wannan abu na farko da ya nema yake shirin kin samu

“Earth to Jay…”

Aisha ta fadi tana yawo da hannunta kan fuskar shi, kallonta yayi yana sauke numfashi hadi da tashi zaune

“Tunani ko?”

Ta fadi cike da tuhuma, kafadu kawai ya daga mata, ba zai mata karya ba yace ba tunani yakeyi ba, itama inta zauna ita kadai ya tabbata abinda takeyi kenan

“Naga kin saka cokali daya, ke ba zakici ba?”

Kai ta girgiza masa tana zagayawa ta zauna a gefen shi kan kujerar, da kanshi ya mike ya dora filet din kan teburi yana janyo teburin wajen kujerar ya zauna

“Ruwa ko coke?”

Kallon kema kinsan me zanfi so yayi mata batare da yace komai ba, mikewa ta sakeyi tana dawowa da robar coke da kuma kofi ta bude ta zuba masa. Suna dan hira yana cin abincin, sanda ya kammala ana kiran isha’i dan haka ya fita zuwa masallaci, itama ta kauda komai ta nufi daki dan yin alwala ta kuma gabatar da isha’in itama. Harta idar ta watsa ruwa bataji shigowar Jabir ba, da ta saka kayan bacci sai ta bishi dakin shi, ya dawo, daga shi sai gajeran wando, gashin shi a jike yake da alama shima ruwan ya watsa bai kuma damu daya goge gashin ba, aiki ya kamata tayi amman bata cikin yanayin da zata iya komai, shisa ta wuce gado ta kwanta, ga mamakinta shima gadon ya nufa yana kwanciya a gefenta

“Banajin dadin komai Tasha”

Ya karasa maganar yana jan sunan da yake kiranta dashi

“Nasani”

Ta furta a hankali tana hade tazarar da take tsakaninsu yanda ta shiga cikin jikinshi sosai, akan maganar dai, kalamai sun fara karewa a tsakaninsu, sun fara gajiya da karfafar juna na cewar zasu samu mafita. Ta rigashi yin bacci, ko addu’a batayi ba, watakila shisa yau ta tsinci kanta a tsakiyar duniyar mafarki, wani abu da take daukar lokaci bai faru da ita ba, duk wasu mafarkai nata ido biyu tafi yinsu, shisa duk da baccin da takeyi bai hanata mamakin abinda takeyi tsaye a filin da babu komai sai kasa ba, da ta juya sai taga wata budurwa da ba zatace ga ta inda ta bullo ba, ta nade kanta da fuskarta da farin mayafi, shisa duk hasken wajen Aisha ta kasa ganeta, abinda take miko mata tabi da kallo, jaririne ko jaririya ba zata iya tantancewa ba, nade cikin farin mayafi.

Ko dogon tunani bata tsaya ba ta mika hannu da nufin karba, sai dai wata irin iska data taso ta hana mata yin hakan, iskar kuma ita ta yaye lullubin fuskar budurwar harta gani, sabon mamaki ya lullubeta tana tunanin inda ta san fuskar, hannunta taji an rike, data juya sai taga Jabir tsaye yana kokarin janyeta, ita kuma ta bude baki tana son ce masa ya tsaya ta karbi yaron, kai yake girgiza mata, bakin shi na motsi amman batajin abinda yake fada mata, sai tabi dayan hannun shi da yake mata nuni da kallo, tana hango wani yaron can nesa dasu a kwance, sai dai gani takeyi yayi musu nisa sosai, ga wannan da yake kusa, gara su karbe shi, idan kuma suka tafi suka kasa cimma wancen fa, shisa take kokarin tirjewa amman Jabir yaki sakinta, data kalli budurwar yanayin da yake cikin idanuwanta ne yasa zuciyarta bugawa ta kara bugawa har saida ta bude idanuwanta cikin duhun dakin, bakinta ya furta

“Sa’adatu…”

Kamar addu’a
Kamar kuma fatan da bata san yanda zata karbe shi ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 17Tsakaninmu 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×